Showing 75001 words to 78000 words out of 188421 words
dake cike da miskilanci,rashin walwala da kuma takurar da takeji tun daga zuciyarta harma da ilahirin rayuwarta gaba daya. Saidai duk da hakan ba zaka rasa hangen wannan sassanyan kyan a tattare da ita ba sanda take saukowa daga cikin motar data kasance mallakinta,bayan ta raka aisa ta tashi zuwa Niamey ta filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez din.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
[1/21, 19:16] +234 903 555 3736: π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 36*
Kamar kowanne lokaci hadimanta guda biyar din dukka suka kasance tare da ita cikin hidimarta,birra na cire sauran diguwar rigarta data rage a cikin mota,buhaina na gyara mata lullubin matsakaicin mayafin dake jikinta,bushira na qoqarin rufe murfin motar,yayin da barratu ke clearing mata hanya. Wani abu guda da a kullum yasa take sake jin jinin sarauta da izza cikin kanta da jikinta,yake kuma qara mata nishadi da jin dadin irin tsatson data fito.
Saidai a yau din wannan zuciyar tasha banban da ko yaushe,wannan walwalar da nishadin da take samu can qasan zuciyarta a yanzun babu shi ko kadan a tare da ita,zuciyar cike take da rudani,tana jinta a quntace tamkar wanda aka sanya a wani saqo daban aka killaceta.
Shehnaz na daga bayanta tana amsa wayar jamaal a nutse,ba wani daga murya ko hayaniya,wannan zai sanya daqyar ka iya jin abinda take fada.
A yanayi irin wannan baushin shehnaz da aisa ke kamata. Sunayi kaman basusan ciwo da dadin rayuwarsu ba?. Namiji ne kawai halittar da zai iya daga hankalin mace,ya sanyata cikin tsananin damuwar da zata iya qare rayuwarta a ciki,amma a hakan dukka sun runtse idanunsu daga ganin kowanne aibu nasu?.
Misali me sauqi a kanta,bata shimfida hannayenta ta karbi kowanne namiji ba......bata marabci kowanne d'a namiji cikin rayuwarta ba.....amma duk da hakan gigita rayuwarta suke shirin yi?.
Ranar gobe tana lissafata cikin mafiya munin ranaku a rayuwarta da bata taba zuwa mata ba. Wata rana da bata taba lissafinta cikin kwanakinta ba na duniya kaf,koda kuwa zatazo bata lissafa zuwanta a nan kurkusa har haka,ta yaya zata manta da MORSA SAFIYYA cikin rayuwarta ne?.
Wani nauyi takeji a qirjinta sosai idan ta tuna qalubale ne yake tunkarota ta kowacce fuska. Mammina ce kawai qarfinta......banda tana da mammina bata da tabbacin ina rayuwa zata kaita.
Wani siririn iska ta fitar daga bakinta.......ba abunda ke sanyata cikin jin qasqanci idan ta tuna waliccin aurenta a hannun waye ya rataya a yanzu?...... MALAMI......BAQON MALAMI.......TSINTACCIYAR MAGE!. Duk da irin tarin darajar da take dashi......tarin dangi da ahalin da zasu iya aurar da ita?......amma sultane ya zabi horar da ita ta hanyar damqa waliccinta a hannun wanda ko cikakken asali bayi dashi?.
Idanunta ta daga a hankali sanda tunaninta ya kawo wannan gabar don yanke hukuncin sassanta zata nufa ko zata shiga daya daga cikin guraren dake bats relief cikin gidan a duk sanda ta shiga rudani irin wannan?. A daidai lokacin ne kuma idanunta suka sauka a kansa,wanda da saukar nata idanun shima ya daga manyan fararen idanunsa suka sauka saman fuskarta dake da wani irin kwantaccen kyau......kyan daya bayyana tarwai cikin dan qaramin hasken ranar daya haske farfajiyar ya kuma nuna ainihin kalar qwayar idanunta.
Idanunsa ya zare a hankali sannan tattausan murmushi ya kubce masa wanda labbansa da suka motsa ne kawai suka bayyana murmushi yayi saboda maganan da maleek ya gaya masa ta cikin wayar.
Idanunta ta janye itama da wani irin hanzari tana jin wata irin faduwar gaba data saukar mata. Wani irin kwantaccen kwarjini da wata ajiyayyar izza ta hanga tattare dashi,abubuwan biyu suka ciccibi tunaninta suna jefashi wani sashe na daban dake cike da zallar mamakin
"MALAMI DA IZZA?....MALAMI DA KWARJINI?" Ta tambayi kanta da kanta wani abu yana mata tsaye qasan ranta.
Me yasa a kowacce siffa data kebanta dasu?,a kowacce siffa da tafi dacewa dasu?,a kowacce siffa data kasance mallakinsu ce sai ya cusa kansa yayi tarayya dasu?.
Meye hadinsa da wannan izzar?,meye hadinsa da wannan kwarjinin da yake nunawa saman fuskarsa?. Abu mafi qona mata rai shine......ta lura a duk sanda idanunsu zasu hadu guri daya faduwar gaba itace abu na farko dake fara ziyartarta......a duk sanda zasu hada idanu da ita shine yake fara janye idanunsa kafin ita. Baisan ma zunubi bane kallonta haka kai tsaye ido cikin ido?. Koma meye sultane ne ya janyo mata,ya bashi dama da yawa,damar kuma har takai ya bashi wuqa da naman zartarwa cikin rayuwarta.
Yadda ta lumshe idanunta haka ta dauke numfashinta a sanda yake shirin giftata. Zuwa yanzu tana tsoron shaqar wannan qamshin.....qamshin da ta soma zargin akwai wani sihiri a cikinsa. Ba wani rana.....ba wani lokaci da zata shaqi wannan qamshin bai maqale mata a hanci da tunaninta ba a yinin ranar gaba daya. Kowanne qamshi a duniya yana da asali da kuma inda aka samoshi,amma wannan mayen qamshin ya rasa asali da dukka wani bin diddigi da tayi masa.
"Barka da warhaka sheikh" Ta tsinci muryar shehnaz a bayanta tana gaidashi cikin tarin girmamawa.
"Barkanki" Amsar daya bata kenan yana maida wayar maleek kunnensa yana ci gaba da takawa.
Idanunta akhnan ta qanqance tana jin wani abu me nauyi yana sauka qasan zuciyarta. Wani irin bacin rai sabo ya soma tasiri cikin ranta tana kuma iya sauraren yadda shehnaz ta qaro sauri tana qoqarin jera kafadarta da tata.
"Me yasa kike qoqarin zubda girma da kimarki shehnaz?.....me yasa kike qoqarin nunawa duniya ke din ba kowan kowa bace?" Dubanta shehnaz takeyi cikin zallar mamaki.
"Kamar yaya biftu?" Ta tamabaya maganan tana warwarewa shehnaz kai. A nutse ta waiwayo tana ajewa shehnaz wani kallo kafin ta dauke kanta,a hankali cikin izzarnan ta fara magana.
"'Yar asali kike.....jinin sarauta cikakka daga agadez.....me yasa zaki zubda kanki akan wancan tsintacciyar magen da ba wanda yasan asalinshi?,ke ya kamata ya fara gaidawa......yakai har qasa gurin matuqar baki girma,amma kuma baiyi hakan ba saboda sultane ya bashi dukkan wata dama,tsananin girman kai yana sanyashi jin cewa wai shin wani ne......bayan ba kowa bane face wulaqantaccen......"
"Biftu mana!" Shehnaz ta fada tana duban akhnan da mamaki,yadda take maganan da wani birkitaccen fushi.
"Kina manta darajar da Allah ya yiwa malamai ne?" Hannu akhnan ta dagawa shehnaz ba tare data waiwayo ta kalleta ba,idanunta na bayyanar da zallar bacin ranta
"Bana buqatar naji komai.......ya isheni" Ta fadi har cikin zuciyarta tana jin takai geji,a yanzun bata buqatar maganan kowa akan komai.
Ta Jima shehnaz tana dubanta kafin ta dauke idanunta a hankali ta maida gabanta. Mamakin yadda kullum akhnan ke qara birkicewa yana kamata,tuna maganganun da sukayi da aisa kafin ta wuce ne kadai ya hanata cewa komai,saitaci gaba da lissafe lissafenta a ranta,tana kuma nema mata shiriya gurin ubangiji.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A nutse ya zare device din daga kunnensa bayan ya yiwa maleek sallama,dab da zai shiga sassan mammina ya hada sabon connection da omari ya maida device din kunnensa a nutse yana sake takawa zuwa ciki.
Wani abune ya gilma cikin idanunsa daya tilasta masa sanya yatsansa babban da manuni yadan shafi idanunsa yana furta
"Subhanallah". Budesu yayi a hankali hoton yana dawowa cikin idanunsa. Baby face dinnan nata dake cike da wani irin yanayi dake nuna zallar gajiyarta rauninta da kasawarta,saidai alamu na tsananin taurin kai kafiya da kuma qi fadi irin nata yasa takejin ita din tsayya ce da ba rauni ko gajiya a tattare da ita,wanda kai tsaye a kuma kallon farko yake iya hangen dukka wadannan abubuwan a tattare da ita. Abu guda daya da yayi masa tsaye a qirji......yadda take kewaye tsakiyar wata da'ira me fadin gaske.......yadda ake wasa da rayuwarta ake juya wannan kafaffen ra'ayin nata daga hagu zuwa dama ba tare da ita tasan hakan ba.......ba tare data fuskanci hakan ba. A nasa idanun wani abune me sassauqan fahimta da ganewa......to amma ya sani a karan kansa,shi dabanne.....shi kuma na dabanne da yake iya hangen komai daga nesa tarwai kamar yayewar hijabi.
Bayaso ya shiga wasan daba nashi ba......amma tabbas wasan zai bada ma'ana inda ace shine abinda ya shigo dashi agadez.......an taki bahaguwar sa'ar da baya kallon kowanne aiki sai nasa aikin.....wannan ya sanya wasan zai zame masa abun kallo yana daga zaune a inda yake. Yana raina izzarta......yana raina tsaiwarta da kafiyarta.....yana kuma raina mulki da sarautar da takeji tana yawo a jikinta. Ya sake raina jaririyar kwanyarta......data bari ake gara rayuwarta tamkar ball a hannun qananun yara tsakiyar fillin qwallo. Baizi agadez don kowa ba sai don MAI LAIFIN DA SUKE FARAUTA......BAIZO AGADEZ BA SAI DON QASARSA ETHIOPIA......BAIZO AGADEZ BA SAI DON MOTII DA NANAY DA AL'UMMARSA......baiga dalilin da zai sauka daga wadannan matakai da tsanin nasa ba.
Saidai duk da haka,duk da tarin wannan raunin......duk da tarin wannan siffofin,yana hangen wani YAQINI da JAJIRCEWA ta cikin dukka motsi da yanayinta. Da gaske ne ita din bata karbar FADUWA da gaske ne TSAYAYYA CE akan dukka quduri da burinta,saidai yanaji a jikinsa da sannu komai zai canza.....da sannu qilan za'a cimmata a rushe komai.....wataqila a sannan ya jima a jimma Ethiopia,har ma ya mance da wata qasa daya taba wanzuwa wato niger.
Kai tsaye suka dinga buda masa hanyoyi har zuwa inda zai riskar mammina. A kowanne taku akwai hadimi guda daya da zai masa jagora zuwa inda take mataki mataki. Tsarin sashenta daban yake,banbamcin da ya bayyana qarara da kowanne sashe na gidan. A zahiri karon farko kenan da ya taba bayyana cikin sassan,saidai a badini kuwa sashen ba baqonsa bane,saidai ya wawantar da kansa yadda ya kamata don yayi kama da mutumin da karon farko daya taba tsintar kansa a gurin.
A kowanne motsi da kuma kowanne taku yana hankalce da yadda ba wata doka data soma aiki a sassan mammina din. Kowanne shiyya na gidan ya samu cikakken rahoton fara wanzuwar dokar da fara aiki da ita,ciki kuwa harda shiyyar sultane duk da bayanan,da sashen morsa safiyya.
Yayi marking hakan da alama ta biyu da zaiyi nazari a kanta,yana sake maida hankalinsa da inda hadimar ke masa iso tana janyewa baya,da alamu iya tata iyakar kenan.
Tun daga nesa kafin ya qaraso ta tattara dukka nutsuwarta,ta kuma bude dukkan basirarta dake mata jagora zuwa fahimtar zurfin tunanin dan adam a sanda taso karantarsa.
"Wa'alaikumussalam......bismillah" Abinda tace da haisam kenan a sanda ya qaraso farfajiyar da take zaune.
A nutse ya taka yana isa gaban wata kujera qwaya daya data fita daban da sauran,yayi bismillah a hankali yana zama,saita daga kanta tana duban yalwa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer π³πͺ*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITAπ*
*HUGUMANKU CE*βπ½
[1/22, 19:59] +234 903 555 3736: π *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*π
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 37*
"A marabceshi kamar kowa.....a kuma wadatashi da dukkan abun ci da abun sha" Ta furta da cikakkiyar izzar dake nuna girma da nisan inda ta dauki kanta da kuma kalar matsayin data bashi.
Idanunta ta daga a hankali,tana iya karantar zallar nutsuwar dake kwance saman fuskarsa,ba wani tsoro ko fargabar kasancewarsa a gabanta,duk da yadda takewa tarin mutane kwarjinin da ko cikakken zama a gabanta ba kowa ke iya yinsa. Wani adanannen kwarjini da tasa aka mata tattalinsa daga kowanne jini dake harbawa a jikinta.
"Sheikh haisam.....tuntuni na aika a kiramin kai......ba'a sanar maka bane?" Tayi tambayar da manufa tayin titsiye da kuma son ganin adadin girma da kwarjinin data yiwa idanunsa da zuciyarsa.
Kai ya gyada a nutse bayan ta ajiye tambayarta harma ta huta ta hanyar shaqar sabon numfashi,yana jin kamar nashi jinin OROMIA din yana shirin motsa masa,jinin ABA JIFAR amma yasa wani abu me nauyi ya danneshi yana daidaita yanayinsa da lokacin.
"Eh an sanar dani" Ya amsa mata a taqaice. Yadda ya amsa mata kai tsaye ba wani kwana kwana ko neman boye laifinsa ya tabata sosai,abinda bata taba gani ba,bata kuma saba gani ba,sai ta jinjina kai.
"An sanar dakai.....amma ka bata wasu mintuna da suka kusa tasamma jimillar awa guda cif,na kiraka ka wofantar da kiran?" Ta fadi da zafi zafi wannan karon a muryarta.
Kamar dazun,sai daya shaqi nutsatstsiyar iska sannan ya sake motsa labbansa.
"Akwai banbamci tsakanin wofantarwa da zuwa a makare......ba kowanne kira bane amsashi akan lokacin da aka yishi yake nuna girmamawa ba......manufar daya ce wanda aka kira ya amsa......gani na amsa a lokacin da yafi dacewa......idan kuma ba damuwa,kamar shiga cikin maganar kai tsaye zaifi,saboda mu ceci lokaci ni dake gaba daya" Yayi maganar kansa tsaye yana zube idanunsa cikin nata.
Kafeshi takeso tayi da idanunta,amma ta rasa wannan qwarin gwiwar,saita janye dubanta a kansa,zuciyar taqi yarda da kwarjini yayi mata,saidai tafi alaqanta hakan da fushin da takeji a kansa. Bata jin zata sakar masa wanna gabar da sauri haka ba tare data saukar masa da warning ba saboda gaba
"Cikin masarautar nan.....cikarta da batsewarta.......yana zama wajibi akan dukkan wanda na kirashi ya amsa kirana a sanda na buqata". Kansa ya juya a hankali,ya fahimci maganan rashin xuwa kiranta a sanda taso ta mata zafi sosai,hakan shi kuma yayi masa.
"A tawa al'adar da yaren.....girmamawa sifface ta dattako.....ga duk wanda ya amsa kiranka ya girmama koda baizo a sanda ka buqata ba" Ya amsa mata yana sassauta harshensa. Bayaso nan da nan tayi fusatar da zata rudar da hankalin omari daga fuskantar abinda haisam din yakeso ya fuskanta. Maganar tasa ya daketa ta kuma taso da wani tsohon al'ada da wata tsohuwar karin magana daga asalin nata yaran,ta kuma motsa idanunta kamar zata waiwaya gareshi ta kalleshi don tabbatar da abinda ya fada,amma koda ta tuna da nata mission din saita kauda hakan. Saidai hakan da tayi bai hanashi daukan haske ba.
"Ka zartar da wasu sabbi kuma baqin dokoki ba tare da neman ta bakina ko ganawa dani ba.....shin waye ya baka wannan izinin?". Murmushi ne dan siriri ya qwace masa,saidai ya tsaya iya labbansa,duk da hakan kuma bai hana tsarguwar mammina ba da rayawa a ranta kamar murmushin taga yayi ba,saidai bai bata dukkan dama ta gane hakan ba.
Ya kamata tambayar ta bashi mamaki,amma kuma yadda ya tsammaci tuhume tuhumenta zasu iso haka suka sameshi.
"Ba kowa".
"Ba kowa?" Ta tambaya a mamakance,tana jin ta samu gaba da zata soke kowacce doka hankali kwance.
"Eh.....ba kowa,saidai bayan na gama rubuta dukkan dokokin,na gabatarwa da sultane,inda hankalinki a nutse yake da zaki iya ganin stamp da sanya hannun sultane qasan kowacce doka" Ya fada da wani irin calmness yana sake tattara nazarinsa a kanta.
Wani shocked taji sosai har cikin jininta,jin da sanya hannun sultane aka wanzar da komai,ba tare da kuma sultane ya kirata yaji ta bakinta ba yadda suka saba sanya kowacce sabuwar doka a tare.
"Na tabbatar daukuwa da hankalin sultane yayi ne kan wannan tafiyar ya hanashi nemana......amma hakan bawai yana nufin kana da qarfin ikon zartar da doka kai kadai ba". Kansa ya sake juyawa a hankali,cikin Tarin nutsuwa idanunsa tsakiyar nata yace.
"Sanya hannun sultane ya wadatar........dokar bata an qirqireta bane saboda ke,an qirqireta ne saboda masarauta.....shi