Showing 33001 words to 36000 words out of 86237 words
dai ya kara yi masu, ya ce" na yi rashin lafia ne Ayya, kuma yanzu alhamdulilah na samu sauki,
Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" na tsorata da yannayinka, ka wani rame, ba komai haka ne idan jiki ya tabu sai a hankali
aman yanzu ka zo kennan sai na ga yarona ya koma yanda yake da koma ya fi haka kafin ka bar gidannan,
Wardugu dake kallonsa ya shafa kansa shima kwata kwata bai yarda da maganar Mu.azam ba! Kai haba a irin yanda suka san juna Mu.azam ba zai layance m
asa ba
Mikewa ya yi ya nufi kofa da wayarsa a hannu inda suka bi shi da kallo,
Mu.azam ya ce" Ayya ya tafi fa kennan??
Ayya ta daga kafadunta ta dan yatsina fuska ta ce " ya gaishe su!
Mu.azam ya yi dariya yana kallonta, a ransa kuwa dadi yake
ji yannayin, kai yana jin dadin zama da su, Wardugu rikitace, mahaifiyarsa ta iya zama da shi, ta kai ta kawo ne idan tama da bukatar ganninsa a wayarsa ya yi mata activen localization, du inda yake idan ta shiga nema za.a nuna mata kawai sai dai ya ganta
kuma sam baya gigin kashewa doka ce!
Suna tsaka da tataunawa mai aikin Ayya ta shinfida ledar cin abinci ta kawo abincin ta ajiye, ta kawo kayan zubawa da na sha, ta kawo su jus na gida da Ayya ke yin abinta da kanta ta saka a frij du ta ajiye, Ayya ta
umarci Mu.azam da ya sauko bara ta dubo yarta.....
Wardugu ya dawo, bayansa *ALHINAYET* kawarsa ce ke biye da shi,
Salama ta yi ta shigo dakin inda Ayya ta tsaya ta saki baki tana kallon Wardugu da Alhinayet din,
Alhinayett na zuwa ta shiga gaisa
r da Ayya cikin yannayin ladabi da mutunta mutun,
Ayya ta dan kebe baki, ta amsata ta juya dan dubo Bak'a
Mu.azam dake zaune ta juyo ta dafe habarta ta ce" su likitoci ne a garin namu???
Mu.azam ya sakar mata murmushi ya ce" lauya, lauya, lauya ma
i kunce mai laifi , zamani lauya iko, lauya mai saka kato ya duka,
Kai ta dafe ta ce" wace ni, rufani ka sayani, ai ba dan an san ni aminiyar *Aboki* bace da an fige ni a Niger!
Mu.azam ya ce" kai ai rigimama ta san waye *Oga*
Wardugu ya girgiza k
ai yana zama ya ce" *ALHIN* ki zauna mu hau wannan abubuwan kafin ku ci gaba da kirar da kuka koya!
Alhinayettt ta je kusa da Wardugu ta zauna tana fadin" General ka duba lamarin nan je ten conjure................(plz)
Wardugu ya kaleta zai yi magana
sai ga Ayya ta dawo da Agaishat,
Doguwar riga simple irin ta zaman gida ce Ayya ta bata, bayan ta saka ayya ta bata Dan kwalin rigar nufin ta yane kanta sai dai suka hau rigima kan aa dan Allah ta bata hijab,
Gannin sai su bata lokaci ne ya saka Ayyar
bata hijab ta zumbula suka sauko,
Sai a lokacin Agaishat ta duka ta ce" ina yinin ku,
Alhinayettt da Mu.azam ne suka amsa inda Wardugu ya kebe bakinsa bai wani amsa ba aman yana yi mata kallon tsaf, a ransa yake ayyana black, but ko a baki *BUZU M
AI KYAU NE*
πππππ€ͺππππππππππ€ͺπ€ͺπ€ͺ
na fada a zo a dake ni
π§π§π§π§π§π§π§π§π§π§π§π§π§
May be 23......zuwa dare in sha allah, idan comment ya birge ni
ππππ
ππ€£
π«π«π«
*BAK'A CE*
π«π«π«
Na *SAJIDA*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§
ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*
π
KAINUWA WRITERS
β
πΌ
ASSOCIATION*
π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_________
___________________________
2
οΈ
β£
3
οΈ
β£
Waje Ayya ta samu ta zauna , nan Agaishat ta je kusa da ita sosai itama ta zauna ya kasance an saka baban plateau din a tsakiya,
Ayya ce ta bude inda abincin yake, tuwon tsaki ne
da miyar kubewa wace aka yita da naman shanu ta sha dadawa da kayan miya
π
..ga kuma man shanu na kirki a gefe,
Sai su fruits da aka hi masu yanka mai kyau aka sasaka cikin plat plat, sai jus da ruwa,
A hankali Ayya ta dauko abincin, Agaishat ta dauk
o abin zubawa,
Cikin wannan banban plateau din Ayya ta zuba abincin ta daidaita miyar, ka.ida ne in dai ka zo gidan Ayya daidai cin abinci bata raba assiete, sai dai a hadu a ci a abu guda .......
Bayan ta zuba ta kare Agaishat ta kawo abin wanoe hann
u da kuma cokula a wata yar roba,
Gaba dayansu cokulan suka dauka banda Agaishat da Ayya , hannayensu suka wanke ....
Ayya ce ta fara saka hannunta, sai Wardugu, sai Mu.azam, sai Alhinayettt, sannan Agaishat dake karamar cikinsu, hakane gidan Ayya ba
ba ke fara saka hannu cikin kwanon cin abinci sannan yaro ke rike kwanon dan kar ya ringa yawo, ba.a magana idan ana cin abinci, ba.a dane danen waya, ba.a wani kale kale sai an gama, sannan bata yarda ana tsaka da cin abinci ana shan ruwa ko jus, sai an g
ama ake sha, sannan ana cin abinci daidai ne ba.a matsawa ciki a yi mugun koshi, lamarin gidan Ayya sai yayanta (
π€£
),
Abincin nan ake ci cikin nutsuwa, Alhinayettt ta kure Agaishat da kallo, sam batai mata kama da tubawa ba, sannan ba bahausa bace ko
daya duda hijabin dake kanta gaban goshinta lufluf yake kwonce da gashi, girartama wani irin gazar gazar da ita, du bakinta lebenta haske ne da shi tas tas, ga girar ido ga manyan idannu, wannan cikin biyu daya ce ko bakar balaraba ko bakar buzuwa!
Al
hinayettt dai ba wani yawan zuwa gidan Ayya ba take ba, sukan hadunsu ne da wardugu a wani wajen, yanzuma zuwa ta yi da rigimarsu ta kansu wace ta zo su yi kan irin yanda ake cece ku ce a gari na matarsama idan ta cika dare kwanan cel take bare wani banza!
Alhinayettt kwata kwata ta manta zancen ba.a magana idan ana cin abinci gidan Ayya dan haka ta kali Agaishat da kyau, haka kawai ta yi niyar yi mata magana da buzanci dan ta gaskata zatonta,
*ABZIN?* , ta fada tana kallon agaishat,
Agaishat da ta
hadiye abinci ta kaleta itama, itama ta so ta ayanna hakan cewa wannan buzuwa ce, gannin yannayinta sai dai bata fadi ba dan ba wajen fadin bane,
Ai kuwa Agaishat ta washe baki itama da yaren buzancin ta maida mata cewa" eh , ke fa??
Alhinayettt zat
a maida mata maganar Wardugu ya tsimki hannunta na dama dake kusa da shi, sannan ya zabgawa Agaishat wata muguwar harara wace ta sakata sada kanta hannunta na rawa rawa,
Ayya yatsina fuska ta yi bata yi magana ba,
Sai da aka gama mai aiki ta shiga kw
ashewa, Agaishat na tayata kaiwa komai wajensa ta dawo ta zauna kasa kusa da kafar Ayya,
Wardugu ne ke kallon wayar Alhinayet tana nuna masa hotunnan birthday dinta da ta yi baya nan yana dan murmushi kasa kasa ya ce" Alhinayettt , ina tunanin kin girma
ashe dai na daina tunanin nan?
Alhinayettt ta yi dariya ta dora hannunta saman nasa ta ce" na baka ka sha? (Irin su taba zata bashi wani labarin)
Ai kuwa Wardugu ya dan cafke hannunta yana sauraronta, inda ya bata hankalinsa suna ta hirar su,
Ay
ya ce ta dan ja tsaki, ta girgiza kai tana kallon Mu.azam ta ce" kana ji? Zamani ya zo mana da abubuwan mamaki, sai ka ga mace na tafawa da namiji, tana raba jikinta da nasa wai a zuwan mutunci kawarsa, !
Mu.azam ya zaro ido yana kallon Ayya, a fili k
uwa ya furta" Lah, yana dafe bakinsa,
Wardugu da ya gama jin komai ya saki murmushi yana kallon Ayya, ya ce" Ayya, qna abota mace da namiji, abota sak ba wani soyaya ba kuwa,
Ayya ta juyo bangaren su a takaice , daman jira take wani abin ya hada su t
a ce" wardugu ba abota ba dai yayan awaki! Nace yayan awaki, Ke yanzu Alhinayettt kike ko wa? Aman ke marainiya ce ko? Ina nufin mahaifiyarki ta rasu?
Alhinayettt dake kallon Ayya a dan tsorace ta ce" Aa Ayya,
Ayya ta dafe habarta ta ce" Toh abin mam
aki, aman ita baku rainata kamar yanda kuka rainani ba ko? Ina nufin Wardugu baya zuwa gidan ku a matsayin aboki sai saurayi?
A tare suka kalli juna Alhinayettt da Wardugu, suka maida dubansu wajen Ayya,
Ayya ta ce" to in ba haka ba, ya za.a yi ni i
na mahaifiyarki , kato ya ringa zuwa wajenki a matsayin aboki kuma na zuba ido yarinya kin kai kin kawo min a gida?
Wardugu ya shiga gyada kai yana kallon mahaifiyarsa, ta jima tana son aikata wannan aika aikar wa zumuncinsa da Alhinayettt, yau dai ta
yi hankalinta sai ya kwonta kuma ko?
Ayya kamar zugata ake sai magangannunta take son ranta karshe ta ce" to ni ba tsohuwar banza bace, in sonta kake ka fito a mutun ka fada ku daina boyewa Allah kadai ya san tsakanin ku! Dan haka tun wuri a fasa dauka
na a wata marar ilimi ana ce min wai kawa! Aa abokiyar tagwaitakarka ce Wardugu!
Wardugu kallon Ayya kawai yake, inda Alhinayettt ta dan sada kanta kasa, a ranta ayannawa take ita bata ga laifin zumunci da suke da Wardugu ba, walahi da soyaya suke da
ba haka ba,
kwata kwata ba wani zance wai shi soyaya tsakaninsu, haka kawai Allah ya hada jininsu suke mutunci, Wardugu bashi da shamaki a gidan su, hakama saurayinta wanda zasu yi aure suna mutunci da Wardugu, aman haka ne itama kakarta ta sakawa zumuncin
su ido har sun mayar da ita tamkar mahaukaciya domin idan sun ga zata fice sai su shiga magana kasa kasa da yaren french ai kuwa ta kama zage zage tana fadin ita za.a munafinta? Toh gashi itama maman Wardugu kallon masu soyaya take masu bayan ita koda bind
iga ba zata iya soyaya da wardugu ba domin ta san waye shi, Wardugu dan yana son ki ba zai hana ya yi maki dukan mutuwa ba, dan yana son ki baki fi hukunci a wajensa a gaban koma waye ba, hum soyayama da wardugu ai tashin hankali ce, ita mai ya kaita? Ta f
i son namiji marar rigima mai bata damar ta yi rayuwarta cikin aminci........
Wardugu dake kallon Ayya tar, ya maida dubansa wajen Mu.azam ya ga sai gumtse dariya yake,
Kansa ya girgiza ya maido dubansa wajen Ayya, da hannunsa na dama ya daga ya sara
mata, sannan ya yi mata nuni da ta ci wasanfa , ta more abinta,
Hannunsa na hagu ya mikawa Alhinayettt ta mike itama ya ja hannunta tana waiwaye tana so ta yi hira da agaishat aman ya jata kiiii sukai waje
Kusan motarta suka tsaya,
Alhinayettt bata
bi ta kan fadan Ayya ba, bata nuna damuwarta ko a fuska ba, ta ce" Wardugu, rigingimunka sun isheni haka, ya isheka malan!
Wardugu ya shiga gyada kai yana kallonta bai bata amsa ba,
Ta ci gaba da maga domin ta san ba amsar zai bata ba, ta ce" ta ya z
aka saka Walyn kwana a cel? Wardugu ina jin zafi idan na ji ana fadin baka da sasauci, baka wasa, baka sulhu, Wardugu matarka ce fa? Ya kake so mutane su fasaraka??
Wardugu ya tsura mata ido kawai,
Ta ci gaba murya a sanyaye" ka daina Wardugu, ina so
idan na zo waje na tarda ana fadin alkhairi a kanka, ina so idan ana maganarka ta kasance ana yabonka Wardugu, ka ringa sasauci freind,
Wardugu ya yi mata dan murmushi ya miko hannunsa ya dungure mata kanta bai ce mata komai ba,
Alhinayettt ta ce"
Wardugu ina kula samu buzuwa??
Wardugu ya yatsina fuska ya ce" hum, Ayya ce ta daukota wai ta yi y'a,
Alhinayettt ta ce" yarinyar ce ta birge ni, irin yanda tana buzuwa , bakar buzuwa aman bata bata bakinta ta hanyar shafe shafe ba, ina son mutun hak
a walahi.....
Wardugu ya daga kafada ya ce" daga kauye, can cikin kauyen kauye fa ta fito, inama ta ga man bale ta shafa? Allah dai ya sa idan ta dan waye ta zama dan kauye ya fi na birni shegantaka....
Alhinayettt ta ce " sai dai idan ba tare da Ayya
take ba, Ayya ce zata wani bari haka ya faru? Yarinyar ce innocente, dan Allah ka hada ni da ita mu zama kawaye,
Wardugu ya waro ido, a fili ya furta" kawaye? Ki kirani aboki kuma ki yi kawance da wannan? Aa!
Alhinayettt ta yi murmushi tana kai ma
sa dan dukan wasa ta ce" ina son ta zama kanwata ne Wardugu, ina son na kara nuna mata shafe shafe karma ta saka kanta, sannan na kara wayar da ita......
Kafadunsa ya daga irin ita ta gano, kafin yake bude mata motar ya yi mata nuno da ta shiga
Dariy
a ta yi ta shiga , ta kunna wato dai ta ishe shi da magana ko?
Hannu ta daga masa, ya yi mata nuni da sai ya zo , ta tayar da dankareriyar motarta ta kama hanyar makarantar kannenta dan ta dauko su ta mayar da su gida
Komawa Wardugu ya yi, yana shig
a ya tarar da su sai labari suke suna dariya abinsu, Mu.azam kuwa ya kasance du motsi sai ya kali Agaishat dake zaune tana kallon Tv kuri, ita har yanzu mamaki take mutane a cikin wannan allon suna ta magangannu suna komai abinsu, har bayan take lekawa wai
ko zata gansu ta nan ta sha yiwa Ayya tambayar kuma yanzu idan suka fito fa? Yanzunma Ayya ta kuna mata wakokin dandali, kalo take tana ta sakin murmushi kumatunta na lotsawa dimple har biyu a fuskarta, wani wajen sai ta rufe fuska idan namiji ya fara raw
a, sosai take dan gane hausar da suke tana kara koya ta nan, shi kuwa abin na birge shi, sannan ya yiwa Ayya tambayar wacece ita? Da french, ayyarma ta shiga kora masa bayanin komai.....ya sha mamaki, ya ji wani lamari a tare da yarinyar, yana son inganta
rayuwarta......
Wannan kennan.
Wardugu na zuwa ya ce" tashi mu je,
Mu.azam ya mike ya bi bayansa suka nufi dakin Mu.azam din , Ayya ta yatsina fuska a ranta ta ayanna mai yiwuwa ya yi fushi
π€£
.
Suna shiga Wardugu ya ce" c'est bon, maint
enant tu me dit la veritΓ© sur ce qui t'arrive ( ya isa, yanzu sai ka fada min abinda ke damunka!)
Mu.azam ya tsare shi da kallo, a hankali ya zauna saman kujera yana kallon Wardugu,
Wardugu ya karaso ya zauna shima, ya ce" ka san dai kana iya yiwa k
owa karya banda ni! So ka fada min tun kafin na hasala Mu.azam, wata irin cuta ce wannan wanda baka taba yi a gabana ba ta zugeka haka? Me ya samu kasan gashinka ? Kana tunanin ban lura ba? To gashinan kasan gashinka a aske! Sai ka janyo sauran ka rufe, du
ka zama wani iri? Ka duba fa ka gani wandon vest ne a jikinka ka dauko riga rose (pink) ka saka sai kace mace? Hannunka ba agogo, yannayinka na nuna kama tare da damuwar da ta fi karfin furucinka, ina hawa aiki karfe goma na dare, ka fada mani na juya!
Mu.azan da wata irin murya ya ce" Cancer du cerveau ke damuna..... (cancer ta kai)
Wani irin tsam Wardugu ya yi, ya kaste maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurbat ya mike yana duban Mu.azam, hannayensa duka biyu ya saka ya dafe kansa, baya
baya yake ja ya......
π«π«π«
*BAK'A CE*
π«π«π«
Na *SAJIDA*
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*
π
KAINUWA WRITERS
β
πΌ
ASSOCIATION*
π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain &
motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2
οΈ
β£
4
οΈ
β£
Wani irin tsam Wardugu ya yi ya katse maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurb
at ya mike, duban Mu.azam yake da wani irin kallo, hannayensa duka biyu ya kai saman kansa ya shiga yamutsa gashin kansa , baya baya ya shiga yi da kafafuwansa, bai fi taku hudu ba ya tsaya ya juya ya juyo, hanunsa ya jimke ya daki dayan da shi,
A hargit
se ya dawo wajen Mu.azam, so yake ya zauna aman ya kasa...... murya a cinkushe ya ce" yaushe, yaushe? Yaushe ka sani? Ya aka yi ka sani?????
Mu.azam ya mike yana dan sakar masa murmushi yana kokarin ganin ya saka shi ya dan nutsu aman ya kasa kama shi,
dan haka ya tsaya yana kallonsa ya ce" Wardugu, har na kai wajen da gashina baya zama fa, ya jima a jikina ciwon ....nima ina gannin alamu a matsayina na likita sai dai ina turewa na ki maida hankali, ya kai ni sai na suma na yi awani a sume, na daina shig
a tiyata ba yau ba, ina zuwa asibiti ne dan kar imanina ya yi rauni, ina zuwa ne dan haduwa da wa.inda suka fi ni damuwa, ina yi mana adu.a a tare, Wardugu idan