Showing 15001 words to 18000 words out of 86237 words
ina so wani dan uwana ya zo mu wuni tare yau Algabiiiiitttttt
Ta fada tana jan sunnan
Da ido ya tsareta, wai itama nan ta iya bariki, murmushi ya yi, shi dai buri
nsa ta dauki ciki fa? Ina ruwansa inma 2a zqi dane mata ruwan ciki, shi dai in ta yi cikin ta haifar masa kace komin jaraba ya rike abinsa ko a shekara goma ne ya saida ya kara kama daloli, shi kam haihuwar yaya mata ta yi masa rana ( wani abu zai baku mam
aki a lamarin nan, irin yanda Algabitt baya kishin matarsa? To bara ku ji readers , ban ce duka buzaye ba, ba zan ce duka ba domin mahaifina buzu ne dan tsananin kulle da yake yiwa matansa ko gidan mutuwa da ta shafi gidansu zasu je shi ke kai su da kansa
ba direba ba kuma ya tsaya su fito rufrufruf uwa matan ninja baka gannin komai na jikinsa ko.ina a rufe ruf ba damar ganninsu komai kusancinka da su, sai dai kuma akoy buzayen da b
asu san darajar matansu ba, sam basa kishin matansu, sai su ga matarsu kwonc
e saman bed da kato su fice abinsu ko a kwalar rigarsu, baya hana suma in an jima su taketa abinsu doki ce dan haka suke zaune da ita ba wani abin ba! Gaskiya ce a fadeta
🤷🏻
♀)
Murmushi Algabit ya yi mata ya matsota sosai cikin yannayin rada ya ce" ke
, kar ki damu da fada mini fan yan uwanki maza zasu zo, in dai zaki zauna da ni ki haifa mini mata masu kyau? To na baki dama!
Ai kuwa da murna ta rungumeshi ta shiga bashi kulawa daidai daukar hankalin tsufansa
🤦
♀
Wannan kennan
.............
...................................
A hankali ya jona wayar abinda zai dafa masa ruwan zafin dan ya kada madara ya sha
Komawa ya yi jikin bed ya zauna ya shiga karanta messages din Walyn, daya bayan daya,
Na farkon farkon du yannayin ranta a bace
ne, harda baya jin kunyar a ce matarsa guda ta kwana a cell? Toh garin niamey ya dauka, ita yanzu kunyar zuwa auren da zata hadu da mata take, a jejefeta da habaici ya nuna ita ba kowa bace a fadin duniya
Sai daga baya kuma ta fara nuna wai ina ya je ne
? Ya haka zai yi tafiya bai yi mata salama ba? Ina ya tafi?
Sai daga karshe ta sauko sosai ta yi ta turo masa alamun kuka da nuna ta yi missing dinsa yana ina ne? Tana son ganninsa ta yi missing dinsa
Murmushi ya yi a fili ya ce" Hajia Walyn matar Wa
rdugu, Walyn mai zamani,
Girgiza kai ya yi, kai shi kansa ya sani da ace wani saunan namiji ne da tuni Walyn sai yanda ta yi da shi, kuma ba boka ba malan!
Wayarsa ya kunna wace take kiransa, ya cireta a liste noire (Black list) ya kwonta yana saur
aron ruwan zafin na karar ya dafu aman ya yi masa banza, tunani yake, wai shi shugaban revel zai yiwa haka? Ya fada masa gashinnan zuwa aman ya ki zuwa? Har ya je ya yi ta zaman jiransa wai sai daga baya ya yi masa message cewa ba zai samu zuwa ba,? Ya sa
ni sarai waye shi aman ai shima ya san waye shi! In ba dan tsufansa ba da sai ta tafka masa ashar din da zai gigita!
Wayarsa ce ta shiga kara , irin kukan bindiga ratatatttatatatatatattatatatatatatattatatatatatatatatatatatatatat
Muka hannunsa ya yi
ya dauko yana karanta sunnan mai kiran
Sai da ta tsinke aka sake kira kafin ya daga bai yi magana ba
Oga, bako ne muka yi, ahi kadai yake tafe cikin duhun nan, ya zo ta hanyar boye , ragar wajen nan ta shaida zuwansa domin ta kama masa hannun shine y
a fito yana fada
Kai waye ya zo? Wardugu ya katse shi da kakausar murya
Murya na rawa ya ce" Shugaban Revel!
Wardugu ya lumshe idannuwansa, a nitse ya ce" ku shigo da shi fallon farko, ku juya
Da toh suka amsa suna masu mamakin mai gidansu, yan
a nufin daga shi sai shi zai ganna da wannan hatsabibin mutumen? Lale Wardugu bashi da tsoro, baya dar, baya tsoron uban kowa!
Kwonciyarsa ya yi bayan ya ji wa ke jiransa,
Can cikin tunaninsa wayar ta kuma daukan kuka,
Da haushi haushi ya mike
ya daga da kakausar muryar nasa ya ce" Hello!
Wardu.........ta fada cikin sanyin murya
Tsai ya yi bai amsata ba
Kuka ta fashe da shi ta ce" tu me manque (i miss you)
Ajiyar zuciya ya sauke a takaice ya ce" ki bi Nuger airlines gobe ina Agadez
hotel din sojoji ki sauka nan ko bana nan ki je dakina
Yana gama fada ya kashe kiran yana shafa gefen fuskarsa da sajensa
DOGON wando ya dora saman gajeran ya saka riga fara kar ta ririke damatsunansa ya fito ya nufi fallon da aka sauke bakon dare (
🤣
)
Yana zuwa ya shigo kai tsaye,
Mutumen dake zaune ya sha rawani ya hakimce cikin shiga ta kamala mai daukaka darajar dan adam ya dago ya tsaida kallonsa kan Wardugu, a tarihin rayuwarsa dole ya sako wannan yaro, domin shi ne mutun na uku da ya aj
iye shi jira
Murya a kausashe ya ce" Wardugu ba.a tsayar da ni jira
Shima Wardugu kai tsaye ya ce" *Rhissa agbula* ba.a ajiyeni jira!
Murmushi Rhissa ya yi, ya mike tsaye suka gaisa irin gaisuwar musulunci suka baiwa juna hannu suna yiwa juna salama
Wardugu ya ce" ya zaka zo wajena ni daya bayan ka san ya dace a tatauna da kai a bainar nasi kowa na da magana da kai harda mai zuwa da maganar shugaban kasarka
Rhissa ya ce" shugaban kasarka dai, ka san ni ba nawa ba! Sannan ni kaima da na aminta
ganninka dan na fafata da kai na yarda tsaurin kanka zai je da nawa, bana musanyar yawu da matsoraci, ba.a daukana a tv haka kyauta sai kace wani sakarai!
Wardugu ya girgiza kai ya ce" ya ake ciki? Wa ke son tayarwa kasata hankali? Ina suke? Menene a
bubuwan yakinsu? Ana jitajitar kune kuka dawo bayan kun daina aiki a niger kace niger ta yi maka kadan sata yanzu? Me yasa ake samun
gawarwakin bayin Allah a gidajensu? Masu aikata min haka baki ne! Da sun san idan na damke su zasuna kururuwar na kashe su
da abinda nake masu da basu shiga gonata ba!
Wardugu ya karasa yana dukan table din glass din dake falon ya yi wani jijiga aman bai fashe ba domin irin wannan mai masifar karkon ne, sai bindiga mai tsini ke tarwatsa shi
Rhissa ya mike tsaye ya ce" ba
ni bane, kuma ba yarana bane, abinda ya sa na tsayar da hankalina kennan har na baro aikina na garzayo dan ganawa da kai! Kar ka shiga yaki da ni ba ni bane! Na yi bincike tsageru ne, kan harkar siyasa ne, kuma na ga makwoncinsu, suna cancanza waje ne ina
son sannin tsarin canza wajen nasu, Wardugu nima sai na yi maka maganninsu
Wardugu ya girgiza kai ya ce.....
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*
🌈
KAINUWA
WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1
⃣
3
⃣
Wardugu ya girgiza kai ya ce" ka taba gannin na nemi agaji? Kokowa ai ya dace mutun yayi abinsa! Ka bani hanya kawai ka barni da sauran ai na san tsarin tsagerancin yan tsagera, idan ka yi yaki a kambacina kana so gobe su afko su aikata abinda y
a fi haka? Domin sun san ba zan iya tarbansu ba? Aa ba dai Wardugu ba
Haka tataunawar Wardugu da Rhissa ta kare, kowa na ji da kansa da kuma ikirarin kansa,
Rhissa ya san abu guda Wardugu ba wai cika baki yake ba, yana fadin abinda zai iya aikatawa ne
, ya san da in dai suka yarda ya ci masu kamar yanda ya fada ne sai sun gwamace mutuwarsu da rayuwarsu a hannunsa, Wardugu ya ga damar ya fitar da su jeji su fuskanci juna wanda hakan kuwa ba zai gyara su ba!
Wannan kennan
Bayan kwana
biyu .......AMERICA
Docteur Mu.azam ne ke zaune yana dadana computer,
Can ya dago kansa ya duba time,
A hankali ya ajiye ya mike ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa
Yana fitowa ya dauki kayansa ya saka ya saka vest dinsa ya dauki agogonsa ya daur
a ya fito fallonsa dan madaidaici ba wani tarkace sai kujeru da dan table da tv tankamemiya, sai hoton wasu fararan mutane mata da miji ga dukan alamu suna murmushi a hoto
Kamar yanda ya saba zuwa ya yi ganan hoton ya tsaya ya ce" Abi, amy asalamu alaikum
, yauma na tashi lafia, sai dai har yanzu ya kasa hakuri ya daina fushi da ni, gashi aiki ya taso min a kasarsa banda shi da mahaifiyarsa da mahaifinsa da suka dauke ni tamkar dan cikinsu bani da kowa,
Zan kuma gwada kiransa ku taya ni da adu.a daga inda
kuke, ina mai kara yi maku adu.ar Allah ya sa kuna cikin Aljannah
Shi kadai ya tsaya ya yi zubarsa kafin yake zuwa wajen wayarsa ya zauna yana dan murmushi ya shiga doka kira
Yana kallon wayar na haske ya ki dagawa, Walyn ce ta fito daga wanka ta zo
ta mike abinta saman lafiyayan bed din hotel din itama tana duba saman screnn din dan gannin wa ke kiransa yake sharewa haka?
Murmushi ta yi ta juya abinta ta shiga neman baci a kasan zuciyarta tana ayanna toh fa da shima yana gaba bare ni?
Can dai
ya daga ya saka a handsfree
Soja kake
Ya fada yana danne dariyar farin cikin ya daga kiransa
Murya ciki ciki ya ce" Docter kake, kuma dan rainin hankali kake
Murmushi ya yi ya ce" baka hakuri ne? Baka mantuwa ne???
Wardugu ya kawar da kans
a ya ce" haka, ka san ba nine na watsa taron aurena ranar aurena dan wani gudiri nawa na shirme daga shiga ka ga amarya kafin a daura aure zaka fito ka watsa taro? Kai mahaukaci ne! Mu.azam baka da nutsuwa
Mu.azam ya bushe da dariya ya ce" Wardugu, abin
da ya sa na tsalako fararan fatar, na yi doguwar tafiya niger ba dan ina son na samu *BAK'A* bane?, ni bak'ar mace nake so, ita ce ra.ayina, ita nake son zaman aure da ita! Kar ka manta ni likitan mata ne, idan ka ga na kuke abu kaima ka gwada abokina
T
saki wardugu ya ja ya ce" kiran na menene?
Mu.azam ya kuma yin dariya ya ce" kai ka dena jin haushina mana, ai ni ban shaki mahaifin matana ba
Da sauri wardugu ya kai dubansa wajen Walyn wace ke kwonce, ta ji sarai dan haka ta yi saurin mikewa tana k
allonsa,
Fuska ya hade idannuwansa cikin nata ya ce" eh haka ne na shake shi, domin a lokacin ban san mahaifinta bane, kuma na tarar da shi ya zabgawa mamanta mari , idona ya rufe ban tsaya wata wata ba na shake shi, kai dan ubanka sai yanzu ka tina?????
Ajiyar zuciya ta sauke, tana tine da ranar .....dalilin wannan action din da yayi na ta haukace kansa, wardugu jarabar duniya....komawa ta yi ta kwonta ta ja bargo tana rufe jikinta
Wardugu ya fice a dakin , yana fita ya ce" Mu.azam??
Mu.azam y
a amsa da na.am?
Wardugu ya ce" kana son kashe min aure ne? Tana jinka fa
Mu.azam bai ji dadi ba aman ya ya iya har ta ji, dan tsam ya yi kafin cikin yannayin mamaki ya ce" Wardugu yamzu tsareka ake idan zaka amsa waya ko me? Lale dole na auri batuba
Kai banza ka nutsu ka ji!!
Mu.azam ya yi murmushi ya ce" dadina da soja zagi, ni dai ka fadawa Ayyata in sha Allah ina nan ina faman gama abinda nake zan shigo Niger, ka san bani da masauki sai kusa da ita dan ita ta iya kula da cikina, zan zo ba
zan dawo ba sai na samu macen aure na kuma gama abindq zai kawo ni
Wardugu ya ji dadin haka dan haka ya amsa shi da murnar hakan
Satin su wardugu hudu a garin Agadez yana faman aikinsa wanda tun Anna na fada har ta kawo ido ta zuba masa, gashi t
a yi ta yi aminiyarta ta barta ta koma wani wajen ta kiya ta ki fir sai ma fada da ta dauka cewar masarautar ai girma ne da ita,
ba ita ba ko baki ta kawo suna da wajen zama har lokacin da suke so a masarautar Agadez
A yau suke saka ran komawa bayan y
a fada masu su kiyaye, ya basu magungunna, ya kafa masu sharuda kan lafiar Fatimata,
Jirgin da ya kawo su an basu takarda dan haka suka kai aka saka su a layin wa.inda zai mayar garin agadez bisa jagorancin docter Fannata
Sun sauka lafia inda Fatimata
ke dan takawa a hankali daga nan suka nemi abin hawa dan karasawa Timiya............
Timiya.....me aka kwaba? Me aka yi me ba.a yi ba? Me ake cikin yi? Timiya gari mai abin mamaki, Timiya garin bak'a,
Duka na kawo wuka a yanka Algabitt ya yi mata
bisa taki shafa man da ya fitar da kudi ya saya,
Rai bace ya ce" sai na tsine maki in dai baki shafa man nan ba
Cikin kuka ta ce" Aba, ka yi hakuri ka ji? Bana son canza kalar fatana ka yi hakuri Abanna
Ni ban haifeki ba, ke ba abin alfaharinki ba
ne yau har na yi hakuri na dube ki na nemi intaki aman ki butulce min? Uban wa ke hure maki kune ne ni?
Aba ba kyau, ba kyau, mu ji tsoron Allah
Hannu ya saka ya dake bakinta ya ce" ki rufe mini bakinkin nan mai bakin jaraba! Ke sai kin shafa
Koka
rin shaketa yake dan ya shafa mata Mariama ta fito da gudu tana ihu tana nuna dakinsu
Dakatawa ya yi yana binta da kallon meye ke kuwa
Hankali tashe ta ce" Ashta ce, ashta ce, tun da ta ce maka in dai ka yi mata auren nan sai dai a kai gawarta kai ku
wa kace sai me ba dai ka daura mata auren ba? Ita ce gata can sai wani abu take daga baya ta fasa motsi
Fancakalar da Bak'a ya yi, shi da amaryarsa suka nufi dakin da gudu
Daidai wannan lokacin Su Anna da sukai doguwar tafiya suka shigo gidan da sala
ma bayan su Dogarai ne da suka tarbo gimbiyarsu wace sarki yake hakimce yana ji tamkar ya zo ya tarbi abinsa
Jin kururuwa ya saka gaban Anna ya yanke ya yi wani irin faduwa, cak ta tsaya tana sauraron magangannun dake tashi, ihun kuka yayanta biyu suke
inda Bak'a ke jingine jikin garu ta daga hannunta ta dora saman kanta ta yi tamkar status tana kallon kofar dqkin nasu ,
Muryar amaryar Algabiitt ce ta tashi ta ce" ta kashe kanta, ta kashe kanta
Wani irin luuuuu Anna ta yi wanda ba wanda ya ganta sai
faduwarta da aka ji , nan mutanen gidan suka ankara da dawowarsu wanda nan da nan gidan kai dama anguwar ta cika da dukan jama.a ana ta daga maganar, tabas Ashata ta rasu, ta rasu ne da bakin ciki, tana da ciwon zuciya ne wanda ya yi mata tashin kai tsaye
, wanda amaryar Algabitt ta yi kazafin ta kashe kanta,
Tashin hankali!
Mota ce katuwa irin ta sojoji, direba mai iya janta kawai ya dauka kai tsaye suka karasa gidan Sarki
Ayya na zaune tana gyara akaifunta labari ya zo mata cewar ta f
ito su tafi
Mikewa ta yi fa hanzari tana murnar yau kam Allah ya sa ,
Tafia suke cikin mota, Walyn na zaune tunda ta cewa Ayya ina kwana bata kara magana ba sai shanshan kamshi take domin da yar tsamarsu da Ayya, gani take Ayya ke zige mata miji yan
a wulakantata
Tafia ce suka yi mai tsayi, cikin jeji ne sosai kafin suke shigewa sahara gaba da baya
Wani kara motar take a cikin kasar nan tana cin tafiyar wace kana ganni ka san karfi ne ke aiki
Duda a cikin mota suke aman sun yi budu budu da
su domin kura sosai ke tashi sanadiyar gudun da suke a motar da kuma kasa
A hankali ya ratsa yar gadar da ta kai mutun cikin kauyen, wato *TIMIYA*..............
YA RAYUWAR ANNA?
ALGABITTTT FA?
BAK'A?????
SU WARDUGU DA AYYA DA
WALYN ME YA KAWO SU TIMIYA??????? MU JE ZUWA ...........................................................na yi imanin da ba dan Allah na sakawa bawa hakuri da dangana a zuciyarsa a lokacin da ya rasa wani mutun mafi kusanci da shi da Anna ta samu tabuwar ha
nkali ga wannan lamari na mijinta, kar ku manta na fada ba labarin mutun na dauko ba aa labarin abinda ke faruwa ne, (YA FARU!)......
🐫🐫🐫
*BAK'A CE*
🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
________________________________
____
*
🌈
KAINUWA WRITERS
✍
🏼
ASSOCIATION*
🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is