Showing 75001 words to 78000 words out of 86237 words
na cefa ne, sai da ya dire ashirin wanda zuwa lokacin Ba sai zufa yake jikinsa na rawa yana fitar da harshe tamkar kare shi ya ga kudi,
Wardugu ya ce" bata mutu ba, da ranta da lafiarta, aurenta zak
a bamu, ga gudin auren nan idan kuwa sun yi kadan a karo! Domin *Darajarta* ta fi karfin a yi cinikinta! Ta fi karfin a aureta dan kudi, *Agaishat* na da daraja a idannuna!
Gaba daya dubansa suke, magana ne yake daga zuciyarsa, fuskarsa ta nuna wani ya
nnayi mai wuyar fasara, ba zai iya jure wulakancin Ba a wannan halin ba, sannan ba zai iya biye masa su yi ba dadi ba ko dan albarkacin haihuwar Agaishat da ya yi,
Wani irin rawa jikinsa yake, auren bak'a da sadakin da ba.a taba bashi ba na sauran yaya
nsa?
Wani irin zama ya gyara yana fadin" ai kawai a matso a daura domin kuwa ya shirya, ba ruwansa da tambayar da wa za.a daura, ina take? Tana so? Ina zata zauna? Waima da ranta?
Jiki na rawa Ba ya umarci baba tsofo ya yi alwalin Agaishat inda nan d
a nan sarki ya karaso da jama.ar anguwa ana ta yaba sadaki (kar abin ya baku mamaki ko ya girgiza ku, na gani da idanuwa sadakin buzuwa million arba.in na kudin nigeria bama niger ba, ana amsan karamin sadaki kamar jika hamsin aman yawanci auren garinmu k
ama daga agadez da kauyukan bugaje ana kashe kudi na mamaki wanda ba.a dauki hakan a matsayin laifi ko wani almubazaranci ba,),
A wannan rana , gaban duban shaidu, Mu.azam ya zama alwalin kansa inda Baba tsoho ya zama na agaishat, aka daura auren Mu.aza
m da Agaishat bisa sadaki mai tsoka lakadan,
Sai bayan an gama daura aure Ba ya tatare kudin nan jiki na rawa ya zube a cikin rawaninsa ya daure, bai wani tsaya ya bi ta kansu ba ya yiwa gidan tsinke sai washe baki yake yana ihun kiran sunnan Anna
inda ya yi fatali da sansanin,
Da amarya ya fara cin karo sai murkashi take ymtana rauda kai domin cikin nata mai matukar bata wahala ne, tana ta fama da kanta du ta lalace,
Tsayuwa ya yi ya tofa mata yawu a fuska ya ce" ke kadarara, jeki na sake ki!
Daidai lokacin da Anna ta fito tana dubansa sai kiranta yake yana kashe murya irin za.a tuna da din nan,
Yana karasowa ya ce" ashe *Agaishat alkhairi ce?*
Da mamaki take dubansa tana jiran karin bayani, Agaishat kuma? Ita tana tunanin rabonsa da ya
kama sunnanna da daraja haka tun rada mata shi da ya yi, me ke faruwa? Ina yarta ? Innalilahi wa ina ilaihi raj.une, sam bata daukan fara.ar Ba a alkhairi, hakan ya sa ta fito da sauri ta yi waje ko zata ga Agaishat din
Baba tsoho ta tarar yana yiwa Wa
rdugu magana kansa a sade yana sauraronsa inda jikinsa ke fitar da hucin zafi gaba daya bashinda laka tamkar wanda ruwa ya daka zazabi ya rufe shi, zuciyarda kuwa ba dadi, dandannon bakinsa daci firit, sam baya jin dadin yannayin ranar nan.
Tana zuwa ta
tsuguna infa suke,
Muryarta na rawa cikin yaren buzanci ta ce" me ya same ta?
Idannuwansa ya dago ya sauke kan fuskar Anna, duda turkudi ya rine mata fata ba wani kula take samu ba, aman idan kana neman ainahin kyau, tsararan kyau ka ja ka tsaya waje
n Anna, Agaishat kama take da ita sai dai hasken fata da ya bambanta, yaren tubanci ya juye da shi inda ya shaida mata komai cikin nutsuwa da sada kai da girmamawa,
Kunyarsa ce ta kamata, har ta hanata yi masa wata tambaya,
Kanta ta sada bayan ta hang
i Mu.azam dake tsaye ya rungume hannayensa yana kallonsu ta kawar da dubanta ta mayar wajen Wardugu,
Muryarta a nitse ta ce" *kar ka damu da bani hakuri d'ana, na saba da gannin auren yayana a wulakancema bale ita nata kun mutunta, ai dama halal malak na
baiwa Ayya Agaishat, koda a can kuka daura mata aure bani da ja, fatana zaku ci gaba da riketa da amana, sannan ba sai ka kawota ba, ka barta a can kawai bara na kawo maka sako ka bata, ka fada mata Ayya uwa ce a wajenta, ta yi mata biyaya!*
Asalamu
alaikum,
Rayuwa ce da aka yi nake bi maku, duda na rufe abu dayawa, na kuma gyara wani dan labarina ya yi ma.ana, aman kar ku manta rayuwar nan an yita, kuma a gidan bak'a akoy Alhinayett dake yayata uba daya, team Mu.azam da Wardugu,,.....ku biy
oni sanu zamu ji meye sirin, sanu zamu yi murmushi
😍😍😍😍😅😅😅😅😅
Hhhh yau kam na cika da yawa
😕😕😕😕
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA
WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4
️
⃣
5
️
⃣
Yana kallonta ta shige bata jima sosai ba ta fito da yayun Agaishat, inda Mariama ta hade rai tamkar ta zunduma ihu dan bacin rai,
Sai dai suna zuwa wajen Wardugu ta ji ba zata iya yi masa wulakanci ko kashedi ba, dan haka ta sada kanta ta ce
" Amana kanwata,
Kalonsu kawai yake har suka koma inda Anna ta bashi wani zani a kule wanda bai san ko menene ba,
Kamar bashi da laka haka ya mike jiki a sake inda su Mu.azam suka kama baba tsoho suka saka shi a motar suka dauki hanya,
Mu.azam na
lure da yannayin Wardugu, inda gabansa ya yi ta faduwa kan lamarin, tambayoyi me cike da zuciyarsa *Me ke damun Wardugu? Me ke adabarsa haka? Bashi da lafia ne? Me ya fauke murmushinsa?*
Sai dai bashida mai bashi amsoshin tambayoyinsa domin rabinsa da ji
n muryar wardugu tunda suka baro kofar Baba tsofo inda baba ya baiwa Wardugu wani kuli a baiwa Agaishat shima harda carbi fari ya shaida masa cewa ya fada mata bata da gata sai na Allah.
Rike yake kamkam da sakon Baba da Anna, carbin kuwa sai ja yake ya
na duban hanya har suka karaso garin Agadez,
Fir Wardugu yace qi sai dai su tashi a jirgin sojoji , inda nan da nan aka taso daga garin niamey aka zo Agadez aka dauke su su biyu tal aka juya da su duka a cikin awowi hudu har jirgin ya sauke su inda dare
ya fara tsalawa,
Tunda ya fito a jirgin ya daga kansa sama, garin niamey da yannayin zafi hakan ya sa ya fara jin har kamar ya cire rigar nan ya yar,
Dubansa ya kai wajen Mu.azam ya kirkiro murmushi ya ce" zan karasa gida, zamu hadu gobe in sha All
ah,
Mu.azam ya amsa shi da kai yana kallonsa har ya bace masa da gani,
Wardugunsa ne ya juye haka lokaci daya? Hannayensa ya dora saman kansa ya furta" innalilahi wa ina ilaihi raj.une, me na aikata haka? Na kutsa wajen da ba nawa bane ko me?
Da
sauri ya kawar da zacen nan ya nufi wajen da ya tabata ba za.a rasa motar wardugu ba dan yawan tafiye tafiyensa yakan zo da mota ya bari a aeroport,
Yelemun kuwa ya samu ya shiga ya tayar ya nufi gidan Ayya ransa cike da tunani,
Wardugu bai zame k
o.ina ba sai kofar gudan su Alhinayett
A lokacin karfe goma na dare ya kusa, anguwar ana dan kai kawo domin ba laifi suma anguwar yan gayu ce, manyan yan mata da samari sai kai kawo suke suna bada kala.
Wayarsa ya danna mata kira, tana dagawa ya ce"
ina kofa,
Da sauri ta mike ta daga labulen tagarta, hango mutun ta yi duke a kofar gidansu,
Da sauri ta fito da zumbulelen hijabinta infa kanwarta dake kusa da ita ta nace ita sai ta bita,
Dubanta ta yi da kyau ta ce" *Tghmass*, wajen yaya Wardugu
ne fa?
Thgmass ta turo baki ta koma saman bed tana kunkunnin je ki, ba zan biki ba ya yi min muhunta wannan katoton da bai san yara ba!
Murmushi ta yi ta fice da sauri ta fito ta karasa da sauri tana fadin" Wardugu lafia? Me ke damunka? Me ya faru?
Baka taba zuwa gidan nan a wannan lokacin ba, menene? Wani ne ba lafia?
Wardugu ya dago kansa daga duken ya kamo hannunta na dama murya a dake ya ce" Alhinayett, zuciyata ke min ciwo, ina jina tamkar zan mutu, ina jin dari sosai, na kasa tabuka komai, i
na jin tamkar na rasa wani baban abu a rayuwana, ina jin iskar duniya ta yiwa kofofin hancina kadan, ji nake tamkar jikina na gasuwa da wani irin azabeben zafi da sanyi, ina jin jikina ya yi min nauyi, Alhinayett me ke damuna? Menene wannan?
Ban taba jin
wannan abin ba, mutuwa zan yi!
Da sauri ta dafe kirjinta gabanta na bugawa,
A hankali ta duka inda yake ta ce" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Wardugu baka da lafia ne? Jikinka zafi, ka je asibiti ne? Daga ina kake yanzu? Ayya ke ce min ka je Garin
su Agaishat nemawa Mu.azam aurenta, ko ka yi gamo ne? Bara na kira Abanmu,
Kokarin tashi take ya riko hannunta ta dawo gwarab kusa da shi tana share hawayen amininta yayanta a wani hali, a firgice ta kuma fadin" ka bari na tado abanmu ya baka magani ya
yi maka turare ko ka yi gamo da wani mugun ne Wardugu
Wardugu ya ce" bana tunanin hayaki, tashin hankali, likita, kudina, ko mulkina zasu warkar da ni, tabas zuciyata sakara ce banza ce da take da gagawar yanke hukunci, ke kin fi kowani makusancina saur
arata , na zo ne dan nima yau ki saurareni kamar yanda nake sauraronki, Alhinayett, a yau da inada mace nutsatsiya da na kwontar da kaina saman cinyarta ta taya ni saisaita bugun numfashina, Alhinayett halayen Walyn na tayar min da hankali, ina sane, ina h
ankalce, kawar da kai ne nake dan ta kula da kanta ta gyara, Alhinayett nima mutun ne, kuma inada rauni fa, ina da zuciya, ita a kulun hirarta da ni tuhume tuhume da zargi ne, a jiya jifana ta yi da maganar wai ina tare da watatsinaniyar? Ni ba mashayi ba,
ni ba mazinaci ba, aman ta ki godewa Allah sai fata take yiwa kanta? Yau da zinar nake ta isa ta hana ko ta yi wani abin? *Wani lokacin nakan dauki niyar zuwa na yin na ga sai me?* (hatara mata, walahi yawancin lokuta mu ke jawowa kanmu masifa da bakinmu
da banzan tunanin mu), sai dai har yanzu ban aikatan ba,
Alhinayett sauraronsa take cike da yannayin tashin hankali, ko me ya firgita mata Wardugu ba karami bane, meye shi da yace ba zai iya masa ba? Ya fi karfinsa? Meye wannan? Gashi ya hanata kiran A
ba,
Sai da ya gama ya ce" ki daina kuka, yau nima na yi jajen abinda ke raina ne.
Alhinayett ta ce" me ka fada bayan komai a dunkuke ka fada Wardugu? Me ke damunka a ranka?
Tsai ya yi yana tambayar kansa takamaiman damuwarsa har haka? Kan matar wan
i ko me? Da sauri ya mike ya mikar da ita ya jata har kofar gidansu ya tura ya turata ya ce" asuba alkhairi Alhi........,
A wannan rana Wardugu ya ga dare tamkar rana, ya kwana bautawa allah inda ya roke shi yafiya da nutsuwar zuciya, kuma alhamdulilah
ya samu nutsuwar harma ya kwonta da safe bayan ya gama salar asuba ya samu baci
Gidan Ayya,
Kallon Mu.azam take kafin ta ce" aa, toh shi wardugun ya aka yi baku zo tare ba? Mu.azam yaushe abokinka zai yi hankali? Ina wayar da na ce ku dauko
min komai?
Sai a lokacin ya tina ya mike da sauri ya je dakinsa ya dauko wayar wajen Ayya da ta basu lale lale su dawo mata da dauka,
Yana zuwa ya kunna mata ya mika mata inda ta tsurawa komai ido tana kallo har karshe domin daya daga cikin yaran war
dugu ya dauko komai,
Baya ta maido kadan tana duban yannayin wardugu,
Kanta ta dago da niyar yin magana ta hango Agaishat ta farka tana saukowa a hankali, kanta na duban kasa, hankalinta a yannayin tashe, kayan bacinta ne jikinta dogon wando sakake da
riga budadiya, kitson kanta cikin hula baka, a hankali ta sauko ta dago idannuwanta ta sauke kan Ayya,
Kuka ta fashe da shi ta karasa da gudu jikin Ayya tana ta shesheka
Hankali tashe Ayya ke bubuga bayanta ta ce" me ke damun ki? Lafia? Y'ata menene?
Agaishat ta kankame jikin Ayya ta ce" Ayya, mugun mafarki na yi, wai wuta na cin gidanmu, Aya gobara a gidanmu, an yi an yi da Anna ta fito ta kiya tana jira sai Ba ya bata umarni domin bata fita sai da umarninsa , shi kuwa ya tsaya yana ta dariya ya
ki bata umarnin!
Ayya tana shafa kanta ta ce" mafarki ne fa Agaishana, mafarki ne, ki kwontar da hankalinki, kin ga jiya su Wardugu sun je din , an gama komai kuma harma Mu.azam yace da sakonki da Annarki ta bayar a kawo maki,
Gabanta ne ya yanke ya
fadi, an gama komai? Kennan yanzu ita ta zama matar aure? Ta zama matar wani? Ta zama sa yi hani bari?
A hankali ta dago da dubanta ta kai wajen Mu.azam,
Ido ta tsura masa kamar yanda ya tsura mata,
Murmushi ya sakar mata yana dubanta kafin yake kara
sowa dan kusa da su kadan ya ce" Anna lafiarta kalau, hakama su Mariama, du sun fito mun gaisa, baba tsofo yace a gaishe ki, du suna nan kalau,
Maimakun ta bashi amsa sai ta mayar da kanta jikin Ayya ta lafe tamkar mage, sannan ta lumshe idannuwanta gam
gam
Da ido Ayya ta yi masa magana tana murmushi tana shafa kan Agaishat inda ya mike jiki ba karfi ya nufi tsakar gida.
Karfe shida na yama jirgi ya ajiye su, inda fito bakin titi ta tsaya tana kallon yanda motoci ke ficewa,
Tsarin garin ya yi m
ata ba dati ga kyau.
Taxi ta tsayar, don ta san ba wanda ya kai dan taxi sannin gari, ta san garin akoy tsaro, sannan ta san da wuya a samu wanda bai sani ba,
Tana tsayar da shi ta ce" *Gidan Elhaj Wardugu Marahut nake so ka kai ni*
Juyowa ya y
i yana dubanta ya ce" gidan su ko gidansa?
Tsai ta yi ta tuna yace mata idan ya zo wajen Ayya yake sauka, fan haka ta ce " *gidan sa* domin tana son fara magana da shi kafin ta je ga Mu.azam!
To fa fans, shin bata san walyn ba? Ya kuke hangen wanna
n cakwakiyar?
Ga kari
😕
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;O
ur ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
4
️
⃣
6
️
⃣
Tafia mai nisa suka yi kafin ya dangana da tankamemen
kofar gidan wardugu,
Kamar kowani gidan baban iko , kofar gidansa sojoji ne ke gadi wa.inda suka canji wasu,
Can gefe katuwar motarsu ce ta iko, sunna dan hira tsakanninsu lokaci zuwa lokaci kuma suna kule da aikinsu yanda ya kamata,
Tana sauka ta biy
a mai taxi ya juya inda ta nufi wajen sojojin .
Kamar yanda suke kallonta haka itama ke kallon su, har ta karasa dan kusa da su
Daya daga cikinsu ne ya yi mata tambayar wa take nema a nan?
Amsa ta bashi gamshashiya ta kuma nuna masa carte dinta shai
dar ko ita wacece din,
Waya ya dauka ya yi kiran layin ogan,
Ya jima yana ringin kafin ya daga,
Yana dagawa ya kora masa bayani,
Wardugu dake bacin gajiya ya bada umarnin a sayota a gwada mata part din Walyn su hadu a can.
Mikewa ya yi ya shiga
wanka, bai wani jima ba ya fito da alwalarsa ya tayar da sallah ya yi ramuea domin wani nanauyan baci ne mai wahala sosai ya yi,
Yana gamawa ya bi ta dayar kofar ya fice dan nufan bangaren Walyn wace ya gama tunanin kar a je tana can tana zuba hauka!
Maradin Walyn baya kunya,
Yana tura kofarta ya tarar da bakuwar tsaye rike da jaka tana kallon kasa, jikinta da bakar abaya doguwa ta yane kanta da mayafin Abayar,
Walyn kuwa na zaune saman kujera ta dora kafa daya kan daya tana kadawa ta turo daurin
dan kwalinta gaba tana kaskaskas da cingan
Salama ya yi mata yana duban Walyn, kafin yake fadin bismillah zauna mana ga kujera,
A hankali ta karasa wajen da ya nuna mata ta zauna tana mai duban Walyn,
Gaisawa suka yi cikin mutunta junna, kafin ya y
i shiru yana sauraronta
Gyaran murya ta yi ta ce" Wardugu sunana Nana khadija Canel Noor, muna tare da Mu.azam ne a can wajen aikinsa inda yake aiki can muka hadu, akoy shakuwa tsakanina da shi