Showing 3001 words to 6000 words out of 86237 words

Chapter 2 - BAKACE COMPLETE

SAJIDA   

10 Sep 2026

2

menene sunnanta na gaskiya ne ita wai?

Iya ta kalli Bak'a, ta kal

li Fannata, ta ce" sunnan Hajia ne da ita, karfi da yaji Ba dinta ya mayar da sunnanta Bak'a har ake mata kiranye da haka

Da mamaki Fannata ta karasa kusa da ita tana kallonta,

Yarinyar fa nata wani tsararan kyau, boyeyen kyau, duda mugun bakinta ga ba

kin turkudi na bugajen kauye

🙈🤣

, ga dati da take fama da shi, aman ita tana hango wani al.amari a tatare da yarinyar, to aman me zai hana ta shafa mai itama? A sanninta ba bakon lamari bane buzu farinma ya shafa mai, kai

ba buzu ba yanzu abin ya zama lara

bawama mai suke karawa shi yasa zaka gan su wani farfarfar da su sunna daukan ido, ba sai dan duniya ke shafa mai a duniyarmu ba, mun dauki mai mun mayar da shi abin kmgyaran fata, ra.ayi ne shafa shi idan ka shafa ba mai yi maka kallon dan duniya a karkar

ar mu

Abimcinta take ci kanta a sade tana ji yanda Fannata ke aikin tambaya a kanta, tsoro take kar a je mugun kyankyaminta kamar yanda mutanen garin ke yi ya saka take son sannin ko ita wacece dan ta kara samun damar ci mata mutunci, hakan ya sa take

sauri dan ta gama cin abincinta ta kara gaba , so take ta siyarwa SOFO goro na dala biyar, ta saka dala goma asusun da take tarawa dan ta bawa Ba ko ya daina tsanarta, Gomar kuwa itama ta ci wani abin

*AGAISHAT*

ta ji sunnanta a sama sa

ma yana yawo, sunnanta na gaskiya aka kiraya,

Da dan sauri ta dago sukai ido hudu da Fannata,

Fannata ce ta kirayi sunnanta na ainahi ba bak'a ba.............

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

___

_________________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________

________

4



A hankali ta kai idannuwanta kan Fannata dake kara matsowa kusa da ita

A hankali fannata ta saka hannunta ta dago na Agaishat, kallon hannun take tana jujuyawa, fannata ta fahimci bayan bakinta na hali

tarta da Allah ya yi, akoy tarin dati ga kuma karin bakin turkudi,

Da sauri Ta janye hannunta tana kokarin mikewa daga cin abincin cike da tsoron menene kuma Fannata ke taba mata hannu?

Fannata ta ce" kin ga, ba abinda zan maki

Kallonta take da m

amaki domin da hausa radau Fannata ta yi magana bayan Agaishat kadan kadan take jin hausar itama baba Tsoho ke dan koya mata dan abinda ya iya, yakan ce ba.a san gobe me zatai ba

Goshinta ta dafe ta kalli wajen iya ta ga sai faman gyara Sansanninta take

(tabar buzaye), tana dan kukulewa da zare tana ajiyewa gefe tana yin kulin kadago kadago (dala biyar biyar )

Kurumci Fannata ta shiga yiwa Agaishat,

Ta yi mata nuni da hannayenta da fuskarta gaba daya,

Ta yi saurin taba ruwa ta nuna mata alamar bata

wanka ne?

Agaishat ta shiga faman saka tsohon takalminta na soso tana faman guduwa domin ta saka a kasan zuciyarta wannan abin zai kare ne a wulakanci da tozarci

*WaRDUGU*

Ta fada tana mai daga murya kamar zata kaiwa gabjejen mutumin dake t

saye a gabanta duka,

Ta kuma cewa" WaRDUGU Odon jidu anna indahan yuna yugusnan gwa ( tun kana yaro yake fama da kai)

Kansa ya dafe, ya kai dubansa kan agogon hannunsa, kallota ya yi ya yatsina fuska, can ya ce "Ayya (wato mama), Ayya inda medi mundu

tam (wato mama ke rigimarki ta yi maki yawa)

Hannunta ta dora a goshinta ta shiga kai kawo, kai take tana kawowa, can ta dauki wani ihu ihu tamkar tana buda, ta je ta dawo ta je ta dawo, ta kallo shi cikin yaren hausarta da bata fita da kyau ta ce" s

hikennan rayuwar bariki (gayu) ta lalata min kai, shikennan na zama uwar da ina fadi ba.a saurarena, ko nima zaka kula zazafar gabar da ni ne kamar yanda ka kula da Abbanka (mahaifi)?

Hannayensa ya jimke ya daki garu da su, kafin yake juyowa wajen mahai

fiyarsa,

Taku ya yi zuwa gabanta kafin yake sada kansa, shima cikin yaren hausar sai dai tashi ta fi dan goguwa ya ce" Ayya ba dai saboda wajen wannan bugudin (tsofo) ne kike daga hankalinki harda hada kanki kike min da wannan Bugudin (wato mahaifinsa)?

Kanta ta kawar ta ki bashi amsa hakan ya sa ya mike ya fito daga falon

Yana fitowa ya nufi wani dankareran mashin *ROUTIER* jibga jigban nan masu shegen tsada domin daga million daya abinda ya kai har million shida ne, kuma mashin ne ba mota ba...gu

dunsu ma daban yake da kananun mashin

Bakin gilas dinsa ya fitar ya saka ya tayar da mashin din ya yi masa wani irin ja wanda kana ganni tamkar dambe ake da mai jan da mashin din domin mugun karfi ne da shi ga kyau

Hangame gate mai gadi yayi don kar

ya jawa kansa bali wajen Wardugu

Yana fitowa daga anguwa *Plateau* a birnin Niamey ya nufi *Francophoni* inda gidansa yake

Yana karasawa shima tuni an hangame kofar ya shige da gudun tsiya ya silala wani waje da nan ne ma.ajiyar abinda ya shafi ma

shin da motoci

Dira yayi ya juya da sauri sauri ya shiga hawa matatakalar bangarensa domin bangare daban daban ne da matarsa mai sunna *GALayn*

Wata yar karamar carte ce ya dora mai dauke da hotonsa ya dora daidai wani detecteur ya bada dan kara tit

eeee kofar ta bude

Caicaicaicaicaicaicai wash, gidan tubawa kamshi, wayo gidan batube ni.ima, bale mai auren gimbiya hajiar hajia, sarkin tsafta, sarkin ado, kwaliya ba dai a nuna mata ba, ta kasance cikin kamshi wanda indai kai ka ce zaka kwaikwaya sai d

ai ka tashi da mura (gaisuwa yar baba)

Sanyi mai hade da kamshi ne ya buso shi, sanyi mai sanyaya zuciya

Terrace din dakin fara kal kal kal haka take daukan ido ta sha guga,

Tafka tafkan salon ( kujeru) ne irin na zamani masu kalar fari kal kal sai d

an coussin kananuwa sosai su kuwa masu kalar baki kamar yanda mauquette (capet)

Rido (wato labulaye) yen dakin suma kalar fari ne, sai dai farin ba kar ba kamar yanda kujerun suke , shi ya fi ruwa da kalar peinture (colern) dakin, shima an saka abinnan

na daure labule baki wanda kana ganninsa ka san ba karamin kudi bane dakin ba wani tarkace aman komai ka kai dubanka ka san karshe ne sannan ya bada kala ta mamaki,

Nan ya yada zango, ya daga kansa sama ,

Iska ya furzar yana jin yanda takalmin matarsa

ke tahowa kwaskwaskwaskwas

Kamshin da take fitarwa shima na daban ne, ta shafa turaruka har ta gaji,

Tunda ta fito take kallon yannayin fuskarsa, a cikin ranta ta ayanna" wani masifafe kuma ya hargitsa min yannayin miji?

Bata yi kasa da gwuiwa ba t

a karaso kusa da shi ta daga damatsunnan hannayensa ta shiga masaging a hankali tana kara kallon yannayinsa

Murya can kasa ya ce" *ADIBIRA* (Matata)

Tsai ta yi tana kallonsa kafin ta ce" qu'est-ce qui ne va pas mon Bb? (Me ke faruwa Baby?)

Kans

a ya kawar gefe kafin ya janye hannunta a hankali ya mike ya nufi uwar dakansa

Bakinta ta tabe, Galayn akoy saurin fushi, mace ce iya mace aman bata tunnanin zata tsaya tana wani bibiyar namiji ko waye shi balatanna wardugu? Wardugu zuma ne ga zaki ga h

albi, wardugu ko a cikin tubawa tsoronsa ake, mutumin da idan ransa ya baci idan bai samu ya damki mutun ba yake suma? Mutumin da ya wawuri ogansa ya daga sama ya nana da kasa ogan nasa bama na niger ba domin a niger ba marichal, bako ne da kowa ke tsoro y

ana shayi, gardama kadan ta hada su General Wardugu ya daga shi ya nana shi kasa a gaban yaransa da kuma yaran general, wannan abin ya jaza masa da mukaminsa da komai shugaban kasa ya tsaya kai da fata aka tura shi daji can wajen mali sai da ya yi wata hud

u ya sauko, aman maimakun abin ya yi sauki sai kara gaba da yayi, mutumin dake gaba tukura da mahaifinsa , fada yayi gwa da gwa cewa abansa ya kiyayi hanyarsa kan laifin da ya boyewa kansa sai shi sai mahaifiyarsa suka sani, ita a wa zata tsaya ta bi bayan

wardugu da idan ransa a bace ka bashi hakuri yake hucewa kanka? Du irin yanda yake ikirarin shi yanzu ba ruwansa da fada da mutun na gugar jiki karya ne ! Ka yarda ka yi gigin kai masa wargin baya ce masa komai ya ciro daya daga cikin wukaken dake jikins

a ya burma maka idan ya so a kashe shi, Wardugu nada zuciya ta ainahin tubawa....

Mu je zuwa labarin *BAK'A CE*

🐫🐫🐫

*BAK'A CE*

🐫🐫🐫

Na *SAJIDA*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

____________________________________

*

🌈

KA

INUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

____________________________________

5



Mikewa Galyn ta yi ta fice itama ta bi ta babar kofar danma ya san ta yi tafiyarta ta je ta kara bada turaren ruwa a jikinta ta fito ta je wajen da kys din motoci suke ta dauki guda ba tare da ta tsaya zabe ba domin kuwa kaf ciki manya ne

Tana fitowa ta shige motar ta tayar ta fice abinta wajen auren kanwar kawarta tana mai duba carte dinta ta bank dan ta tsaya ta ciro yayan banki na kari a wajen wasa....

Wannan kennan

Ya yi kai kawo ya fi a kirga, ya dafe kansa yana tunanin

irin nacin mamansa kan abu, ita yanzu dan wani tsoho can daban zata dame shi kan sai ya kaita, shi ya san wani bai isa ya bashi lafiya ba aman har fadi take shi ya taimake shi yana yaro, an dai dudura masa itatuwa haka kawai za.a kashe masa kwayoyin jiki

Tsaki ya ja mai karfi, ya mike ya shiga cire kayan jikinsa masu nauyi ya rage masa culotte kawai

Da dan gudugudu yake kara taka matatakalar benen bangarensa har ya karasa bangaren da piscine dinsa take

Ba tare da wani tsaye tsaye ba ya fada cikin ruw

an nan ya shiga iyo tamkar wani kifi yana kai yana kawowa ba wani alamun gajiyawa a tatare da shi

Ba ita ta kai gidansu ba sai can dare har wajen karfe tara abinka da jeji shiru garin sai kukan tsuntsaye sai jefi jefin

samari da yan mata ana tadi domin

sukan kai har goma suna tadinsu

A hankali ta shige gidan nasu ta samu ta leka kanta

Fitilar kwai a kunne, sai dai tana jiyo minsharin Abansu dan haka a hankali ta kutsa ta nufi dakinsu yan matan gidan

Mahaifiyarta ta gani zaune saman abin sallah, d

a alama ita take jira duba da irin yanda ta tsareta da ido

Jiki a sanyaye ta karasa kusa da ita kanta duke ta ce" ANNA

Bata amsata ba sai kureta da ta yi da kallo,

Ta jima duken nan, aman bata mike ba domin ta san wani abu guda da mahaifiyarta ke

da na buzaye tamkar wata yar gidan sarauta koda yake du buzuwa ko buzu haka ne dadaya ne basu da shi wanda mutane ke jifansu da sun cika *Ashak* ,

Can kamar ba zatai magana ba ta ce" kin ga, ko wani hali zaki shiga, ko wace rayuwa zaki fuskanta *AGAIS

HAT*, ki guji sabawa mahalicin ki, ki rike mutuncin ki , ki ci gaba da hakuri watarana sai labari

Kanta take gyadawa, kuma wani dadi ta ji har cikin ranta, ko ba komai ta san a duniya bayan baba Sofo Annartama bata kyamatarta, tana kawar da kai a lamura

nta ne dan gudun fitina, irin yanda Abanta ke binta da shari kwararo kwararo ya sa mutanen garima haka, ba mai kulata da daraja, ko magana za.ai mata ba.a mata ita a mutunce, ya kasance ko gaishe da mutun ta yo sai ya yi mata yatsina domin Abanta bai barta

haka ba har shari ya yiwa annarta kan cewa ko dai wajen baba Sofo take zagayawa gannin irin yanda ya damu da ita ?

Wannan wutar kafin ta mutu sai da aka sha tashin hankali, baba tsoho ya yi kuka sosai aman bai daina kula Bak'a ba domin tana da mutunci ya

rinyar, shi Allah bai azurtashi da yin auren bama domin bashi da lafia ko ya yi ba anfani hakan ya sa yake jin yarinyar tamkar yar da ya haifa, itama tana mutunta shi tamkar mahaifinta

Mamanta na gama fadar haka ta yi shiru kanta itana a saden tamkar ta

na gaban sarakuwarta

A hankali ta mike ta nufi dakin su

Tana zuwa ta tarar du sun yi baci abinsu dan haka ta dauro alwallah ta shige ciki ta tayar da sallah ta shiga ramuwar wa.inda batai ba , tana so du rintsi ta ringa samun gurin sallah sai dai tan

a tsoron mutane da kwagirar su, yanzu za.a wulakantata dan haka take bari idan ta zi gida sai ta yi wanda bata samu ta yi ba

Tun karfe takwas na safe Aba ya fice bayan ya canza rawaninsa daga baki zuwa maroon turkudi sabo fil, ya sayi tufafi ya sayi raw

anininka harda waya, ya fito sabo kudi sun fado shikennan a haka zai fada su tamkar wuta shima ya dankaro aure daga an cinye kudin shikennan ta gudu abinta

Bai jima sosai a wajen ba ya dawo,

Daidai lokacin Anna na fitar da dawar masararsa a ruwa wace r

a jika dan tana son yin garin tuwo

Bai yi mata magana ba ya zarce dakinta dake baban daki idan ka cire nasa a gidan, daman dakuna uku ne, da nasa da na Anna da na yan matan gidan

Bai yi wata wata ba ya shiga kwasar kayanta yana kaiwa dakin yan matan ya

na jibgewa gefe guda,

Ba wanda ya tanka shi ko ya yi mamakin lamarinsa domin sun san halinsa, haka yake du idan zai yi aure dakin mahaifiyar su yake fitar da ita ya hadeta da su ya kawo amarya, bama zai barta a dakinta ba sai dai ya hade su ya kawo amary

a su sha shagalinsu ba wanda ya isa ya yi magana yanzu zai cici masa uwa ko waye

Ko kallo bai isheta ba, don ta daukarwa kanta alkawarin in dai ba mutunci ne lamarinsa toh ba zatana kai kanta yana wulakantata ba gaban yayanta.

Sai da ya gama fitar da

komai kafin yake fita ya shigo da magini

Sosai aka gyara dakin ya yi tas da shi

Tare suka fita , sun jima sosai kAfin yake dawowa

Wannan karon kuwa masu shigo da kaya ne

Mariama dake wanke fuskarta bayan ta shafa kurkum ta yi tsai tana bin kayan

da kallo,

A gaskiya siyayar idan ka yita a kauyen ka isa ne, tun daga gado har kayan abinci na gayu ya kwaso abinsa sai dai abin haushin babu rabonsu a ciki na amarya ne, domin idan ka auri jar buzuwa ko duniya zaka kai gidansu nasu ne ba za.ai mata komai

ba sai dai a kawo maka ita daga ita sai butarta (a kauye fa kar a ce inji sajida

🤣

)

Sai da suka gama kawo kayan tsaf Mariama ta je faban mahaifinta ta tsaya masa kerere a gabansa, somin kuwa in dai haihuwar rashin mutunci ne ya haifa Mariama ta isa ta

iya tsayaya tamkar mahaifinta

Ido tar cikin nasa da yaran buzanci ta ce" Aba ya haka? Na ga ka fara kwaso kaya alamun aure zaka yi? Ya baka fitar da mu ba? Baka ba anna kudin siyayar kayanmu ba?

Kun san wasu iyayen sun fi son yaya masu tsayayar nan,

domin Aba yana dan shayin lamarin yar tasa domin a yanda yake gani tama fi shi rashin mutunci dan haka ya dan gyara rawaninsa

irin zai yi magana ya ce" wani siyaya kuma? A sanina cikakiyar buzuwa ba.a yi mata kayan daki?

Ta yatsina bakinta ta ce" sai ku

ma cikakiyar buzuwa ana yi mata sutura

Karya ne Mariama, ya fada yana matsowa kamar zai doke ta, ya ce" ku ne yayan zamani kuke zuwar mana da abubuwan da suke neman fin karfin tunanin mu, ko uwarki haka aka bani ita, haka ake kai ku daga ku sai turkudin

amarci da buta, kudin auren ku kuwa mu iyayen ku ke siyan maku kadara mu ajiye maku a nan wanda idan kun waiwaya zaku ji dadin su

Wani malalacin murmushi ta saki tana kallonsa

Ya ci gaba da fadin" ke da kin ga minister ne ya turo a nemi aurenki, ya

saya maki komai, sannan ke da auren wata shida ne zaki yi ki kwashe komai ki dawo mini mu more da kudi?

Tar ta kara saka idannuwanta cikin nasa kafib take juyowa ta ga mahaifiyarta ta fara daka dawar da ta wanke ta baza a rana ta sha iska tana so ta m

ayar da ita gari kennan , ta kuma kai dubanta wajen yayarta *BAK'A* dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login