Showing 3001 words to 6000 words out of 188421 words

Chapter 2 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

69

bayanta,abinda ya hanata kaiwa qasa kenan.

Numfashi ta sake zuqa da wani irin qarfin daya sabbabawa qirjinta dagawa. Fata take ta samu koda qarin mintuna ne da zata tabbatarwa kanta shine yake tallafe da ita......shine yake riqe da ita,kamar dai a wancan lokacin.....

.a wannan filin.......a wannan yanayin da thunder yaso kayar da ita,tana ganin gurin yana ninka duhu a idanunta da ainihin duhun data sanshi dashi,amma still fuskar nan......idanuwan nan masu wani irin kaifi sun juye mata......ranar da lokacin duka a yanzu suna dawo mata kamar yanzu abun ya faru. Hancinta na sheqar qamshinsa fiye da ko yaushe,fiye da yadda ta saba jinsa......da wani irin kusanci,da wani irin taushi,kamar dukka duniya ta tattaru a iya gurinne.

Bakinta da zuciyarta na dauke da maganganu......na dauke da abubuwa da yawan gaske da zataso fada.......zataso tayi abubuwa da yawa a gurin,amma tana jin kamar duniyarta tana qarewa,kamar numfashinta na qarshe take zuqa. Qirjinta na qara matsewa da yadda ta tabbatar cikin hannuwansa take a yanxu haka,kuma batajin zata iyayin komai akan hakan

"Toi encore toi?......pourqoui toujours toi? (Kai?.....kaine kuma dai......me yasa ko yaushe sai kai?" Ta motsa labbanta tana maganan a hankali muryarta tana kakkaryewa....ganinta na qoqarin dusashewa amma tana qoqarin tsaidashi.

Janye idanun nasa yayi da sauri daga kan labbanta yana lumshesu gami da furta

"Hasbunallahu wani'imal wakeel" Saboda sosai wani irin abu yayi tasiri cikin jikinsa......tsigar jikinsa yayi mummunar zubawar da banda namijin qoqarin da yayi ba abinda zai hanashi saketa a gurin. Mamakin qarfin halinta yakeyi,yasan akan me take magana,tunda already shi din ya riga yasan wacece........amma a wannan yanayin da take......a abinda yake iya hasashe?.

Sake maida dubansa kanta yayi karo na biyu,dabara tana qwace masa na abinda ya kamata yayi. Idanunsa ya sake sauka saman lips dinta,saidai abinda ya gani a karo na biyu ya dakeshi sosai.

A dazu a kuma dukka ganinta da yayi a rayuwarshi idan bai manta ba pink lips ne da ita......amma a yanzun lips din canzawa suke suna komawa wani color na daban.

Wannana abun daya gani ya sanyashi matsawa da fuskarsa dab da tata zuciyarsa na bugawa a hankali saboda irin kusancin da suka samu me yawan gaske. Idanunta ta lumshe abubuwa biyu suna kutsawa cikin rayuwarta da takejin kamar tana kan gargara,na farko gaurayar numfashinsu guri guda da suka fara musayarsa wanda duk numfashin da take zuqarsa da qyar dinnan yana cakuda da wannan qamshin dai natacce......na biyu kuma wani abune taji ya taso a qirjinta zuwa maqogoronta ya kuma ga mafitar numfashinta na qarshe.

"Subhanal malikul quddus" Ya fadi da hanzari saboda kai hancinsa da yayi daidai lips dinta.

"Qaseera" Sunan ya doka a tsakiyar kanshi farat daya. Baya manta komai......kaman yadda baya manta dukkan wani training daya samu a yayin horon aikinsa. Dukka wani training nasa yazo ne cakude da personal baiwan da Allah ya bashi.

Qwayar idanunta ya sake kalla,a hankali suna sauya launi zuwa kalar yellow daya sake tabbatar masa qaseera tasha.

"How comes?" Ya tambayi kansa da kansa idanunsa still a kanta yana jin wani irin yanayi yana ratsashi. Laluben sunanta ya soma yi cikin kansa,don ya zame dole yayi keeping maimaita sunanta don ya samu yadan riqeta conscious.

"Akhnaaan" Ya furta sunan da wani irin sauti da zai gaya maka akwai banbancin yare a tsakaninsu. Idanunta da suka lumshe,ruwan hawaye kuma na azaba ya soma jiqa zara zaran eyelashes dinta ta bude a hankali,ya kalli tsakiyar idanunta yana ganin yadda blue pupil dinta ya nutse cikin sclera(farin dake cikin idanu) wanda suka canza zuwa yellow din.

Har tsakiyar kanta taji kiran,duk da yadda take kokawa da numfashinta. Da hanzari ya dagata cak wani abu yana dukan qirjinta ya soma takawa da ita ganin dafara kadan saman labbanta da suka koma purple shar.

โ˜…"Alhamdulillah". Morsa safiyya ta furta sanda motocinta sukayi parking a muhallin adana motoci na sassanta. Tana shirin daga idanunta taji an bude mata bangaren da take zaune,koda ta daga idanu sai taga Armelle ce wadda ta sadda kanta qasa ta kuma ja da baya riqe da murfin motar.

"Armelle......ina kyautata zaton ke kika koyawa falaak shegen son kada nayi nisa.....duka duka fa ko awa daya banyi ba,ba'a kammala karbar lefen bama na taho......" Ga mamakinta gyada kai kawai armelle tayi,sai ta zubawa armelle idanu.......tana hangen wani baqon yanayi a tattare da ita,amma batayi gaggawar tambaya ba,har zuwa sanda ta sako qafafunta waje.

A mamakance take bin dukka fuskokinsu da kallo,kusan kowa ta kalla a cikinsu sai taga ba wani sauran kuzari ko fara'a a tattare dashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Armelle?......me yake faruwa yau?....tun daga farkon gate nake ganin gidan ba kamar yadda na fita na barshi ba" . A nutse armelle ta saukar da kanta qasa,tana jin wani irin nauyi. Ta yaya matar data sadaukar da dukiyarta girma da matsayin da Allah ya bata domin inganta rayuwarsu da qoqarin sakasu farinciki?,ta yaya ita din zata zama mutum ta farko da zata zo mata da mummunan labarin da tayi imani ba wani labari mafi muni a gurinta da zai biyo bayansa.

Sautin murya da kukan falaak shine ya fanshi armelle,abinda ya sanya armelle janyewa baya a hankali,ya kuma saka morsa safiyya waiwaya zuwa ga inda takejin sautin kuka yana fita.

Falaak ce......cikin gudu gudu sauri sauri,abinda ya tsinka jinin morsa safiyya kena,ya sanyata mata tarin fargabar data hanata motsawa,har falaak ta qaraso ta kuma zube a jikinta tana rungume morsa safiyya da kyau tana sakin wani sabon kukan daya ratsa har tsakiyar tsokar zuciyar morsa safiyya din. Shafa gadon bayan falaak kawai takeyi,ta gaza tambayarta komai saboda tsoron abinda zataji. Kukan da falaak takeyi kuka ne me tsananin nauyi da ko wanda ke nesa ya jishi yasan yana fita ne direct ne daga ainihin cikin zuciyarta.

"Momma.......yaa biftu tasha guba......tasha guba momma.......tana can batasan inda hankalinta yake ba" Falaak ta qarasa fada tana fashewa da sabon kuka. Wani irin dokawa qirjin morsa safiyya yayi da wani kalar tashin hankali.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.......innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta maimaita sau kusan hudu tana qoqarin tattara hankalinta da a yanzu tasan tafi buqatarsa sama da komai.



A hankali ta sanya hannu ta zare falaak daga jikinta,sai ta miqa hannun ta damqi tsintsiyar hannun falaak.

"Tana ina?".

"Sassanta......amma mammina tasa an hana kowa shiga.......daga ita sai bappi ne a ciki" Falaak din ta fadi cikin jin ciwon yadda taso shiga din,amma mammina ta leqo tana gaya mata kukanta zai tta'azzara yanayin da akhnan take ciki,so ta tsaya a baya ta mata addu'a.

Ko gane sauran bayanan falaak morsa batayi ba,tasan kawai tace dasu armelle

"Ku wuce bakin ayyukanku" Taci gaba da jan hannun falaak suna takawa zuwa shiyyar da zata sadata da sassan akhnan din.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[12/31, 19:36] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 05*

___________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

________________________________

Shuru kawai parlor din ya dauka,kai kace babu wani sauran me rai dake raye a cikin sa. Cikin wani irin salubabben yanayi sultane ke tsaye gaban akhnan,cikin wani yanayi dashi kansa bazai iya fassarashi ba.

Tsahon mintuna kafin ya tsugunna gabanta a hankali,inda take kwance kawai,banbancinta da gawa qalilanne. Hannunsa ya sanya ta qasan duvet din da take lullube dashi ya kamo hannunta,wani irin sanyi tafukan hannun nata sukayi,a hankali ya furta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". A nutse haisam dake tsaye gefe daya ya daga idanunsa ya zube akan sultane din,dukkan jikinsa yana jin ya masa wani iri. Tun wanzuwarsu a gurin har zuwa kwantar da ita da akayi da bata taimakon farko da yayi gudun kada illar gubar tayi barnar da ba zata gyaru ba,bai sake daga idanunsa ya kalleta ba ko sau daya.

Kwata kwata tsaiwarsa a gurin ma ta zame masa kamar lalura ne kawai saboda shigowar me martaba a sanda yake qoqarin fita,shigowar da sultane din kuma yayi,wani yanayi yake ciki da yake buqatar wani a kusa,wanin da zai riqe koda hannunsa ne yaji sassautin abinda yakeji.

Yanayin sultane din kadai ya gama bayyanawa haisam rudun da yake ciki,saidai zallar jarumta irin ta basaraken mutum,irin jarumtar dake nasa jinin kenan shima,irin jarumtar kuma da aka sani cikin jinin dukka wanda yake da jibi da SARAUTA.

"Muhammad" Sultane ya kirashi muryarsa da tayi laushi can qasa,kansa kawai haisam ya daga yana duban sultane din,saidai kafin yace komai muryar mammina cikin wani irin yanayi ta tunkarosu,sai kuma gata ta iso.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.......ya Allah.......ya Allah ka taimakemu.....ka rufa mana asiri.....kar ka bari wani abu ya samu yarinyar nan" Tayi maganan sanda take wucewa kai tsaye zuwa ga inda akhnan ke kwance numfashinta yana fita da wani irin yanayi da ba haka ya saba fita ba.

Gaba daya ta rungumeta cikin jikinta,wani irin kuka me tafe da hawaye ya qwace mata.

"Me yasa zaki aikata haka?,me yasa zaki illata kanki akhnan?.....ashe dama baki haqura ba?,dama baki janye kalamanki ba?,dama da gaske kike sai kin sha din........Allah ka taimakamin.......d'iyata ya Allah" Ta qarashe fadi tana sakin wani sabon kukan.

A hankali ya lumshe idanunsa sai kuma ya budesu,ya motsa a hankali yana gyara hannun rigarsa. Yana da nufin fita ne daga sassan gaba daya,don dama dole ke tsaye dashi a gurin,shi ya gama nashi part din,ya gama iya abinda zai iya. Bayason kallon drama din matar nan,kanshi shuru yafi buqata,hayaniyarta kuma ya karanci me yawa ce,da gaske damunsa zatayi.

"Muhammad........ba wani qarin taimakon da zaka mata?,likita baya kusa........amma yana hanyan isowa" Sultane ya fada cikin wata muguwar karaya yana dauke idanunsa daga kan mammina,kalamanta kuma suna huda qirjinsa,karayar data sanya tausayin sultane din saukar masa lokaci guda.

Lallai koda ba'a gaya maka ba zaka fahimci tsantsar soyayyar da sultane yakewa akhnan......sosai haisam ya gama fahimtar irin girman wannan qauna da soyayyar....wadda a ransa yakejin indai har yana son yarinyar har haka,to lallai ba qaramin qoqari yayi ba gurin horata ta hanyar aura mata wanda babban muradinta shine ya janye aura mata shi din.

"Akwai........za'a iya bata injection na Atropine" Ya furta a hankali,duk da yana jin kamar bai dace ya buda sirrinsa ba ko yaya ne.

Ga duk wanda ya qware a aikin binciken sirri a qasarsu,suna da horo na musamman wajen irin wadannan abubuwa saboda shirin kota kwana da kuma yiwuwar faruwar irin wadannan abubuwa kan daya daga cikinsu ko su kansu,sirrinsu ne da ba wanda ya sani,amma a yanzun da yake kallon tsakiyar idanun sultane din dake jirkice da tarin rudani da abubuwa iri daban daban......yanajin kamar wajibinsa ne ya taimaka.......kwanyarsa kuma na bankado masa daya daga cikin ayoyin qur'ani dake fadin DUK WANDA YA RAYA RAI QWAYA DAYA TAMKAR YA RAYA MUTANE GABA DAYA NE kamar yadda farkon ayar ke fadin idan ka kashe rai daya kaman ka kashe al'umma gaba daya ne.

Cikin wani irin gaggawa da zafi sultane ya saki umarnin nemo ruwan allurar ko a ina yake cikin qasa da mintuna goma.

*MORSA*

Dukka hankalinta dama tunaninta baya tattare da ita sam sam. Kawai dai tana d'aga qafarta tana kuma saukewa ne bisa tabbacin ba zata fadi ba,saboda ko ina na cikin gidan wani shimfidadden terrazzo ne me matuqar kyau da daukan hankali.

Kukan falaak kawai ke yawo cikin qirjinta da kunnuwanta,yadda falaak ke kuka yana sake tabata gami da sake motsa wani tashin hankalin a tare da ita. Wai akhnan ta sha guba?......guba dai?,ko daya hankalinta da zuciyarta basu dauka ba basu kuma nutsu ba.

Tana tunkaro sassan akhnan din duk wani hadimi dake tsaron gurin wanda mammina ta sanya ya soma buda mata hanya ba tare da tace komai ba,taci gaba da kutsawa falaak na riqe a hannunta.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Shine abinda bakin mammina ke maimaitawa tana riqe da akhnan cikin jikinta. Ko ina ina jikin mammina rawa yake,wani irin tashin hakali yana bayyana kansa saman fuskarta,hatta da hailalan da take ambatawa bakinta rawa kawai yakeyi.

A nutse da irin nutsuwar da ba kasafai take barin gangar jikinsa ba ya taka zuwa ga box din da yasa aka shigo masa dashi yanzun na allurar daya buqata din.

Kunnuwansa suna kan sautukan mammina da bakinta ya kasa daina maimaita hailalan da takeyi duk da yadda yakeso ya raba kanshi da hayaniyar matar,a daidai lokacin da sultane ke tsaye saman kansu idanunsa akan akhnan din cikin wani irin yanayi me wuyar fassara,ya kasa matsawa,abinda ke yawo cikin kansa kawai shine zantukan mammaina data furta dazu

"Kenan dama ita ta shirya poisoning din kanta?" Tambayar da yaketa maimaitawa kansa ita kenan.

Tun dazun ya gaza sake cewa komai,yanayinsa wani yanayi me wahalar fassara da kai tsaye ba zaka iya karantar abinda yake ranshi ba.

Tas haisam ya zuqe ruwan allurar da nutsuwa,a daidai sanda gaba daya hankalin mammina ke kanshi. Qatotuwar ayar tambaya ta ajiye

"Me ya hada malami da iya allura?.....meye hadinsa duka duka da harkar lafiya?" Ta fadi tana nazartarshi da wani irin yanayi da ba lallai ka fahimta ba.

Yana fidda iskar data shiga cikin syringe din sallamar morsa safiyya da muryarta ke shaking ta wanzu a falon,abinda ya janye hankalinsu su duka kenan,banda haisam da yaci gaba da abinda yake a qoqarinsa na bata allurar ya kuma fice daga gurin don bawa iyalin daman ci gaba da abinda ya shafesu.

"Sheik muhammad" Falaak dake maqale a bayan morsa safiyya ta fadi da sautin da morsa dince kawai ta jishi,saita dan dubi sashen da falaak din ke kalla kafin ta zare idanunta daga kansa. A karon farko data kalleshi cikin yanayinta da ba na nutsuwa ba,ta hangi tarin kamala da kuma nutsuwa a tattare dashi.

Wani kallo mammina din ke bin morsa safiyya dashi,saidai kallo ne dake qudundune tsakanin duffan daba kowa zai masa fahimta ta kai tsaye ba.

Kai tsaye morsa safiyya ta isa gabansu idanunta akan akhnan dake jikin mammina. Idanunta suna bude,amma ba alamar tana iya gani ne ko gane kowa......ba kuma alamar tana tare dasu a duniyarsu,ba kuma alamar tana fahimtar abinda ke gudana a dakin.

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Abinda morsa safiyya ta maimaita kena har sau uku tana qoqari kada ta rasa nutsuwarta a tare da ita. Hannunta ta miqa a hankali ta aza saman qirjin akhnan. Yanayin bugun zuciyarta da fitar numfashinta sai ya tuna mata WATA RANA WANI YANAYI makamancin wannan......a sanda SAFEENA mahaifiya ga akhnan ke kwance a qirjinta kamar a haka,a sanda a hankali tana furta kalmar shahada har harshenta ya karye,ruhinta kuma ya fita daga gangar jikinta.

Jarumtarta ce taji ta karye,hawaye suka taru sosai a idanunta. Mammina dake karance da ita wani boyayyen murmushi ya subuce mata,sai ta saitashi ta kuma dulmiyashi cikin tsakanin kwataccen baqincikin dake saman fuskarta,da wata raunannan murya tace

"Momma safiyya......kinga kalar ibtila'in daya samemu?,wallahi ban taba tunanin biftu zata aikata abinda ta furta ba....." Ta qarashe maganan hawaye na gangarowa daga idanunta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login