Showing 51001 words to 54000 words out of 86237 words
office na buga, kuma shegema mutun ne!
Murmushi marahut ya yi ya karasa wajen kujera ya zauna ya ce" to ka fido mani matata mu tafi gida Wardugu,
Wardugu ya yi murmushi a bayane shima ya ce" ba zan so shakar iskar
da kuke shaka ba ko na second daya, sai dai ya zama dole ne, matarka mai laifi ce
Meye laifinta wardugu? Me ta yi da tsanani haka? Ka san yara da kin ji suke,aman ai koma me ta yi ina gannin sai mu kashe mu birne abinmu a tsakaninmu ko wardugu? Marahut
ya fada yana dubansa
Wardugu ya ce" zan so haka, sai dai ka ga rashin jin nata ne ya yi kamari, tana shigo da kwaya ne tana siyarwa wannan ba boyayiyar shaida bace, abinda nake bincike kawai na samu hanyar da take shigo da ita ko wanda ke bata sai na m
ika su kotu koda kuwa *kai ne*, sai dai ban san ba yin hakan ko Allah zai kama ni da shi?
Da sauri marahut ya ce" Quoi? (What?), wani irin kwaya? A Wardugu place din? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, wardugu ka kara mani haske a lamarin nan
Wardugu
da ya ji ya dan samu sasauci, domin a sama yake, jininsa a saman akaifa, tsoro yake kar a je rinjayar nata ya kai ta saka Marahut a wannan harka? Aman yanzu ko ba komai ya ji dan sanyi a ransa dan kuwa har gobe da sunnan mahaifinsa yake anfani,
Wardugu
ka fada mani mana, Marahut ya fada yana dubansa da yannayin serius
Wardugu ya yi umarnin a kawo AISATA,
Shigo da ita aka yi, dare daya tak du ta fara fita hayacinta abinka da wada ya saba da hutu,
Tana gannin Marahut ta sauke ajiyar zuciya mai nau
yi kafin da sauri ta nufi wajensa ta saki kukan kirsa,
Tana kukan ta ce" ka ga abinda Wardugu ya yi mini? Wannan wani irin tsana da cin mutunci ne? A gaban jama.a ya saka mini anker tamkar wada na yi sata, ai a tunanina ya dace komai ya fice tsakaninmu
ko me na yi sai ya hukunta ni a gida ba wai a gaban duban mutanen da zasu yi min dariya ba,
Hannunsa ya saka ya dagota daga jikinsa yana dubanta, kadara, Aisata kadara ce mai wutsiya, a dalilin Aisata ya rabu da farin cikinsa da girmansa a idannuwan iya
linsa, maciya ce Aisata, Aisata zinari ce,
A nitse ya ce" me da me kuke aikatawa a Wardugu place?
Aisata ta yi tsam kafin ta shiga cicira ido ta kali dan ta kali uban, cikin yannayin barikinta ta ce" me muke yi kuwa banda neman kudi? A wardugu place ba
abinda muke yi,
Wardugu dake rubutu a takarda ya dan yi tsam ya dago ya dube su ya maida kansa ya ci gaba da aiki,
Bai jima ba ya daga wayar office din ya danna kira,
Cikin girmamawa ya gaisar da jujun kafin yake fadin" mai girma na gama nawa bin
ciken, yanzu ana kawo maka takardu ka duba, daga nan na mika maka su kawai ,
Amsa shi ya yi kafin yake kashewa,
Marahut da ya gama fahimtar wayar da Wardugu ya yi shima yana dubansa, cikin yannayin nutsuwarsa dai ya ce" har yanzu baka daina jin haush
ina kan Aisata ba?
Wardugu ya juyo da sauri, ido ya zazaro baki daya kafin yake mikewa ya tofar da yawu a nan cikin office din ya ce" kan wannan? Ya fada yana nuna aisata,
Ya girgiza kai ya ce" ai koda me daraja ce bata kai na yi anfani da damata dan
wulakanta ku ba, ka gane laifi ta yi, idanma baka yarda ba ai kai din oga ne kawai ka je wajen wa.inda zan mikawa takarda idan sun baka matarka ruwansu ni dai ai na tono barnar ko? Ka fi kowa sannin waye wardugu domin kaine mutun na farko da ka rikeni a du
niya bayan likitar da ta fitar da ni daga cikin mahaifiyata!
Yana gama fada ya ja kys din motarsa ya dauki gilashinsa ya fice a office din yana mai jin haushin yanda mutane ke magiya kan a bari a ci gaba da yada barna!
Jikin Ayya ne ya yi sanyi
bayan korar Agaishat da ta yi, a hankali ta mike ta nufi dakinta tana mai jin wani iri me ya yi zafi harda laifin wani zai shafi wani?
Tana zuwa ta shiga da salama,
Agaishat dake zaune kasa ta dora kanta a gefen gado tana jan carbi da hannunta ta da
go da sauri tana kokarin mikewa tana duban Ayya,
Karasawa Ayya ta yi ta riketa ta zaunar da ita gefen gado,
A nitse ta ce" ki yi hakuri yar gidan Ayya, ba zan kuma yi maki irin haka ba ,
Agaishat ta sauke ajiyar zuciya tana dubanta,
Ayya
ta ce" bara na baki labarin mu..... na fada maki wacece *AYYA?*, na fada maki waye *MARAHUT a rayiwar Ayya?*, na fada maki wanene *WARDUGU* sannan wani irin girman daraja yake da shi a rayuwar Marahut da Ayya? Yarinta bara na baki labarin da ba kowa ya sa
ni ba................
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain &
motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
2
️
⃣
labarin Wardugu da tushensa a gajarce
.
........ ........
..........
Sunana *Zanaba SHAU*, sunnan Mahaifin Wardugu *MARAHUT ELUM*, ni marainiya ce gaba da baya, na taso a hannun kakata ta wajen uwa da ta yi min saura,
Marahut dan gata ne gaba da baya, ya kasance a lokacin anguwarmu daya domin gida uku kawai
ke tsakaninmu,
Tun wayona bai gama fahimtar Marahut na sona ba har na gane domin kiri kiri idan na yarda wani lokacin na yi dan shirin atampa na yafa mayafi na fito zai rufe ido ya kora ni yana masifa,
A anguwa ana girmama kakata domin mace ce da ta san
girmanta, ba abinda ya shafeta da abin hannunka, ga mutunci ga zumunci,...du juma.a zaki ga an kawowa kakata abinci daga gidajen anguwar nan ciki kuwa harda gidan su Marahut inda mahaifiyarsa shuwa arab ke turowa kakata da gurasa ta kasa, irin wace ake yi
a kasa ta ainahin da miya mai dadi harma ki ga an zuba tawa miyar mai magi domin a lokacin an hana kaka shan magi.
Sosai muke soyaya da Marahut, duk da wani lokacin nakan zauna na yi shiru ina tunanin Marahut na so na kamar yanda nake son sa kuwa?
Haka
n sai ya tayar min da hankali sosai domin Marahut dai jarumin namiji ne mai cike da abubuwan da mata ke marari har suna kai wawa, harma wani lokaci na kwatanta masa....
Tsareni ya yi da ido kawai, zuwa wani dan lokacin ya mike ya fice abinsa hakan ya haif
ar min da faduear gaban ko ya yi fushi ya bar ni ne?
Kwana biyu tsakani na dawo daga makarantar dare islamiya da nake zuwa a kusa da mu na tarar da kakata zaune tana jan carbinta da rufarta bata kwonta ba, ba kamar sauran lokutan ba,
Da sasarfa na ka
rasa wajenta dan gannin abinda ke damunta sai dai ina zuwa ta rike hannayena tana kallona ido cikin ido ta ce" Zannaba, kina ta adu.ar neman Allah ya baki miji na garin nan kuwa?
Na amsata ina dubanta da wani irin yannayi ta ci gaba" an zo neman auren ki
daga gidan Elum, Zannaba kin ji zuciyarki ta aminta da Marahut?
Wara irin kunya ce ta diro mani, domin fa Agaishat yata tubawa na da muguwar kunya, batuben mutun na da kunya harda ta mamaki, hakan ya saka na sada kaina kasa harma jikina ya fara rawa,
Kakata ta ce" kul, na hane ki da ki yi haka da ni, ke kawai gare ni kema ni kawai na rage maki, Allah shi ne gatanmu, zan so ace na bar ki hannu mai kyau, dan haka maza bani hankalin ki mu gama magana,
In takaice maki a wannan rana bamu kwonta ba du s
ai da muka dauki niyar istihara wace cikin kwana uku hankalin mu ya gama kwonciya har ma muka aminta da auren nan,
Marahut ya yi min gata , agaishat ya kai kudin aurena ya yi min kayan da aka jima ana labarinsa, aka daura aurena irin na kowace yar gata
inda kakata ta bada mamaki ashe tana ajiye da sarkokin aurensu ita da mahaifiyata, ta kai aka buge akai min tafkekiyar sarka da abubuwan hannu na zinari irin na kowace batuba yar gata, sannan ta fitar da kadarorin mahaifanna harma da nata gaba daya ta raba
aka yi min kayan daki sauran ta damkawa mai anguwar anguwarmu amana,
Wsshe garin auren mu Marahut ya dankara min wata makekiyar sarka ta zinari tatare da kwacakwablarta bisa al.adun tubawa wanda hausa ce cikin hausa, ba.a jima ba muka daga dan komawa b
akin aikinsa inda aka maida shi domin baban likita ne kuma yana harkar kasuwanci da kiwo.....
Mun kasance cikin farin ciki, mutunta juna, da kaunar juna, muna tafiar da rayuwar aurenmu bisa tsarin islama muna kiyaye du wani abinda zai firgita mu sai dad
aykun da baza.a rasa ba na yau da kulun!
A haka na samu cikin wardugu,
Mu kai rainon abinmu har na tashi haihuwa inda Allah ya taimake ni na haihu a hannun mijina a asibitin da yake aiki da taimakawar nurse..
.
Mun koma gida dan zanen sunna, nan Ma
rahut ya gabatar da sunnan *WARDUGU* a matsayin sunnan da ya zaba,
Kowa ya jinjina lamarin sai dai ikonsa ne, dansa ne, aman sunnan Wardugu linzami ne ga mutun mai zuciya, mai fada, mai balaki, kai ba.a zama lafia da mai sunna wardugu, Wardugu! HUM, ko c
anfawa ne mun yi kuma yana bin mu, kwarai zahiri ne Wardugu duniya ne guda, ba sai an koya masa ba da abinsa aka haife shi.......
Ina wanka a gida wajen kakata, tana kula da lamarina sosai da sosai, wata rana muka wayi gari da kyautar Allah, inda mutuwa
ta sake zagayowa ta tsame min wace ta min saura a tarihin iyayena,
Ayya ta yi shiru ta share kwalar da ta zubo mata,
Agaishat da ta yi lamo ta dora kanta a hannun Ayya, Ayya ta ci gaba" Agaishat na ji mutuwar baiwar Allahn nan, domin ni ita ce duniyat
a, ko me na kwaso ita nake fadawa a nitse ta warware min, ta rasu ta bar ni da jaririn da a lokacin bana iya daukansa da garaje dan girmansa masha Allah, ta bar ni da dan labubun yaron da yakan calara kuka wai shima nice mahaifiyarsa, na ga rana na godewa
Allah,
Agaishat ta kara jimke hannun Ayya itama tana jin yanda hawayen ya zubo mata, Ayya baiwar Allah, bata da kowa gaba da baya, ashe du yanda mutun ya kai ga malakar arziki bashi da cikeken farin ciki na yanayin rayuwar yau da kulun?
Ayya ta ce" n
a dawo ga marahut, bani da kowa bani da komai sai Shi a nan cikin duniya,
Bayan an yi bakwai muka juya garinmu inda na dauki girma na ajiyewa kaina na karfi da yaji na ci gaba da karatun likitana da nake yi a Ensp,
Can tsakiyar dare nakan dadaba Marahu
t, idan ya farka sai nace" Marahut, kar ka wulakanta ni a duniya, kai ne duniyata, kai ne farin cikina,
Yakan riko ni jikinsa ya ce" ban aure ki ba sai da na gane ke ce lumfashina, a duniya baki daya me ya kai lumfashin mutun tsada? Ba zan yi garajen ga
nnin hawayenki ba sai na kadara!
Magangannunsa da alkawarurukansa suka saka na samu nutsuwar zuciyata harma na warware na ci gaba da shagulgulana na yau da kulun tare da yarona,
Tun Wardugu na da wata bakwai ya mike, yana tafiya da kafafuwansa digir
digir tamkar dan gwari,
Du inda na yarda na je da shi idan ya damki yaro ko matashi sai an kwace da kyar,
Ya kasance ba.a gardama da shi da ya warware, yana fama da ciwon athsm wace in dai na yarda ransa ya baci toh fa a kadan mu yi kwana uku a asibiti
domin athsmar nan zata tashi ne ya kasance daga ta kwonta sai ta kuma tashi domin ba zai kwontar da hankalin nasa ba,
Wardugu zuciyar mahaifinsa ne, domin daga shi ko batan wata ban kuma yi ba, muna bibjyar komai nasa tamkar ranmu, kai har bama kawaici
a nuna soyayarsa,
A haka Allah ya hada mu da baba tsofo, wanda kawai salama ya yi yace yana bayar da magungunnan hausa ne,
Nan muka zanta a bayan idon mahaifin Wardugu domin baya son lamarin hausan nan wai tsoro yake ya taba masa reins,
Cikin iko
n Allah ya ki karbar kudina, muka ajiye magana idan Wardugu ya samu lafia zan yi masa kyauta,
Yakan zo lokaci zuwa lokaci ya kawo mana magannin da cikin ikon Allah muke bashi da nonon rakumi sabon tatsa da sasafe, tun ina boyewa har na bayannawa Marahut s
hima ya kama mani domin sauki kamar da wasa Wardugu na samu a hankali a hankali har ya daina lumfashi da bakinsa ya dawo yi da hancinsa,
Agaishat na kasance mutun mai shegen son mutane, ko dan na sakawa kaina bani da kowan nan a duniya sai Allah sai mij
ina? Ya kasance son yaya da yawan kula zumunci da jama.a,
A haka na hadu da babar aminiyata matar sarkin agadez, na hadu da kawata ta damagaran hajia Falmata, da sauran su,
Wardugu rashin lafiarsa kawai ya warke aman halaya na nan, a haka aka tsahe mu
aka maido mu garin nan inda kwata kwata
baba tsoho ya bace min na neme shi na rasa har muka taso aman abin na tsaye a raina sannan ina yawan tambaya,
Kwonci tashi wardugu ya tashi da niyar shi fa soja, soja, hakan ya sa mahaifinsa ya sama mana waje a Ba
bar makarantar sojojin niger wace ke a kwalo, wace tun yaro na karami ake kai shi shikennan shi da iyayensa sai jifa jifa,
Karatu yake, sannan kwazo yake da shi ko a filin training,
Hakan ya sa babansu yake kaunarsa harma yake zumunci da mahaifinsa
Wardugu na da shekara ashirin da biyu ya fito gagarumin comandan, jikaken saurayi, kaukauran namiji, zakin zamani, yaro da kudi kamar yanda ake kirarinsa.......
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____
________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_____________________________
_______
3
️
⃣
3
️
⃣
To tunda Wardugu ya dawo sai kuwa yan mata suka ce bismillah, ba kalar wace bata zuwa , kin dai ga yanda yake uwa kurman nan? Toh haka zasu zo su karaci haukansu sai dai su yi su gama su tafi,
Ban sa
n ya aka yi, ta ina aka yi suke kawance da wannan mai sunna Alhinayettt wace ni hakanan nake gannin karya ne ba wani kawance may yiwuwa soyaya suke ba halin aurenta domin aurensa bai wani jima ba,
Ana haka ya amincewa yarinya daya soyayarsa, yarinyar da
ta yi kundubala da sauran yan matan,
Soyaya suke ta hauka irin soyayar yayan zamani, ni ba zan shaidi yarona ba ba kuma zan ce yana aikata masha.a ba, aman
a lokacin da yake kwana a gidan nan har kwana ta sha yi a wajensa dan kuwa sai da na rufe idannuwa
na na ci masa mutunci sannan na daina kamata a dakinsa,
Waye shi da zai rantse min ba abinda ya shiga tsakaninsu? Namiji ne, ita kuwa mace, sun kadaice a wajen da ba kowa sai su sai Allah, ai hankalina ba zai dauka ba!
Ire iren abubuwan da sukai ta fa
ruwa kennan da yarinyar da ta gama kwana gidan mu, mamaki nake da tsoro, Wardugu ina ya zubar da kunya irin ta batube? Gaba daya wannan karatu da ya yi ya saka du ya zama wani kiritace wani tsayaye! Sam ya zubar da al.adu da dabi.un tubawa idan na yi magan
a sai yace ai ba wani adini bane, shi gaskiya ya girma a birni ba zai ci gaba da rayuwa irin na daji ba, ! ALLAH ya shirya,
Ana haka ya tafi karo karatu inda suka hadu da mu.azam suka kula zumunci mai ma.ana, a can ya hadu da matar da yake aure yanzu wa
ce a lokacin ba irin azabar da bata sha ba domin shi soyayarsa tana kan *AISATA* ,
Aisata? Agaishat ta tambayi Ayya,
Ayya ta ce" kwarai Aisata dai wace ubansa ya aura,
Agaishat ta ce" aa, Ayya na shiga rudani,
Ayya ta ce" bara na warware maki,
....
Haka kawai mun ci gaba da fahimtar juna alhamdulilah har wardugu ya dawo daga tafia,
Nan ya zo da maganar a tura wajen yarinya a tambayo aurenta,
Tashin farko ya dira cewar ba da yawuna ba, kuma in har ni na haife shi ba za.a yi haka da ni ba
, domin yarinya bata da da.a , zan so matar da zai aura ta fari ta kasance mutuniyar kirki ko dan