Showing 66001 words to 69000 words out of 86237 words
yakin su, yanzuma ba wai ya zo ne dan Wardugu ya yi magana harkar Aisata ba, shima yana iya sakawa a saketa aman ya barta ta je ta yi kason
ta kawai domin ta taka doka, ciki harda ta musulunci , da aurensa a kanta take bin wasu mazan.
Ya zo me dan ya kara ganninsa su sami hira ta kusanci na da da uba, sai dai ga yanda ta kare,
A hankali ya juya dan barin Office din,
Ja ya yi ya tsaya, a
hankali ya dawo ya dube shi, hularsa da ta dage ya janyo ya gyara masa a kansa, ya gyara masa gaban rigarsa da kyau ya ce" Allah ya yi maka albarka, na yafe maka dukan abinda ka yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya kare gabanka da bayanka!
Yana gama fadar haka ya juya ya fice a office din,
Ran Wardugu a cakule ya hade takardun ya fito gaba dayansa a haukace ya mikawa Lieutenan Jalo takardun bai masa magana ba yana kallon mashin dinsa ya fice ya bar shi a wajen aikin ya kama tafia a kaf
arsa cikin sauri, ya yi niya a kafa zai je gidansa ba zai hau mota ko mashin ba, ya ki din , kai bama zai kuma hawa ba! Zai je a kafarsa , du wanda ya fasa kawo masa wargi ya ki Allah! (
π₯΄
wani da laifi , wani da shan duka? Tap
π€
),
Bayan kwana biyu, f
itina ta dan lafa gefen Wardugu,
Juma.a ce yau, ranar da ake bada damar shiga gannin yan gidan kaso harma a dan jima a wajen su,
A wannan ranar ne mutane ke cika prison dan gannin nasu,
Wannan damar Walyn ta rike ta yi shiga irin ta larabawa ta y
ane kanta da dan kwalin bakar abayar da ta saka ta yane har habarta sannan ta saka bakin gilas,
A kafa ta samu ta fito bakin titi nan ta ja ta tsayar da mai taxi ta yi shatar ita daya.
Basu zame ko.ina ba sai justice ta ciri takardar gannin dan priso
n ya dauketa ya sadata da gidan kason,
A hankali ta cire gilas din idonta, sannan ta dan ja mayafin dan bude habarta dan kar ta jawa kanta matsala da masu tsaron gidan kason
Takarda ta nuna, ta je saman kuje ta zauna inda aka shiga aka kirawo mata wa
nda ta zo nema,
A hankali take takowa har ta karaso wajen warda aka nuna mata a matsayin uta ke nemanta,
Kallonta take, irin kallon san sannin wacece? Hakan ya sa Walyn ta bude rufarta dan ta shaida ta,
Murmushi Aisata ta yi tana dubanta, aman a k
asan zuciyarta mugun kishin Walyn take, kai da tana da dama da ita ce ajalin yarinyar da ta auri gwarzonta!
Walyn ta kare mata kallo sama da kasa, cike da yanka da jan aji ta ce" *wanene shi*?
Bata amsa ba , sai da girarta irin na rikakun yan duni
ya da suka san kansu ta yi mata tambayar *Wane?*
Walyn ta fara shaka ta dubeta da kyau ta ce" *waye malamin da ya miki aiki kan Wardugu da mahaifinsa?* waye shi?, idan kika fada mani komai, zan saka a fitar da ke daga wajen nan.
Murmushin rainin hank
ali ta yi tana dubanta, cikin kissa ta ce" kina da damar sakawa a fitar da ni din ne kika shigo cikin gidan kaso dan samu adress din malamina?
Kina son samun kanki ne a wajen Gwarzona?
.........
π«π«π«
*BAK'A CE*
π«π«π«
Na
*SAJIDA*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*
π
KAINUWA WRITERS
β
πΌ
ASSOCIATION*
π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/k
ainuwawritersassociation
____________________________________
4
οΈ
β£
0
οΈ
β£
*Walahi ni ba kowa bace, ni ba komai bace, Allah ne gatana
ππ»πππ»
*
Walyn ta zaro ido, rai bace ta ce" zan datse harshen ki idan ki
ka kuma kiran mijina da gwarzon ki!
Aisata ta ce" da kuwa na ji dadin yin makota da ke, da zan gani idan kema da ya kilace zai saka ki a kaso dan kin zalinci wani!
Walyn ta tsareta da ido, a hankali ta ce" zan biya ki, ki fada min kar lokacin da aka
bamu ya kare ,
Aisata ta ce" na sani kina da damar iya biyana aiki, dan ni mai nema ce, ina nema kamar me, kudi baya isata, da yana isata da na tsaya da sirikin ki kawai!
Walyn ta ja tsaki ta ce" lokaci!
Aisata ta ce" kar ki damu, yau ai akoy lo
kaci isashe ,
Walyn ta kuma tsareta da ido, ta ce" me zai rage ki dan kin fada mani? Kin san dai kin haramta wa wardugu tunda kika kwonta da ubansa!
Aisata ta lumshe idannuwanta, a hankali ta lashe lebenta na kasa, rage murya ta yi kamar zataiwa Wal
yn rada ta ce" *Ke ba fa kowa ke da haram ba*,
Walyn ta daki table din ta ce" zaki fada mani ko ba zaki fada mani ba?
Har sai da hankali ya kawo kansu inda wani soja ya karaso yana tambayar lafia?
Nan Aisata ta kalamance shi da"Oga ba komai,
Juyaw
a ya yi ya koma, Aisata ta dubeta da kyau ta ce" kina tunanin na taka farar kafata na je wajen Boka dan tsibu dan
ya malaka min saurayi? Kina tunanin aikin boka ya malaka min mazaje biyu ?
Walyn ta ce" kin gane, ni fa ba yarinya karama bace, kuma na san
bariki ki ka yi ! Dan haka kar ki bi min ta wannan hanyar ba gyara mu zata yi ba.
Aisata ta ja rigarta kadan, hakan ya baiwa saman mamarta damar fitowa sosai, ta ce" *kin ga malamaina*
Walyn dake kallonta ta yi dariya tana girgiza kai ta ce" ba dai
Warsuguna ba, Wannan abin bai isa ya ja ra.ayin namiji mai sunna namiji ba!
Aisata ta ce" haka ya fada maki? Ko irin zaman da kike yi da shi?
Walyn ta ce" ba sai ya fada mani ba, haka ne, Wardugu kamili ne, girman kansa ba zai bar shi bama ya lura
da wani abin jikin yar bariki!
Aisata ta bushe da dariya har tana rike ciki, nunata ta yi da yatsa ta kuma kecewa da dariya, sai da ta yi mai isarta ta ce" lale kin rako mata, ina mai baki albishir din in dai kallon da kike masa kennan ki farka tun kaf
in ki kuma jaza mana wata yar balakin da ta fi mu ta karbe mana Gwarzon mu!
Walyn bata ce mata komai ba, sai duban kin raina min wayo da take mata,
Aisata ta tsagaita tana duban Walyn ta ce" Walyn Wardugu, ba kowace mace ce ta san kofar boka ba, kod
a kina jidana da na yi bariki dan na fita da d'a na kuma dawo kan uba , ina mai tabatar maki ba boka ne ya tsaya min ba.
Ya zan zo cikin wannan wajen mai fitar da wari ki saka ni gaba kina yi min rainin wayo? Walyn ta fada,
Aisata ta juya idannuwanta
ta ce" kar ki yi garaje, zuwa gidan yari rubutu ne wanda Allah ke kadara shi, diyawa a wajen nan basu taka basu karya ba....
Walyn bara ki ji wani abu....: du namiji na duniya yana da abinda idan ya ganshi a gabansa yakan ji ya rasa dabararsa,
Wani nam
ijin mace mai kissa, mai kisisina, mace mai kyan dan maciji ke tafia da imaninsa, wani namijin mace mai adini mai rufe jikinta, mai mutunta kanta ke tafia da imaninsa, wani namijin yana son mace mai halaya irin na yan bariki ce zabinsa, wanin mace mai kyau
ko muguwa ce zasu taka rawar, wanin yana son mace mai shiru shiru, wanin yana son mace mai kamar maza irin mai kafkaf da ita, wani baya jure gannin mace a cikin yannayi na abin tausayi...zaki ga ya fada tarkon kaunarta, wani farar mace ce zabinsa, wani ku
wa *bak'a*, ke wani duka biyun yana so....tambayar a nan shi ne *Sai ka
karanci mutun kake gane waye shi harma ka tabo wajen da ba zai jure ba, da kansa zai nuna shi sai kai*,
Walyn kallonta kawai take,
Aisata ta ci gaba" mijin ki dan ra.ayi ne, gwa
rzona ya bani wahalar da wani namijin bai bani ba , kyauna, zubina, yannayin rayuwana na saka shi fadin"Aisata ke matar kilacewa ce, ki yi zamanki a gida zan zo na dauke ki na mayar da ke matata. kafin na samu kansa na jigata.da kuka da komai ya furtan kal
mar so, domin na kai karar tsohon saurayina wajensa inda na biya mutumin ya yi min dukan tsiya, ke dai na takaita maki sai da na zama tamkar kaska, du inda wardugu yake ina nan, da naci da taimakon aminiyarsa ya furtan kalmar so...
Sai dai abin haushi du
irin yanda muke soyaya da shi idan na nuna koda shan minti ne a dan zaga sai ya fatatake ni,
A ranar da na tube zindir a gabansa sosai na kusa cin masa wani tsinanan abokinsa ya shigo dakin domin ke shaidan ba abinda baya hasawa , kwana dakin wardugu na
kusan cinma burina nan na fahinci irin zaman da ake tsakanin matar Marahut da shi,
Ayya ta kasance mace mai tsafta, ta iya girki, tana yiwa mijinta biyaya ....sai dai na sha na fito tsakiyar dare falon su na kunnuwana su tsinkayo min rigimar ba zata bas
hi ba, ta gaji da ayyuka ya bari sai da safe!
Wani wal wal wal ta yi da idannuwanta ta ce" *Walyn ba.a matsa lamarin nan, idan aka tashi a yi kawai!*,
A lokacin da na gama gane Ayya ba zata aminta na auri farin cikina ba, na dauki damarar itama sa
i na cusa mata bakin ciki , kuma ko da kwaya sai na kwonta da d'anta!
Walyn ta ce" shi Marahut din asiri ki kai masa ko?
Aisata ta ce" na fada maki ban san wannan ba!
Walyn ta rafka tagumi ta ce" fada mani yanda kika tarwatsa su , mai yiwuwa na y
arda da labarin wai Wardugu ba asiri ki kai masa ba.
Aisata ta buda bakinta zata fada mata kennan aka zo aka ce ya isa haka sun jima suna hira domin dai Aisata harkar kwaya ya kaita kaso, ido a kanta yake dan kar a kawo mata har gidan kaso...
Haka Wa
lyn na ji na gani ta fito ta kama hanyar gidanta ba tare da ta samu komai ba!
Alhinayet ce zaune tare da saurayinta, malamin university ne, saurayi ne domin bai taba aure ba, bazabarme ne baki dogo , hira suke cikin nishadi nan yake shaida mata yana
son turowa,
Alhinayet ta fada masa zata fadawa abanta tukunnan , abinda ya ce in sha Allah.
Haka suka gama hirar su ya mike ya yi mata salama ya shige motarsa ya tafi,
Mikewa ta yi ta je cikin gidansu ,
Shiryawa ta yi ta saka dogon hijab dinta b
lue, ta dauki bakar leda ta je wajen mamansu , wato matar mahaifin su ta shaida mata zata je ta kaiwa Agaishat hijaban
Adu.a ta yi mata kafin take fita ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan Ayya.............
Aghali ya zo garin Niamey ne dan duba
gininsu da ake yi a unguwar citΓ© laraba,
Ya gama abinda ya kawo shi aman ya ki tafia bisa bukatarsa na Wardugu ya siyar masa da mota , sun tsayar zai shigo ranar lahadi wato gobe baya aiki sai su fita su je ya gani......
Soyaya suke a nitse, a hankali
yake koya mata mecece soyayar ma wace a kulun sai sun gama bitar zai jefo mata tambayar" Agaishana, shin kina jin du abubuwan da na zana maki a kaina?
Dariya take yi a fili sai tace" ni yaya Mu.azam gudun fankan dakin Hane mai aiki kawai ke saka zuciya
ta gudu, ka ci gaba da koya mani na san zata yi gudun wata rana idan na ganka
Yakan tsareta da ido ne kawai , bai san me zai da ita ba, soyaya ai shigar farat daya take yi, shi da yake so ya kai kudirinsa wajen Ayya kan a aura masa ita da wuri? Kai ba z
ai wani jira har ta kamu da sonsa ba, zata so shi a zaman da zasu yi, shi kam yana kwadayin zama da ita a rayuwa....
Docter Mariam ce tsaye tare da shugabansu ta asibiti, kanta duke kuka ne take har jikinta na bari ta ce" nima marainiya ce docter, a lok
acin da na zo wajen nan shi ya tarbe ni, ya ciyar da ni da aljihunsa, kafin na tsaya da kafafuwana shi ne komaina, tun a lokacin nake mugun son sa, ba zan yafewa kaina idan ban je na dawo da shi ba, ki taimaka mani ki sama mani takardar nan na roke ki,
Cike da tausayi take dubanta, su musulmai haka suke ko kuwa wasu da wasu ne? Tana jinjina girman son da Mariama ke yiwa docter mu.azam, in sha Allah zata sama mata takardar su biyu wace zata bata damar zuwa ta zo da shi su shiga aiki, koda bai tashi ba , b
a zata tsangwami kanta ba,
A hankali ta dafa kanta ta ce" kar ki damu Docter, ki je zan neme ki, zan nema maki takardar
Da murnarta ta yi godiya ta fito ta shiga office dinta, hotonsu ta kaiwa duba kafin a fili ta ce" wai baka son farar mace ko? Dol
e ka so ni docter, ni ina son ka
πππ
Wayo hanuna
ππππππ
π«π«π«
*BAK'A CE*
π«π«π«
Na *SAJIDA*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*
π
KAINUWA WRITERS
β
πΌ
ASSOCIATION*
π€π»
```{United we st
and and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4
οΈ
β£
1
οΈ
β£
Ayya ki duba lamarina na roke ki,
Mu
.azan ya fada kansa a kasa, kunya ta hana shi dago da kansa ya dubi Ayya domin ya fadi abu mafi nauyi a bakinsa
Da mamaki take kallonsa, so? Aure? Yana son Auren Agaishat? Aman yaushe suka yi wata soyaya da fahimta har za.a kai ga aure?
A nitse ta c
e" Mu.azam, aman me ya sa kake sauri haka?
Mu.azam dake kallin kasa ya ce" Ayya , ina so ne a yi mu juya tare da ita.
Aman ai ka san sha.anin aure na bukatar nutsuwa ko? Sannan yarinyar nan amana na daukota daga garin su, eh lale mahaifiyarta ta bani
damar ko aure ya tashi na yi mata aman da ransu da lafiarsu ba zan yanke hukunci irin na aure ba tare da yawun iyayen yarinyar ba ko? .... Ayya ta fada jikinta sanyaye tana dubansa
Mu.azam ya gyada kansa, hankalinsa ya dan fara tashi ya ce" Ayya, ki tu
ra ni wajen dagin nata, na je na nemi a bani aurenta, bana son jan abin ne
Ayya ta kuma kale shi da mamaki, bai taba naci kan abu irin wannan ba, jikinta ta ji ya kara yin sanyi, aman Agaishat dinta dukanta ma nawa take da har za.a yi gagawa a lamarinta
haka? Sai dai kuma bata tunanin Mu.azam zai wulakanta mata yarinya, duda haka tana son bin hanyar da kakarta ta bi da ita, zasu kai kulansu wajen Allah, a hankali ta ce" yarona, na ji, kuma zan fi kowa farin cikin sannin tana hannu mai kyau, kar ka damu z
an san abin yi nan kusa in sha Allah, in dai Agaishat matarka ce zaka aureta kisa ba da jimawa ba.
Cike da murna ya yi mata godiya ya mike ya nufi dakinsa dan yin wanka,
Tsaye take a tsakiyar gidan tana kallon manyan tantabarun gidan dake kiwo nan ba
lbalin gidan , tana yi tana duba kofa domin ranar juma.a da alhinayet ta zo tace zata dawo ranar lahadi su je gidan kitso Ayya sai fadan kitso take,
Kallonta yake daga inda yake tsaye, inda ya shiga takowa a hankali har ya karaso inda take tsaye, ma.ana
suka jera,
A hankali ta dago da kanta daga kallon tantabarar ta kai dubanta wajensa , nan da nan ta matsa gaba sannan ta sada kanta kasa cikin yanayi na bawa wanda ke kusa girma.
Aghali ya ce" a garinku ke yar gidan waye?
Agaishat ta dube shi, t
a kuma sada kanta, sarkinta ne, ita talakarsa ce, sarkinta ma talakansa ne, dan haka cikin yannayi na girmamawa ta ce" sunnan mahaifina *Ba*,
Ba , ai sunnan du uba ne a garin buzaye! Aghali ya fada yana kara tsareta da ido,
Agaishat ta ce" ka yi haku
ri,
Aghali ya ce" baki min laifi ba,
Soyaya kike da shi? Kina tunanin zai mutunta ki zai so ki da zuciya daya?
Kallonta ta dago wannan karon ta sauke kan nasa,,
Bata kai ga bashi amsa ba Wardugu ya shigo da wata galeliyar mota fara kar, kusa d
a shi Alhinayet ce da ya dauko zai ajiye su wajen kitso wai
π€¦
ββ,
Birki ya ja irin na ka taka baka shiryan nan ba, da bakin gilas dinsa ya dan kale su kafin yake taka motar ya karasa wajen da ya dace a ajiye motar.
Yana tsayawa ya kai dubansa wajensu
,