Showing 6001 words to 9000 words out of 188421 words
A nutse morsa safiyya ta daga idanunta tana azasu saman fuskar mammina. Kafeta tayi da idanun tana mamakin jin kalaman daga bakinta. Dama akhnan din tayi wannan iqirarinne.......dama ta furta hakan?,amma ita ta sani bata shaidawa ITA KO SULTANE ba?,koda bata gaya mata ba me yasa bata gayawa sultane ba?.
"Jinin safeena bazai aikata wannan ta'addancin ba ga wani bama bare kanshi" Bakin morsa safiyya ya motsa a hankali ta furta maganan tana duban mammina kai tsaye.
Ta fada ne ba tare da tasan ma ya fita daga bakinta zuwa zuciyarta ba. Ta fada ne saboda tana jin hakanne har tsakiyar ranta,ta kuma fada ne saboda kowanne sashe na jikinta yana gaya mata bai yarda da faruwan hakan ba.
"Bismillah muhammad" Sultane ya fadi yana yiwa haisam izinin yiwa akhnan allura.
Zare idonta mammina din tayi daga kan morsa tana azawa kan haisam. Shi takeso ta yiwa maganar......shi kuma takeso ta dakatar,amma sai ya mata wani irin mugun kwarjinin da taji ba zata iya magana dashi ba,don haka ta maida idanunta kan sultane.
"Biftu tana cikin mafi hatsarin yanayi........kalleta sultane,ta yaya wanda bai qware ba a aikin lafiya zai mata allurar da dukkaninmu bamu da tabbaci akan ita ta dace ayi mata?" Ta fada tana nuna tsananin hargitsewarta.
"Ni na aminta da muhammad.......na kuma aminta da dukkan komai da duj wani bayanai da zasu fito ta bangarensa" Sultane ya fadi da dukka qwarin gwiwarsa yana duban mammina.
"QALUBALENA......SHINE QALUBALENA.....NOTED" ta furta qasan ranta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kusan baima ji abinda mammina ke fada ba,don tayi maganan ne qasa qasa a sanda wayarsa shi kuma ta dauki hankalinsa saboda jerin gwanon kira da yake gani daga abdii da maher.
Riqe allurar yayi a hannunsa,sai ya waiwayo yana daga qafansa,idanunsa suka saukan kan falaak,abinda ya sanyata yunqurin dauke idanun nata da sauri gabanta yana wani irin mahaukacin faduwa. Bata taba zaton zai ganta ba,tunda ta zauna a gurin ya janye hankalinta gaba daya,duk rudewar da take ciki hakan bai hanata ganin tsantsar kyan da shigar tayi masa ba. Ya sake shammatarta da wani mamakin na ganin cawa shine zaiwa yaa biftu allura.......dame dame ya iya?.....dame dame ya sani har haka?" Take tambayar kanta.
Bai barta ta gama janye idanun nata ba ya riqe kallonta da kyau cikin idanunsa yana mata sign din ta fiddo masa hannuwan akhnan.
A hankali ta miqe,ta kuma tsugunna gaban akhnan din ta miqa hannu zata zaro hannunta.
"Tsaya" Mammina ta fada tana yunqurin yin aikin da falaak din ta taso tayi.
Wani irin zafi da bacin rai ne ya sake sauka saman zuciyar safiyya,sai ta saka hannunta gaba daya tana janye akhnan zuwa ga nata jikin,ta kuma kamo hannun falaak ta dora kan na akhnan sannan ta miqe a hankali don bawa haisam space yadda zai mata alluran a sake. Ta sani zamansu a gurin zai sanya ya matse da yawa,daga yawan zancansa da falaak ke mata ta sake samun tabbacin mutum ne shi da bai fiya son cakudayya da mata ba,matsawan zai bashi peace.
Miqe dogon hannun akhnan din falaak tayi wanda ke dauke da lafiyayyar fara tas din fatarta me daukan idanu. Fatar da ake kashe ma wani maqudan kasafin kudi duk shekara don ta kasance cikin lafiya da kulawa.
A nutse ya qaraso gurin,yakai idanunsa ga hannun,sai ya janye kallonsa da sauri can qasan ransa yana furta.
"Astgafirullah......astgafirullah" A yau cikin awanni qalilan yana jin yawan zanubansa a saman kansa. Yana baqinciki da ranar da zata bullo ya zamana yana da wani rubutaccen sabo da yayi,yana kunyar Allah akan haka,yana kunyar ayyukansa na sati suje da wannan rubutaccen sabon a cikinsu.
Alama ya sakewa falaak kan ta juya masa iya tsintsiyar hannunta kawai. Ta fahimceshi,iya zaman karatunsu,don haka ta jawo duvet ta kuma lullube hannun akhnan din,ta bar masa inda ya buqata.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
[12/31, 19:36] +234 903 555 3736: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE06*
_________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_______________________________
A nutse ya sunkuya ya kuma fara sanya qarfen allurar cikin fatarta yana kallon yadda take shiga a hankali. Idanunta ta juya a hankali sanda tsinin allurar ya caketa tana dagasu zuwa sama inda take iya hangen blurry face dinsa. Yanayin buguwar poison din a jikinta ya sanya take ganin fuskarsa kaman dab da tata......yake kuma sake maida fuskarsa zuwa ga wancan ranar wadda ke lullube da yadin rawanin daya zagaye habarsa dashi.
Allurar na shiga tana jin ganinta yana sake daidaita,yanar data rufe ganin nata tana wankewa tana qarawa ganinta qarfi,wannan ya sanya kafin ya gama mata allurar wadda ake turata zuwa jikinta a hankali a hankali ganinta ya dawo tar.......ya kuma bata daman ganin fuskarsa sosai da clear view.
Zare allurar yayi,falaak ta sanya hannuwanta dukka biyun ta amsa ta taka zuwa ga dustbin ta sanyata a ciki,wani abu yana motsawa sosai a qirjinta game da haisam. Kusancinsu a yau,yanayin yadda yayi allurar cike da qwarewa da takatsantsan. Ita din dalibar lafiya ce,amma daga yadda yake allurar ta tabbatar akwai qwarewa me tarin yawa a cikin aikinsa.
"Zan wuce" Ya fadiwa sultane a taqaice cikin girmamawa. Kai sultane ya jinjina,ya fahimci baya buqatar ci gaba da zama a cikin su,amma yayi masa dukkan abinda ya kamata yayi,ya katse uzurorinsa da dama saboda matsalan iyalinshi......duk da cewa inda haisam zaici gaba da wanzuwa a tare dasu zaiso hakan,to amma kuma bai kamata ya qure kawaicinsa da yakanarsa ba,don haka yace
"Na gode qwarai sheikh muhammad......na gode"
"Allah ya bata lafiya" Ya furta a tausashe da yanayin daya sanya morsa safiyya sake ganin kimarsa,su ukun kuma sultane morsa safiyya da falaak suka amsa da ameen.
Yana takawa don ficewa mammina ta aza idanunta a kansa. Akwai tarin abubuwa da yawa......akwai tarin damarmaki da take dasu ta samesu a yanzun......akwai hanyoyi da suka bude mata da zata iya bata tsakaninsa da sultane......a gabansa takeson yin haka,amma batasan wanne irin kwarjini gareshi ba da ta kasa tsaidashi bare ta fadi Koda abu guda daya a akanshi da zai jefa koda kokwanto da wasiwasi a zuciyar sultane.
Sai daya kammala ficewa tas sannan ta maido hankalinta dakin,yanayin takunsa daban yake da takun data saba gani......akwai wani abu me girma da nauyi a cikin character dinsa.
Numfashi ya sauke sau uku a jere don ya samu yayi calming kanshi. Abubuwa da yawa......abubuwa da yawa idanunsa da kwanyarsa gaba daya suke hange.
Wayarsa ya sake fiddawa,sai ya samu miscall din su abdii ya qaru,wannan karon harda na omar,ga na maher daya tabbatar yana dai ci gaba da jiransa ne.
Duka bai kirasu ba,don bayason dogon magana ko dogon bayani,omari kawai zaifi fahimtarsa kaman yadda aka saba,don haka shi din ya kira kai tsaye.
Bugu daya ya daga da cikakkiyar sallama,haisam ya amsa masa can qasan maqoshinsa.
"Kazo ka dauke yaron nan abdii,ya sakani a gaba da tashin hankali,wai yayita kiranka baka daga ba,maher ma kuma yacemin ya kasa samunka,gashinan zaune kaman zai fashemin da kuka?".
"Ka cewa maher na daga fitan sai gobe......ka gayawa abdii ina lafiya,amma yau kam duka bana buqatar shashancin nan nasa........please ka karbi mota gurin salana kazo ka daukeni".
"Yanzu?" Ido ya lumshe yana girgiza kai.
"No.....zanyi wanka ne"
"Amma maher yacemin ka shirya har ka fito kuma".
"Eh.....wani dalili ya sanyani komawar". Ya furta very calm,yana fatan shima omari din kada yaja maganan da tsaho.
" Xan shigo palace kenan da motar?".
"Idan tunaninka ya kwance omar zaka iyayin hakan" Ya amsa masa a gajarce kawai yana kashe wayar,sannan ya sanyata a aljihunsa yana ci gaba da komawa sashensa na cikin gidan.
"Astagfirullah" Yaketa maimaitawa sanda yake fidda kayan jikinsa,kayan da bai taba tunanin akwai wani abu da zai sanyashi dawowa nan kurkusa ya canzasu ba.
Ruwa me matuqar dumi yana sauka saman kansa idanunsa na runtse yana tambayar kansa.
"Why?,me yasa ko yaushe sai ita?" Ya tambayi kansa yana jin wani abu yana bin sassaj jikinsa da ya sanya jikinsa wani mugun mutuwa tubus.
Zai iya rantsuwa da Allah hannunsa bai taba kaiwa jikin kowacce d'iya mace ba. Yana bala'in kame jinsa ganinsa dama hannuwansa harda qafafunsa daga dukkan wani abu irin wannan. Amma me yasa ta zama mace ta farko da gangar jikinsu keta haduwa haka?,ba daya ba ba biyu ba?,kusan sau uku kenan,kuma dukka ta dalilin wani abu?.
Zuciyarsa tana yin sanyi idan ya tuna komai bai faru bane akan son rai ko son zuciyarsa,ya faru ne kan akasi kawai irin na dan adam.
A gurguje ya shirya,don akwai maganganun da yakeso yayi da omar masu muhimmanci. Ya taka a nutse tun daga sassansa har zuwa ficewarsa daga gidan,yana takawa a nutsensa har zuwa inda suka saba tsaida mota su jirashi.
Tun daga nesa da omar ya hangoshi ya bude masa gaban motar kusa dashi,don yadda haisam din ya bashi command ya sanya baima sa salana ya tuqoshi ba,kawai sai ya karbi motar.
Tab ne a gabansa wanda yake video call shi da maleek da naseeb. Naseeb din suna guri daya da maleek ne saboda ziyara daya kai masa. Duk da yadda aiki ya banbamta musu guraren rayuwa,amma hakan baya hanasu kaiwa juna ziyara lokaci bayan lokaci. Kowa a cikinsu yana iya ziyartar dan uwansa a duk inda yake,kafin lokacin da suke haduwa ta lokaci guda dukkaninsu yayi.
Da tattausar muryarsa yayi sallama yana sako gangar jikinsa cikin motar,sam hankalinsa baya kan tab din,baima lura da ita ba,yayin da idanun maleek da naseeb da sukayi shuru suna son surprising nasa yake kansa cikin murmushin nan dake cike da soyayyar juna.
Hannu ya bawa omari sukayi musabaha kafin ya zame hannun yana azashi saman qirjinsa,sai kuma ya sake zame hannun yana neman madannin da zai bashi daman kwantar da kujerar yadda zai samu daman yin relaxing sosai. Tsaiwa kawai yayi yana kallon screen din,yayin da naseeb ya saki dariya sosai,maleek na tayashi ta hanyar murmushi kasancewar shima din ba ma'abocin yin dariya bane kaman dai haisam din.
"Mr lowering gaze......wai meye hakan?" Maleek ya tambaya da yanayin sarauta cikin jininsa shima kamar dai haisam din. Kai kawai haisam ya girgiza murmushi yana qwace masa,omari ya shammaceshi,hakanan wannan karon yaji kunya ta yadda aikin gaba daya ya shagaltar dashi daga barin nemansu.
"Wanne irin aiki ne ya shagaltar dakai haka?.....na dauka wata me rabon muka samu data dauke mana hankalin sheikh dinmu?" Maleek ya sake fadi yana murmushi.
"Ka sani ko ya samu nasarar kammala aikinsa da kuma gwagwgwabar kyautar princess of agadez?" Naseeb ya fada yana dariyar tsokana. Tsokana dabi'ar naseeb ce,har sun riga sun saba da haka,amma wannan karon maganansa ta yiwa haisam girma tare da maido masa mode da dabi'u dukka na akhnan daya sani,da sauri ya furta.
"A'uzubillah......a'uzubillah" Gami da miqa hannu ya kashe gaba daya karatun qur'anin dake tashi can qasa ta speakers din motar.
Harara ya fara watsawa omari........ya tabbatar akwai wata magana da suka fara dasu naseeb din,sai omar din ya fuske gami da mazewa yaqi yarda ya kalleshi,duk da yadda yakejin nauyin idanuwansa kamar kullum
"Don Allah......na roqeka wannan maganan ya fita a bakinka naseeb koda wasa kake......ban shirya wasa da zazzafar wuta ba" Ya qarashe maganan yana hade tafukan hannayensa biyun guri guda alamun roqo.
Dukkansu dariya ya qwace musu,maleek ya jinjina kai sannan yace.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Me kake tsoro obbo?......There's no woman on earth you can't deal with". Kansa ya jinjina a hankali yana kadashi. Ya lumshe idonsa a nutse sannan ya bude yana motsa labbansa da yanayin daya tabbatar musu akwai gajiya a tattare dashi,walau ta jiki kota tunani.
"I want peace always.......am not interested in drama". Maganansa ya sanya omari da naseeb sakin qaramar dariya,yayin da maleek yayi murmushi.
Kasantuwarsu daga gidan sarauta dukkansu shida haisam......hakan ya sanya akwai kamanceceniya na wasu dabi'u a tsakaninsu,don haka duk cikinsu bakwai din yafi kowa fahimtar haisam,saidai yafi haisam din mu'amala da 'yammata duk da cewa tsaftatacciyar mu'amala ce da yake sanya ran zaben matar aure a cikinsu. Kai ya gyada yana duban haisam din
"Kaima kasan ka taro match......tunda ka kayar da ita a gasa cikin yankinta". Kansa ya juya kadan,sai yanzu yanayin kallon da take masa ya dawo masa. Ya sani,ya kuma fahimta tanason fahimtar cewa shine abokin takararta ne,duk wani motsi da acting nata ya nuna masa hakan,saidai shi kuma sam bazai taba bata wannan damar ta gano komai ba. Ba drama ko wasa bane ya kawoshi yankinsu,ya kuma kawoshi masarautarsu,yazo ne kawai ya kammala wani aiki ya fice ya koma zuwa qasarsu. Aiki ne da zai tabbatar da zaman lafiyan iyayensa......zaman lafiyar qasarsa......da kuma zaman lafiyar yankinsa da qabilarsa.
Akan wadannan abubuwan daya lissafa ba shakka zai iya sadaukar da komai,shi yasa yakeji a cikin jikinsa da jininsa......ya shirya tunkarar komai don cimma nasara,musamman a yanzun da yake ganin wasu kebantattu kuma baqi sabbin abubuwa suna gilmawa ta gabanshi.
Hira sukai sosai irin ta abokai shaqiqai da suka saba da juna,hirar har takai sai da aka tabo su mutallab,dukkansu suka hadu cikin video call din cikin yanayi na kewar juna,duk da haisam din kusan yayi relaxing ne cikin kujerar,sai daya biyu kawai yake jefa bakinsa yayi murmushi a wuce gurin.
Sun saba da irin dabi'ar nan tasa,musamman a lokutan da bayason dogon magana,suma kuma sun iya tafi da 'yan miskilancinsa.
*AGADEZ PALACE*
Dukkaninsu hankalinsu idanunsu dama numfashinsu dukka sun tsaidashi ne akan doctor hadizatu data kasance qwararriyar likitar dake aiki cikin masarautar,qarqashin babban clinic na masarautar da yake aiki don duba marasa lafiya na cikin gida da ciwukansu basuyi girma da yawa ba.
A hankali ta zare allurar da kafin ta kammalata ta jiqe da gumi,allurar da tayi ta cikin cannula cikin takatsantsan da nutsuwa.
"Alhamdulillah" Ta fada tana goge fuskarta da handkerchief tana kuma kallon yadda gumi ya fara jiqa goshin akhnan.
Falaak ce ta sanya tattausan handkerchief din da aka kawo cikin tarkacen da aka ajiye a gurin ta soma share mata goshinta,yayin da aisa ta dauki remote tana dan qara qarfin Ac din dakin.
"Anyi nasara gubar ta fara sakinta in sha Allah,ga alamu nan.......amma tabbas lallai duk wanda ya kawo idea din mata allurar farko ba qaramin sanin abinda yakeyi yayi ba......allurar ta taimaka qwarai wajen saurin saukar da tasirin allurar da akayi mata yanzu.......sannna ta dakatar da harbuwar gubar zuwa sassan da idan ta tabasu to xai wahala a samu rai da rayuwa,kamar hanta qoda hunhu da kuma zuciya" Sosai wani irin kima da qaunar haisam ta sake samun kyakkyawan gurbi a zuciyar sultane. Da gaske muhammad din ya zama wani sashe me muhimmanci a tattare dashi raywarsa dama ta iyalinsa.