Showing 24001 words to 27000 words out of 188421 words

Chapter 9 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

76

/>
"Subhanallah" Ya fadi a hankali yana zare idanunsa daga kanta gami da saukesu saman keyboard na system dinsa yana sauraren wani bugu qwaya daya tal da zuciyarsa tayi daya aika jini me gudu da yawa zuwa sassan jikinsa gaba daya.

Shuru yayi yana sauraren kowanne motsi da amsawar da jikinsa yayi gami da yanayin bugun zuciyarsa,can qasan ranshi ayar nan da Allah madaukakin sarki ya saukar zuwa ga muminai maza da mata kan runtse gani tana masa yawo akai(lowering gaze).

Numfashi yaja sosai yana saukeshi,yana kuma qara imani da gasgatawa cewa babu kuskure cikin dukka umarnin da Allah ya bayar. Akwai fitina me yawa cikin KALLO kawai......shi yasa Alla sw t yayi qoqarin datse fitintinu ta hanyar kallo da dama wajen umartar bayinsa su runtse ganinsu.

Numfashin ya sake saukewa a karo na biyu........wani baqon yanayi ne da bai taba jinsa ba akan kallon kowacce diya mace......duk da kasancewarsa ma'abocin kame ganinsa daga kallon dukkan abinda yake ba halalinsa ba.....amma wani lokaci yanayin aiki ko tafiya yakan hadashi da matan da ba musulmai ba da suke shigar data sabawa shari'a,amma bai taba jin komai game dasu akan wannan ba.

"Dole ka sake nisantarta" Zuciyarsa ke gaya masa tana kuma tariyo masa yadda arashi ya dinga hadasu shi da ita da irin kusancin daya kusa zame masa alaqaqai kowanne kwanciya baccinsa.

Kauda idanunsa ya sakeyi daga kan camera din,yana miqa hannu cikin qwarewa yayi cancel front camera din dake kawo masa hoton gaban balcony dinnata ba tare daya kalli system din ba. Sai daya samu wannan tabbacin sannan ya maida dubansa kai yana ci gaba da aikin ba tare daya sake maida idanu ko hankalinsa a kanta ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

[1/6, 19:52] +234 903 555 3736: πŸ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 13*

_________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

___________________________

Qaramin tsaki taja,tana jin wani haushi haushi qasan ranta da batasan na meye ba,sai kawai ta zabi ci gaba da tsaiwa a gurin,tana zuba oil din da take amfani dashi wajen gyara gashinta cikin tafukan hannuwanta tana mutstsukawa a hankali.

Tun kafin su qarasa shigowa muryoyinsu suka marabceta. Shehnaz aisa......su kadai ne ke iya rantsa dukka wasu dakuna nata ba tare da neman izini ko iso ba.....su kadai ne ke iya bata mata tsarinta.....su kadai ne ke iya karya mata dukkan wasu tarin dokokinta.

Tana iya jiyo muryar shehnaz a gaba da wannan harshen nata daya qware ta kuma saba da yawan magana da harshen faransanci. Sam bata iya dogon hira dakai ba tare data sanyoshi ba,sai ta daga kanta a nutse tana dubansu sanda suke shigowa gurin.

"Bansan iya guraren dana shiga nemanki ba wallahi....." Aisa ta fadi idanunta suna sauka a kanshi cikin ba zata,sai magananta ya zama cikin slow.

Sosai ya dauki hankalinta,har bata maida kai wajen jin amsar da akhnan ke qoqarin bata ba. Hannu ta miqa a hankali ta tabo shehnaz tana mata nuni da balcony din.

Hasken system din dake gabansa ya qara sosai don sake bin kowanne siririn ado da zane da yayi a jikin bracelet din,wannan kuma ya taimaka sosai wajen sake haske kyakkyawan fuskarshi dake cakude da wani irin kyau da kwarjini da yawaitar karatun qur'ani ke dawwamar dashi saman fuskar ma'abota karatunsa.

"Sheikh muhammad haisam......twinnie din qira'ar sheikh afif?" Shehnaz ta fada da sigar tambaya bawai don tambayar takeyi ba.

Kai aisa ta gyada tana maida dubanta ga shehnaz.

"Kin sanshi ne?"

"Ke baki sanshi ba?" Shehnaz ta dawo da tambayar ga aisa. Kai aisa ta jinjina.

"A gidan nan na fara ganinsa.....duk da inaji kamar na taba ganinsa,sheikh dinsu falaak ne........don Allah kallarmin guy dinnan sosai.......ta ina yayi miki kama da sheikh.......kinga yadda yake sarrafa system fa?" Aisa tayi maganan tana maida dubanta saman fuskarsa data sake fita tarwai da wani irin kwantaccen kwarjini.

"Na taba ganinsa a wani gidan TV ana hira dashi.......amma tun daga ranar ban manta karatunsa ba......in fact ma qira'arsa folder guda nake da ita.......haka kawai ni tun a ranar yayimin" Shehnaz ta fada itama tana maida dubanta kan fuskarsa.

Haka kawai a cikin jikinsa yake jin akwai wani abu dake faruwa cikin veranda din dake facing nasa.......yana jin kamar akwai idanuwa a kansa,kaman lokacin tashinsa daga gurin yayi,duk da yadda yakejin dadin gurin. Aikinsa yana buqatar sirri me yawan gaske,irin sirrin da baya buqatar ido ko wani kallo komai qanqantarsa. A nutse ya miqa dogon hannunsa ya zare charge din system din,ya tattara dukka wayoyinsa da komai ya zuba saman keyboard din yana miqewa.

Kiran sunan MALAMINSU FALAAK shi yaja hankalinta,baya da niyya ko sau daya ta kalli maganganunsu,amma rarrabuwar da hankalinta yayi da son samun tabbaci ya sanyata maida idanuta gurin cike da tantamar karatun da takeji daga gareshi ne......cike da tantamar shine maqocinta kaf cikin gidan mafi kusanci bayana kusancin da yake cusa kai wajen sultane ya sami?......bayan matsayinta da yake harin karbewa daga hannun sultane?.....matsayin da duk duniya tafi ji dashi sama da kowanne irin matsayi da take dashi?.....shine a ginin da koda sassanta zata shiga sai sunyi tarayya a balcony daya wajen shiga qofofinsu indai bata qofar baya zata shiga ba?......shine a gini a muhallin da sultane kadai take ganin ya kamata ya kuma cancanta ya zauna a gurin,tayi maqotaka dashi?......muhallin da aka tsara fasalinsa tun dan uwanta yana raye a masarautar agadez?.....tun ahmad bai bacewa idanunsu ba?..... Muhallin ahmad ne,shi aka kafawa harsashin gininsa,ya za'ayi wani yazo bayan shekaru ya mamaye gurin bayan mamayar da yakewa sultane a hankali a hankali?. Mamayar data fara ji a jikinta zai wahala idan bata kasance me manufa a cikinta ba?.

"Ya salaammm.......giant.....giant man aisa" Shehnaz dake bala'in son giant din namiji ta fada da yanayin da zai gaya maka da gasken gaske structure na jikinsa ya tafi da ita.

Ta fadi maganar ne a daidai sanda idanun akhnan suka sauka a kansa sanda yake miqewa daga durquson da yayi ya gama aza dukka kayansa saman keyboard din. Maganan shehnaz saita zama kaman tana mata describing dinsa ne..........bata kuma sake bari ta qara second daya idonta a kansa ba ta janye tana jan wani tsaki. Qululun takaici yana kamata,sai ta ajiye man hannunta a hankali,ta zura lausasan flip-flops dinta ta soma takawa zatabar gurin ba tare da dukkaninsu sun ankara ba,daidai sanda taji shehnaz na fadin.

"Wannan dukka tsahonmu kanmu bazai kai kafadarsa ba......ko akhnan banajin kanta zaikai can" Tayi maganan da sautin dake shaidawa akhnan maganan tana bata nishadi.

Furta sunan akhnan din ya sanya aisa ta waiwaya gareta tana murmushi,don tasan sun tsunkulo mutuniyar. Sam indai zasuyi hirar samari ko wani namiji sai sunga bacin ranta,sau tari takanyi banza dasu,har suyi su gama,wani lokaci takan ja tsaki kota jefesu da harara,lokuta daidaiku ne zata sake musu magana ta kuma watsar da hirar tasu kaman bata nan,takan ma zarce da maqala earpiece ne ko saka headphones a kunnenta.

Amma yau din duka tabar musu gurin?. Mamaki kadan ya kama aisa,bata taba barin wajen saidai suyita cakar da ita.....amma yau gurin tabar musu,sai kuma a hankali tunanin mode din da take ciki ya sanya ta mata uzuri,ta tabo shehnaz tana mata nuni da akhnan din,sai kawai suka tattara sukabi bayanta.

Tana jinsu suna biye da ita amma bata dakata ba ta zarce abinta,ta sauka daga stairs din sukayi kacibus da buhaina,tana tafiya tana gaya mata ta fiddo kaya tazo ta shiryata zata gurin mammina......ta gayawa birra ta kasance a kusa zata mata rakiya.

A nutse ta zauna saman ottoman,kamar batasan suna biye da ita ba. Haushinsu takeji,haka kawai tana fama da issue dinta zasu biyota har inda ta kebe kanta da zancan maza?. Bayan mazannan ba komai a tare dasu sai mugunta zalunci da bautar da 'ya mace?. Zallar son kai da yasa suke ganin kamar dole kowacce mace ta zama a qarqashin ikonsu?......rayuwarsu cike take da cutar da 'ya mace da son qasqantar da ita da bautar da ita a qarqashin qafafunsu. Wannan take yaqa......tana ji kuma har abada ba wani namiji da ya isa ta buda masa rayuwarta har ya samu daman cutar da ita ko mulkarta yadda yaga dama.

"Fisabilillahi haka ake tarbar baqi?,baqonka annabinka fa?" Aisa ta fada tana zama gefe daya. Kaman ba zata tanka ba saboda haushinsu da izzarta data motsa,kafin daga bisani da zuciyarta ta tunasar da ita aisanta ca da shehnaz dinta fa.....uwa uba ma idan har bata amsa su din ba ba zasu bar zuciyarta ta huta ba,itama kuma mutum ce bame iya riqe abu ba,koda ta riqe gaba kadan saita furzar maka.

"Wadannan ba baqina bane......ba kuma gurina sukazo ba.....koda baqina ne ma tunda sun samu topic din tattaunawa ni ba gurin zamana bane muhallin tattaunawarsu" Murmushi aisa ta saki,ganin yau duka lokaci daya ta bada doguwar amsa haka kai tsaye,duk da tana cikin yanayin da bata fiya dogon magana haka ba a cikinsa.

"Bansan yaushe zaki gane sirrin dake tattare da irin wadannan mazan ba......."

"Bazan gane ba......kedai tunda kin gane ba shikenan ba......ina cewa kin zabi naki kin kuma samu?". Tace da shehnaz wadda ita tayi maganan. Dariyarta ta qunshe tana gyadawa akhnan kai.

" Qwarai.....amma Allah inda nasan zan hadu da sheikh Muhammad da bazanyi saurin zabar jamaal ba". Wani irin ware idanunta akhnan tayi akan fuskar shehnaz dake nuna dimbin mamakinta. Waisu mazan har wani zaqi ne dasu da wani taste a idanu da har shehnaz keta musayarsu daga wani zuwa wani?.....taketa wasa da hankalin kanta da kanta saboda su?. A qasan ranta taji tabbas shehnaz bata da hankali,namiji qwaya daya ma a yanzu aka bata zabinsa wahala ce nakasa ce kuma tawaya ce ita a tattare da ita ballanta wasu maza har biyu.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Zare idanunta kawai tayi daga cikin na shehnaz wadda ta gyada mata kai tana kore shakkun dake ran akhnan tare da bata tabbacin magananta.

"Ni nasan me na gani........a idanunsa kawai da yanayinsa nasan zai zama romantic man wallahi billahi......wani boyayyen character ne dasu da sai matansu kawai suke sanin wani boyayyen sirrin....." Matsa mata hannu aisa tayi wanda hakan shi ya katse bayanan shehnaz din,saidai ba shehnaz kadai ba......hatta da aisa tana gasgata duk wani maganan shehnaz,amma a yanzu hankalin akhnan suke neman tattarowa ta dawo yanayinta da hayyacinta gudun gurguncewar SAHEL COUTURE da dukkan hasashen aisa abinda take iya ganowa kenan.

Ta kasa jin nutsuwa da gamsuwar hawa kujerar akhnan ko karbar shugabancin kamfanin,sam zuciyarta da ruhinta sun kasa aminta da hakan.

*_SHEIK HAISAM_*

_BAYAN MINTUNA TALATIN DA BIYAR_

Yatsunsa ya tura cikin sumarsa yana yamutsata da kyau bayan fitowarsa daga wanka da daurarren towel a qugunsa,mintuna talatin da biyar kenan daga barowarsa balcony din.

Tabbas......indai har zai fara jin qaqqarfan yanayi har irin wannan a tare dashi.......a sanda yake tsaka da aikin da yafi dukkan aikin daya taba yi a national intelligence security hatsari da muhimmanci......lallai tabbas kuma dole yayi aure. Aure ya kamashi......aure kuma ya kamaceshi da gaske kaman yadda su hakeem suka jima suna zolayarshi da gaya mishi.

A nutse ya taka zuwa gefan gadonsa ya zauna yana sauke zazzafan numfashi daga bakinsa,yatsunsa ya soke cikin na juna. Baya wasa da dukka wani abu da zai iya kaishi ga sabawa Allah komi qanqantarsa,yana kiyaye wannan don yana tsananin kunyar ubangijinsa da kuma kiyaye saba masa. Don ubangijinsa yayi masa dukkan komai da kowanne dan adam yake buqata ga rayuwarsa.

Ya yishi a musulmi.......cikin tsatso ahali da family mafi daukaka shuhura da kuma qarfin iko cikin qasar Ethiopia dama sassan duniya gaba daya. Ya sanyashi ya zama IRI na farko kuma D'A na farko da mahaifansa suka fara samarwa. Yayishi me cikakkiyar lafiya da cikakkiyar surar data zama abar qauna da kwadayi ga halittun jinsin mata. Ya bashi zuzzurfan ilimi ta kowanne sashe.....na addini dana zamani na rayuwar duniya......zuzzurfan karatun bokon daya tabbatar a karan kansa za'a tara dubbanin matasa basu da matakin karatun da yake kai a yanzu a qananun shekaru irin nasa.......matakin da hatta abokansa aminansa shaqiqansa da sukayi rayuwar secondary har suka hada degree tare suie sha'awansa......uwa uba cikin tarin dubbannin addinai dake fadin duniya Allah ya zabeshi ya sanyashi musulmi......wacce ni'ima ce ta Allah da bai cancanci ya gode mata ba?.....

Bazai taba bari shaidan yayi galaba a kansa ba akan AURE......bayan ya cika dukkan sharuda.......yana kuma da ikon yinsa koda mata hudu da qwarqwara yake buqata.....cikin qasa da awa ashirin da hudu zai mallakesu gaba daya.

(*TUNASARWA*:~Yar uwa,yana da kyau ki dinga yawaita tunasar da kanki ni'imomin da Allah yayi miki a rayuwa. A duk sanda zuciya ko rai ya raya miki kiyi wani sabon Allahn....maza ki tunasar da kankin yawan ni'imar da Allah yayi miki,shin ya cancanci ki saka masa ta hanyar saba masa?......ya cancaci wannan sakamakon?...... Anan haisam yana jin kamar ya gaza gurin runtse ganinsa ne kawai.....bawai sabawa Allah yake da sha'awar yi ba,amma sai yake ganin maganin kada ayi kada a fara,bara ya taimakawa kansa wajen sake kiyaye haqqoqin Allah yayi aure.......tunani ne me kyau daya kamata mu dinga yi,qoqarin gujewa da yin nisa da dukkan abinda zai iya kaimu ga shiga hurumin ubangiji,Allah ka bamu ikon binka,ka kuma bamu ikon kaucewa duk wani abu da baka so)

To amma babbar tambayar da yakewa kansa......a daidai wannan gabar da ayyukansa suka fara daukan dumi.......a sanda ayyukansa suka fara bude sabbin qofofi da shafuka......shin ya shirya zama da wata mace ya kuma sauke haqqinta dake wuyansa?......idanma ya shirya WACECE?.

"Saamee" Zuciyarsa tazo masa da amsar da har qasan ruhinsa yaji bata gamsheshi ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

[1/6, 19:55] +234 903 555 3736: πŸ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 14*

__________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

___________________________

Ba wani naqasu ko kasawa da saamee ke dashi......ta cika macen da za'a sota da dukkan quality dinta,to amma hakanan baisan me yasa yakejin a ransa bata hau mizani ba. Ya jima yana bincikar kansa me yasa yakejin kamar saamee ta rasa wani abu?.....me yasa yakejin kamar akwai wani hali dabi'a da yake nema da saamee ta rasa?. Ya dade yana tambayar kansa indai har saamee nada wani dabi'a ko halayya data rasa.....wacece?.....wacece zatayi?,wacece kuma zata cika?. Amsar daya ce har yau BAI SANI BA.....BAISAN ME TA RASA BA.....BESAN KUMA ME TAKE NEMA BA.

Abu daya daya sani wanda baisan ko yana da alaqa da ganin gazawar saamee ba bawai don ta gaza din ba?..... Mutum ne da komai yafison ya mallakeshi da JARUMTARSA......komai yafison yayi YAQI kansa bawai ya sameshi daga kwance ba. Jininsa na GWAGWARMAYA NE......yana ganin komai akayi yaqi a kansa yafi zama da kima da daraja.....anfi kuma riqeshi da dukkan qarfi.......har abada kuma idan zaka kalli wannan abun zakafi tuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login