Showing 183001 words to 186000 words out of 188421 words

Chapter 62 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

133

taji wani abu ya tsarga mata tun daga saman kanta har qafafunta,kafin ta sakeji ko fuskantar komai ya karkatar da fuskar tablet din zuwa ga inda idanunsa suke.

Daya bayan daya takebin mutanen dake zaune saman lausasan carpet din masallacin da kallo. Daidaiku ta gane,kaman imam dinsu da wazeer. Kanta ya kulle da yanayin data gansu a zaune sunyi da'ira. Zaman kaman na masu daukan karatu,idan kuma ta lura da kyau ma kaman wata tattaunawa sukeyi a tsakaninsu,kafin kuma taga an ajjiye daurin kudi CFA dinsu me yawa da daurin goro da wasu kwalaye data fahimci alawa ce a ciki.

"Me sukeyi ne haka?,me sultane yake nunamin?" Ta tambayi kanta da kanta ba tare data iya fidda tambayar sarari ba saboda yadda taji tana neman shiga rudani.

"Daurin aure ne" Taji zuciyartata tana bata amsa saboda tunawa data tabayi. Cikin wani film data taba gani shehnaz na kalla ta taba ganin irin wannan zaman,don itadin ba ma'abociyar kalle kallen finafinansu na gargajiya bace. Fina finanta dukka basa wuce na fada da gwagwarmayar rayuwa,saina soyayya da takan kalla a sace gudun kada su aisa su sanyata a gaba.

"Ni sarki abubakar al'assad.........na bawa sheikh muhammad haisam ibraheem auren d'iyata khadeeja muhammad hammud.......bisa sadaki na sisin gold dubu d'ari da hamsin,lakadan ba ajalan ba,bisa sharadin ciyarwa tufatarwa da Matsugunni......bisa kuma sunnar annabi muhammad S A W". Yayi maganar cikin girmamawa yana duban bobbo muhammad dawud dake sanye cikin manyan kaya da suka sake kwarxantashi.

"A matsayina na waliyyin muhammad haisam.....na karba masa auren 'yar abokinmu khadeeja,bisa sunnar ma'aiki S A W da kuma yarda da duka sharuddan da addinin musulunci ya tanadar mana".

"Kun amince?" Me martaba sarki abubakar al'assad ya fadi har sau uku,bobbo muhammad dawud yana fadin

"Mun amince mun karba" . Sai sarki abubakar al'assad ya juya zuwa ga sauran dake zaune a guri dama hausawa da mutanen niger da suka marmatso wadanda jin auren diyar sarkin agadez ake daurawa a gurin wanda wasu daga cikin su tuni suka fara nad'ar recording na video don su samu abun dorawa da bada labari.....sai ya dan daga sauti kadan daidai da yadda kowa zaiji yace.

"Jama'a kun shaida?" Har sau uku nan ma kowa yana amsawa da

"Mun shaida"

"Ma sha Allah,salati goma ga annabi". Sarki abubakar al'assad ya furta yana hada hannuwansa guri guda ya fara karanto sigar daurin aure.



*HAISAM*

Baya ya koma a hankali yana jingina bayansa da sofa din da yake kai. Bai taba yarda da gaske aure wani abu ne me girma da nauyi ba sai a yanzu daya tabbatar kammaluwar bayarwa da karbar sadakin da baisanma wanda ya biyashi ba ya gama maida akhnan din sunan MATARSA HALAK MALAK ba sai yanzu. Abinda yakeji a dukka jikinsa dama kansa bai dauka zaiji wani abu me nauyi kwatankwacin wannan ba. Aikin na nasaeeb ne,yana Riyadh gurin wani aiki da aka turashi gurin aikinsu,ya katse dukkan abinda yakeyi yayi tattaki har zuwa madeena,yayi umra kuma yayi joining wadanda suka zauna don shaida daurin auren,takanas kuma ya kirasu sanda yake tare dasu omar.

Su sunsan da kiran.....shine kawai abun yazo masa a bazata.

"Congratulations captain" Ya tsinci muryoyinsu a sanda bai taba zata ba.

Da hanzari ya buden idanunsa,sai suka sauka akan khadeem......mutallab da Amjad. Idanu ya zuba musu,kaman yadda suka zuba masa idanu. Wani murmushi na fita a fuskarsu,wanda a hankali tasa fuskar ta soma washewa da murmushi. Miqewa yayi da wani irin kuzari da zafin naman daya rasa a dazu ya qarasa gaban khadeem yakai masa wani naushi da hannu,sai khadeem din ya tare yana dariya,sai kuma suka cakume juna suna huggin din juna.

"Komai Nisan inda kake obbo....komai nisan tazarar dake tsakaninmu hakan bazain hanamu zuwa a lokaci me muhimmanci irin wannan a rayuwarka ba. Koda ma yaya ne kayi auren nan congratulations.....congratulations once again Capt sheikh" Amjad ya fada yana suna sakin juna shida haisam gami da sake bawa junansu hannu sukayi musabaha me zurfi da kyau.

Yasan wannan aikinsu maleek ne.....yasan sunsan da komai,sun kuma shiryawa komai,gaya masa ne kawai basuyi ba. Zuwan ya masa dadi,bai kuma San yayi kewarsu haka ba saida suka wanzu a gurin,sai kawai ya yanke su wuce zuwa personal home dinsa. Ya waiwaya ya dubi abdii da ya fahimci walwalarsa kawai yakeyi,da gaske farinciki yakeyi da auren ta kowacce fuska.

"Idan ka kammala ka samemu a gida"

"Tom in sha Allah" Ya fada yana hada kayayyakin da haisam din ya sanyashi hadawa.

"Awa biyu ta ishemu,don dole mu dawo muyi sallar juma'a cikin gida" Haisam din ya fadi yana jin wani sassauci cikin ransa.

*AKHNAN*

Yadda dakin yayi shuru haka akhnan ta tsinci wani irin shuru cikin kanta. Shurun data jishi ne kawai bawai don ta gama fahimtar ahinda ma yake shirin faruwa da ita ba. Abu daya ne kawai ya tsorata tunaninta,yake kuma yi mata kai kawo.

"Ina nemawa sheikh muhamamd haisam ibraheem auren d'iyarku khadeeja muhammad hammud.......na bawa haisam auren diyata khadeeja hammud?..... Wannan wacce irin rubututacciyar qaddar ce da zata hada sunayensu guri guda?.....wanne irin mummunan arashi ne da sunayen wadannan ma'auratan yazo iri daya nata dana wancan bagidajen malamin?......malamin da ko sunasa bata qaunar taji an kira?.....malamin da take da imani da kuma yaqinin yana dasa hannu gurin faruwar abubuwa da yawa a rayuwarta. Tushen baqincikinta shine....tushen takurarta,silar nesantata da masoyinta mahaifinta da bata da kusanci da kowa a duniya sama da irin kusancin dake tsakaninta dashi.

"Wai meye amfanin zaunar dani a nunan wadannan abubuwanne?" Ta fadi tana raba idanunta tsakanin shehnaz aisa da nannie don batabi takan yakumbo ba,saboda tasan harkar na'aura ba cikin lissafinta suke ba.

"Ke kika hadamin AI ko?" Akhnan tayi tambayar tana dage dukka girarata biyun tana duban shehnaz fuskarta na nuna tsananin bacin rai.

"Amma dai wannan ba wasa bane shehnaz.....shine kika saka aka tasoni a lokutana masu muhimmanci irin wannan.......yakumbo" Ta fadi tana waiwayawa ga yakumbo din,saidai idanun yakumbo dake kanta ya daketa sosai.

"Juya zuwa ga mahaifinki,yanason yayi magana dake" Yakumbo ta fadi kai tsaye da wannan dattijankar tata dake qara mata kwarjini itama.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[2/14, 19:12] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 87*

Wani mummunar faduwa gabanta yayi,kamar wadda aka riqewa wuya ta juya a hankali zuwa ga screen din karo na biyu tana maida dubanta ga sultane. Yana tsaye a wani guri na daban,a wani guri can wajen masallaci gefe inda ba zirga zirgar jama'a,ba kamar dazun da yake cikin masallacin ba.

"Khadeejatu" Yayi kiranta da wani sauti,da wani yanayi daya sanyata shiga hankalinta tilas.

"Na'am bappi" Ta samu kanta da amsawa da wata irin nutsuwar dole datazo mata,nutsuwar dake cakude da zallar tashin hankali daga can qasan ranta.

"Haqqine na iyaye su zabawa yaransu mijin aure.....mijin aure na gari daya dace da rayuwarsu......na baki wannan damar duk da cewa ina da ikon yin hakan,haka ne?" Ya jefeta da tambayar data saukar da wani abu me nauyi saman zuciyarta. Qasa tayi da kanta,tana jin kamar ba abinda ya rage a duniya a sannan sai sautin bugun zuciyarta.

"Haka ne" Ta amsa masa da wani irin nauyi,tsoro da tarin fargabar abinda zataji a gaban bayanan nasa,wanda tafi damuwa da qaguwa kawai yayi mata conclusion ba tare da wani tsawaita bayani ko shimfida ba.

"To alhamdulillah....akwai wani haqqi dana tauyeki dashi tsahon haihuwarki kawo yau?" Ya tambayeta idanunsa car bisa kanta. Kai ta girgiza.

"Da baki nakeso ki amsamin"

"Babu" Ta sake amsawa muryarta kamar zata yanke daga maqogoronta.

"Kin shaida har a gaban Allah baki da hujjar da zaki kai qarata gurin Allah?.....na cika miki komai.....na baki dukkan wata dama....na cike miki dukkan gurbi?". Kai ta daga da hanzari,maganar kaisa qara gaban Allah ta mata nauyi da yawa,amma sai ya sake tabbatar mata.

"Eh.....baki da hujjar kai qarana gaban Allah?" Kai ta girgiza da sauri,hawayen da take qoqarin riqeshi ya silmiyo mata.

"Babu bappi...babu,ka cika dukkan wani ma'auni,ka cika dukkan wani mizani,kai din uba ne daya tamkar da million,kaidin ubane daya cika dukkan ma'auni bappi".

"To alhamdulillah.......a yau abu guda daya zaki sakamin dashi shine......zama gidan sheikh hasam.....rayuwa ta dindindin a mazaunin matarsa.......a yau ni mahaifin dana haifeki,na aurarwa da sheikh haisam ke bisa sunnar manzan Allah...sadakinki in sha Allah zan taho miki dashi na damqa miki,dukkan wanda ya dace ya shaida ya shaida.....dabi'ata tason bawa me haqqi haqqinsa ya sanya na saka a zaunar dake don kema ki shaida hakan,kuma alhamdulillah kin shaida,ki zauna kuma da shiri na komawa qarqashin ikonsa da kulawarsa,daga yanzu zuwa kowanne lokaci" Dif ya yanke kiran,ya kuma maida akalar kiran nasa ga morsa safiyya daya lura bata agurin,don yasan mammina bata nan.

Shuru ya sake ratsa falon,kafin a hankali ta soma jin wasu maganganu a kunnenta.

"Alhamdulillah,sai kiyi biyayya ga umarnin mahaifinki,donn yaron duk da bansanshi ba amma ya samu yabo qwarai daga bakin kowa.....ballantan sultane da nayi imanin bazai aura miki qasqantacce ba wulaqantacce b....."

"Qasqantacce mana.....kuma wulaqantacce yakumbo,fadi ki qara fada!!!" Akhnan da take tunanin zata iya shanye abinda ta soma ji yana taso mata kaman zai hallakata ta fada cikin qaraji tana duban yakumbo.

"Baida asali.....baida dangi.....bawa ne kuma hadimi kaman sauran hadiman dake gidannan......kamar sauran hadiman dake rayuwar qarqashin ALFARMARMU......shikenan ni na zama tamkar wata mara galihu?,shikenan saboda mahaifiyata ta rasu sai yadda akaga daman yi dani?" Ta furta tana nuna yatsarta da qirjinta.

"Me yasa ya gaza fahimtar gwara ya auramin kowa da malamin can?.....me yasa ya kasa ganewa zuciyata da tasa ba daya bace?,don zuciyarsa taso shi ni ba dole na bane na soshi......bakusan me nakeji a qirjina ba ko?" Ta fada tana fashewa da kuka,idanunta cikin na yakumbo kamar itace ta aikata laifin.

Tsam aisa ta miqe daga mazauninta,ganin maganganu sosai akhnan ke fadi kamar ma wadda tayi loosing control nata. Kafadunta ta kama tana zama daga bayanta.

"Shuru mana akhnan?.....akwai nadama me yawa cikin magana cikin fushi fa!"

"Dalla ki sakeni.....akwai wata nadama data ragemin aisa?....akwai nadamar da tafi auren malami ga diyar BASARAKE irin akhnan zama mafi girman nadama?.....idan akwai KI FADAMIN". Da gaske fushi ne yake neman cire akhnan daga saitinta,da gaske tashin hankali ne yake neman gigita mata tunani,don haka aisa ta zare hannuwanta daga kafadarta,hakan kuma ya bawa akhnan din damar miqewa da wani irin hanzari,aisa ta miqe itama,saidai suna taku daya biyu ana uku akhnan din ta sulale tana zubewa a gurin,Allah ya bawa aisa iko ta nufeta tana tarbeta a hannuwanta suka zube qasa tare aisa din tana qwalla kiran sunanta kusan lokaci daya da kiran sunanta da shehnaz tayi,abinda ya sanya dukkanin wanda ke parlor din miqewa yayo kanta.

*HAISAM*

Duk wani shaqiyanci da suke masa yana jinsu. Duk wani shaqiyanci da suke masa yana binsu da idanunsa ne kawai. Suma sunsan bazai ta ka din ba,saidai abinda basu sani ba nasa tunanin yana nesa dasu,yana can gurin kallon da tunanin QADDARAR yau me zata canza?.....rayuwar wa zata canza?,rayuwar wa zata taba?,meye MAKOMA na al'amarin gaba daya?.

Wani sashe na zuciyarsa ya harbo masa tunaninta,yata tsinci batun?.....ta yaya ya risketa?. Yanzun qila tana can tana ji a ranta shi ya zabeta ko?,.....tana can tana tunanin shi ya bayyanata a zuwan ita din ZABINSA CE.

Siririn tsaki yaja....qaddarar mammina ina ta jona tasa qaddarar da tata,banda hakan baya tunanin ita din tana cikin sahun matan da zai karba da hannunsa da sunan MATAN AURE.

Lafiyayyen abinci cook dinsa ya shirya musu saman dining,dukkaninsu kuma suka wuce can din don cika cikinsu. Ba ma'abocin cin abincin a waje bane shi sam,duk da irin wayewa tarin dukiya da matsayin da yake dashi yafi aminta dacin abincin gida. Uwa uba da kare lafiyarsa ma,don ya sani masu sana'a da aiki irin nasa koda yaushe ababen farautar masu laifi ne,tako wacce fuska ana iya shiga a cutar dasu. Baya ga haka kuma albarkar dake cikin abincin da aka girka cikin gida,ya sani tana da banbanci da abincin siyarwa na waje.

Rudu kawai ake saman dining din,hira ce irin ta amintattaun shaqiqan abokai,hira ce irin ta yaushe gamo tsakaninsu,jifa jifa kuma sunqi barin haisam,lallai saisun taboshi. Yana jinsu bai hanasu ba bai saka musu baki ba kuma,sunata tsara yadda zasu gudanar da biki sosai idan komai ya lafa. Ajiye spoon dinsa yayi yana duban idanunsu.

"Biki?.....wanne biki khadeem?......auren da za'a yiwa biki nayi?" Ya tambaya yana duban su. Dariya sukayi suna kallon juna,sai ya lura kaman akwai magana a qasa.

"Aure dai ai duka sunansa aure.....manufar cikinsa mu da duniya duka babu ruwammu a ciki. Abinda muna sani kawai captain dinmu yayi aure,so zamuyi duk kalar bikin daya halasta ayi.....ba ruwanka" Amjad ya fadi yana daga hannunsa. Da kallo yabi Amjad din,don dama kusan duk a cikinsu shikam yana son hidima sosai ta tasowa dayansu,kan jiki kan qarfi yake tsayawa akai.

"Ya kamata ma mu nemi gafarar dukka 'yammatan da kayi rejecting a baya" Khadeem ya fada yana daukan tissue gami da matse hancinsa kaman irin wanda yake qwalla.

Harara ya bisu da ita yana watsa musu daya bayan daya. Maleek ya saki dariya yana dan kare fuskarshi.

"Ka rufa mana asiri ango da wadannan manyan idanun naka......suna saka mutum yana feeling guilty bayan baiyi komai ba.....muma labarin auren mukaji daga sama" Numfashi yaja sosai ya fesar,ya lura ba wanda ya gasgata magananshi,wanda kuma yana da kyau su fahimci baiyi aure saboda SOYAYYA BA.....yayi aure ne don ya D'ANA TARKO.....yayi aure ne don ya ceci rayuwar dake cikin halaka da musiba ba tare da girman kanta ya bata daman fahimtar hakan ba. Baiyi alqawarin saki ba.....amma kuma baiyi alqawarin zama na har abada ba.

"Mijin wata" Omari ya fada qasa qasa har yanzu yana shan mamaki qasan ransa. Harara ya balla masa yana dubansa.

"Ka sake fadin haka sau daya saina koreka daga gidana".

"Wallahi ba zagi ko tsokana bane.....bazan boye maka ba dukkaninmu mamaki muke har yanzu......mr lowering gaze?....kai?.....aure kuma da akhnan?". Idanunsa ya maida ya lumshe kawai yana relaxing bayansa jikin kujera.

"Kuci gaba da mamaki.....lokaci ne dashi,zaizo zai wuce,zakuma miyi accepting abinda dukka na fada muku"

"Amma mutumin da bai taba kallon mace da idon aure ba......"

"Har yanzu ban fara ba" Ya katsi numfashin Amjad.

"Ka jishi......yana magana kamar auren wata takarda ce kawai" Khadeem ya fadi yana duban fuskokinsu

"A wannan halin dai tamkar takardar yake" Ya amsa musu still idanunsa suna a lumshe har yanzu. Sake kallon junansu sukayi,haisam din sake shayar dasu mamaki kawai yakeyi

"Kana wasa da mace fa haisam duk da ka fimu karantarsu.......zakasha mamakin nan da kwanaki kadan zaka fara sanya ido kan yadda take tafiya.....yanayin maganarta....."

"Omar!" Haisam din ya fada da sauri yana dan dukan table din gabansa kadan.

"You know my mission omar.....kada ka lalatamin target mana.......baya ga haka I married her to protect her,she was in a tough spot ba tare da tsukakken tunaninta ya barta ta fahimci haka ba......zanyi hakanne kuma ba don ita ba.....zanyi hakanne badon so ko qauna ba.....zanyi dukka haka ne saboda JININ SAFEENA da take tare dashi.......saboda darajar wasu mutane data d'amfara da rayuwarsu.....nothing more.....hope you understand guys?" Ya qarashe maganan yana bude idanunsa sosai a kansu yana duban fuskokinsu daya bayan daya.

"It's okay.....mun fahimta......amma,why not ba zaka bude mata zuciyarka ba......why not ba zaka bada qofa zuwa ga wannan killatacciyar zuciyar ba?" Maleek ya fada a nutse dukkaninsu fuskokinsu suna nuna seriousness dinsu.

Girman idanunshi ya rage ta hanyar lumshesu sannan ya budesu fes akan fuskar maleek. Baisan me yasa suke putting pressure a kanshi ba game da maganan ba.

"Wannan zuciyar budeta shine babban kuskuren da zan aikata.......na gaya muku a baya.....yanayin aikina banajin zai bani daman budewa wata mace zuciyata harta shiga ciki.....zata iya zama weakness dina....mafi girman abinda na tsana kuma kenan......wannan zuciyar" Ya furta yana nuna qirjinsa da yatsarsa

"Idan tanayin so bata yinsa d'an kadan......bata kuma yinsa da sauqi.....wannan ne ya sanya nake qoqarina sosai gurin ganin ban tsani mutum ba.....gurin ganin ban tsani kowa ba,saboda nasan idan na fara QIYAYYA itama bata zuwarmin da sauqi......ina dukka qoqarina na canza kaina.... Amma haka aka halicci wannan zuciyar.....shi yasa nake qoqarin fahimtar kowa....shi yasa nake qoqarin bada uzuri ga kowa.......shi yasa bake qoqari sosai kar naqi kowa......ina fatan wannan bayanin ya gamsar?". Shuru ne ya dauki falon gaba daya,na wasu sakanni ba wanda ya motsa ba wanda kuma ya sake cewa komai. Ya musu magana da wannan yanayin nasa na seniority da dukkaninsu suke shakkarsa idan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login