Showing 69001 words to 72000 words out of 86237 words

Chapter 24 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

17

gani ya yi aghali na magana, yar gidan Ayya kuwa na kallon kasa, kansa ya girgiza kafin ya maida dubansa wajen Alhinayett ya ce" Alhi, Aba ya saka na yi bincike a kansa, yace bai yarda da adinninsa ba , hakan ne kuwa ba musulmi bane yace shi musulmi ne d

an ya saje da jama.ar garin nan,

Alhinayett ta ce" General ya kuke so na yi ne? Ina zan shiga na samo wanda ya yi 100/100? Wannan na uku kennan yana zuwa da niyar aure abin na watsewa tun kafin a je ko.ina, Wardugu bana son auren Lieutenan na fada maka

bana son auren soja.

Wardugu ya yi musrmushi yana dubanta ya ce" kuma ki ce ke aminiyata ce, a gabana kina fadin bakya son auren mai sana.ata, me zamu yi maki ne? Me muke yi?

Alhinayet ta girgiza kanta ta ce" Wardugu, bana iya zama da namiji mai mu

gun karfi, ba zan iya rigimar sojoji ba, ba zan iya firirita irin ta matan sojoji ba, ka san ko ni wacece ban iya fada ba, ban iya ihu ba Wardugu ina son namiji mai sanyin hali ne,

Wardugu ya ce" ba daga nan take ba, sai ki ga kin auri wanda ba sojan ba

kuma ya kasance irin wanda bakya so din, kin gane Alhi ke dai ki yi adu.a , aman na san kina son lieutenant sosai, ke ra.ayinki na ba zaki auri soja ba dan bakya son mai fada, wannan ai shirme ne, ni na fi son ki auri wanda yake na san shi , du ranar da y

a taka min ke na nuna masa bashi da wayo!

Murmushi ta yi ta kai hannunta suka cafke ta ce" Wardugu, aa fa, ba zaka dakar min miji ba wollah....

Ido ya zaro ya ce" kai, har kin fi son shi da ni?

Bakinta ta yatsina tana hararsa da wasa ta ce" oyah

bude na gaishe da Ayya mu tafi kar yama ta yi sosai ,

Idannuwansa ya kai wajen su, nan ya ga Aghali baya wajen aman ita tana tsaye,

Cikin hijaban da Alhinayet ta kawo mata ne ta saka milk mai haske, hijabin har kasa yake mai hannaye sannan tamkar zub

in riga aka yi masa ya dinku ya yi kyau sosai, ta saka takalminta mai dan tsini kadan da igiyoyinsa ta daure abinta das da ita,

Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen Alhinayett da ya ga ta tsare shi da ido, sarai ta ga me yake kallo duda ya saka ba

kin gilas ya tamke kar a gane me yake ciki,

Kuma kallon wajen ta yi ta ga Agaishat ta juya wajen kofar falon ayya tana murmushi,

Wajen ta mayar da dubanta sai ta ga Mu.azam ne ya fito cikin shigarsa ta shada ya yi shar da shi , daga inda yake tsayen

sai turo mata irin abin nan na soyaya yake sai yace Muah,

Ita kuwa sai ta rufe ido tana dariya,

Tsaki wardugu ya ja ya ce" ji wani shirme kuma?

Alhinayett da lumshe idannuwanta, ta ce" na me? Ba wani shirme walahi sai soyaya,

Dubanta ya yi kaf

in ya yi murmushi ya girgiza kansa, motar ya bude ya fita inda itama ta fito,

Tafiya ya fara da sauri sauri kamar yanda yake yi kulun, dakatawa ya yi ya dubota ya ce" kuma na saka ya tura magabatansa wajen Aba ,

Ido ta zaro ta ce" Wardugu, Wardugu,

Ina tuni ya yi tafiarsa,

Murmushi ta yi itama a fili ta ce" Wardugu zai min auren dole da soja.........

Yana zuwa suka gaisa da Mu.azam ya tsare shi da ido ya ce" haka ka koma kan mace? Ka saka yarinya gaba kana abu irin na yara?

Mu.azam ya

daga girarsa ya ce" kai raba ni amini, soyaya ce,

Kai ya dafe yana mai jin matsanancin faduwar gaba, juyawa ya yi ya shige ya barshi nan kar ya hadasa masa hawan jini,

Ayya bata falo dan haka ya haye sama dakinta dan ya san Aghali wanka ya shiga ...

..

Yana zuwa ya gaisheta kamar yanda ya saba sannan ya zauna daf da ita yana dan mamatsa mata kafarta,

Ayya ta ce" Mu.azam ya zo min da maganar yana son auren Agaishat,

Wardugu dake rike da kafar Ayya yana matsawa sai tsayawa ya yi tsam da matsawa

r yana duban kasa,

Baka ji bane? Ayya ta fada,

A hankali ya dago dubansa ya sauke kanta, idannuwansa ya lumshe dan ji yake har kansa ya fara sara masa sanadiyar faduwar gaban da yake ji, me ke damuna? Ya tambayi kansa, me ya sa da an kirayi sunnan ya

rinyar nan ko na ganta sai na ji faduwar gaba?

Kansa kawai ya gyadawa Ayya,

Bakinta ta yatsina ta janye kafarta da haushi haushi ta ce" Wardugu bafa na son rainin hankali, ya zan fada maka magana ka wani gyada min kai sai kace inai maka wasiya?

W

ardugu ya hadiye yawun bakinsa da kyar ya ce" Ayya, wai ya aka yi bakya yiwa sunana kara irin na d'An farin nan? Sai kawai in ji kin kama sunana kai tsaye wai Wardugu,

Ido ta zaro tana dubansa yanda ya yi maganar walahi sai ta ji wata kunyarsa ta kamat

a, ai kuwa ta juya ta dauki filo ta juyo dan buga masa sai gani ta yi ya fice da gudu a dakin,

Murmushi ta yi ta ce" ja.iri, ja.iri, ja.iri, !

Zan yi magana da yarinyata , in dai tana son sa, zan baiwa Aghali sako ya je da kansa wajen Mahaifanta ida

n sun amince ya kai kudin aurenta a daura kawai, Allah ya sa Alhairi ne......

To fa

🥴🥴🥴🥴

😎😎😎😎😎😎😎😎😎😎

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

___________________________

_________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________



4





2





Alhamdulilah Alla kulli halin...

A wannan rana bayan Wardugu ya ajiye su agaishat saloon dan yin kitso suka zarce park dinsa tare da samarin, inda Aghali ya zabi daleliyar mota irin ta ratsa rairai mai shegen tsada,

Ba

yan sun gama magana da yaron Wardugu, Mu.azam ya tsaya gurin wata mota mai ruwan ash , karama mai kyan gaske, kallonta yake yana murmushi,

Wardugu ya gama da Aghali yace" ku mu je ....

Mu.azam ya ce" wardugu, wannan motar nake so,

Aghali ya ce" me

zaka yi da motar nan kai kuwa? Ta mata ne fa,

Mu.azan zai bashi amsa ya ji lumlumlum lema a hancinsa,

Da sauri ya juya yana mai ciri hankicin a aljihunsa ya goge jinnin da ya zubo masa ta hanci, a hankali ya karasa motar Wardugu ya bude baya ya shiga

ya jinginar da kansa jikin kujera,

Ajiyar zuciya yake saukewa yana kara goge jinnin inda wata number ta fara shigowa saman screen dinsa, number saudiya ce,

A kasan zuciyarsa ya ji nutsuwa da number dan haka ya daga ya yi shiru ba tare da ya yi magana b

a,

Ajiyar zuciya ta sauke kafin take share dan guntun hawayenta, so take ta yi magana tana tsoron kar ya ji muryarta ya kashe , ta godewa Allah da da ransa, ta godewa Allah da ya daga wayarta duda bai san ko wacece ba,

A hankali ta ce" ina son ka Mu.a

zam

Sai da ya ji wata kasala, a hankali ya dubi screen din, ya mayar kunnensa, ji ya yi wata nutsuwa na kara ratsa shi, a nitse ya ce" docterna, me kika je yi saudiya a tsakiyar shekara?

Idannuwanta ta lumshe ta ce" na zo rokar Allah ya baka lafia, y

a nuna min jininka a duniya,

Murmushi ya yi ya girgiza kai, ya ce" kin ga jini ke zuba a hancina, bayan ina son na yi aure, har na saka a tambaya min auren yar, ina son yarinyar a raina ina son na aureta koda shi kadai zan yi a duniya,

Wani irin fadu

war gaba ta ji, jikinta ya dauki rawa, a hankali hawaye ya shiga zarya a idannuwanta, a hankali ta ce" zaka aureta, kar ka damu, zaka rayu Mu.azam,

Shima idannuwansa nasa ya lumshe yana mai jinta gaba daya jikinsa, yana son yarinyar nan fa tamkar ransa

, sai dai ba zai yarda haka ta faru da ita ba, ba zai yarda yana ji yana gani ya tsareta haka ba, ya sani ne idan ya nuna mata eh yana so zata sakawa ranta da zata jima da shi bayan yana ji a jikinsa an kusa zare sauran numfashin da ya ragewa gangar jikins

a,

A hankali ya datse kiran inda ya shiga shafa kansa yana mai jin jikinsa ya dauki zafi,, a hankali ya furta Agaishat ki aminta da ni na dan lokaci, ina son ki kema (

🙄

)

Wardugu da kansa ya fitarwa da Aghali motar nan dan baya so a komawa su yi mot

a daya, yana gama fitar masa da komai ya bashi hannu ya ce" aboki, ka gama da Muhsin ni sauri nake,

Amanda aghali ya yi inda ya raka Wardugu da kallo yana ayyana a ransa ko lafia?

Wardugu na tafiya yana sake sake a zuciyarsa, yakan tsinci kansa wani

sakarai idan ya ganshi gaban wanda yake so a ransa yana cikin wani halin da ba zai iya fitar da shi ba,

Motar ya bude ya shiga, a hankali ya juya fuskarsa gefensa ya ga ya lumshe ido tamkar mai barci,

Motar ya tayar ya juya a hankali ya nufi saloon din

da ya ajiye su Alhinayett

Yana zuwa ya yi mata message cewar ta turo masa Agaishat, yana kofa,

Ba tare da ta tambayi komai ba ta dubi Agaishat da aka gama yi mata tsararan kitso a kanta mai dan girma girma aka saka wani dan roba a karshen kitson dan

kar ya warware , ta mugun yin kyau tace da ita ta je mota wardugu na kiranta,

Duda gabanta ya fadi, aman sai ta dake ta mike tana tunannin lafia? Domin yace idan sun gama su yi tafiarsu, wani abu ya faru ne?

Bata da amsar da ta fi ta fice a nitse tan

a mai jin faduwar gaba,

Wardugu dake kallonta tunda ta fito, du takunta daya na kayar masa da gaban da bai san na meye ba, ya dai ajiye hakan a matsayin zai shige gaban abinda bai taba shiga ba, zai shiga rayuwarsu ba tare da izininsu ba, zai yi iya yin

sa dan faranta ran amininsa,

Kare mata kallo yake, a kasan zuciyarsa ya ayanna"""""meye na naci a kan bakar mace? Menene sirin Mu.azam?,

Tana kara kusanto motar yana kara dubanta dan so yake sai ya karanto sirin a tare da ita, ,

Da yake ta gaban mota

r take nufo motar, kuma Wardugu ne ke tuka motar hakan ya saka idannuwanta sauka cikin nasa, manyan idannuwanta masu ruwan madara da bakin dake tsakiya mai girma wanda ke watso da hasken ruwa ruwa yana sheki , kallon nan mai shige da mai jin bacu shine kal

lon Agaishat wanda hakan ya samo asali da tun tana karama mahaifinta bata isa ta daga ido ta kale shi ba, sai ta saba da yin kalli a lumshe tamkar zata rufe idon aman kuma ta fi wanda ke kallo tar tar ganni domin wata kibiya ce ke jefo gannin nata har waje

n inda ta yi niyar kallo,

A hankali ta lumshe idannuwanta wa.inda ta yi niyar cire nata idannuwan a idannuwan Wardugu, domin kuwa tsai kallo na cikin ido sukaiwa juna wanda basu san da haka ba sai fa ta cire nata ya farka ya yi gagawar mayar da dubansa w

ajen Mu.azam dake jingine da kofar motar,

Murya a dake ya ce" malan dan bani waje zan tatauna da yarinyar can,

Sai a lokacin Mu.azam ya ga Agaishat ce ke karasowa wajen motarsu , a wannan lokacin har ta karaso sosai jikin motar tana jira a bude mata ka

nta a kasa,

Mu.azam ya kali Wardugu , murya a raunane ya ce" war, kar ka yi min haka , me ta yi? Dan allah kar ka yi mata fada ko ka rikitata, na tuba ,

Wardugu ya tsare shi da ido yana mai jin wani tsoro a ransa da faduwar gaba, mutun ne shi tamkar

kowa, dole abinda zai kayarwa kowa gaba ya kayar masa, sai dai ba zai taba nunawa ba, ba zai taba bari wani ya san halin jin tsoronsa ko faduwar gabansa ba,

Da ido ya nunawa Mu.azam ya fice fa,

Mu.azam ya turo baki ya bude motar ya fitar da kafa daya

ya juyo fa haushi haushi ya ce" idan ka batawa abin kaunana rai , sai na tarar da wannan matar taka na nuna mata waye bos Mu.azam!

Wardugu dai bai ce da shi komai ba har ya fita a motar ya tsaya yana kallonta kafin ya bude mata gidan bayan ta shiga mot

ar jikinta a sanyaye ta gyara hijabinta ta kai dubanta Wajen Wardugu,

Yana son magana da ita wanda zai fuskanceta, ya sani shi ya dace ya koma baya ko dan saboda gaban ana iya kallon su ta gaba du wanda zai fice, aman wani abu ya tsaya masa ya hana shi

fita ya koma bayan motar,

Dakewa ya yi , ya ce" dawo gaba.

Agaishat dake duban gaban motar ta kai dubanta wajensa, a ranta fadi take" shi koda yaushe fuskarsa ba wani fara.a zai wani tantankewa yake yiwa mutane, to ni me na yi masa ?

A hankali ya

dago da kansa ya juyo fuskarsa dan bai ji ta motsa dan bin umarninsa ba,

Kamar na dazu yanzun ma idannuwansu ne suka sarke da juna, a tare gabansu ya shiga luguden duka ,

Wannan karin Wardugu kasa cire idannuwansa ya yi a nata , tsai ya tsaya cikin kogi

n idannuwanta yana mai jinsa baki daya a cikin idon,

Da sauri Agaishat ta janye kwayoyin idannuwan nata a nasa ta shiga kokarin bude motar hannayenta na rawa baki daya tana neman nutsuwarta na neman gagararta,

Bude motar ta yi ta fita, shakar sansan

yar iskar duniyar ta yi kafin ta juya da dukan kuzarinta ta bude gidan gaban ta shiga,

Shi kam binta kawai yake da kallon da bai ya kureta da shi har haka ba, sam bai san yanai mata kallon da ya fice ka.ida a adinnance ba,

A hankali ta ja ta rufe ko

far, aman wannan karon ta gagara dubansa cikin ido kamar yanda shi ya tsareta da idannuwansa wa.inda ta rasa gane me yake kallo,

Zuciyarta ke ingizata da ta dube shi, domin bayan ta dawo gaban ma ya yi shiru ne bai ce da ita komai ba, hakan ya saka a ha

nkali ta kuma buda dara daran idannuwanta cikin nasa,

Lumshe ido ya yi ya kuma budewa kan fuskarta, haka kawai ya ji baya iya yi mata magana tun karfi ko eani gatsai gatsai, ji yayi yana kokarin sanyaya muryarsa fiye da yanda yake yiwa kowa magana a dun

iya, girmanta, tausayinta ne ya ji a lokaci guda, yana jin kunyarta wace bai san ko ta meye ba, ya ajiye hakan kan dan tana abar kaunar amininsa, tabas zai ci gaba da jin haka a tare da ita balema idan ta aminta da zuciya daya zata kular masa da amininsa,

Sangartar da muryarsa ya ci, marainiya ta zama a makogwaron sa, da kyar ya iya sarafata wajen fadin" *Kina son sa? Zaki rayu da shi?*

Ajiyar zuciya ta sauke mai cike da ma.anoni, kanta ta sada a hankali ta ce" *shi ne zabina*

Furucinta da faduwar

gabansa ba zai tantance wane ya fi wani karfi wajen saka jinnin jikinsa gudu a karfin da ya zarce yanda yake, kirjinsa ke duka da sauri sauri inda ya ji hankalinsa ya tashi, ya rasa menene haka? Me ke faruwa da shi,

Dakewa ya yi ya cire hular kansa yana

dan alamun fifita da ita, bai daina kallon Agaishat ba, ya ce" zaki iya rayuwa da shi da zuciya daya? Ki so shi domin Allah? Zaki sadaukar da komai na rayuwarki wa shi?

Dagowa ta yi ta tsurawa fuskar Wardugu ido, a hankali ta ce" *ka damu da amininka

ko ka damu da amanarka?*

Bai bata amsa ba, domin bai fahimceta ba, dan haka ta gyara zamanta ta ce" a gida, muna da Anna daya, du yaran gidan yan uwa ne, daga bakin ranar da Anna ta baiwa Ayya ni na zama yar Ayya, hakan na nufin ni kanwarka ce, baba tso

fo yace idan iyaye ko yayu kai dangi baki daya zasu yiwa yarinya aure hankalinsu a tashe yake, su ne bincike kan waye mijin? Halaya da sauransu, su ne tabatarwa idan yarinyar na son sa ne domin Allah, kai dai a firgice suke,

Dan Allah, *zaka zama yayana?*

mai saurare na? Mai share kukana kamar yanda yayuna ke yi?

Tunda ta fara labarin lebenta yake kallo tamkar mai koyon yaren da take magana da shi, a hankali ya ringa jinta a jikinsa har ta zagaye ilahirin jikinsa, wani irin nanauyan abu ya ringa ji wand

a zaka ji shi ne idan kana son abu, ko dan uwanka ko wani na jikinka sosai , farat daya Wardugu ya ji ya yi kanwa daya kwalin kwal, jal, kwara , wace yake mararin samu, ya jima yana son samun kanwa daga mahaifiyarsa dan ya shagwabata , ya ririta ta, ya san

garta ta, ta fi yar shugaban kasa gata, a yau a yanzu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login