Showing 78001 words to 81000 words out of 188421 words
yasa ya zamana ba wani laifi don an kafata ko an zartar da ita bada saninki ba.....dukkanin dokar an yita ne saboda tsaron masarauta"
"Tsaro ga masarauta ko kuma neman ikon sarrafa komai da kowa?" Murmushi ya sakeyi kadan,na wannan karon yafi na dazu bayyana.
"Ikon sarrafa komai wannan siffar Allah ce mahalicci shi kadai.....ni dake da sultane duk bamu da hurumi a kanta". Maganar tasa sai taji kaman yana qoqarin tube mata rawanin ikonta ne,don haka cikin qanqance idanu tace masa.
" Kasan wacece ni kuwa?".
"Kowa nasan wayeshi.....kowa kuma nasan wa yake qoqarin zamantowa ko kasancewa kamar shi". Wani irin abu taji ya sauka yana sarar gabban jikinta. Wani irin gumi taji yana qoqarin tsatstsafo mata,saidai tasan barin hakan ya faru,barinsa ya karanci hakan babban kuskure ne a tare da ita,don zuwa yanzu cikin jikinta takejin BA HAKA KAWAI YA SHIGO AGADEZ BA....BA HAKA KAWAI YA SHIGO MASARAUTA BA.....BA GAMA GARIN MALAMI BANE.
"Amma kasan cewa masarautarmu a zaune take lafiya kafin shigowarka cikinta?" Ta sake fadi yanayinta yana nuna fara daukan zafi.
"Zaman lafiya ba shine shuru ba......wani lokaci shuru yana boye abubuwa masu nauyin gaske....cikin rashin sa'a saika dauka lafiya ce ta kurmantar da komai din" Ya amsa mata da wani irin nutsuwa a tattare dashi. A karo na biyu ta sake jin kamar dutse ya dauka ya jefeta dashi cikin tsakiyar kanta.
"Waye shi?" Ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,zuciyarta da tunaninta suna neman zamewa. Zuciyarta ke mata wani irin tsalle,tana kuma cikata da shakku a kansa,sannan tana son jefa mata rudanin da bata shirya ko tunanin fuskantarsa ba a daidai lokacin.
"Akwai wani da kake zargi?....ko akwai wani abun zargi cikin masarautar damu muka gaza hangoshi sai kai?". Tayi tambayar cikin zafi,tambayar data sanya ita da kanta wuta dauke mata,don bata tsara ta fidda masa zafinta har haka akan komai ba.
Shuru ya ratsa dakin,haisam kallonta da wani irin duba da takejin kamar yana toxartata ne ko kuma qoqarin karantar dukkan wani plan nata.
"Zai iya yiwuwa......amna zartarwa a yanzu ba na daya daga cikinmu bane....saidai ki taimaka wajen tabbatuwar amincin amanonin rayukan dake tsakanin hannunki da na sultane.....saini yanzu da aka sakani a ciki zuwa lokacin da zan miqa muku amanarku" Yakai qarshe yana miqewa a nutse,yana kuma jin yakai gejin maganganunsa,yana sake ji a ranshi tako ta ina matar ta tabbatar ABAR ZARGI TA FARKO!.
Yadda take takawa a nutse yake tabbatar mata fita zaiyi,hakan kuma yana nuna zai tafi ne koda bada izininta ba,koda batace ba,koda kuma bata gama fadin abinda ke ranta ba,wanda tana da tambayoyin da amsarsa ce kadai zata gamsar dashi.
"Kabi a hankali sheikh haisam......masarauta tana iya hadiye baqi ba tare da ganin koda burbushin da za'a bi diddiginsu ba......karka manta gidan nan nawa ne,kada kayi abinda zai sanya da kanka ka fahimci KAI DIN BA KOWAN KOWA BANE" Wani faffadan murmushi sama dana dazu ya kubce masa,ya sakeshi a nutse ba kuma tare daya waiwayo ba.
Ya yadda kalaman baki sune abu na farko dake fara fada maka WAYE WANE?. Ya aminta su din wasu maqullaine da a yanzu suka bude masa wata qatuwar qofa da zai sake zurfi a bincikensa
"Gida mallakin sultane ne.....ina tsaiwa daidai iyakokin da zasu amintar dashi ne shi kadai.......isata kuwa....." Ya fada yana waiwayowa a nutse.
"Lokaci yana tafe da zai baki amsarta......na isa? Ko akasin haka?" Ya fada yana tsaiwa daga nan gami da bata space,saidai bata iya cewa komai ba,wannan ya bashi daman juyawa yana ficewa,saidai duk da hakan bai hanashi jin furucinta na qarshe ba.
"Zan tabbatar da cewa na nunawa duniya kai din ba kowan kowa bane.....zan nunawa duniya baka isa a komai ba face zallar malami me cin takarda allo da tawwada".
A nutse ya zare Device din daga Kunennensa don ya fara jiyo karadin omari.
"Ina mamakin yadda yariman jimma yake iya dauke wadannan kalaman.....don Allah ko sau daya kayi abinda zatasan your not an ordinary man" .
Goshinsa kawai yake murzawa a hankali yana qoqarin calming kansa. Idan ya biyewa zancansu omari shirme zasuyi kawai a agadez,su kuma bata lokaci a banza cikin agadez din,su komawa Ethiopia a empty zero hands.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
____**Hannu ta miqa tana sake jawo takardar tana fidda wani huci daga bakinta zuciyarta tana jin kamar zata fasa qirjinta ta fito. A karon farko a rayuwarta ta d'an d'ani yadda dacin jayayya da qasqantar da isa take ga wanda yakejin ya isa yakai ta kowanne fanni. Idanunta ta maida saman dokokin tana sake bitarsu tun daga farko,tana so kuma ta dire kan sanya hannun sultane din da yayi iqirari akai.
_daga wannan daren,bayi da hadimai ba'a lamunce musu zirga zirga tsakanin sassa ba daga bayan sallar isha,har sai da rubutaccen izini_
_Dukkan masu ziyara zuwa cikin kowanne sashe zasu rubuta sunayensu asalinsu yare da qasarsu,da dalili na ziyarar kaman yadda tantancewa zata hau kan kowanne hadimi da bawa dake rayuwa cikin MASARAUTA daga gobe_
_an haramta kowanne ganawa da bayi a kebantattun dakuna ko gurare_
Kasa qarasa karantawa tayi,saboda tsananin bugu da qirjinta yakeyi. Tanajin kowacce doka qwaya daya tana kiran sunan ZAITUNA ne kai tsaye,saita zarce da idanunta kan sa hannun sultane. Sa hannu ne da tafi kowa sanin girma da qarfinsa. Sa hannu ne daya kasance na daban wanda muddin sultane yayi irinsa saman takarda to kowacce magana ce komai qarfinta ta zama TABBACIYAR da babu sauyi a cikinta!!!.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
[1/22, 19:59] +234 903 555 3736: π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 38*
"Yalwa!" Ta kira sunanta kai tsaye a yau din da kanta.
"Ki nemomin tamim yanzu.....ki gaya masa kada yazomin da tsohon labari,sabuwar magana nake son ji" . Umarnin daya qara yawan rawar jikin yalwa da son cikashi,wataqila wannan ya shafe hukuncin da take zaman jiran fuskanta kan aikenta na dazun.
β
"akwai boyayyu kuma nannadun al'amura masu girma da yawa cikin masarautar nan......haisam,akwai wani abu daban dake cikinta bayan abinda muke nema.....akwai wani abu na daban dake faruwa bayan bincikenmu......girman abinda ke cikin masarautar nan yafi qarfin princess akhnan kawai....yafi qarfin rikicin cikin aurenta kadai......inaji a jikina haisam.....matar nan tana hadarin gaske,me yasa ba zaka taimaki sultane ba?." Omari dake zaune suna fuskantar juna shida haisam ya furta damuwa zaune fal saman fuskarsa. Wani irin kallo haisam yayi masa yana qoqarin daidaita kansa tsakanin idanun omari din.
"Kasan me kake fada kuwa omari?" Ya masa tambayar calmly,saidai idanunsa na nuna girman abinda yake fadi din.
"I know haisam.....na sani" Ya fadi kai tsaye yana duban idanun haisam,yanason ya fahimci da gaske yana jin interest na fadada bincikensu da bin diddigin cikin gidan.
Kallon kallo ne ya wanzu a tsakaninsu na wasu sakanni kafin haisam ya zare idanunsa. Da gaske ya karanci tunanin omari,kuma da gaske yake fadin abinda yake fada din,ba wasa sam a ciki.
"I wasn't cross boarders to save the palace" Ya furta da wani irin accent dake nuna tasirin yaren oromo cikin harshensa,yayi maganar ne kuma yana dauke dubansa daga kan omari,yana maida dubansa ga cup din gabansa da omari ya zuba masa coffee.
Idanu sosai omari ya zubawa haisam din,a karon farko yana mamakin sauyawar dabi'ar haisam din. Baida kutsa kai kan sha'anin mutane.....amma yana damuwa kan mutumin da duk yaga zai cutu muddin yana da ikon taimaka masa. Me yasa a yau a yanzu yake kauda kai daga taimakawa akhnan da mahaifinta?.
"Amma......me yaci gaba da shigo da issue dinta cikin maganamu inde haka ne?" Omari ya jefa masa tambayar. Sau daya tak ya daga ido ya kalli omar,sannan ya dauki mug din coffee dinsa ya shanye,kana ya miqe a nutse yana zube hannayensa cikin aljihun trouser din jikinsa,ya taka a hankali zuwa bakin qarfen balcony din.
"Saboda tana kanannade da wadda nake zargi....dole a wasu lokutan maganan case dinta ya dinga ratsowa cikin aikinmu" Ya amsawa omari a nutse can qasan zuciyarsa kuma yanason canko dalilin da yasa omar ya masa wannan tambayar. Ya sani dukkansu ba wanda ke magana ko tambayar da bata da fa'ida ma'ana ko dalili......ko akwai wani dabi'a ko halayya ta daban da yake nunawa kan abinda ya shafi case din?. Bai iya gano komai ba,bayaso kuma ya waiwaya ya kalli omar kada ya dauka akwai wani abu daban da yake rayawa a ransa. Kaman yasan kuwa kallonshi omar din yake,kaman kuwa yasan neman reaction qwaya daya omari yake daga gareshi.
Ya jima yana raya wani abu a ransa game da haisam din. Bai taba masa wani dogon zance daya shafi akhnan ba.....amma ya dade da sanin wata dabi'a kebantacciya daga haisam din,dabi'ar da baya jin ko haisam din yasan yana da ita,dabi'ar da yasan itace SILA SANADI da saamee da MENELIK suka kasa samun matsugunni a zuciyarsa,duk kuwa da cewa suna da kowanne irin quality da ake buqata na zahiri daga gurin d'iya mace.
"Amma kasan sultane ya amince da kai?....."
".....wannan ne ma ya bani dalili na qauracewa iyakokinsa da shiga al'amuran da suka kebanci iyalinsa.......ina da kishi me yawa da nauyi,yadda bazan bari a kusanci iyalina ba daidai da d'ani ko taku guda ba.....hakanan bazan kusanci iyalin kowa da zarafinsu ba sai akan wanda gaskiya take buqatar tayi adalcinta a kansa" Ya qarashe maganar yana waiwayowa idanunsa cikin na omari.
Wani kallon kallon suka sake yiwa juna,sai kawai omari ya jinjina kansa a hankali sannan ya sauke idanunsa yana cewa.
"Nan da kwanaki uku maleek zai kawo maka ziyara,ba kuma iya gidanka kawai ba,har cikin masarauta yake sha'awar shigowa"
"Allah ya kaimu" Ya fadi kawai cikin nutsuwar rai. Dukkanin aminan nan bashi da haufi a kansu,sunsan boyayyen aikinsa da ko cikin ahalinsa ba kowa bane ya sani,tsananin amincin dake tsananinsu ya sanya sukasan kowanne doka da strategy na aikin,don haka bai shakkan haduwa da kowannensu a kowanne lokaci a kuma kowanne irin yanayi,bare maleek da abubuwansu da yawa yazo daya,saidai ta wani fannin sukance maleek ya fishi sauqin sabo da jama'a,duk da shi dinma SARAUTA na yawo a jininsa.
*MAMMINA*
Abinda takeji a ranta a lokacin wani irin yanayi ne da tun zamanin SAFEENA bata qara jin irinsa ba. Wani irin qanqanci takeji har a cikin jininta,wani irin tozarci da ya sanya takeji wani irin zafi saman fuskarta kaman an watsa mata borkono.
Kafin tamim ya iso tafisu ta rigashi isowa,tayi dukkan me yuwuwa ta kwantar da hankalin mammina amma hakan bai samu ba.
"Wai me kike tsoro game da malamin dake rayuwa qarqashin alfarmarku?" Kai ta jijjiga sosai tana gote da hannayenta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ba malami bane gama gari......ba irin malamin da kika saba gani bane.....wannan idan na runtse idanuna ZAKI nake gani a gabana tafisu.....idan na kulle kunne na TSAWA nakeji tana fita a bakinsa maimakon magana irin ta kowanne dan adam.....shi ba irin kowa bane tafisu......tabbas akwai wani abu na daban a tare dashi". Shuru tafisun tayi,tana son gwargwaje magangun mammina cikin ma'aunin nazari da lissafinta,amma sai sallamar tamim ta yanke mata wannan hanzarin.
"Me ake ciki game da labarin Ethiopia?" Ta tambayeshi kai tsaye. Bai zauna ba,don bata bashi wannan damar ba yayi qasa da kansa ya soma magana cikin girmamawa.
"Sun gaya min,akwa alamu gwada biyu da suka gwada akwa wani shinge daya motsa daga muhallinsa.....alamu ne ba'a samu tabbaci ba"
"Su maida kai akan wannan alamun!.......su bani tabbaci a nan kusa!!" Ta furta atsawace tana jin wani abu yana motsawa daga qasan zuciyarta,tamkar an fusgi zuciyartata an kuma jijjigata.
"An gama ranki ya dade......amma ki sani.....kallon kallo yana da hadari a wadansu lokutan,sai gwani shike iya satar kallo ya kuma fusgi abinda ganin ya bashi a sanda na kewayensa basu ankare da haka ba" Shuru ya ratsa tana fahimtar saqon da tamim ke aike mata da karkataccen harshe,saidai a yanzu zuciyarta bata aminta da shawarar tamim ba.
"Tafiyar hawainiyarmu bata kawomin alfanun komai ba bayaga MAFAKA,mafakar fa wani lokaci nake Allah wadai da ita...,hanzari nake buqatar gwadawa wannan karon,koda bayani ya motsa wasu sassa da zasu farka daga dogon baccin da suke......akwai wani taku na musamman.......dama ya kamaya susan KIFI NA GANINKA ME JAR KOMA!" Tayi maganan a wannan karon tana jin itama ta shirya ta kowanne bangare!!!.
_Uhmmmm.....me karatu,tafiyar fa zazzafa ce......abubuwa da yawa na shirin qulluwa agaba ba'a bigiren da aka shirya qulluwarsu ba,FADUWA DA NASARA......YIWUWAR FARA AFKUWAR SABON WASA TSAKANIN MAMMINA DA HAISAM......SHIN WASAN WAYE ZAIWA DADI?......WAZAI AFKA CIKI?.....KU BIYONI MUJE......._
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
[1/23, 20:08] +234 903 555 3736: π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 39*
*AKHNAN*
Idanu kawai takebin mammina dashi,wanda ta zauna tana bude kyautan da suka kusa cinye kaso daya cikin uku na dakin hutawar nata daya bayan daya kowanne tana ajiyeshi a gefe bayan ta bude.
"Ba zaki takura ba da rayuwa dashi.....nasanshi nasan mamanshi tsahon shekaru,bayason takura wannan shi ya hanashi aure tuntuni,yana neman matar da zatayi rayuwarta ne kawai ba tare data dameshi ba.....zaki samu dukkan wata izza daga sunan family dinsu kawai....zaki samu kalar sakakkiyar rayuwar da kikeso......kalli a iya yau kawai kyautukan alfarmar daya sauke miki" Mammina ta fadi tana ci gaba da bude kyautukan,wanda kusan kowanne box dake gurin tasan meye a ciki,amma yadda take nuna zumudinta zaka dauka karon farko data fara ganin kayan alatu na rayuwa irin haka.
Baki kadan akhnan din ta tabe,don sam bataji wata burgewa tattare da almaz ko daya a ranta ba. Eh ta karanci abinda mammina ta fada a kansa,da gaske bayason damuwa,ganinsa na farko ta tabbatar da hakan,ta sauke numfashi kadan tana sake tabe baki tare da tuna awannin baya da suka wuce.
Cikin qasaita dake cakude da fargaba ta yiwa kanta matsugunni saman daya daga cikin lafiyayyun kujerun da aka qawata gurin dasu. Wani irin ado da wani irin yanayi da tunda take ganawa da dukka mazajen da siltane yake mata ba'a taba tsara gurin irin haka ba.
Juyawa birra tayi da nufin fita daga gurin ta basu sarari,saidai a nutse da salon kalar umarnin data saba basu ta tsaida birran,sai birra din ta koma gefe daga bayanta ta tsaya tana sauke kanta a qasa.
Da dukka manyan kyawawan idanunta ta qure mutumin da kallo,wanda ke sanye da wata qawatacciyar alkyabba,bayan takalmin da aka yiwa wani irin qawataccen ado daya zame ya ajiyeshi a gefansa.
Kansa yana duqe a qasa,wanda bazai bata dama da ikon gane fuskarsa da kyau ba,saidai mamaki ya soma ratsata a hankali na rashin tantance bacci yake ko gyangadi?,don sam bataga alamun waya a hannunsa ba ballantana tayi tunanin waya yake dannawa.
Izzarta ta hanata magana,a haka suka shafe a qalla mintina biyar kafin ya motsa a hankali yana daga kansa gami da jinginar da bayansa a kujera.
Idanunsa ne ya soma sauka akan fuskarta,kaman yadda nata idanun suka sauka a kanshi,kallon kallo kuma ya sarqafe tsakaninsu na wasu sakanni kafin ta fara janye idanunta mamaki yana sauka a hankali saman zuciyarta.
"Shin me mammina ta gani tattare dashi data hangi dacewarsu?" Tambayar data soma yawo kenan saman kanta,wadda ta tilasta mata maida idanunta a karo na biyu kansa.
Still shima ita yake kallo,saidai a wannan karon yayi qoqarin sakin murmushin daya dan fidda kyansa ya kuma haska wani abu cikin idanunta. Sake zare dubanta tayi daga kansa tana rasa kowanne feelings a kansa. Soyayya dai dama tasan bata da lokacinta,bama kuma batunta akeyi ba,saidai wannan tarin baqincikin da bacin rai da tsananin tunzura da takeji a zuciyarta a duk sanda wani namiji ya tsaya a gabanta