Showing 27001 words to 30000 words out of 188421 words

Chapter 10 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

124

kanka da sunan JARUMI bawai LUSARIN NAMIJI BA.

Idanunsa da suka shanye ya daga a hankali,daidai sanda yaga gilmawar inuwa ta bayan labulen dake tsakanin parlor din Bedroom din nasa. Kamar gilmawar walqiya komai ya bace,ya zubawa gurin idanu a hankali kafin kuma wani miskilin murmushi ya subuce masa.

"Wannan shine iya zurfinka?......wannan shine iya qwarewar taka?" Ya furta can qasan ransa yana gyada kansa da cikakkiyar nutsuwa sannan ya miqe yana takawa a nutse yana nufar parlor din.

Baiyi zaton komai zaizo da sauqi har haka ba.....bai dauka kuma zatayi zaben lusarin me binkice irin wannan ba. Amma ta wani gefen sai ya mata uzuri,tabbas ya sani,inda tasan girman had'arin da yake dashi......dan sanya idanu na gaske zata nemo ta hadashi dashi ba wannan qaramin halittar ba........amma ko meye shi ya masa daidai......zaiyi wasa da hankalinta yadda ya kamata.

*AKHNAN*

Komai batace musu ba,illa kunnuwanta kawai data basu tana sauraren mitarsu a kanta sanda birra ke miqa mata kayanta tana shiryawa da kanta.

Tanaso komai zasuyi cikin daren nan da mammina suyishi a qare.......mafita take nema,ba kuma mafita irin wannan da sultane ya bata ba. Mafitar da zata fita gaba daya daga cikin sharuddan sultane,taci gaba da rayuwarta kamar yadda take a baya.

Duk kusan mita da qorafinsu akan ta koma sahel couture ne. Jinsu kawai takeyi.....yadda takeji da kamfanin.....yadda kamfanin yake qunshe da wani irin tasiri a rayuwar qasar niger gaba daya,da yadda aikinta tuquru yakai kamfanin wani tudu da bata taba tsammani ba ko a mafarki abun ya bata tsoro. Daidai da sultane abun ya daure masa kai.......ya kuma sake daga darajar akhnan a zuciyarsa da idanunsa. Wasu irin tarin nasara da ninkuwa da komai na kamfanin yayi wanda ba wanda a cikinsu ya taba hango masa nasara irin haka a kurkusa.

Sahel couture wata kyauta ce ta ba zata da sultane ya taba mata a rayuwa. Ruhin dukiyarsa gaba daya,kuma sirrin dukiyarsa,ba zatan data girgiza mutane da yawan gaske,ta sake kuma haska girman matsayinta a zuciyar sultane din,wanda hakan ya sanyata alfahari me yawan gaske. A wannan lokutan bata taba tunani ko kawowa ba akwai wani abu me suna DAMUWA da yake da tasirin nesanta da Niamey ma gaba daya bare sahel couture din kansa ba.

A nutse ta karbi bakin mayafin da birra ke riqe dashi,ta kuma soma Rolling saman sumarnan tata me sulbi da data kwanta luf saboda yadda birra ta gyarata sosai ta matse mata ita cikin siririn band da bazai takurawa darenta ba.

"Ba wani tunani nawa da yake daidai a yanzu.....ba wani sauran qwarin gwiwar data ragemin da zata ban damar jagorantar sahel couture yanzu.....mammina tasan da hakan,ta kuma gaya miki ke kikafi cancanta kici gaba da jagorantarsa......bansan me kike jira ba" Tayi maganar a nutse da tasirin izzarta cikin fitar kowanne lafazi daga labbanta.

"Kinsan wani abu?" Shehnaz ta fada tana qarewa akhnan kallo,wadda tayi wani irin sassanyan kyau,kai ba zakace nan da wanni zata kwanta ba,saika dauka ta shirya ne don fita wani guri daban a wajen gidan.

Akhnan bata amsa ba,sai aisa data dubi shehnaz alamun ita suke saurare.

"Ke kika maida komai me zafi akhnan.......amma inda zaki sassauta zuciyarki......wallahi na hango miki wani kyakkyawan zabi....zabin da nake da yaqinin zaki samu nutsuwar da baki taba hange ko tunani ba......sheikh haisam akhnan......."

Wata irin wawiyar juyowa akhnan din tayi......sannan ta zubewa shehnaz idanun nan nata dake da surkin kwarjini irin na d'iyoyin da sarauta ta game jininsu.

"Koma meye kikeson fada abu mafi alkhairi ki barshi a bakinki.......idan kuma har shaye shaye kika fara shehnaz daga yau ba zaki sake marmarin kusantar irin abinda kika sha ba ballantana ya suranta miki qazamin tunani irin wannan har abada.........ba wani namiji daidai dani a yanzu a duniyar nan......bansan ko gaba ba,koda qaddara ta sanya na amsa sunan MATAR AURE.....to koma waye wannan mijin....." Sai bata qarasa ba ta girgiza kai da wani irin yanayi daya tabbatar musu da tarin abubuwan dake binne cikin zuciyarta,take ganin baki yayi kadan ya furtasu daidai.

"Zanje naga mammina" Iya abinda ta fada musu kenan ta soma takawa tana fita a dakin.

Cikin qasaita da jinta cikin cikakken tsaro take takawa a filin da zai kaita kai tsaye zuwa sassan mammina din. Wata irin iska ce me ratsa jiki take kadawa gami da kai kawo daga kowanne kusurwoyin duniya.......idanunta ta zare daga duban qasaitattun katangun dake zagaye dasu,wadanda iya kallonsu kawai na sake sanya mata jin izza da qasaita. Tabbas.....lallai inda za'a tasheta a wata rayuwa ta daban,a kuma bata zabi,babu shakka zata yita zabar kasancewarta cikin ahalin SARAUTA.

Iya ginin da masarautar agadez ta mallaka da wani irin tsari da aka zamanantar dashi tayi imanin zai wahala a samu tsarin masarauta tasu kaf Africa.

Sararin samaniya ta maida dubanta,duk da cewa duhun dare mamaye saman gaba daya,hakana bai hana hasken farin wata nuna hadarin dake lullube a saman ba,hadarin da ya jima yana haduwa,kuma a yau kamar yana nuna ya tumbatsa da yawa,nan da wasu mintuna ko awanni yana iya hade jikinsa dukka tsaf,ya kuma jirayi umarnin sarkin sarakuna wajen shayar da al'ummar agadez dama na nijer gaba daya ruwan farko.

Iskar ta mata dadi qwarai.....kamar yadda yanayin ya mata dadi.......saidai hakan bai hana kalaman shehnaz yin suya sosai a qirjinta ba.

Iya fitar furucin daga bakin shehnaz sai takejin kamar ta qasqanta......kamar neman kai ake da ita......yanzun har araharta takai haka?......me yasa sultane yakeson lallai sai ya zabtare dukkan wani girma nata da darajarta ya watsar?,har wadanda kimarsu da martabarsu batakai ba suyi tsammanin sunkai tsaikon da zasu kusanci iyakokinta?. Ba wani taku da zatayi ba'a zube a qasa bisa saman gwiwoyi ba cikjn gaisuwar ban girma,wanda ko daya bata amsa ba sai birra dake amsa mata.

Wannan din dabi'arta ce......kaman yadda yake girmanta ne......baka isa tana takawa a farfajiyar guri ba kaima naka qafafun suci gaba da takawa ba,zaka jira har sai sanda ta bada baya ko tabar gurin. Girman da dukkan al'ummar masarautar ke bata banbancinsa kadanne dana sultane,kowa fata yake......qoqari yake ya kyautata mata da dukkan girmamawa saboda farincikin sultane.

Tun daga qofar mammina ta farko masu tsaron qofar ke janyewa gami da sauke idanunsu qasa tare da kaucewa kallon akhnan din da yake kasancewa zunubi ne ga kowanne d'a namiji cikin masarautar muddin ba ita ta lamunce maka hakan ba.



*MAMMINA*

Zare wayar dake kunnenta tayi a nutse tana duban bakin qofar inda yalwa ke durqushe ta yadda bata iya hangota.

"Ina neman izinin yin bayani idan an lamuncemin haka" Ta fada da wani yanayi da ya gayawa mammina akwai labari a bakin yalwa din.

"An baki" Ta fada tana gintse wayar gami da ajiyeta.

"Gimbiya akhnan na dab da shigowa sassannan". Shiru mammina tayi......kafin wani shu'umin murmushi ya subuce mata.

Tun kwanaki data diba mata a ranta basu cika ba sai gashi akhnan din ta gaza jurewa ta nemota?. Lallai ba shakka ta wannan fannin tayi tinjimin aiki da ya kamata ta yabawa kanta da kanta. Tayi aikin daya zame mata makami mafi muni a idanu da zuciyar morsa safiyya......ta yadda bata yadda za'ayi morsa safiyya ta iya karbe akhnan daga hannunta......har gaban abada,koda itace tace akhnan din ta koma hannun morsa safiyya din,ta juya akalar girma da biyayya shawari da matsayin uwa data bata.

"Banaso kai tsaye a barta ta iskeni......banaso ta samu ganina kai tsaye cikin sauqi kaman yadda yake a baya". Ta fada fuskarta na sake fadada da fara'a.

"An gama" Yalwa ta fada tana miqewa da hanzari da kuma sassarfa tana sauka qasa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Sanda tazo matakalar qarshe akhnan na shigowa. Ita daya ce,ta baro birra a baya,don birra din tazo iyakacin shingen da ba wanda ya isa ya d'arashi cikin bayi ko hadimai.

Qasa yalwa tayi da kanta,duk da yadda zuciyarta ke bugun uku uku amma idar da abinda ran uwar gijiyarta keso ta kuma tsara tamkar bauta yake a wajenta.

"Allah ya taimaki hasken agadez......Allah ya baki yawan rai da nisan kwana......kamar giwa ta samu kwanciya nake zato......ko za'ayi haquri a koma zuwa gobe?". Cak akhnan ta tsaya daga daga qafarta da tayi zuwa stairs na farko sannan ta waiwayo ta zubewa yalwa idanunta.

"Kinsan dawa kike magana?" Ta furta cikin izzar data kada hantar yalwa.

"Kinsan me kike cewa?......."

"Tuba nake ranki ya dade,ayimin aikin rai" Ta fada muryarta da labbanta dukka suna rawa saboda tsananin tsoron akhnan din daya shigeta. Kamar ba zata sake cewa komai ba......amma saita jinjina kai ta juya taci gaba da takawa.

"Koda wasa karki sha'awar xaki sake maimaitawa"

"Na tuba in sha Allahu" Ta amsa mata tana jin gwiwoyinta kamar ba zasu dauketa ba.

Duk taku daya da takeyi ranta yan sake suya,yaushe tayi arahar da kamar yalwa wai itace zata mata iso?,iso fa akan mammina......mamminarta na da bau irinta kaf rayuwarta.

Kaman yadda batayi sallama ba bayan ta canko dakin da mammina din zaune,sai kawai ta jingina da qofar dakin tana harde hannuwanta a qirjinta,fuskarta shimfide d wani nannuyan yanayi.

Taji shigowartata,amma ba lokacin nuna batasan ta shigo din ba. Tana so ta sake shuka wannan qagautar a zuciyarta......tanaso komai ya kasance cikin shimfidadden tsarin da idan ta hau ha zancan sauka.....shakku ko kokwanto. Tanaso komai ya kasance daidai ta yadda zata iya fito na fito da dukkan wanda yace zai kawo naqasu ko gyara a tsarin.....tanaso akhnan da kanta da kuma hannuwanta tayi mata yaqin da ita ya cancanci ta yishi ba tare da ita din ta daga koda yatsarta ba.

Tasan tunda ta shigo ta tsaya ba zatayi magana ba,ba kuma zatace komai ba,don haka ta waiwayo kamar me shirin daukar wani abu,saita zube idanunta a kanta.

Fuskarta shimfide da alamun mamaki take dubanta.

"Biftu......yaushe kika shigo?". Kai ta girgiza a hankali,tana iya hangen taruwar ruwan hawaye saman qwayar idanunta dake da wani sheqi kaman an diga mai a cikinta,idanun da idan ka kallesu zaka dauka tun asali hawayen ne a ciki,saidai yanayin halittarsu kenan.

Tashi tayi daga jinginar da tayi ta tsaya da qafafunta tana duban mammina din.

"Ni nazo.....nazo mammina,tunda ana dab da shiga tsakaninmu" Ta qarasa maganan tana jin duk wani rauni nata yana dawowa sabo,muryarta na karyewa,alamu suna gaya mata kuka zai iya qwace mata daga yanzu zuwa kowanne lokaci.

Kai mammina ta girgiza,ta miqe a nutse ta soma takowa zuwa inda take. Hannayenta ta riqe a tausashe,ta kuma sanya idanunta cikin na akhnan ta fara magana.

"Bazanci gaba da kusanta kaina da gurin da zan zama abar zargi ba......ko meye zanyi cikin rayuwarki na alkhairi biftu cikin zargi nake gurin morsa safiyya da ire ir.......".

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[1/7, 19:36] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 15*

__________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

____________________________

"To tayita zargin mana......uwata ce?.....ko ta haifeni ne?....mahaifiya daya ce mutum keyi a duniya,sauran saidai su zama uwaye kawai......tawa mahaifiyar kuma ta rasu.....ke na zaba.....ke kika cancani ki maye gurbinta,harma gurbin da yafi nata din,don kece kikayiwa rayuwata komai da dukkan kulawa garkuwa da kuma gata". Idanunta mammina ta lumshe tana budesu lokaci guda. Wani abu me dadi taji yana rantsa kwanyarta yana sake sanyaya mata zuciya. Iya wannan aikin kawai da tayi yana sake gaya mata ita din JARUMA ce.....me jumurin jiran shekaru dubunnai domin wanzar da fansa a inda ya dace.

"Sultane fa biftu?....kin shirya fiddani kunya?". Hannuwanta ta zame daga cikin na mammina,ta soma takawa tana zarcewa cikin dakin gami da barin mammina a tsaye a nan tana fuskantar qofa.

" Na shirya fiddaki mammina.....saboda ke daya TAK!......saboda in saka miki farinciki da sadaukarwar da kika dade kinamin......amma ban shirya samar da mafita ni daya ba.......kin barni nayi aikin da bazan iya yinsa ni kadai ba......kin sani idan ba mammina ba akhnan?" Takai qarshen zancanta da sigar tambaya tana kuma waiwayowa gami da duban mammina duk da cewa har yanzu mammina din tana tsaye ne tana fuskantar qofa ta bawa cikin dakin baya.

Dole murmushi ya subucewa mammina din. Ta sake yarda tabbas taci galaba tako ina ta wannan fannin......ta mallaki halitta mafi soyuwa a zakutan ahalin guda biyu.....halitta mafi soyuwa qirjin macen da data kasance MAQIYIYA ta biyu wadda ta maye muhalli da gurbin maqiyiyarta ta farko.

Ta sani......akhnan ba zata iya wani motsi ba cikin rayuwarta.....akhnan ba zata iya yanke kowannw hukunci ba cikin rayuwarta......akhnan bata da wani zabi cikin rayuwarta face abinda ta shirya ta kuma dorata a kai.....a haka ta raineta......a haka ta girmar da ita don ta dace da irin wannan yanayin da wannan lokacin da suke ciki A YANZU!.

Sai data tabbatar ta maida yanayin fuskarta yadda ya kamata ta kasance sannan ta waiwayo tana takawa da salon tata qasaitar gami da dawowa cikin dakin.

Dukkanin hannuwanta akhnan ta riqe tana mammina din da wani irin rauni da tsaf zaya karya zuciyarta banda zuciyar tayi wani irin nisa da koda alamun kira bataji ballantana sautinsa.

"Na baki wuqa da nama mammina......ki yanke duk abinda kike ganin ya dace.......ki zabarmin mijin aure......indai hakan shine burinki.......na tabbatar bazan cutu ba......ba kuma zaki zabamin wanda zai cutar da dukkan burika da mafarkaina ba".

Hannu mammina ta sake zamewa tana kada kai gami da rabe akhnan din zata wuceta.

"Sultane ya zaba miki mazaje masu yawan gaske akhnan,dukkaninsu baki karba ba,shin wacece mammina da zata aikata hakan?.....morsa safiyya ita yafi kamata ki bawa wann....."

"Mamminaaaaa......" Ta kira sunanta da wani hargitsatsen yanayi. Da gaske har cikin jini da tsokarta bata qaunar shiga ko rab'ar matar cikin dukkanin lamuranta. Kiran sunanta kawai a inda take tsaye yana sanyata tana jin kamar komai nata zai tabarbare ne.

"Da sultane da morsan dukkaninsu ke na zaba a cikin su.....zakimin wannan alfarmar ko bazan samu ba?" Ta fadi kanta tsaye sarautarta tana motsawa.

Sosai wani abu yake sake kwanciya cikin ran mammina........tana jin dadin yadda komai yake wanzuwa......amma a wannan taqin bata shirya amsa komai ba.......tanason komai ya zamana wankakke ne daga zargi,don haka ta girgiza mata kai kanta tsaye,fuskarta na nuna lamu alamu na bacin rai.

"Baza yi ba biftu a wannan karon".

Cak ta qame a wajen,kwanyarta na cika da tarin mamaki. Tana duban mammina dinne amma tana ganin kamar ba mammina dinta ba?. Me jiran kokenta a kullum don ta share mata hawaye?. Me zaman jiran jin matsalarta ta kaudar mata da ita?.

Wadannan mutanen dake kai kawo a ranta zuciyarta na sake tabbatar mata da sunyi nasara,su suka shiga tsakaninta da mammina dinta.

"Shikenan......zanje nayi duk abinda naga dama......rayuwata ce" Ta fada kawai a taqaice sannan ta juya da wani irin fusata tana laluben qofa.

Shuru tayi tana rufe idanunta,ta kuma zurfafa gami da aika kaifin jinta can nesa.

"Daya....biyu.....uku....."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login