Showing 81001 words to 84000 words out of 86237 words

Chapter 28 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

13

*SAJIDA*

4





8





Da sauri docter ya b

ai Wardugu amsa gamsashiya tare da nuna masa echo din cikin, cewar bai yi kwari ba ya so zubewa aman Allah ya tsayar da shi, dan haka a kiyaye du wani abinda zai zo mata da garaje har ya zauna ya yi kwari,

Kansa kawai yake gyadawa kafin ya mike ya nufi

number dakin da aka fada masa take

Yana zuwa ya kwonkwasa , bai tsaya an bashi izinin shiga ba ya tura ya shiga,

Walyn ce zaune tana rusawa mahaifiyarta kuka inda uwar ke fadan da bai fahinci na meye ba,

Gannin mai shigowar ya saka gaba dayansu suka

i kit suka daina maganar inda Wardugu ya nuna tamkar bai ga abinda suke ba,

A hankali ya karasa wajen kujerar dake dan nesa da su inda mahaifiyar Walyn ta saki hannunta ta mike daga kujerar dake kusa da walyn din tana mai son ta bar dakin

A nitse ya

gaisar da ita inda ta amsa kafin take barin dakin tana jin wani irin haushin Walyn, ta sha jus din nan ne dan cikin ya zube, da ba.a yi gagawar kawota asibiti ba da tabas sai mai afkuwa ta afku, bata san wa zata fadawa dan ya tsoratar da Walyn ba domin ba

wanda take tsoro!

Bayan fitar mahaifiyarta a hankali ta kwonta saman bed din tana kallon sama,

Wardugu dake yi mata kallon kasa kasa ha jima a haka kafin yake tasowa ya dawo kujerar dake kusa da ita ya ja ya zauna,

Rigar jikinta ta atampa wace aka

i mata dinkin zamani ya dora hannunsa wajen mararta ya samu ya dage rigar a hankali,

Lalausan hannunsa ya dora saman mararta, a hankali ya shafa ya jara shafawa, ba zai gane komai ba shi dai yanda cikinta yake ne bai wani canza ba, tana da dan teba kadan,

ko dan an ce cikin bai girma bane?

Kalonsa ya maida wajen fuskarta a hankali tamkar bai so magana ba ya ce" ina son cikina Walyn, kema kina so?

Wani katutun abu ya tsaya mata a makogwaro, ina ita fa ba zata iya wannan lamarin ba, ka haifi dan uban

ya dawo sonsa fiye da kai, ba zata iya barin wannan cikin ba duda kuwa azabar da ta sha,

Gannin tana ta yamutsa fuska ne ya saka shi kara kusanta kansa da ita ya ce"wani waje na maki ciwo ne?

Da haushi haushi ta dube shi ta ce" tun cikin bai zama gud

an jini ba, ba.a kai ga halitarsa ba, har ka fara manta abinda ya dace ka fara damuwa da shi? Har ka fara manta nice damuwarka ta farko domin nice zahiri?

A hankali ya janye hannunsa daga wuyanta yana dubanta da wani irin yannayi, tafia ya yi ya dawo b

asu wani hadu ba, tun maganar da ta yaba masa a agadez basu wani hadu ba, shima ya shareta ya shiga harkokin gabansa, yanzu sun hadun zata wani saka shi gaba da hayaniya kamar yaronta, du irin murnar karuwar da ya samu da dokin da ya afka sai ya ji lokaci

guda ya dishe, dubanta ya yi irin na tsai din nan,

Hannunsa ya saka a aljihun doguwar jalabiyarsa ya ciro cart dinsa ta bank,

Ajiye mata ya yi nan ya juya ba tare da yace da ita ufan ba,

Tana kallonsa har ya fita a dakin,

Ba.a jima ba mahaifiya

rta ta shigo dakin tana dubanta ,

Wani uban tsaki ta ja ta ce" kin masa haukan ne?

Walyn ta dafe kanta ta dauki cart din ta mikawa uwar ta ce" Ma, ga abinda kike nema! Plz kama ki barni na ja numfashi mai dadi!

Yannayin maganar walyn, da irin furuci

nta bai taba zuciyar mahaifiyarta ba, hasalima dokin karbar tikitin bankin Wardugu ya sakata sakin murmushi ta karba ta fita da hanzari bayan ta shaidawa yar zata turo a tayata komawa gida ta karbi code number dinsa.

Bayan ya karaso gida dakinsa ya shig

e,

Yana shiga ya cire rigar da ya kusan wuni da ita ya kaita wajen injin wankinsa ya ajiye ba tare da ya wanke ba dan hankalinsa ba nan yake ba

Dawowa ya yi ya shige bayi ya yi wanka ya dauro alwallah,

Sallah ya yi a nitse, bayan ya salamce ya mika ha

nnu ya dauko wayarsa android ya kuna,

Yana kunnawa data na hawa domin baya kasheta kwata kwata,

Ba.a jima ba messages suka shiga shigowa na mutane daban daban, tun daga abokan aiki, manyan mutanen da yake hulda da su, da yawa kan harkar mota ne da yake s

iyarwa, wasun kan kamen da ya yi ne watani da suka shude, wasun baima bude ba dan bakin number ne,

Yana bin messages din yana karantawa sai dai baya bada amsa,

Nan ya fita ya shiga Facebook, roger banasaran da suke harkar motoci da shi ya masa sababin z

ubi, zubi na sababin motaci na manyan mutane,

Yana dubawa ya ga number yarinyarnan dai sai kara turo masa gayata take , a whatsupp ma sai message take turo masa tana karawa,

Fita ya yo ya koma whatsupp ya shiga message dinta,

Duka kalamaine na rarash

i, da magiyar ya kulata, da yannayin kaskantar da kai, wai ita BASMA yar gidan minister,

Hotunanta da take ta turo masa ya bude,

A hankali ya tsurawa hotunan ido yana kallo,

Kansa ya girgiza ya fita ba tare da ya bata amsa ba,

Mesage ta turo kamar h

aka" du bakin da zai furta kalmar so ba makiyi bane, sannan adini bai haramta mace ta nuna tana son namiji ba, kuma ni ban roki wayar gari da kaunarka ba, kar ka ja zuciyata a kasa dan Allah ya baka dama,

Mesage din yake bi yana karawa, bai iya bata w

ata doguwar amsa ba sai mikewa ya yi da wayar a hannunsa ya haye saman bed dinsa ya kwonta ya jawo pilow ya dora kansa, a ransa ya ayyana" haka fa suke idan suna so, da dama ta same su sai su fara gwada halaya na rashin tarbiya da hadama,

Yana kokari

n neman baci wayarsa ta shiga ruri,

Kansa ya shafa yana jan tsaki,

Kin kula wayar ya yi sai da ya ga mai kiran ya fishi naci ya dauko wayar ya daga yana fadin" ai aikin nan sai kai daman!

Mu.azam ya yi murmushi, ya ce" me tace da kai Wardugu,

Ward

ugu ya yatsina fuska ya ce" wace fa?

Mu.azam dake zaune yana hangen shige da ficen Agaishat kicin tana girki ya ce" wardugu mana, bakuwata man

Wardugu ya bude idannuwansa ya ce" meye tsakaninka da ita bayan amintaka?

Mu.azam ya yi tsam gabansa na

dan faduwa, a hankali yake goge zufar da yake ya ce" amintaka ce mafi kusanci,

Budurwarka ce? Wardugu ya kaste shi,

Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya, ya kasa magana hakan ya tabatarwa da Wardugu zarginsa

Ransa ne ya ji ya mugun baci, hannunsa ya jim

ke ya kaiwa garu duka ya kausasa murya ya ce" dan me ka shigi yarinyar mutane bayan ka san amana ce?

Mu.azam ya mike zumbur dan yannayin muryar Wardugu ya shaida masa ransa ya baci,

A nitse ya ce" ka kwontar da hankalinka Wardugu, bamu yi soyaya da ita

ba, itace ke so na, bamu tana soyaya da ita ba, ban zowa Agaishat dan na cuceta ba, kuma ba zan taba gigin cutar nata ba,

Wardugu dake tsaye shima ya dafe gaban goshinsa, baya jin zai baiwa Mu.azam amsa a wannan maganar,

Mu.azam ya ce" Wardugu, dan

*ina sonta* na aureta,

Wardugu ya matse karfen jikin bed dinsa yana rintse ido, kansa yake ji na mugun sara masa, hakama juwa na dibansa,

Mu.azam ya kara sasauta murya ya ce" ina son mu tafi , na san ka san komai game da abinda yarinyar nan ta zo da

shi, Wardugu koda ban auri Khadija ba tana da darajar da ba zan misalta maka ba a raina, tamkar yar uwata na fauketa kamar yanda na dauke ka, zan bita a min aikin nan, idan Allah ya yi na rayu zan tashi na rayu da *Matata*, idan ban rayu ba na san zaka ku

la da *Iyalina*, gobe ake bani passport din Agaishat, Khadija bata zo ba sai da ta shirya domin komawata da shigana block duka ta irga min kwana tara ya yi saura, Wardugu ka......

Wardugu ya katse shi da wani irin yannayi ya ce" *Zaka rayu in sha Allah*!

Ku ci gaba da shirin tafia, in sha Allah ina nan za.a shiga aikinka, zaka rayu Mu.azam......



😔

*



IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO

🌤

*

____________________________________________



*Fad'akar da al'umma tare d

a nishad'antar da masoya shine fatanmu*

😘🤝🏻😘

🐫🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫🐫

Na

*SAJIDA*

4





9





Bai jira amsar Mu.azam ba, Wardugu ya silale yana

dafe kansa, a fili ya furta" *ban shirya ba, ba zan iya dauka ba, bani da karfin kokowa da hakan, sannan haramun ne a gareni, ya Allah baka dorawa rai abinda ba zata iya dauka ba, Allah ka cire min wannan gingirmin mikin , domin ni dai ban saba ba*!!!!!

Timiya

Duniya sabuwa ce ta budewa Ba, wannan karon da sabon salo domin kuwa tafe yake da isa da takama da nuna kansa a matsayin uban *BAk'a*,

Anna dubansa kawai take idan yana abubuwansa, bata taba buda bakinta tace da shi uffan ba

, a cikin kudin ya basu million guda wada Mariama ta karbe , ya canza masu katifa ya kawo masu buhun dawa guda ya yar masu sannan ya shiga fakar takun Anna yana so ta koma turaka

Kamar yau, zaune suke su hudu domin Gaishata ta zo masu , labari suke duka

yawan zancen a je a dawo ne a tile kan maganar Agaishat,

Anna ta sauke ajiyar zuciya tana dubansu ta ce" mahakurci mawadaci, du wanda ya ce zai yi hakuri Allah ba zai bashi kunya ba, sannu sannu kuma bata hana zuwa, sai dai a jima ba.a je ba,

Gaish

ata ta yi murmushin itama da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe ta ce" ni abinda ke bani mamaki Ba, wai shine har yake yi mana kallon mutunci?

Mariama ta tabe bakinta ta ce" na dan lokaci ne, idan kudin hannunsa ya kare zai dawo kamar da,

Anna ta

ce" ki daina mumunan zato Mariama

Mariama ta yi mata wani malalacin murmushi dan kar ta yi fada,

Suna tsaka da zancen sai gashi ya shigo yana jan arzizimin wando bakinnan kuwa jajajir sansani su ta bata shi,

Bai yiwa yaren magana ba sai Anna ya

kalla ya yi kiranta ya shige dakin

Da kallo suke binta dan gannin zuwa zata yi kuwa?

Gani sukai ta mike ta nufi dakin ba tare da ta yiwa kowa cikinsu magana ba

Tana shiga ya damko hannunta yana washe baki ya ce" Ke bakya marmarina? Kin jima baki n

eme ni ba, kin ga baki fice haihuwa ba, ki zo mu kara samun wata Bak'ar, ina son samun yarinya a gidannan,

Sakai kawai ta yi tana dubansa, kanta ta girgiza ta janye hannunta ta juya da niyar barin masa dakin

Ba da yannayin fushi ya ce" in kika yarda

kika fita a dakin nan , sai na nuna maki na fi yan yamai *Niamey* iya rashin kunya!

Wani irin birki ta ja ta juyo da madaukakin tashin hankali da kuma tsoron da ya bayana karara a fuskarta,

Bakinta ta buda zatai magana sai dai ina jini ne ta shiga bi

n hancinta, juwa ta kwasheta ta zube nan tana fida wani irin numfashi

Karar faduwarta ya saka Mariama mikewa domin da marfin kwano a hannunta marfin ne ya kai kasa ya bada kara wanda sam Mariama bata yarda da shi ba dan haka da hanzari ta fada dakin tan

a mai kiran sunnan Anna,

Tana shiga daidai Ba ya kai kasa zai kamata jikinsa sai rawa yake,

Da mugun gudu da taratsi ta ce" kar ka tabata, kar ka taba mini uwata!

Bai sanma tana yi ba, shima fama yake ya ga ta mike, yau dai haukansa ya kaishi taka

dokar da aka dodora masa na ya kiyaye kama mata sunnan garin haihuwarta, ya kiyaye du abinda zai alakantata da garin makarin duhun kan Anna shine Ba ya kusantata da asalinta, ya kama sunnan garin haihuwar Anna garin neman jarabarsa,

Ihun da Mariama ke y

i masa ne ya saka yan uwanta shigowa suma a guje sunna nufar inda Ba da mariama ke turayar juna kan sai sun taba Anna

Gaishata ce ta dora hannayenta saman kanta da karfi ta ce" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Ba Mariama ku dagata ku dagata na ce!

Tsai Ba ya yi , jikinsa na rawa ya nufo Gaishata tamkar zai maketa ya raba ta gefenta ya fice a gidan yana dumumuwa shi kadai ,

Da kyar suka iya cicibata domin Gaishata ba wani kokari zata iya yi ba sai su biyun ne suka iya kamata suka dora saman tabar

mar kaban dakin

Hurhutu suke mata suna shafa mata ruwa aman ko motsi, sai numfashinta dake fita a hankali iamar a cicire ta samkame ita ba gawa ba ita ba rayaya ba,

Gaishata ce ta ciciba ta mike tana jin yanda mararta ke wani irin juya mata ta nufi k

ofa tana takawa da kyar tana saurin da zata iya ta nufi fada

Tunda ta karaso dogaran sarki ke mata sannu inda aka sakar mata hanya ta shige fadar suna mamakin ganninta domin sarki ya hanata zuwa fada kar a kake masa ita,

Kanta tsaye ta nufe shi inda

ya mike da sauri daga kujerar mulkinsa dogarai suka shiga baza manyan rigunansu suna kare su, yan zama fada suka fara darewa da sauri sauri

Tana isa jikinsa ta zube wanda sukai taga taga dalilin kibar da ta kara ga kuma tsohon ciki,

A hankali ya samu

ya daidaitata a jikinsa ya dora hannunsa inda ta dora nata wato saman cikinta da take ji baki daya yana wani irin yamutsa mata bayanta na sarawa,

Me ke damunki Gaishana,

Ya fada yana mai nuna tsantsar damuwarsa da tashin hankali, yanaiwa Gaisha soyaya

mai karfin gaske,

Da kyar ta iya sauke ajiyar zuciya muryarta na rawa ta ce" Anna ce, Anna ce ta fadi, kuma tana numfashi aman ta ki farkawa,

Rigarsa ta jimke jin ciwon na tsananta ta ce" idan wani abin ya sami mahaifiyata zan shida duhu sarkina

👏🏻

Zaunar da ita ya yi saman kujerar ya cire babar rigarsa ta turkudi ya rufa mata ya yi gyaran murya,

Dogari ne ya amsa masa,

Sarki ya ce" ka je wajen jakadiya ingozoma ka fada mata Gimbiya na Daka.

Da gudu ya juya inda sarki ya daga karewar da ak

ai masa ya fita da niyar zuwa gidan su Ba, yau kam za.a yita ta kare, ba zai yarda haka ana tayarwa matarsa hankali ba, ! Gashinnan tashin hankali ya sakata nakudar dole,



*Niamey*

Tunda Ayya ta fara magana tana duban

Agaishat da dukan kulawa kan Agaishat ke kasa tana zubar da hawaye,

Abaya ce baka mai shegen kyau , bata da wata kwaliya sai zif din da ya hadeta a jikinta, gyaran fatar kwana biyun da Ayya ta yi ta dilketa ya saka fatarta ta kara wani haske da santsi wan

da ko a ido ka dubeta zaka ga ta gyaru iya gyaruwa,

Dan kwalin Abayar ne ke dan zamewa tana rikeshi har ya kai karfinta ya kare ta sake shi ta duke sosai tana kuka inda gaba daya jikinta ke jijiga

Idannuwansa ya rintse da karfin gaske, sannan ya jimki

kujerar da yake kai,

Kansa ya juyar gefe yana jin saukar kukan nata tamkar ana narkar masa da dalma a kahon zuciya,

Mu.azam dake gefensa shima cike da tausayin matar tasa ya mintsini hannun Wardugu yanai masa nuni da ya yi wani abin mana?

Wardugu y

a juyo inda take suke Ayya na rarashinta itama na sharar hawayen ya hade fuska sosai ya ce" ke!

Yannayon yanda ya ambaci ke din sole ka tsorata, yannayi ne ya garwaye da halin da yake ciki,

Da sauri ta juyo tana kara shigewa jikin Ayya,

Mikewa ya

yi ya ce" mu je!

Da sauri ta waigo wajen Ayya, wace rake cikin damuwar rabuwa da yar tata, wace kamar da wasa shakuwa mai girma ta kara shiga tsakaninsu,

Tun jiya ya dace su tafi aman cikin ikon Allah Agaishat ta rikice ta yi ta kuka har zazabi ya ruf

eta wai ita ba zata bisu ba,

Ayya ta yi gargadin ta yi fadan, ta dawo lalaba tana mai shaida mata tamkar suna tare ne, ga waya, ta bi mijinta zai dawo da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login