Showing 63001 words to 66000 words out of 86237 words
kallo da yake binta da shi na mamakin yaushe ta iya saka kaya haka? Yana gannin yan aikin gidansa har kulun su shigarsu tamkar an tsamo su daga rafi, domin Walyn nata daukan yan aiki yan birni sai yan kauye, baya taba gannin sun waye
su kulun tamkar mahaukata, shi ya sa koda wasa ya hana su taba wani abin a bangarensa, hakan ya sa ta samo masa namiji mai aikace aikacen bangarensa wanda ta yi ta rantsuwar ba dan daudu bane, shi kuwa dan daudu ne idan ya shigo gidan ne yake namiji!
A
hankali ta karasa ta dauki dan kwalin atampar ta daure gashin kanta da kyar , wanda yake lumbuk gaban goshinta, ta koma gaban madubin ta zauna abinta ta shiga daure gashin kanta,
Wani irin mamaki ne zai kashe wardugu dake tsaye yana biye da ita da kal
lo, kai! Ya fada a ransa, ya shigo ne dan ya tambayeta kys din dakin Ayya dan ya san ita zata barwa, sai dai mamakinsa, ya hadu da macen da bata nuna tsoronsa, kakahin ta birge shi, shishigi a gare shi ba, ita bata nuna tana tsoronsa ba , ita bata nuna bat
a tsoronsa ba, ita dai ta gaishe shi, gaisuwar da ya tsana wai wani *Ina kwana*, sai kace wani sa.anta!
Yana nan tsaye har ta gama daurin dan kwalin da ya boye baki daya gashin kanta, ta dauki turaren ruwa ta kuma fesawa a jikinta mai sanyin kanshi wan
da Ayya ta sayi kwali guda irinsa sunnansa princesse ,
Kwali ta dadage ta saka sannan ta shafa dan man lebe kadan, ,
Mikewa ta yi ta juyo facing dinsa tana dubansa yana dubanta, a hankali ta shiga takawa tana nufo shi, wanda du takunta daya sai ya
ji gabansa ya dadage ya fadi , da sauri ya kawar da dubansa a kanta daidai nan ya jiyo muryar Ayya,
Tamkar an hankada shi haka ya fito daga dakinta wanda har ya waiwaya da sauri yana duban kofar, hankali ya furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, abin
da Wardugu ya furta kennan kafin yake tura dakin Mu.azam dake kasa kadan da dakunnan su Ayya ya shige ya rufo ya nufi gaban madubi da sauri,
Duban kansa ya tsaya yi, kaki ne a jikinsa, sosai yannayinsa na ban tsoro ya bayana a jikinsa, sai dai kaki din
wandon ne kawai sai bakar rigar da ya saka, a fili ya furta" ko dai makauniya ce?
😳😳😳😳😳😳
Ba laifi yau kun yi comment, dan haka ga kari
😍😍😍😍😍😍
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرح
من الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________
________________________
3
️
⃣
8
️
⃣
Murmushi ya yi bayan ya tabatarwa kansa da yarinyar ba makauniya bace tana gani sosai,
To aman ayar tambayar shi ne me ya sa bata tsoronsa? Ko ta tsaya ta shagalta a kallon sa kama
r yanda du yawancin mata da mata ke yi? Bale ita da ga irin wajen da ta fito wato kauye zai kasance shi ya zama abin kallo a wajenta, sai dai abin mamaki tamkar ba.a yi halitarsa a gabanta ba,
Kansa ya girgiza a fili ya furta" Ayya kwashe kwashe, idan k
uma aljana kika kwaso mana ba sai ki huta ba
🥴
.
Sai da ya gama abubuwansa sannan ya juya ya fice ya tafi falo domin yana jin hayaniyar samarin biyu da muryar Annarsa.
Agaishat tsam ta yi bayan fitarsa ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ya kubuce mata a
fili ta furta" idan Mu.azam nawa zai aure ni, cikin abokan ango da zasu zo daukana a rakumi (
🙁😕😟
ke malama a birni kike
🙄
), harda wannan mai kama da mutanen cikin alon nuno mutane (tv),
Dariya ta yi tana dafe goshinta ta ce" kai aman katoto ne, kuma
wai dan Ayya ne
🤦
♀, ko ta yaya ta goya shi?
Kys din Ayya ta dauko ta juyo zata fita, ta ja ta tsaya ta dubi wajen da Wardugu ya tsaya ya zuba mata ido, nuna wajen ta yi da hannunta ta ce" kai katoto, ka daina irin kallon nan, baba sofo yace ba kyau ir
in kallon nan da kake!
Yatsina fuskarta ta yi , ambaton sunnan baba sofo da ta yi ya sace mata lakar jiki, a hankali ta shiga takawa da zancen zucin ko ya yake? Ya Annarta? Ya yan uwanta? Ko da wasa bata tuna yannayin mahaifinta, sai ta tuna da baba tsof
o sau dari bata kawo sunnan Ba a layin zuciyarta ba, tsananin tsoronsa da ya dasa mata ya saka har a zuciyarta idan ta yi kamar ta tuna shi sai ta gargadi kanta cewar ki kula Agaishat kiyayarsa gare ki madaukakiya ce.
Agaishat na saukowa, kanshin turara
nta ya fara karasowa, kafin a hankali ta idasa fitowa fallon,
Da murmushi Ayya ke kallon ta, domin ta ji dadin irin yanda yar tata ta koyi saka kaya da wuri haka,
Mu.azam da ya dago daga hirar da yake yiwa Wardugu ya zuba mata mayatatun idannuwansa ,
zuciyarsa na luguden kida yana dubanta da wani yannayi mai nuni da " kin azabtar da ni,
Wardugu dake gefensa yana sauraron sa, jin ya yi shiru ya saka shi duba wajen nasa, nan ya bi abinda ya tsurawa ido, ya kai dubansa wajen Aghali da yana tsakar waya
da mamansa yana shaida mata ya sauka lafia, aman ya tsaya mamakin wai yarinyar da Ayya ta dauko ce haka?
Da sauri Wardugu ya mayar da dubansa wajen Mu.azam, shima zuba masa idon ya yi yanai masa kallo mai cike da ma.anoni,
Salama ta yi , kafin ta za
rce wajen Ayya , inda a takaice ta ce" ina kwana.......... (wannan na cikin abubuwan da Ayya ta koya mata, cewar ta ringa kiyaye sakin baki, kai ko gaisar da bako zatai ta takaita , in dai ta yi salama cikakiya halas!)
Tana zuwa ta zauna inda Ayya ta nu
na mata,
Hannunta Ayya ta kama tana duba faratunnanta , domin ta umarce ta da sakawa yatsutsanta jan lale,
Ta kuwa saka , ya kama yai mata das a hannun ,
Ayya ta saki hannun ta lakaci kuncinta, kafin ta yi kiran Hanne, kan ta kawowa yarinyarta abin kar
i,
Kai Wardugu ya girgiza, ya mike yana daukan wayarsa ya kai dubansa wajen samarin dan ya ankarar da su , da haushi haushi ya ce" ni zan tafi,
Da sauri Aghali ya mike yana fadin" zamu tafi dai oga,
Wardugu ya ce" a mashin fa nake Aghali,
Aghal
i ya dafe kansa, ya kai duban sa wajen Mu.azam ya ce" docter tashi mu je ka kai ni ,
Mu.azam ya dubo su, irin yanda Wardugu ya yi kicin kicin da fuska ya san ko sun bi shi walahi zai bace masu ne, dan haka ya ce" ni sai na karya,
Idan kana so ka kary
e! Wardugu ya fada ya juya yana fadin" premiere dame (First lady, wato Ayyarsa), sai na dawo ,
Ayya ta amsa shi da" ka dawo lafia *War*,
Haka ya fice a gidan cike da takaicin girman kan yarinyar, domin shi kawai ya ajiye haka a matsayin girman kai, w
ai su *Ashak* ko? Ba buzuwa ba dai, su waye ma su buzayen nan da suka raina mutane har suke yiwa mutane Ashak?
Sosai ya kunsa a lamarin Agaishat ya bashi mamaki, wanda hakan ya saka ya dauki aniyar nazartarta a tsanake, shi zai koya mata ladabi da biyaya
a haukace! (Toh fa),
Kuka take na tashin hankali tun da ta shiga bayin da kamar minti biyar, da gudu ta fito ta mikowa mamanta abinda ta yi gwajin fitsarin nata dan gannin ko ciki ne da ita? Domin tunda Wardugu ya yi maganar komai nata ya tsaya ya
daina aiki,
Da yannayin farin ciki uwar ke dubanta, ta ce" kukan murna kike ko na me Walyn??
Da madaukakin tashin hankali ta ce" ba zan haihu yanzu ba, bana son cikin nan walahi sai an zubar da shi, bana so!
Da mamaki uwar ta mike tana dubanta, k
afin take nunota da yatsa ta ce" ke ke ke, da hankalin ki kuwa?
Walyn ta dan tsagaita kukanta ta dubi uwar, kafin take kara barkewa da wani kukan ta ce" ba zan yarda na dauki ciki da Wardugu a wannan lokacin ba, a bai tabatar ina da ciki bama ya yi min
rantsuwar sai ya yi mini kishiya ina da ya gane ina dauke da ciki?
La haula wala kuwata ila bilah, maman Walyn ta fada, ke bashi da hankali? Yaushe ma aka yi auren da har ya fara yi maki maganar zai maki kishiya? Me kikai masa da zafi? Ki bakya barins
a zuwa wajen ki yanda ya dace?, fada mani me ki kai masa da zafi haka?
Nan walyn ta warwarewa mahaifiyarta yanda suka yi da Wardugu,
Haushi kamar uwar zata dake ta ta ce" yaushe zaki gane mahaukaci ki ke aure ki iya takun ki da iya zama da shi?
Da
sauri Walyn ta ce" Ma, Wardugu ba mahaukaci bane !
Uwar ta yatsina fuska tana dubanta ta ce" toh dan uban ki ba mahaukacin bane, aman wannan cikin ko aman jini kike sai kin haife shi kin sama mana magaji, ke ko me zaki yi sai kin kawo shi duniya, bara
ma ki ga na fada masa, ai shi kina tsoron sa tamkar ran ki! banza sakarya marar tunani!.....
Rigima ta kirki suka kwasa kafin da kyar ta samu ta zaunar da ita ta ce" Walyn , kina bani kunya a rayuwa, wani lokacin har kokonto nake ko dai an canza min ke
a asibiti ne? Ina yi bakin kokarina dan gannin kin yi fice a gidan ki aman a kulun sai da hadu da abin takaici abin mamakin da zai saka ni jin kunya,
Matar Batube, ta kasance tamkar abinda ya malaka kwalin kwal a duniya, wanda tamkar numfashinsa ne, yan
a ririta ta, yana kulawa da lamarin ta kafin na kowa, na sani ci sha sutura kilacewa, kayan burga ba wanda baki da, matsalar daya ne baki
isa ki saka mijin ki ko ki hana shi ba! Menene dalilin haka? Na kasa ganewa, na kasa ganewa walyn,
Walyn dake zaune
du ta hade jikinta, a ranta kuwa ayannawa take ko da jaraba sai ta zubar da wani tsinanan ciki, a haka ma tana cas cas dinta yanai mata maganar kishiya, ina da ta haife? Bama zai yiwu ba, idan ta haifi guda ai ta kama hanya, kofa ta budu, sauran zasu zo k
o fa balaki ne, kennan shikenan kishiya ta tabata a gare ta ? Duda tana tsoron lamarin wardugu, ya yi aure haka ba tare da ya cika al.ada ba ba damunsa zai yi ba, tsohuwar uwarsa kuwa ba tirsasa shi zatai ba!
Mrning alll
🐫🐫🐫
*BAK'A
CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
http
s://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
9
️
⃣
*baki ba zai iya misalta maku irin yanda zuciya ke cike da farin cikin karanta ku Bak'a fans, Allah ya bar kauna baki daya*
Ya Allah, kar ka kai labarin mutuwarmu zuwa kunnen da baki ba zai fadi alkhairi kan gawarmu ba
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😭
Haka Walyn ta wuni wajen mahaifiyarta , inda uwar ke kwatanta mata yanda zata yi ta ci ribar zama da wardugu, ita kuwa tana tsara y
anda zata rabu da ciki!
Tana komawa gidanta ta zauna falo, ko kayan bata iya cirewa ba tsabar tana cikin tashin hankali, fatar jikinta kuwa du ta yi ja abinka da jan mutun,
Tv ta kunna ta kamo tashar labaru,
An yi sa.a kuwa ana watso labarun su
Aisata kan an yi bincike har an fara cafko masu shigo da kwayar, inda alkali zai yanke masu hukunci, , nan aka hasko sunnanta baro baro hade da sunnan mahaifin wardugu, aka fadi cewar ta bada hadin kai wajen kamo wasu masu harkar dan haka zata samu sasauci
kan hukuncin da aka yanke mata,
Tsaki ta ja ta kashe tv din ta mike nan ta shiga baci domin ji take tamkar idannuwanta na dauke da yaji ne dan tsabar nauyin da su kai mata.
Wardugu na tsaka da aikinsa aka shigo aka shaida masa Marahut na son ganni
nsa, a shigo da shi ko kuwa?
Wardugu ya dafe goshinsa, a ransa ya ayanna me ke damun Elhaj Marahut ne da zai mayar min da office wajen zuwa haka?
Umarnin a shigo da shi ya bayar , ya ci gaba da aiyukansa yana hada takardun wasu yan gudun hijira ne da
aka kamo , ya duduba da kyau ya ga du yawanci yan libia italia da dai sauran su, yana son mika su hannun likitoci a duba lafiarsu kafin su yi masu takardun tafia su juya garuruwan su!
Shigowa Marahut ya yi ya zo ya zauna saman kujerar zaman mutun daya
yana duban Wardugu,
Kai shima yana alfahari da namijin yaron nasa, suna mugun kama aman ko a zamanin da yana saurayo bai kai Wardugu tsayi da yannayin karfi da cikowa irin nasa haka ba,
Murmushi ya yi masa ya miko masa hannu ya ce" Asalamu alaika Wardu
gu
Dago da kansa ya yi , a nitse ya miko masa hannun shima ya amsa da" amine wa.alaika salam *Elhaj Marahut*.
Murmushi ya kuma yi ya rike hannun na wardugu, sam baya son sakin hannun, rabonsa da rike hannun yaron har ya manta,
Da ido Wardugu ya
yi masa nuni da ya cika shi mana?
Sakin hannun ya yi , a nitse ya ce" Wardugu sunana kake kamawa haka ko?
Wardugu ya dube shi, ya yi masa murmushi ya mayar da dubansa kan takardarsa,
Ka saka baki wajen alkalin nan ya sasauta mata hukuncin da ya
dauka a kanta, kaso har na shekara biyar ya yi tsauri Wardugu,
Wardugu ya dago yana dubansa , ya ce" ka san ba hurumina bane, sannan bana saka hanuna a irin haka, kaima ai kana da hanyar hanata yin kason ma domin ka fi ni fada a ji a wajen su,
Wardu
gu sunana zai bace Wardugu, sannan hakinta a kaina yake! Marahut ya fada yana dubansa da yannayin iya gaskiyarsa kennan
Wardugu ya ce" ni nawa sunnan sai na kai na dulmiya ko? Ah koda yake daman sunana a bace yake a bakin al.umar da suka aikata laifi, s
ai ya yi ta baci jar a bakin wa.inda basu taka dokar bama?
Marahut ya dafe goshinsa, ransa ya fara baci ya ce" har sai yaushe zaka daina mugun fushin nan a kaina? Ni fa na haife ka! Baka tsoron goben ka? Kai idan naka suka ki yi maka biyaya fa? Wardugu
ba laifina bane abinda ya faru a baya ,
Wardugu ya dube shi ido cikin ido ya ce" wannan tsohuwar magana ce Marahut, kana iya tafia ba zan saka bakina a maganar iyalinka ba!
Wardugu! Ya fada da dan karfi yana mikewa,
Wardugu ma ya mike ya ce" Mara
hut!
Marahut ya tsura masa ido, a hankali ya ce" dan na kula wata, na aureta , ba laifina bane, laifin uwarka ne! Sannan dalilin halayan da na gane nata na rabu fa ita yanzu,
Wardugu ya hadiye abinda ya tsaya masa a wuya, ya karya kansa ya ce" sai d
ai yanzu Wardugu bashi da budurwa bare ka kwace,
Marahut ya daga hannunsa ya zabga masa mari wanda ya yi mugun kara kara, ji kake tas, ya maya masa a gefen kuncinsa wanda hakan ya sa hularsa dagawa,
Kan Wardugu a kasa a hankali ya dago jajayen idannu
wansa ya sauke a fuskar mahaifinsa, Mahaifinsa, ubansa, wanda ya haife shi, a yau ya so a ce wani ne ya kai hannunsa jikinsa, kai kai kai, balaki,
Ido cikin ido suke duban juna, Marahut ya ce" ko me ka zama, ko me kake takama da shi dai haihuwarka aka yi
, na yi tunanin rashin mutuncin naka zai saka ka daga hannu ka rama! Ka rama marin mana Wardugu!
Wardugu ya sakar masa murmushi mai ciwo , a hankali ya ce" ko shege mai mutunci ba zai rama ba bare kai da ka haifi dan halal ka bashi tarbiya?, kar ka dag
a murya yarana su ji, domin ban san in zan iya rike kowa, wai ina gudun ba nan gaban idona ba, ka san soja shegen yawo ne da shi, gashi da ramuwar gaya,
Ka je kawai Marahut.
Jikin Marahut ne ya yi sanyi, ji yake dama da hali da ya rungume shi ya shafa
wajen da ya mare shi ya bashi hakuri,
A hankali zuciyarsa ke sauka har ya ji dumbin kaunar dan ta kuma mamaye khalbinsa bashi da wani , baya tunanin zai samu daga shi, fatansa su sauko daga dokin zuciyar da suka hau bisa gangancinsa, sai dai ya rasa ya
ya zai yi, shi ba zai duka gabansu ya basu hakuri dan ya kara aure ba, su ya dace su yi hankali su zubar da makaman