Showing 36001 words to 39000 words out of 188421 words

Chapter 13 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

117

irin walqiya me kashe idanu da wata irin tsawa gauraye ta karade sararin samaniya. Idanunsa ya lumshe yana motsa labbansa a hankali da addu'ar tsawa da ma'aiki ya koyar

"Alhamdulillahil lazi yusabbihur ra'adi bi hamdihi.....walmala'ikatu min kifatih". A hankali ya bude idanunsa suka kuma sauka a kanta. Tana tsugunne a qasa ta cure guri daya. Ko ina na jikinta rawa yake,wanda yake bayyanar da tsananij tsoro a tattare da ita me yawan gaske.

Idonsa ya sake daukewa ya maida gefe,sai ya qara sautinsa yana maimaita addu'ar a fili daidai da yadda zata iya ji.

Duk da muradinsa shine ya wuceta abinsa kafin bacin ransa yakai ga bayyana......amma fuskar sultane yake iya hanga a gurin......kebantattun maganganunsa da sukayi......maganganun da suka tilasta masa aminta da alfarmar da sultane ya nema a tare dashi bai ko iya musa masa ba.

"Ko yaya idan akhnan na cikin hadari.....nakanji wani abu a jikina,nauye nauye sunyimin yawa.......bazata samu kulawata yadda ya kamata ba,don Allah ko yaya koda sau daya ka zama me kula da lamarin daya shafeta daidai yadda zaka iya,ba don kowa ba saidon GIRMAN ZATIN ALLAH" Sautukan dake dawo masa kenan a yanzu.....yana kuma sake ji da ganin yadda dan qaramin amincin dake tsakaninsa da sultane keson takurashi.

A tsanake ya juya a hankali yana nufar sashen qofar balcony din nata bayan wasu sakanni. Maqullansa ya zaro,cikin hikima irinta qwarrarun jami'ai da suka goge ta fannin aikin tsaro binciken sirri dana qwaqwafi ya bude qofar. Takowa yayi a nutse yana dawowa nashi qofar,tsugunnawarta ya bashi space sosai da ya samu ya wuce a tsanake,ya isa qofar balcony din nasa ya zura key ya bude qofar ya turata sanna ya sanya qafarsa a hankali bakinsa dauke da addu'ar shiga gida.

Da sauri ta daga kanta sannan ta waiwaya zuwa bayanta,daidai sanda yake maida qofarsa ya kulle abinsa.

Zumbur ta miqe tana waiwayen hagunta da damanta. A yanzun ba kowa a gurin,a yanzun ita daya ce sai ruwan saman dake sauka,wani tsoro ya sake mamayarta,ba shiri ta fara tattakawa da sassarfa tana nufar qofartata wanda ta sameta a bude,da hanzari ta shige sannan ta maidata ta rufe tana maida numfashi a jejjere kamar wadda tayi tseren gudu.

Sai data kusa kashe a qalla mintuna goma sannan numfashinta ya daidaita,ta saka hannu ta zare yalolon mayafinta daya jiqe ta yar a gefe,ya kuma sauka daidai kwandon Cherry dinta dake dauke da Cherry din. Wani tsaki taja baqinciki yana taso mata.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 18*

_________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

__________________________

Yadda yayi matan yafi zubda Cherry din bata mata rai,ita zaya bari a gurin da ko izinin tafiya bata bashi ba?.....wai yana Manta wacece ita?......baiga yadda kowa ke treating nata ba da kulawa da kuma respect?.........matsayinta yake mantawa ko kuwa?.....lallai dole ta sanyashi yayi dana sanin aikinsa a kanta....dole ta sakashi ya koyi yadda zai girmamata......ko wanne matsayi kuwa sultane ya bashi dole ya gane akwai banbamci tsakanin d'an gida da yaron gida.

Inda wani abun ya sameta a inda ya barta ma kenan baida asara shi?. To waye ya bude qofar balcony din?,don tayi imanin ba wani a kusa ballantana ta dauka shine ya bude,saita dora tafin hannunta saman kanta tana jin gaba daya lissafinta yana dagulewa. Ta saba da a girmamata cikin kome da zata buqata........ta saba ta bada umarni nakai tsaye abi........ta saba tayi kome da takeso bame iya daga kai ya kalli qwayar idanunta ballantana yace tayi ba daidai ba......a yau din sai takejin kamar an mata babban wulaqancin da duk duniya ba abinda yake sama da wannan,sai kawai ta juya tana shigewa ciki cikin wani irin fusataccen yanayi.

Duk sunan hadimar da yazo bakinta shi take kira da qarfi,wani irin gini ne da ruwan da akeyi a waje sam idan kana ciki ba zaka sani ba saidai ko idan ka kalli windows ko glass doors din da aka qawata wasu bangwayen dasu,wannan ya bawa duk wadanda ke kusa da nan damar jin muryar uwar gijiyar tasu,suka kuma bar dukkan abinda sukeso kowacce ta taso don amsa kiranta.

Kamar kowanne mutum da ya kwana ya tashi cikin agadez qasa sukayi da kawunansu kamar yadda suke tsugunne a gabanta.

"Uban waye yace ku tafi ku kwanta ba tare dana shigo ba?" Tayi tambayar data bawa kowa mamaki a cikinsu,kasancewar sunsan tsarikanta. A lokuta irin wannan bata buqatar a dameta,bata buqatar kuma kowacce irin hayaniya a kusa da ita,kowa yasan wannan,kowa ya haddace wannan,don haka kusan tafiya kowa yake zuwa makwancinsa.

Maimakon ta dauki shurunsa a matsayin girmamawa,don babu me iya bata amsa a cikinsu,sai kuma hakan ya tunzarata da wani irin kalar bacin rai. Fada sosai ta dinga yi,kalar fadan daya sake bawa kowa mamaki a cikinsu......kalar fadan da ko sanda tasha guba bata yishi ba.

"Ranki ya dade...." Birra dake da wannan qarfin halin ta matso dab da ita ta fada da yanayin da yaja hankalinta kadan.

"Kayanki a jiqe suke,sanyi yanata shigarki.....kiyi haquri ki canza kaya sai kizo kiyi mana duk kalar hukuncin daya dace". Maganan birra kenan data sauketa,ta juya tana haurawa zuwa sama a zafafe ba tare data sake bi takan kowa ba,tana isa kuma ta wuce dakin data zaba kwana a ciki ta murza key,don ko birran bata buqatar ta kusantota a sannan.

Da d'aya da d'aya ya rage hasken fitilun dakin yana jin zuciyarsa wani iri ba dadi. Fushi ke motsa masa amma yanata maimaita a'uzubillahi minashshaidanir rajeem don ya sani saukowar fushi daga shaidanne.

Yana saisaita room heater ko zai samu sanyin jikinsa ya ragu ya fahimci omari yana nemansa,sai ya qarasa ya dauki na'urar ya azata saman table hade da wayarsa da damshi kadan ya tabata,ya sakata a hands free yana yana qoqarin balle links din hannun rigarsa don zare rigar daga jikinsa,ruwan da ya tabashin ya sanya wani lallausan qamshi na tashi a jikinsa na unique perfume dinsa.

"Barka da dare captain sheikh" Omari ya fada da salon tsokanar da wani lokaci yakanji sha'awar tsokanarsa da ita.

"Yauwa" Ya amsa masa can qasan maqoshinsa,adams apple dinsa yana motsawa daga sama zuwa qasa,daya daga cikin alamun fushinsa kenan.

Dan shuru omar yayi,yana jin sauyi tattare da haisam din,saidai kuma ya sani,shi din wani kalar introvert person ne,ko a yanzun daya dauka wayarsa yana kyautata zaton haisam din yana tsammanin maganar aiki ce,baisan wasu awanni zai nema a bashi ba.

"Ya palace din?" Ya tambaya a taqaice kada sakannin daya ware na amsashi ya qare.

"Fine" Kawai yace yana zare rigar samanshi,fara qal din cotton singlet dinsa tana bayyana wadda ta lafe a jikinsa,ta kuma fidda qirar ginannen jikinsa da faffadan qirjinsa dake cike da lallausar gargasa.

"Awa ashirin da hudu nakeso a bani aro" Omar ya fada

"Zuwa ina?" Ya tambayeshi yana duqawa zuwa ga fuskar wayar ranshi yana jin yana sake jagulewa.

"Zinder kawai zanje....."

"No..." Ya fada kai tsaye yana katseshi.

"Baka tambayeni abinda zanje nayi ba"

"Ba buqatar hakan" Ya sake amsashi a taqaice.

"Just 24hrs fa?"

"I said nooooo!....." Ya fadi a zafafe da wannan zuzzurfar muryar tasa.

Shuru ne ya ratsa tsakaninsa da omar din,lumshe idanunsa omari yayi yana ji a ransa akwai abinda ya taba zuciyarsa a yau din. Ya sani haisam din yana da fahimta yana kuma da sauqin hali.....saidai idan ya tashi baudewa ko bacin rai yana da tsananin taurin kai da kafiya. Ba ma'abocin fada bane.....don yafi ganewa shuru a yawancin lokutan da ransa ya baci maimakon magana ko nunawa a aikace......dole yasan akwai abinda ya taba ranshi daya sakashi replying masa maganansa a haka.

Wayar kawai omari ya sauke a kunnensa sanda yaji alamun ya gintse wayar,qaramin murmushi yayi ya ajeta gefe,ya jawo daya wayar tasa yaci gaba da amfani da ita,da cikakken tabbacin haisam din zai sake nemansa.

Silent ya maida wayar da kuma na'urar tasa,ya sanya dukka yatsunsa goma cikin jiqaqqiyar sumarsa yana jin yadda ransa yake sake dagulewa.

Kome meye ya zama dole ya gaggauta matse kwanakin aikinsa yabar masarautar. A dazun banda tasirin sabo da aikinsa da yayi,saura kadan wannan jinin na SARAUTA dake motsawa cikin jininsa ya sanyashi yin wani abu da yasan dole zai d'arsa zargin WAYESHI a zuciyar yarinyar.

"She's stubborn......" Ya fada yana motsa fresh lips dinsa da suka sake wani irin kyau da daukan hankali.

Numfashi sosai yaja ya kuma fesar,ya lumshe idonsa yana budesu sanda yake nufar hanyar bathroom. Me yasa?......me yasa?,tambayar da yaketa maimaitawa kansa da kansa kenan,ba tare da yasan akan ainihin meye yake tambayar ba.

Yana da hadari a karan kansa ya sani......aikinsa ya dauke hankalinsa daga kan komai da kuma qoqarin bin umarnin Allah da yake cewa.

"Ka gayawa muminai maza mu runtse ganinsu su kuma kiyaye farjinansu" Me yasa take qoqarin shiga kowanne runtse ganinsa?....kame kansa da idanunsa?.

"Me yasa kake damuwa bayan a baya baya damunka?" Zuciyarsa ta jefa masa tambayar sanda ruwan daya saisaita ta hanyar shower me tsananin dumi ya soma sauka tsakiyar kansa.

"Zaka kai lokacin da duk wani guje guje bazai maka ba saidai aure......kana da lafiya......cikakkiyar lafiyar da ba kowa keda irinta ba......kaga kuwa aure ya zama wajibi....dole a kanka.......ka gama duk ayyukanka na watanni ko shekarun daka tsara....wallahi dole sai aure.....shi kadai ne ya dace dakai". Daga daga cikin maganganun amjad kenan a wani yammaci da suka shirya picnic cikin gari jimma iya su yasu.

Baice da khadeem komai ba,shi da Amjad dake goyon bayansa,ya bishi ne da idanu kawai. Bakasafai ya fiya magana me tsaho da khadeem ba,don ta fannin magana ba zaka taba kadashi ba,don baya gajiya da ita......shi kuma daya daga cikin abubuwan dake masa wahala kenan,musu ko maimaita magana,yafi ganewa zama shuru don yafi bashi nutsuwa da nazartar abubuwa a yanayin da suka dace. Wannan ya sanya maleek wani lokacin yakan kirashi da mr introvert bayan mr lowering gaze da suka bashi.

Murmushi kadan yakanyi,bai hana kowa kiranshi da sunan da yayi masa ba a tsakaninsu su shidan,don kusan alaqa ce da aka ginata tun kafin a gama mallakar hankalin kai.

Duk wani magana da bayani da sukeyi akan aure ya sani.......ya karanta komai,yana da tarin ilimi akan aure da ma'amalolinsa wanda su sam basusan yana dashi ba.......ya tara ilimi akan fannnin aure da mu'amalar miji da mata masu tarin yawa cikin litattafan manya manyan malaman addini masana asalin ilimin zamantakewa wanda basu da adadi. Ya karanci zamantakewa a gidaje masu yawa......gidajen sahabbai gidan annabi S A W kanshi baisan adadin littatafan daya dubasu ba.....bugu da qari ya fisu sanin aure ya wajabta a wuyansa.......don idan akwai inda yake da rauni to ta wannan fannin ne.....shi yasa ya lazamci azumi ya kuma lazumci kame idanunsa da nesanta kansa daga dukkan wata mu'amala data shafi 'ya'ya mata.....to amma yanaso ya yishi ne a sanda ya samu gamsuwar zai iya doguwar rayuwar da BABU SAKI tsakaninsa da duk macen da zai aura din.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yanason ya zabi macen da yakejin komai nata yayi masa,macen da hankalinsa bazai sake kaiwa kan kowacce 'ya mace ba bayan ita.......yanason kuma komai ya kasance a right time da zai spending rayuwarshi da ita cikin tarin nutsuwar da zataji a ranta gidanta na aljanna......mijinta na aljanna ne aka gaggauto mata dashi duniya.....ba a irin wannan lokacin da ta kowanne bangare tunaninsa yake a jagule da rashin samun gamsuwa da tsaro rai lafiya da rayuwar motii ba.

A gaggauce ya shirya kansa cikin wata long sleeve riga ne nauyi da zata bashi kalar dumin da yakeso,sannan ya sanya wandonta da yake mahadin rigar. Yana gaban mirror yana sake kwantar da sumarsa tunanin abinda ya faru dazu ya sake dawo masa. Dauke idonsa yayi daga mirror din yana jan tsaki jin yadda tsigar jikinsa ta zuba.

Bata da kunya ko kadan.......shi din kuma mutum ne me mutuntawa da baya shiri da masu wannan dabi'ar,wannan ya sanya ya tsaya tsayin daka akan ANANI sanda ta fara irin wannan dabi'un,sai daya tabbatar ya saitata yadda ya dace.

Da kanshi ya hadawa kansa coffee,yana jin sassan ya masa shuru. Dole tasa ya sanya abdii ya koma personal gidansa,don kwanakin kadan kadan ya tsara zai dinga yi yana komawa ainihin gidansu,harsai sanda yaga abdii din ya dauki saiti da salon da yakeso,ya kiyaye duk abinda yace ya kiyaye din.

Hannun hagunsa ya soke cikin aljihun wandon nasa,na damansa kuma yana sipping coffee din kadan kadan. Shan tea da coffee wata halittacciyar halitta ce a jinin duk wani dan Ethiopia,musamman jimma oromia dake noman coffee din gaba daya.

Cup din ya dire bayan ya shanye,omari yana fado masa,sai a yanzun yaji kamar baiwa omar din daidai ba. Aboki ne kuma dan uwa shaqiqi a gareshi,saidai wasu lokutan dole yanayin aiki ya sanya ya mu'amalanceshi irin mu'amalar uban gida da yaronsa.....don komai a rayuwa yana buqatar saiti.

Na'urar ya dauka ya kunna,ya kuma tura masa permission letter gajeriya ya tura masa. Sanda saqon ya sameshi murmushi ya saki,dama ya sani......indai haisam ne zai dawo. Dabi'unsa masu ban sha'awa ne qwarai da burgewa,saiya maida masa amsa cikin girmamawa a matsayinsa na ogansa bawai abokinsa ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[1/9, 19:36] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 19*



โ˜…โ˜…โ˜…Dare makwantar mugu inji hausawa......tabbas haka yake,a irin wannan daya daga cikin wadannan dararen da suka kasance da busawar sanyi sakamakon saukar ruwan saman da aka samu a daren jiya,hakan sai ya zamanto sanadin daukewar sawayen mutane da wuri daga waje zuwa gidajensu dama dakunan baccinsu.

A tsakiyar wannan daren mammina ke ratsa cikin unguwar. Daga gefanta TA FISU ce......tafisun da sunanta yayi daidai da aikinta dama alfanunta a gurin mammina. Tafusun ta kasance wani bangare me girma da muhimmanci tattare da mammina wanda yawancin mutane basu san da hakan ba basu kuma fahimci haka ba.

Duk da kasancewar ta fisu me girman matsayi a sassan mammina din......amma dukkan wani aiki da motsi nata yana nuna zallar rashin jituwa da rashin samun fada da fuska tattare da mammina din.

Yana da wahala ka samesu sun kebe.....kamar yadda yake da wahala kaji ta ambaci sunanta idan har wani muhimmin abu ya taso mata. Hasalima saita kasance me yawan tafiye tafiye.....don kusan cikin gidan kowa ya sani cewa tana tafiya wasu qasashen sarin kayan kasuwancinta,tazo dasu gidan ta siyar tas ta sake komawa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login