Showing 12001 words to 15000 words out of 188421 words
da akhnan. Kai kawai ta daga,ta sanya hannu tana daukan wani dan qaramin scarf ta dora saman kanta bawai don kwalliya ba,amma sai ya zame mata tamkar ado ya sake qawata fuskar nan take dake da wani irin sirrintaccen kyau.
Cikin mutuwa da rashin qwari jiki take saukowa. A dazun tana kwance mammina ta shigo,bata bude idanu sunyi magana baki da baki ba,amma kunnuwanta na iya sauraren fadan da taji tana yi harta gama ta fice.
Ko a yanzun tana tsaye ne kawai cikin falon da ba kowa daga ita sai mammina. Wani yanayi take hanga saman fuskar mammina da bata taba ganin irinsa ba.
"Ways kika aika ya siyo miki gubar da kika durawa kanki?" Ta tambayeta a kausashe,da kuma wani bayyanannen fushi da ya raunata zuciyar akhnan din karon farko.
"Kema mammina......kema kin yarda ni da kaina nasha guba?" Ta motsa labbanta tana fadi da wani yanayin karaya daya tara ruwan hawaye cikin qwayar idanunta duk da basukai ga zubowa ba.
Rauninta ya bayyana sosai,raunin da ba wanda ya sanshi ko ya taba ganinsa,daga ita sai sultane,sai kuma morsa safiyya data kasance ta ukunsu.
"Bansha komai ba mammina......ki yarda dani,banda tea da nasha a lokacin,dana kammala kuma nayi nufin amsa kiran da kikayimin.....a hanya abun ya faru dani". Ta sani,wannan itace amsar da zata bata idan ta matsa,saidai kuma bata shirya amsar wadannan bayanan ba.....bata kuma shirya bata ko qofa guda daya da zata fidda bayanan zuwa ga wani ba ko kuma wani guri ba......don wannan shine makaminta......sassauqar hanyar kuma da zata sadata zuwa ga cikar burinta MATAKIN FARKO.
Dubanta takeyi ba wani sassauci a tattare da ita.
"Yaushe kika fara yanke hukuncin shirya qaryawa mamanki biftu?.......kin manta da iqirarin da kikayi da kanki?,kin manta cewa keda bakinki kika ce sai kinsha?......okay.....yanzu kina son qaryatawa kenan?,kinason nunawa duniya da abokan adawar mahaifinki cewa sultane ya gaza bawa gudar d'iyarsa kariya?......idan ya gaza bawa gidansa cikakken kariya da tsaro hakan yana nufin baya iya mulkar jama'arsa al'ummarsa da talakawansa yadda ya dace,tunda har aka iya keta dukkan wani shinge da tsaro aka zuba gubawa gudar diyarsa......hakan yana nuna shi gajiyayye ne kasasheshe ne da bazai iya tabuka komai ba.......to kiji da kyau......muddin hakan ta faru KEMA KIN RASA TAKI DARAJAR.....duniya zataci gaba da kallon mahaifinki ne a matsayin uba me rauni maras alfanu.
Tsaye kawai tayi tana duban mammina......yadda a yau din mamminan ta gaza fahimtarta,yadda ta gaza mata uzuri......ta gaza fahimtarta. Mammina tafi kowa saninta a duniya,tafi kowa fahimtar halayenta,tafi kowa sanin abinda zata aikata da wanda ba zata aikata ba. Tafi kowa sanin qarya sam bata burgeta,qarya bata bata sha'awa......qaryar kuma tana cikin jerin sahun abu na qarshe da bata iya aikatawa a rayuwarta.
Tafi ganewa ta tunkari tsanani ko sauqi da dukkan gaskiyarta,tafi ganewa bayyanar da zahirin abinda yake rai da zuciyarta a madadin yin qaryar.
"Koma me kika aikata bazai canza sunanki daga sunan DIYATA ba,kuma hakan bazai karyamin gwiwa ba,bazai kuma hanani tsaiwa don samar miki da masalar rayuwarki da abinda rai da zuciyarki suke muradi ba". Mammina tayi maganan a sanda take qofar qarshe na fita daga falon.
Hanyar data wuce akhnan take bi da kallo. Koda mammina bata fita ba,bata da wani sauran energy da zatayi mata wani bayani,ta gama bayaninta tana ji har ranta yarda da ita ko takurawa wani ya aminta da ita bai zama dole ba.
Wani shu'umin murmushi ne yake fita saman fuskarta,tana kuma takawa zuwa qaramar fadar sultane daya shirya zama dasu a wannan lokacin cike da cikakken qwarin gwiwar lallai zata fito da nasararta.
Taji dadi qwarai da yadda maganganunta suka dakushe yunqurin akhnan na bayyana gaskiyarta. A yanzun ba gaskiyar akhnan take da buqata ba.........shurunta shi tafi buqata,shirunta shine tsani na farko kuma hanya mafi sauqi da zata sadata da muradanta.
Tun daga qofar farko ta samu sanarwar yana tattaunawa ne da wazirinsa alhaji ahmadu sallau,da alama kuma ba dashi kadai yake ganawa ba,don haka ta zagaya ta wani daki na musamman dake liqe da gurin wanda aka tanadeshi don zaman jiran sultane din irin haka.
Duk bayan daqiqa saita duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta,tana sane ta rage wasu daqiqu masu yawa daga lokacin da sultane yace zasuyi zaman,saboda tsarinta da plan dinta yafi tafiya a daidai,sai kuma tazo ta cimmasa da baqi.
Qaramin tsaki taja sanda takejin fitar baqin sultane,ta miqe a hankali ta buda qofar da zata sadata da ainihin falon faadar tana sanya qafafunta da zummar jiransa. Ko yaya ne tana lissafin akwai mintunan da zasu bata daman kebancewa dashi kafin zuwan kowa,saidai kuma tana zama sallamar morsa safiyya wadda suke takowa tare da sultane ta yanke mata dukkan wani hanzari da takeyi.
Fes momma ta ganta,amma saita dauke idanunta daga kanta tana tattara hankalinta ga sultane cikin sakin sassanyan murmushin da tayishi ne saboda jifan tsuntsu biyu da dutse daya.
Cak wani abu yayi mata tsaye a qirji,daidai sanda idanunta ke sauka akan morsa safiyya din,da alama wata magana sukeyi da sultane din da batasan meye suke tattaunawa ba.
Iska sosai ta furzar daga bakinta tana qoqarin daidaita numfashinta da kuma sanyaya zuciyarta da takejin ta matse sosai a qirjinta,sannan tattaro dukkan wani yanayi da zai iya baka cewar cikin nutsuwarta da walwalarta take ta dora saman fuskarta.
"Marhaba......barka da shigowa zaki gwarzon mazaje" Ta furta da wannan salon na girmamawa tana miqewa tsaye,sanda morsa safiyya ke qoqarin kwashe masa pillows din saman kujerar da zai zauna a kai,abinda ya sake dasa wani kakkaifan mashi saman zuciyarsa sanda morsa safiyya ke neman gurin zama daura dashi ta zauna da wannan nutsuwar da basarwar tata. Yanayi da nature dinta guda daya dake taba mammina kenan......tana da fada......tana da zafin zuciya,amma tana da wata kalar kamewa da idan bataso ba ko fuskarka ba zata kalla ba bare tasan da wanzuwarka a wajen. Wani lokaci wannan dabi'artata......wannan halin nata yana ma mammina kwarjini sosai.
"Barkanki giwar agadez" Ya fadi da yanayin da yasa mammina alfahari sosai,duk da fuskarsa bata nuna ainihin abinda bakinsa ya fada.
"Ina fatan ka yini cikin aminci da qoshin lafiya?"
"Alhamdulillah.....kema ina miki fatan hakan" Anzo gurin da takeso,tambayar kuma tazo mata daidai,saita rusunar da idanunta cikin wani yanayi.
"Ba wannan nutsuwar sam a tare dani......banajin wani aminci ko kwanciyar hankali,tun daga sanda na fahimci akhnan tasha guba dalilin auren dole" Ta furta da wata irin rusunanniyar murya. Shuru sultane din yayi yana dubanta,kamar yadda morsa safiyya ta dakata da komai,ta kuma zuba idanunta akan mammina din.
"Ban zaci abun zaikai har haka ba......ban dauka da gaske take zata sha ba me martaba......."
"Wannan hujjar kika riqe kika qi shaidawa kowa iqirarinta?......" Muryar morsa safiyya da dukka qoqaromta na hadiye abinda yake ranta ya kasa cimma gaci.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Yadda tayi tambayar da wani irin yanayi cikin muryarta.......yadda sautin ya fita yaja hankalin sultane da mammina,harma da nanay dake sanyo kai gurin ba tare da kowa ya ankara da shigowarta ba.
Kai tsaye,kuma ido cikin ido morsa safiyya ke duban mammina.
"Indai har da gaske ne iqirarin da kikeyi.....ke kika raini biftu.....kinsan kowanne hali da dabi'a nata.....kinsan komai da zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya aikatawa ba.......indai har da gaske ne kina jinta kamar diyar data kwanta a mahaifarki watanni tara kika haifeta,koda baki gayawa kowa ba.....koda kowa bai sani ba,mahaifinta......sanadinta,kuma jigonta yana da haqqin yasan iqirarin diyarshi......indai ba akwai manufa shiri ko wani tanadi ba cikin shurun......bai cancanci ayi shuru ga dukka iqirarin da d'iyar dake da kafiya da taurin kai irin AKHNAN ba".
Idanun morsa safiyya da kallonta kawai a kanta ya gaya mata akwai babbara barazana......akwai abubuwa masu tarin yawan daya kamata tayi garkuwa dasu kafin wani abu ya girgiza gaskiyar dake lullube da ayyukanta a zahiri.
"Me kike cewa safiyya?.....me kike shirim cewa?" Ta fadi tana son gano bakin zaren komai ta dora ga aikinta na gaba.
"Bance komai ba,ban kuma shirya fadin komai ba......saidai tarin qalubalantata a gareki na rashin shaidawa mahaifin biftu iqirarinta har sai dame afkuwa ta afku......nayi imanin inda kinsan ZAFIN HAIHUWA inda kinsan DARAJAR 'YA'YA ba zaki aikata haka ba" .
Maganan ta daketa da zafin data saba dukanta,saidai kuma da wurwuri ta gano ta kuma fahimci akwai wani d'anannen tarko cikin maganan morsa safiyya,da biyu a yau ta maimaita maganan gaba sultane,gaban nanay da ta lura ita daya ta ankara da tsaiwarta daga qofa. Duk da cewa tarko ne maganar tata,amma ta hango tarin mafita a cikin tarkon......ta hango hanyar bullewarta.
"Ya isa safiyya" Sultane ya fada da sigar dakatar da momma safiyya,amma saita murmusa don har yanzu batakai gaci ba.
"Ka barni na gaya mata,zan gaya mata abinda yake shine.......illar bada tarbiyya ga macen da batasan ciwon haihuwa b........"
"Ya isheni haka safiyya!.....ya isheni!!!" Mammina ta magantu cikin wani irin fushi tana miqewa tsaye. Irin wannan fushin morsa safiyya ke fata da burin gani a tattare da ita......irin wannan fushin da take fata ya kaita ga yakice akhnan ta barta zuwa gareta......ta barta zuwa ga ainihin UWAr data cancanci rayuwarta........ta barta da AHALINTA na haqiqa........ta barta taju GARDIN soyayya da 'YAN UWANTAKA daga ahalinta na asali.......ahalinta na tsatso.
"Ki jima kina jifana da miyagun kalamai saboda haihuwa......kin dade kina fadamin dukka maganan da yazo bakinki akan akhnan......."
"Baki kyauta ba safiyya.......ba halinki bane,bai kuma kamata a yanzu ace kinyi ba,bai dace ki rama alkhairi da sharri ba" Muryar nanay dake bayyanar da zallar bacin rai ta iso gurin Nanay din tana takowa zuwa ciki gami da gaza jure ci gaba da tsaiwa daga bakin qofar don kada ta shigo ta yanke maganar da yakeyi da iyalin nasa. Amma ganin maganganu suna neman juyewa zuwa zafafan musayar yawu daka iya bada sakamako maras kyau taga ya dace ta qaraso ta kamawa d'an uwanta wannan rigimar da take hange cewa ta yau din ta dabance......ta yau din me girma ce.
Da sassarfa mammina ta taka tana cimma Nanay. Idanunta cike fal da hawaye ta kama hannunta.
"Don Allah ki gaya mata.......ki kuma tambayeta sai yaushe zata ga alkhairi na?.......sai yaushe zan zama MACEN ALKHAIRI a idanunta. Me takeso,me take buqata nayi bayan wanda nayi da zai gamsar da ita?" Mammina ta fada hawayen da ya tarar mata yana saukowa.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
[1/2, 20:07] +234 903 555 3736: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 09*
___________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
"Tsahon shekaru ashirin da suka yita shudewa kawo yau.....ko meye ya kamata morsa safiyya ki fahimceshi......ko menene ya kamata ki yafeshi" Murmushi me dauke da wani nannuyan ciwo morsa safiyya ta saki. Tana hangen wani kwantaccen hali dabi'a zubi da tsari na musamman daga kowanne motsin mammina din. Abubuwan suna sake kwance mata kai,amma alqawari ne ta yiwa kanta,bakin rai bakin fama......ba zata taba sassautawa muradan mammina ba......ba zata taba rusuna musu ba......ba zata taba sauke mata kai ba......ba zata taba bari ta mulketa ba......ba kuma zata daina adawa da kowanne tsari da shiri nata ba muddin bata saki kurwa da rayuwar akhnan ba.
"Akwai wani lulluben duhu dake nannade cikin wasu irin yankuna masu tsananin duhun daya kusa fin duhun da suke boye dashi......ba zaku fahimci komai ba......wani yare ne da baya buqatar harshe ko motsi na labba ballantana akai ga fitar sauti.........abu daya data tambayeni kan me zatamin na yaba.....abu dayannan shine KI 'YANTA RAYUWAR AKHNAN.....KI RABU DA ITA DA DUK ABINDA YA SHAFETA".
Sosai kalmarta ta farko tayi duka me sauti a qirjin mammina.......bada hankali ga kalmar kuma na nufin d'arsuwar alamu masu tarin yawa ga zukata da kuma ayyuka,don haka ya zabi yin duk wani tattaki nata da fidda salon iya kauda hankalinta akan jimla ta biyu,don haka ta saki hannun Nanay a hankali,wani murmushi yana subuce mata maras armashi,tayi taku uku tana sake kusanta kanta da inda morsa safiyya ke zaune.
"Wannan shine cikar burinki......shine cikar burin da har ki mutu ba zaki sameshi ba muddin ba kyakkyawar niyya da nufi bane a zuciyarki......HAR ABADA bazan wulaqanta akhnan ta hanyar banzatar da ita da rayuwarta ba kaman yadda kike fata,jinin sultane yafi qarfin wulaqanci ko kuma tozarci na har abada a hannun zaituna.......idan baki da labarin soyayya KOMA KI TAMBAYA cikin hamshaqiyar qasar data tara isassun mata irin ZAITUNA.......Zan sadaukar da farincikina saboda farincikin akhnan.....zan iya yaqi da kowa don akhnan ta samu 'yancin da yayi daidai da rayuwarta........kamar yadda a yanzu nake tsugunnawa saman qafofina nake roqarka ka janye auren hakeem akan akhnan......ko don ka ceto rayuwar da qwaya daya tal da ita kadai SAFEENA ta iya baka" Mammins tayi maganan tana sulalewa saman gwiwarta gaban sultane.
SAFEENA dukkan rauninsa ce......safeena dukkan qwarin gwiwarsa ce a sanda yake raye. Sa'insarsu gaban should wani abune daya jima irin haka bata sake faruwa ba a gabansa. Kamar kowacce ta mance da wanzuwarsa a gurin,kamar kowacce ta mance da hukuncin aikata haka a gabansa?.
"Zan dauki alhakin komai......amma bazan iya jurar rasa biftu ba.......ta fara da shan guba.....dukkanmu gaba bamu da tabbacin abinda zai faru da rayuwarta".
Wani irin masifaffen tashin hankali ne morsa safiyya taji yana yanko mata. Idan ana lissafin ANNOBA tana ganin cewa mammina tafi gaban a kirata da sunan ko a sanyata a sahun......tafi qarfin sunan ANNOBA saidai wata halitta daban da tasha banban da yanayi da tunanin dan adam. Soke auren akhnan da hakeem hakan yana nufin dawowar kowanne lissafi baya?. Hakan yana nufin maida kowanne lissafi izuwa farkonsa?,tarin gwagwarmaya tarin dauki ba dadin da akayi dukka sun koma farkon lissafi?. Akwai wani tunani......akwai wani target akwai kuma wani ajiyayyen abu kuma boyayye a bayan kowanne faruwar al'amari.
"Soke auren hakeem da akhnan da zakayi shine babban kuskuren da zaka aikata sultane...." Morsa safiyya ta fadi tana girgiza kanta gami da qoqarin boye dukkan tsoron dake cin ransa.
Da wata irin fusata mammina ta waiwayo tana duban morsa safiyya.
"Wannan shine kalar maqaryaciyar soyayyar da kike iqirarin kina yi mata?......kar ya soke auren?.......yau tasha gube gobe tasha ruwan batir?......burinki kawai tayi aure?,tabar gabanki bayan ba saman kanki take rayuwa ba?,me ta tsare miki?.....tayi aure kowanne yanayi ma zata shiga ba damuwarki bane?,saboda BAKE KIKA HAIFETA BA?,SABODA BA FALAAK BACE?"
"ZAITUNA!......kul dinki.....kul bakinki ya sake....." Maganan da morsa safiyya ta fara da wani irin zafi daya sanyata miqewa tana nuna mammina da yatsa maganan ya katse saboda tsawar da sultane ya sakar musu.
Ba wadda bataji ta koma hayyacinta ba,don baquwar halayya ce ga sultane din. Yana da wani irin girma da yake bawa kowaccensu saboda kowacce akwai wani ajiyayyen dalili da yasa take da girma da daraja a idanunsa.
"Idan har wanzuwata a guri bata hanaku aibata kawunanku ba.....meye zai sanya ku fasa?" Yayi tambayar da harshen da yasa kowacce jinin daya fara tafarfasa a jikinta ya fara sanyaya.
Ganinta da jinta taji kaman ya makance na wucin gadi,yau ita ake duban cikin idanunta ake cewa jinin safeenarta BA ITA TA HAIFETA BA?. Wata bare can?,wata cikakkiyar abokiyar adawar da dukka tsahon rayuwarsu basu data biyunta?,tabbas.....idan tayi rantsuwa ko kaffara ba zatayi ba.....inda safeena tana raye a yau,zataji ciwo sama da ciwon da ita takeji yanzu cikin qirjinta,saidai wannan ciwon.....wannan radadin ta haramtawa mammina ganinsa.....ba zata taba bari ta fahimceshi ba.
"A shirye nake na dauki mummunan mataki akan kowaccenku......muddin kasancewata a guri ba zata zama sitiyarin control dinku ba!" Ya sake fadi wani fushi me kaifi yana gilmawa ta cikin idanunsa yana nuna yatsansa dan manuni.
"Kayi mana afuwa" Nannie ta furta ita kanta a yau