Showing 72001 words to 75000 words out of 86237 words
aminta da bakuwarsu, ya ji ta zama jikinsu, zai iya cewa ya samu kanwa, zai kare mata duka cuta, zai iya yin fito na fito da koma waye kanta! Agaishat Agaishat kanwa ce a ransa wace yaje jinta tamkar
jini daya suka fito,
Ji ya yi zai iya sakewa ya yi hira da ita irin ta dan uwantaka, lokaci daya ta shiga kokonta idan ya aura mata mu.azam ya kyauta mata kuwa? Nan da nan zuciyarsa ta kwabe shi ta hanyar tunasar da shi ai komai na Allah ne , .
A hank
ali ya dan jirga jikinsa bangarenta yana dubanta , ya dan saki fuskarsa ba laifi, dan karamin yatsarsa ya miko mata ya ce" zaki zama kanwata?
Murmushi mai hade da dariya da farin ciki ta dan yi masa ta ki bashi hannun sai alamu da ta nuna zata hade hann
ayen nasu ita da shi ,
Shima murmushi ya sakar mata yana mai nuna alamun dimple dinta har biyu sun shige sosai,
A hankali ta ce" yayana,
Duda suna ne wanda kowa ke fada, karamin suna, sai da ya ji dadin abin, ya amsa mata da ido,
Agaishatt ta
ce" *ina son sa!*....................................
I.m back
😕😕😕
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝
🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4
️
⃣
3
️
⃣
😕😊😊😊😊
😊
😊😊
A hankali murmushin fuskar nasa ya bace, shima ya yi kalar serius ya ce" kina son sa? Zaki aure shi?
Agaishat ta dan kawar da kanta daga dubansa, ta ce" *eh zan aure shi,*
Ajiyar zuciya ya sauke ya wauga bangaren Mu.azam, ya ga yana za
une kasan wata bishiya yana dadana wayar hannunsa, dubansa ya dawo wajen Agaishat, ya dan jima kafin ya ce" *Zan aura maki shi*,
Agaishat bata ji wani yannayi na daban game da abinda wardugu ya fada kan aure da za.a yi mata, duda abu ne da take cike da
murnar itama zata yi, aure da mutun kamar Mu.azam, itama zata yi rayuwar aure, aman zumudin da farin cikin ba wani can can ba , bata san dalili ba ko fargaba ne ya hanata jin madaukakin farin ciki kan lamarin?
Murmushi ta sakar masa ta kai dubanta wajen
Acn motar da ya gama kashe mata gabobin jiki dan mugun sanyin sa,
Wardugu a hankali ya kai hannun sa wajen ky din motar zai kashe sai kuma ya bari, duban Agaishat ya yi ya ce" mu ga kitson yan matan Ayya?
Ai kuwa ya washe baki tana zabga murmushi ci
ke da farin cikin irin yanda ya sauko daga hararanta ya mayar da ita mutun gashi har ya damu da kitsonta take dubansa tana kokarin jan hijabin baya ta bude masa kitson tana fadin" Alhinayett ne tace kar a yi min kananuwa dan kar na wahala sosai, ka san me
, kuncewa yake yi fa, Ayya ne taki yarda na daina kitson nan, kuncewa yake yi shi kadai.....ta karashe tana dan turo bakinta irin na shagwababun yaren nan,
Murmushin da a yau ya kai sau hudu da ya yi du a gabanta ya kuma sakar mata yana duban kitson har
ta rufe , bai san ta ina ba bai san lokacin ba sai ji ya yi ya ce" aa, ki yi ta yin kitson ki, yana yi maki kyau,
Tsai ta yi tana dubansa, a ranta fadi take...da gaske ne ko kuwa? Me ke damunsa yake magangannu irin haka yau ne?
Bata bashi amsa ba sai
lumshe idannuwanta da ta yi ta bude motar tana fadin" Allah ya tsare ka,
Da ido ya bita bayan ta bude motar inda yana kallo Mu.azam ya karaso wajenta da sauri yana alamun tambayoyi inda ya hangi ta sakarwa Mu.azam din murmushi bata ce komai ba, daga na
n ta juya ta tafi cikin saloon din.
Karasowa motar ya yi ya bude gidan gaba ya shiga ya tsare Wardugu da kallo,
Wardugu ya tayar da motar ya juya akalarta zuwa gidan Ayya
Tafiyar kurame ne suka yi har suka karasa gidan Ayya, suna tsayawa Wardugu ya
daga karamar wayarsa ya danna number ya kara a kunne
Ana dauka ya ce" ka cira min tiket biyu zuwa agadez yau.
Yana gama fada ya katse kiran ya fita a motar shima ya bi bayan Mu.azam
Yana shiga dakin Ayya ya zarce direct, yana zuwa ya tarar da ita
tana ninke abin shinfidar da ta cire
Kama mata ya yi suka ninke sannan ya gyara mata wanda ta shinfidar da kyau ya nemi waje ya zauna ya tsura mata ido,
Bakinta ta tabe ta karasa inda yake zaune ta ce" menene?
Murmushi ya yi mata yana dubanta ya ce
" sai da wani abu d'a zai kali mahaifiyarsa kyakyawa Ayya?
Kanta ta girgiza , ta ce" da ace uwar bata san halayen dan nata ba, me ke tafe da kai malan?
Wardugu ya yi murmushi kafin yake yannayin magana mai mahinmanci, ya ce" na tambayeta idan tana so
n sa, amsarta ita ce" *Ina son sa, zan iya zaman aure da shi* , zan je na nema masa aurenta domin shima yana son ta,
A hankali ta zauna tana mai yi masa wani irin duba, ta ce" baku da hankali ne? A me kuka dauki kalmar aure? Sai kace wani abin wasa? To
ko yar zan baku ai sai da alwalin da zan gindayawa dokoki kan yata bale ni bamu wani yi magana da ita ba, aikin banza gagawar me kuke haka ne? To naki din!
Kallonta kawai yake har ta dasa aya tana kawar da kai da yannayin haushi a fuskarta,
Murmushi
ya yi , a hankali ya ce" Ayya, aure ai tayashi ake ko? Sunnar mazon Allahn salalahu alaihi wa salam din kike cewa baki bada ba? Haba Ayyana,
Yatsarta ta nuno masa ta ce" Wardugu ka kiyayeni, ni ban ce ba zan bada kwata kwata ba, aman yannayin yanda kuk
e maganar ne ya fara bani tsoro, meye na gagawa bayan kun san aikin shedan ce? Sannan yarinyar nan dai amana na dauko daga gidansu, idan wani abin ya sameta ba zan yafewa kaina ba!
A hankali ya dawo kusa da Ayya ya zauna, hannunta ya kamo ya rike yana
dubanta ya ce" abinda ke sakawa ana jan aure bincike, da halin rayuwa na yau da kulun, Mu.azam namu ne, mun san waye shi, sannan Allah ya hore mana abinda zamu kawo mu nemi auren ko nawa ne, Ayya, bana son mu zurfafa bincike ne, ina so ki yi min lamuni ki
duba , ba zan saka kaina a maganar idan na san shirme ne, ba zan tarki tarbenta a haka da garage ba idan na san cutarwa ne wa amanarki, ina iya yiwa aminina alwali, kuma tare da shi zamu tafi namiji alwalin kansa ne, ki taya mu raya sunna da yar ki, kina d
a damar bibiyar rayuwarta da shi ...idan an yi maki abinda ba shi ba ki raba
Ayya kam du jikinta ya yi sanyi, tana dunansa gabanta na faduwa tana ayana lale da kwakearan dalilin da ya saka Wardugu shiga wannan maganar auren,
A hankali ta ce" menene? M
e ke faruwa ne?
Wardugu ya kara sada kansa yana jin yanda zuciyarsa ke bugawa ya ce" alkhairi ne, ki taya mu.
Can daman Ayya ba mai musa maganar wardugu bace, hakan ya sa ya yi gagawar shawo kanta kan zasu je garin su Agaishat neman aurenta wa iyayen
ta......,
Bai bar dakin Ayya ba sai da ya tabatar da ya samu kanta ta bada amanarta da dukan yawunta, ta yi fatan alkhairi
Haka ya fito ya tisa keyar Mu.azan dake cike da mamakin lamarin sukaiwa Ayya salama suka nufi aeroport dan tafia garin agadasawa
su nufi timiya gari mai gawo
🙁
........sowi kadan ne.....
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stan
d and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4
️
⃣
4
️
⃣
Basu dauki tsahon lokaci a jirgi ba
Allah ya sauke su lafia,
Direct hotel suka nufa infa Wardugu ya yi kira kan q shirya masa mota da yan tsiraku sojoji zasu je kauyen Timiya,
Sai bayan ya yi wanka ya mike saman bed ya danna wayarsa ya danawa hajia Walyn kira yana mai lumshe ido,
Dag
a bangarenta ta daga tana duban agogon dake dakinta, hakimce take ta hada uban maltina tana son kwankwada tana tsoro, ance mata yana zubar da jaririn ciki wai, dan haka ta gyara zama da niyar sha sai ga kiran Wardugu,
Dagawa ta yi gabanta na faduwa kar
a je ya zo yana nemanta ne,
Walyn........ya fada yana mai jan sunnan,
Idannuwanta ta lumshe ta kwontar da kanta saman hannun kujerar tana sauraron yanda ya wani ja sunnan har tsakiyar kanta,
Bakya neman mijinki wuni guda? Ki ji na ci abinci? Me ke
damuna? Da wa na hadu? Karshema inda nake? Ko kin yarda da kanki har haka ne?
Walyn ta yi murmushi ta ce" na yarda da kaina ne,
Murmushin ya yi shima ya ce" baki da matsala,
Kana ina? Ta jefo tambayar
Wardugu ya daga kai yana karewa dakin kal
lo ya ce" ina hotel , a Garin Agadez.
Me? Hotel? Agadez? Yaushe ka je? Me ka je yi? Kuma a hotel? Kai da wata yar iskar?,
Idannuwanda ya lumshe, a hankali ya dora hannunsa na hagu saman kansa, shafawa yake yana lalabar kansa, shiru ya yi mata wanda h
akan ya saka take ta kiran sunnansa da karfi tana fadin ka fada min da wata tsinaniyar kake hotel? Har ka bar gari da gari ka je garin agadez? Me ka je nema? Farin, kyan, ko gashin? Wanene bani da? Ka ban amsa Wardugu,
A hankali ya katse kiran da wayar
baki daya ya furzar da wata zazafar iska ta kai dubansa wajen Mu.azam da ya yi tsai cike da takaicin matar abokin nasa yana dubansa, mamakin irin rashin hankalin Walyn yake, du yanda wardugu ya kai ga zafin rai yana raga mata, yana matukar kawar da kai a s
hirmenta, tunda ya zo niger bai ga inda Walyn ta taka kafarta gidan mahaifiyar mijinta dan ta gaisheta, bayan kulun sai ta fice yawo kwararo kwararo,, ga abubuwa na rashin da.a da take shukawa suna zuwa kunnuwansa , sai ta tafkawa talaka rashin mutunci ta
yi ikirarin me ka isa ka yi bayan ikon a hanuna yake a matsayina na matar General Wardugu,
Karfi da yaji ta saka wasu talakawan na shayin tunkarar iko koda da gaskiyarsu , suna tsoron gawo ya juye da mujiya! Sam halayar Walyn suna bukatar gyara,
Bai
iya cewa Wardugu komai ba, domin du tsakaninsu basa irin maganar nan, sam Wardugu baya bada fuskar a yi maganar iyalinsa da kowa, idan abu ya ishe shi yakan ja dogon numfashi ya ce" Mata kennan, kwakwaluwarsu irin ta yara ce,
Wardugun ma dubansa yake
har ya karasa wajen bed yana dana waya ya ce" Wardugu, yanzu kayan buzaye ne zamu nada , kawai kai tamkar diarhee kake idan ka tashi abu yi kake? Bamu wani shirya ba, bamu zo da datijo ba zamu je a bamu aure? Ni dai kar ka ja iyayen yarinyar su hana min A
gaishat ba zan jure hakan ba , zan haukace maka ne!
Tsuru ya yi masa daga kwoncen yana jin wani iri da maganarsa, wani irin tashi ya yi zaune yana dubansa ya ce" kai zo zauna mu yi magana!
Mu.azam na dubansa ya karaso ya zauna yana kara kare masa k
allo,
Wardugu ya ce" dan tausayi zaka aureta ko dan so domin Allah?
Mu.azam ya yatsina fuska ya ce" ina sonta mana, meye a tare da ita na tausayi? Nine ma ai abin a tausayawa,
Wardugu ya ce" kana ji, bana son ka yi auren nan da wata manufa, Mu.az
am, ba zan jure gannin hawayenta ba koda kai ka jawo shi ranka zai bace, ka kara tunani !
Yana gama fada ya muke ya nufi bayi dan ji yake kamar ya yi ta ihu, sam baya jin dadin duniyar,
Yana kasan shower idannuwansa rintse, zuba take da karfin gaske
ga ruwan sanyi karara da su,
Idannuwansa da sukai ja ya bude ya barsu haka ruwan na shigar masa ido , hanunsa na dama ya jimke ya daki bangon yana wani irin nishi mai nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki,
A kadan Wardugu ya kai minti arba.in a ba
yin nan sai da ya saisaita kansa ya kashe gudun showern ya dubi hannunsa da ya daki bango a kala sau uku wajen ya dan tashi abinka da farar fata,
Towels ya dauka ya daure jikinsa ya fito ya nufi bed ya kwonta rigingine yana adu.a a cikin ransa
Da id
o Mu.azan dake saman salaya ya bishi, kansa ya dukar ya ci gaba da jan carbinsa yana tunani barkatai a kasan zuciyarsa..........
Bayan ta gama ibadarta , zuwa ta yi ta hada complet dinta biyu ta saka a jakar computerta, ta duba kudin dake
jakarta , ta kuma duba wayarta da passport dinta ta koma bakin dan madaidaicin bed din da take kwana tun zuwanta ta dauki carbinta fari kar ya fito tana mai kuma kiran docter Elisabeth
Dagawa ta yi suka gaisa, nan docter Khadija ta yi shiru,
Docter
Elizabeth ta ce" kina ji, sati biyun nan shi dai kawai na iya sama maki domin kin ga aikinki ya kasance aiki mai daraja, bangaren zuciya bama so koda wasa masu kula da lamarin mu rasa daya koda na minti daya ne, na yi iya yina a haka aka tsaya, dan haka k
i hanzarta zuwa niger din ki gama komai kafin likaci ya cika, ni dai fatana ki yi ki dawo da shi mu shiga aikinsa ,
Kanta kawai take gyadawa , bata san ya zasu kwashe da masoyin nata ba, ta so ta samu lokaci isashe sai dai hakan bai samu ba , zata je da
wannan din ma Allah ya sa ya amince.
*Timiya*
Tunda suka iso suka sauka wsjen baba tsoho suka fada masa abinda ke tafe da su,
Baba kam tsufa ya kara rufe shi, bawan Allah daga ringeshe yake binsu da kallonsa domin idannuwansa ramr
am suke ganni, murya irin na datijai ya ce" na ji dadi na yi farin ciki, aman me zai shaida min da gaskiyar maganarku? Ina mahaifiyar taku? Ina agaishat? Ina alwalin mai neman auren? menene shaidar da zata saka na aminta da ku?
Wardugu dake dubansa ya k
araso a hankali kusa da shi, kai shi yanzu yana jin nauyin tsohon wanda a da nauyin bai kai haka ba,
Yana karasawa ya kama hannun Baba tsoho cikin yaren buzanci ya ce" bamu zo da su ba, sai waya da na dauke su suna magana, mai neman auren Agaishat aboki
na ne , aminina, shine wannan , ya nuna Mu.azam, ya ci gaba da fadin" Allah ne shaidar mu, shi ne alwalin kansa, idan kuwa ni zaka baiwa amanar yarka zan dauka baba domin ina jinta tamkar kanwata ta jini,
Baba tsoho yana dubansa da wani yannayi, a lamar
in Agaishat du idan ya yi istihara yakan hango wani duhu kafin ya ga haske, , dubansa yake ta kaiwa kan samarin biyu, Mu.azam da bai sani ba , da kuma Wardugu da ya zubawa ido, ya rasa me ya sa bai ji wani zumudi ba,
Bashida ikon hanawa ko sakawa a lam
arin agaishat duda shine silar zuwanta da mutanen nan, bai isa ya yanke hukunci ba, sannan idan ba zaka fadi alkhairi ba ka yi shiru,
Shiru ya yi ya yi masu jagora inda suka talabe shi sosai suka shiga motar aka nufi gidan Ba
Zaune suka same shi kofar
gida , ya tisa sansaninsa a gaba yana zaune kan tabarmar kaba yana ta gyara sansanin yana kukulewa da zaren daure abu yana kashi kashi , shi nan sana.a ce ya fara,
Da ido ya bisu har suka firfito infa ya hade rai yana hararar baba tsoho
Daidai wannan
lokacin suka karaso inda sukai masa salama,
Wani kallon ya bisu da shi, yana tatare sansaninsa,
Wani uabn tsaki ya ja ya ce" ai ko ba.a birne gawarta ba sai na siyar da tabata , ka ga bakin ciki, du ranakun nan baku zo fada min ta mutu ba sai ranar d
a zan fara sana.a? Ni na san *Bak'a* bata son ci gabana, wato dan ubanta mutuwarma ba zata yi ba sai ranar da zan fara sana.a
Baki dayansu dubansa suke, wardugu da tunda gari ya waye jikinsa a mace yake bai iya ce masa komai ba sai sakin baba tsoho da
ya yi wajen Mu.azam ya karasa saman tabarmar ya zauna ,
Hannunsa ya mika wajen sergent,
Da sauri ya karaso ya dire wata bakar jaka ya koma wajen da suke tsaitsaye,
Bude jakar Wardugu ya yi ya shiga fitar da daurin daurin kudi cefa yan jika goma go
ma yana direwa gaban Ba,
Du daurin nan million guda