Showing 57001 words to 60000 words out of 86237 words
mai dauke da dara daran idannuwan da a kowani yannayi kike su kadai sun ishi mutun, Agaishat Allah ya tsara ki da hanci mai tsayi mai yan kofofi
wanda ya yi das da dan madaidaicin bakin ki,
Rashin hayanniyar ki ya hadu ya kara kawata halitar ki, ke da ba dan kar na kauce hanya ba da na fada maki sauran tsaruwar ki,
Dan dakatawa ya yi gannin yanda ta zuba masa ido, sai a lokacin ya tuna ya saki
baki sai zuba yake mata,
Dan kimtsa kansa ya yi a hankali ya ce" Agaishat arrrakam (Agaishat ina son ki),
Wata irin faduwa gabanta ya yi, da wani irin firgici ta akle shi, tsoro, mamaki, surprise, murna suka hade suka saka jikinta ya dan fara rawa, So
na? Ji ta yi wani nauyinsa ya diri mata,da sauri ta sada kanta kasa, kafin take mikewa da wani irin sauri ta jua inda Mu.azam ya mike yana kiran sunnanta daidai Wardugu ya yi kokarin kawar da kansa dan kar su ganshi bayan ya jima wajen,
Ganninsa ta yi
yana ta faman taba labulen ayya wanda ke gyare tsaf a wajen aman kamar wanda yake gyara shi,
Kanta ta shiga sosawa kafin take dan rabar gefensa ta shige ta taka matatakalar da gudu gudu ta nufi dakin ta,
Da ido ya bita, da wani irin kallo, a hankali
ya lumshe idannuwansa ya juya ya fice a dakin ya nufi wajen mu.azam da ya koma ya zauna ya dan dafe kansa da hannunsa cike da tsoron kar a je ta ki karbar sa,
Gaban wardugu ya ji na wani irin gudu wanda har ya ji wata yar zufa ta karyo masa,
A dan
hanzarce ya karasa wajen amininsa yana mai cike da zulumin yannayinsa, a nitse ya kai hannunsa ya ce" Mu.azam?
Agaishat na shiga dakinta ta karasa da sauri wajen madubi, lufayar jikinta ta warware ta tsurawa kanta ido, du abinda ya fada take son gani
sai dai ita bata wani gannin kyanta, , .....
A hankali ta kai zaune ta cuje abinda ta daure gashinta da shi wanda hakan ya baiwa gashin damar zubowa baki dayansa ya yi lumbuk a jikinta, hannayenta ta cusa ta fashe da wani kuka mai zafi, a hankali, muryar
ta na rawa ta ce" Anna, ina kike? Anna wai yana so na? Ashe nima mutun ce Anna? Anna wai ina da kyau, wai nima mai daraja ce, Anna nima na yi saurayi...........tana kukan kuma ta shiga dariya a hankali ta furta" Mu.azam, nawa
😌😌😌😌😊😊😊😊😊😊😊
I.m sowi fans , jiki da jinni ne
🤦
♀
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our
ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
5
️
⃣
A hankali Wardugu ya kai hannunsa ya taba Mu.azam, murya a
sanyaye ya ce" Mu.azam?
Da sauri ya dago da kansa daga yannayin da ya afka, ya kali Wardugu da kyau kafin yake sakar masa murmushi,
Wardugu ya ce" me me ke damun ka?
Mu.azam dake dubansa ya dan sada kai, ya kuma dagowa yana dubansa ya ce" jinta na
ke a raina har jikina Wardugu, sai dai ban san ba ko zata aminta ta aure ni a dan kankanin lokaci kafin mai yiwuwa ta yiwu da ni?
Wardugu ya ji gabansa ya fadi, Allah yana ganni idan da abinda ke tayar masa da hankali a yanzu bai fi rashin lafiar Mu.A
zam ba, lamarin na girgiza shi in ya tuna, yakan tsinci kansa ba karfi bare laka a jikinsa idan ya tuna, .......
Duk da ya fahimci wa yake nufi aman sai ya kashe ido guda yana kallon Mu.azam ya ce" kai, soyaya ka afka daga zuwa garin mu? Fada mini wacece
mai sa.ar samun abokina ?
Mu.azam ya lumshe idannuwansa ya ce" Wardugu, na kan ji wani iri idan muna hira da kai a yanzu, domin du ka canza min kan da, a da idan muna hira tamkar yaki muke, ka warto ni na tsokaneka mu yi ta shirirta har sai an shiga tsa
kanin mu,
aman a yanzu du abinda zan maka sai na ga ka wani yi shiru ka kyale ni ko kuwa ka wani lalaba ni, malan matarka ne ni? Ko dan bani da lafia? Ni irin yanda muke da ya fi birge ni, sai ka wani dawo ladabi?
Wardugu dake kallonsa ya ji zuciyarsa
ta mugun karye, hakan ya saka wata zufa ta karyo masa, a yanzu da suke zaune a haka ba mamakin shi wardugun shi ne gawar fari, aman kuma rashin lafiar Mu.azam da ta bayana kanta ne ake kiran kisan mumuke, domin dai ta hana kowa walwala tsakanin mutane ukun
nan, Mu.azan din, docternsa, sai Wardugu da ya sani shima,
Wardugu ya saka hannunsa ya share gumin da yake , ya miko hannunsa kusan na Mu.azam ya ce" wa kake so? Ko yar gidan waye, ko wa take takama da shi nan duniya sai ta aure ka, kuma dole ta so ka
!
Mu.azam ya kwace hannunsa yana dubansa da yannayin tausayi, ya san waye Wardugu farin sani, wannan yannayin da yake ciki yayi imanin da ace zai samu kuka da ya koka tun karfinsa ko zai samu sauki,
Goshinsa ya dafe yana dubansa, ya ce" ka daina dam
uwa da lafiata Wardugu,
Wardugu ya katse shi da fadin" idan muka gwada aikin nan fa?
Mu.azam ya ce" bayan ka tirsasa ni shan lemun tsami cikin ruwa masu zafi, kana tirsasani cin tafarnuwa, kuma zaka bijiro da maganar aikin da na guduwa ? Wardugu aiki
n nan fa mai yiwuwa shigar da za.a yi da ni a fitar maku da gawata,
Wardugu ya ce" kuma tana iya yiwuwa a fitar mana da kai ras ka sami lafia,
Mu.azam ya ce" mafi akasari idan Allah ya yi an sami lafiar ma kwakwaluwa na tabuwa, ko a samu shafewar tun
ani, cikin kaso dari bai fi 2/100 suke mikewa garas ba Wardugu, na fi son idan ta Allahn ce zata kasance da ni nan kusa ya kasance ina kusa da mutanen da nake so suke so na,
Wardugu ya kura masa ido, kallon cikin ido, ya ce" ba zan iya ba, zuciyata mai
mugun rauni ce a kanka, ina jin rashin karfi a abinda ya shafe ka, baka yi min adalci ba idan har ka yi min haka, !
Ya mike ya dauki kys dinsa, ya dora hanayensa saman table din yana dubansa ya ce" baka isa ka min haka ba, ba zan taba barinka ka yi min
haka ba! Zan nemi karin bayani ......
Juyawa ya yi ya fice inda yake jin kansa na mugun sara masa,
Mu.azam ya girgiza kansa bayan ya bi shi da kallo, a hankali ya furta" ban so ka ji ba, sai dai rigumarka ta saka ka tankalo abinda zai hana maka nuts
uwa!, ya hana maka jin dadi!
Tukin garari ya yi wanda ikon Allah kawai ya kai shi gidansa lafia,
Yana zuwa ya sauka daga motar ya rufe ya nufi bangarensa kansa duke yana mai jin yanda yake sara masa,
Har zai bude ya shiga, sai ya fasa ya dubi ban
garen Walyn,
A hankali ya juya akalar tafiar tasa ya nufi bangarenta yana wata irin tafia wace da ka gani zaka fahimci da karfi ne ake yinta ba dan ana jin dadinta ba,
Wardugu na shiga ya zarce falonta baba inda kamshin turaren da aka turara ya yi masa
salama.
A hankali ya shige yana hangenta kwonce saman doguwar kujerar falon nata tana danna waya ranta da yannayin bace, sannan da maganin zazabi mai tafasa a gefe da alama dai ita ta sha bata jin jikinta,
Da sauri sauri ya karasa gareta yana mai ci
re rigar tasa ta sama ko zai ji dan sanyi sanyi ya karasa wajen Walyn da ta zabura ta mike tana dubansa da wani irin yannayi mai fasara abu uku, na farko ganninsa a bangarenta, na biyu yannayinsa ya firgitata, na uku mugun haushinsa da take ji domin yanzun
ma a cikin grup dinsu na manyan mata ne ake tatauna maganar har wata na ikirarin ita walahi a duniya ba wanda ya yi mata irin wardugu halayensa na kasheta da dadi, idan ta kali hotonsa takan jita a wata duniya, tunani take wannan mutumen ya kasance hazars
a a gabanta kadai ya isheta, duda an kwabeta cewar da matarsa a gidan fa , kamar an zungureta ne an tirata domin a lokacin ne ma ta ce" Wardugu ai mijin mace hudu ne wanda Allah ya halita masa ba wani shege ba, duniya kuwa idan takamarka sauko wani a can y
a kwana,
Tana wannan tunanin wardugu ya karaso jikinta, batai tunani ba ta ji ya rungumeta da karfi wanda sai da ta ji kamar numfashinta zai tsaya dan ya kanainayeta ya hana ta motsi,
A hankali ta rungume shin itama, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana
shakar turaran jikinsa wanda koda ya yi zufa bata hadewa da turaran ta bayar da wari wari, turaran ke cin karfinta bama zaka gane ba sai dai idan mafi kusanci da shi ta ji gishiri gishiri a jikinsa a irin wannan yannayi
🤣
,
Gajiya ta yi da tsayuwar dom
in daman ba wani karfin jikinta take ji ba,
A hankali ya bita saman kujerar domin shi a wannan lokacin bashi da bukatar komai sai na ya jima a jikinta , ta rungume shi, yana so ne kawai ya ji shi a jikinta ba komai ba,
Haushi Walyn ta ji, aa me wardu
gu ya dauketa ne? Jiya ya gama wulakantata, ya fanshi jikinta, ya tashi ya yi tafiyarsa, ta je saloon ta kwashi rashin mutunci dan shi, ta zo gida mata na wawarsa shi oga! Yanzu ya kuma dawo mata da bukatar sa? (Domin a tunanin ta , bukatuwa ce ta dawo da
shi a irin wannan lokacin ),
A hankali ta zame jikinta tana dubansa yanda ya yake ringeshe jikin kujerar idannuwansa du a lumshe,
Baki ta dan yatsina, a fili ta ce" ka san yau a saloon wata karuwa ke ikirarin sai ka aureta?
Daga yanda yake kwonce
yake dubanta, a hankali ya ce" ki zo gare ni Walyn.....
Ya mika mata hannunsa,
Kafadarta ta make irin na yangar nan na mata ta ci gaba da fadin" ka saurare ni mana, ina maka hira ka wani basar,
A hankali ya kai hannunsa wajen goshinsa kafin yake m
ata alama da ta ci gaba, domin ya lura kwata kwata matar tasa bata lura da yannayinsa ba, bata da niyar fara sauraronsa, zata tiso abinda ke damun nata wato *kishi da isa*,
Zamanta ta gyara tana mai dubanda da kyau ta ce" ni kuwa na bata amsar cewa , W
ardugu mijin mace daya ne, ba zai kula wace ta san mutuncin kanta bama bare ita karamar yar bariki, Wardugu nawa ne ni kadai!
A hankali, ba tare da wani damuwa ba ya ce" *wa ya yi miki wannan albishir?*,
Da sauri ta dubo shi, da yannayin mamaki ta
ce" me kake nufi?
Dagowa ya yi yana dubanta ya ce" *Auten zobe muka yi da ke?*,
Walyn ta kara zabura da mamaki ta ce" kana nufin sai ka kula wata macen?
Wardugu ya buda idannuwansa da kyau, ya ce" *To waye ni?* , an fada maki ni ba mutun bane? ,
Yanzu sai ka ci amanata Wardugu? Sai ka dubi wata macen da sunan so?
Kallon kar ki raina min wayo ya yo mata sannan ya ce" tunda hirar kike so mu yi bari ki ji, da farko dai ni mutun ne dan Adam wanda nake tara ba goma ba wanda nake cike da laifuka
, nake dauke da zuciya mugun nama, wanda na kwonta da sannin Allah ya halasta min auren hudu na jera, nake da sannin ina da wajen saka su, ina da abinda zan ciyar da su, na tufatar da su, sannan ....ya yi murmushi ya ci gaba da fadin" na
sauke hakinsu sam
an lit (bed) ba tare da gajiyawa ba! Ke kin san wa kike aure shi ya sa kike kishi! To a haka da nake, akoy wa.inda ban yi masu ba, sam bana gabansu, bana cikin tsarin da zan samu koda gaisuwarsu ne! Walyn, ana aure dan soyaya, da tausayi, dan sha.awa, dan
arziki, ba zan maki karya ba, ba zan yi maki rantsuwar ni na isa na kauce kaina daga kan *mace yar dagwas dagwas mai dorinar dukan maza ba* , ciki kuwa koda yar barikin ce da kike fadi mai yiwuwa na zama silar shiryuwarta!
Gaba daya har Walyn ta fara
fita a hayacinta , ta hayayako ta ce" me na gaza da shi Wardugu da kake kiran min sunnan wata a gabana?, *Kyau, fari, tsafta, girki, iya tarairayarka,* wane na gaza a cikin nan?
Haushi ya kara kama shi, itace ke ikirarin iya tarairayarsa bayan yanzu ya
shigo mata a wani yannayi maimakun ta dubi halin da yake ciki ta zauna a kusa da shi aa, sai ma ta tsankalo kabarun banza da wofi, kai da Walyn a wajen aikinsa take kai koda ficewa take ta hanyar da an kwashi yan kalo da ita da matan dake kai masa ziyara,
wai kuma ta yi ikirarin ita ta san kanta ita mai kyau me memememe, *Isarta* ta hanata ta duka masa yanda ya dace, takamarta da halitarta sun hanata gane ainahin biyayar aure, sai idan baki ya bude ta shiga zubo masa abubuwa mararsa tsari, dan haka da yann
ayin haushin nan ya mike yana daukan rigarsa ya ce" *Kin san dadin miya ke sakawa a yi kari!*
Wai wai wai wai , shin fans zaku kuwa iya zama da mai hali irin na wardugu
🤦
♀
🤦
♀
🤦
♀,
Su waye wardugu ke ikirarin ko arzikin gaisuwa baya samu
daga wajen su? Me ke damun wardugu?
Me ke damun kwakwaluwar Wakyn? Ta hada kyau, fari, tsafta, kanshi, girki, bata isa ta daki kirjin mijinta na ita kadai bane?
🤔
Mu.azam, zai kai labari kuwa?
Agaishat Ayya, Anna, Ba, Marahut, ya labarin su ne?
🤔🤔🤔
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the m
ind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
3
️
⃣
6
️
⃣
Rigarsa ya rataya a kafadarsa, ya juya da niyar barin mata bangarenta domin bai ga dalilin fa zai
saka a caza masa kwakwaluwa a waje, ya zo wajenta dan samun nutsuwar zucuya itama ta caza masa, yana bauwa Walyn damarta ta mace, na ta yi korafi a kan abinda bai mata ba, ya sha duba korafinta ya nuna mata ya tuba a aikantance ta hanyar daina abinda ta ka
wo masa korafin a kai, sai dai abubuwa na damunsa na irin yanda ita ba abinda ya sha kanta da damuwa da damuwarsa, bata wani damu da yannayin da zata ganshi ba indai da abin fada zata rufe ido ta fada da gatsali,
Murmushi ya yi yana girgiza kai bayan ya
kare mata kallo du ta fice a hayacinta daga wannan yar maganar? To idan Allah ya kadarto min kara aure yaya zamu kwashe da Walyn?
Rai bace tana kokarin fashewa ta kuka ta ce" Wardugu, idan ka yarda, idan ka saki, ka yi saken kula wata mace sai dai a kwa
shi gawarwakin mu baki daya! Wardugu kamar yanda Batuben namiji zai iya suka da wuka dan an kali matarsa toh zan iya suka da wuka dan an rabe ka!
Tsayawa ya yi yana dubanta, iya gaskiyarta ta fada domin a tsaye take tana dubansa ido cikin ido, jikinsa
ya ji ya dan yi sanyi, karasawa ya yi kusa da ita , ya dan sasauta murya aman a cunkushe ya ce" Walyn, bakya aiki da adini ne ke? Kin san da sunnar ma.aiki ce? Me ya sa zaki daukarwa kanki zafi haka? A haka Walyn ban ma nuna zan yin ba idan zan yi fa?
I
dannuwanta ta dago dan sakawa cikin nasa domin ya darata tsayi, ta ce" na tsinci kaina a zazafar kaunarka, haka na wayi gari na ganni zundum , na shanye wulakanci kala kala dominka, kai da kanka ka sha wulakanta ni mai girma, karaya uku ka min a gabai na,
du na shanye! Kai a tunaninka ba zan shanye azabar kawar da du wata tsagerar da ta tunkaroka ba? Wardugu, mahaukaciya ce ni a kanka! Sakara ce da a yaren ka!
, kamar yanda ka sumar da saurayin da ya yaba maka ni, ni kuwa ka yi min marin da na yi ta ihu sai
da kyar jina ya dawo dan na yi kwaliyar da aka yaba ni, haka zan iya rike makigwaron du wata yar iskar da ta yabe ka!
Kansa kawai yake dan girgizawa yana dubanta, Walyn, walyn Wardugu...ya saki murmushi ya juya,
Haushi ya kara rike mata zuciya ta d
aga murya ta ce" ciki kuwa harda wannan tsohuwar kilakin da ta ki aure take binka gida ma.aikata, anguwa! *Alhinayett*, ciki harda ita,
Dawowa ya yi ya tsura mata ido, kafin yake fadin" ki daina zagin Alhinayett domin mai