Showing 114001 words to 117000 words out of 188421 words

Chapter 39 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

116

babban glass cup daya cikashi da tataccen lemon inibi wanda ya cakudashi da sinadarai daban daban.

"Kaidai ungo wannan kasha mu tafi.....yanzu ba lokaci bane na tunanin wannan.....tunda harka yadda ka shiga cikin masu sa'a ai shikenan,ba abinda ya rage maka saika zuba idanu kaci gaba da irgen lokutan sa'arka". Dan shuru almaz din yayi,kafin kuma ya saki murmushi yana miqa hannunsa ya karbi lemon hannun tamim din.

"Inason lemon nan sosai,inajin dadinsa" Ya furta a hankali sannna kuma yakai cup din bakinsa.

Tas ya shanye lemon a kurba daya,sannan ya miqawa tamim cup din yana cewa.

"Kamar zai bani freshness din da nakeso,na gode tamim" Ya damqa masa cup din yana juyawa. Da wani kalar shu'umin murmushi yabi almaz din,rabin aikinsa ya kammala saura rabi,yana duban takunsa da yakeyi cikin wani yanayi daya bayyanar da b'urbushin qasaita.

"Matsiyaci ya samu guri,wai har ya iya yanayi na masu mulki da saruta" Ya fada a fili can qasa yana jifan hanyar da almaz yabi da harara.

Jerin gwanon motocin alfarmar guda shida ne cass suka takewa motor din da almaz ke ciki baya. Ya saki wani irin murmushi sanda dukkan wani hadi dake cikin lemon ya fara zagaya sassan jikinsa,ya kuma soma jinsa a sama,uwa uba yadda yaga manyan motocin alfarma irin wannan na take masa baya sai ya sake sanya yanayin yabi jikinsa sosai

"Shege almaz,yau shine kamar gomna?" Ya tambayi kansa da kansa yana dariya. Sam a rayuwarsa ya rayu cikin wani madaukakin yanayi ba burinsa bane,damuwarsa daya shine ya rayu cikin 'YANCI. Bayason UMARNI,yafison ya rayu cikin sakewa da kuma zabawa kansa duk kalar rayuwar da yakeso,ba tare da an bashi umarni ba,ba tare da an sanyashi ko an hanashi ba. Ya sani......yanajin wata izza da girma a cikin jininsa da baisan wacce iri bace,wannan ya sanya sau tari yafi zabar kebance kansa tare da qin amincewa ya shiga taron jama'a.

Duba daya tamim yayi masa ya tabbatar ya fara fita daga hayyacinsa,ya fara buguwa,sai ya gyara zamansa sosai yana dubansa.

"Kasan meye almaz?" Kai ya girgiza yana duban tamim da idanun nan nasa da tamim din yake ganin suna masa kama da wasu idanu.

"Akhnan matarka.....tana da tsananin girman kai....bata girmamawa kowa saboda tana ganin mahaifinta shine sarki a wannan yankin....."

"Ashe?" Almaz ya fadi da wata irin murya yana bude idanunsa da kyau. Kai tamim ya jinjina cikin bashi tabbaci da son isar da saqonshi

"Qwarai da gaske.....kai baka lura ba?,a matsayinka na namiji kuma mijin dake aurenta.....ta taba gaidaka?,kota taba zuwa gurinka nemanka?,kota taba nemanka din koda a waya ne?" Shuru almaz yayi,wasu abubuwa suna cakudewa cikin kansa tsakanin maganganun tamim da kuma abinda tamim din ya bashi yasha. Gefe daya wata izza tana huruwa cikin ransa,yana jin kansa yana girma da fadi.

"Ba ko daya" Almaz ya fada muryarsa tana kaduwa da wani irin yanayi na wanda ya fara buguwa.

"Ahto....to kai kuma saika bari aci gaba da tafiya a haka?"

"Inaaaa......daga yau zan fara nuna mata ina da iko a kanta" Ya fada yana ji a ransa dole ya zama tsayayyen namiji.

A hankali tamim ke buda masa wasu abubuwa,yana kuma sake karanta masa abubuwan da ya tabbatar zasuyi tsananin tasiri a kansa game da akhnan din. So samu komai ya fada jagule musu a yau,shi yasa ya fara da horashi da kadan daga cikin kayan mayen dana tanada,wanda wannan shine zai bashi damar dorawa kan tsarinsa d'od'ar ba tare da sunansa ko alamar ayar tambaya ta hau kansa ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: πŸ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 54*

Idanu mammina ta lumshe tana kuma budesu idon nata akan akhnan din. Duk da yanayin da take ciki ba abinda ya gusar da wannan sassanyan kyan......wannan kyan irin na safeena......wannan kyan da ya zamewa rayuwarta dukka qalubale da baqincikin da har kawo yau ba wani abu daya sassauta a ranta. Wannan kyan tana fatan lokacin gushewarsa ya zama a kurkusa.......a shafe tarihinsa cikin qasar agadez. Shi ta yaya ma wai zata bari AKHNAN ta fita daga tasarrufinta?. Ta yaya zata yarda tabar ruhin safeena ya kwanta lafiya cikin kusewarsa?. Yadda ta sanya darare da yawa na rayuwarta suka gagara zuwan mata da dadi,haka takeso tayita rasa nata dararen a qasan kushewa cikin baqinciki da takaici.

A zahiri hannuwan akhnan din ta kamo a tausashe,har yadda tayi din ya sanya akhnan duban idanunta,tashin farko kuma ta hangi wannan tsantsar qaunar da kulawar data saba gani a tare da mammina din.

"Ina cikin tsananin farinciki yau biftu,kinsan saboda me?" Kai ta girgixa a hankali.

"Yadda naji sultane yana jero miki addu'o'i na sanya albarka cikin masallacin haram. Yadda sultane ya nunamin duk wani fushi da yakeyi da ke ya kau,yadda sultane ya nunamin ya.yafe miki,kuma a yanzun kin koma akhnan dinsa ta tun tale tale" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki tana jin wani nauyi dake kwance a qirjinta yana raguwa. Wani sanyi taji gami da sassauci yana sauka saman zuciyarta,sai takejin wani girma da qaunar mammina suna saukar mata. Duk wani kyakkyawan albishir na alkhairi daga bakin mammina take fara jinsa,ita daya ce take dauke da dukkan wani albishir me dadi da zai faranta rayuwarta da duniyarta.

"Amma kinsan wasu lokutan nakanji nadama tana saukarmin na hadaki da almaz?" Ta furta muryarta can qasa tana kuma sadda kanta qasa jikinta yana nuna wani irin mugun laushi da yayi.

"Mammina......nadama wacce iri?" Ta tambayeta tana jin wani fargaba kadan. Kai ta daga tana sake kallonta.

"Nayi wannan abunne don na samar miki da 'yancinki,ki sake cikin rayuwarki kamar yadda kikeso,amma abun mamaki shine.....sai walwalarki take raguwa,takura take maye gurbin sakewa,me yayi zafi biftu?,bayan a yanzunne kike da 'yancin yin kowacce rayuwa da kike so?" Kai ta girgixa a hankali,tana jin wannan raunin nata da bata bari kowa ya gani yana taso mata.

"Ban saba bane mammina.....a hankali zan saba zan saki jikina".

" Amma ko kinsan wannan rashin sabon naki yana aje ayar tambaya me yawa saman zuciyar mutane a kaina da kanki?......kinsan yau ne ranar da za'a rakaki kwanan gida?" Kai ta daga da sauri ta zubewa mammina wadannan blue eyes din. Karon farko da mammina taji kalar kallon akhnan din ya mata nauyi gami da haifar da wata jaririyar faduwar gaba.

"Mammina.....kwanan gida?.....ni da almaz?" Ta furta da sigar tambaya me wani irin nauyi.

Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci,sannan tace.

"Haka yake a al'adar buzaye......haka yake tun kaka da kakanni,indai baso kike ki fadawa duniya cewa almaz ba zabinki bane". Shuru akhnan tayi,wai tana qoqarin daidaita kanta tana kuma qoqarin daidaita abinda takeji a qirjinta. Wani kwana ne da amarya zatayi guda daya tal a gidanta da ango,sannan washegari ya rakota ta dawo gidansu,sannan a sake shiryata a maidata.

Kai ta shiga girgzawa don ta kasa tausar zuciyarta ta karbi maganar. Sam ba zata iya ba......ba zata iya bin kowacce al'ada da akazo da ita ba wai akan aure,to a wanne dalili ma?,auren da dole ce ta kaita ga yinsa,dolen amintar da sultane da maido kyakkyawan alaqansu ta baya.

"Bazan iya ba mammina.....ba,bazanje ba,ko sama da qasa zata hadu bazanje kwana da almaz gida daya ba a yanzun,qarshen satinnan zan wuce Niamey,bana buqatar wani tsari da zai sanya yace zai bini,ko ke kice saimun tafi tare". Numfashi mammina ta sauke a hankali,dama ta sani,tasan za'a rina,kuma dama itama bata shirya tilastata kwana gida tare da almaz ba,to amma kuma tafiya Niamey bata hangen wani abu da zai sanya ta rushe tsarin tafiyarsu a tare.

"Bazan tilasta miki ba biftu......zan sauya tsarin,saboda ya kasance dole a al'ada kuyi zaman fahimtar juna a yau,zaizo ku gana ke dashi din koda cikin gidan nan ne" Shuru akhnan tayi tana jujjuya abun. Shin meye abun damuwar cika komai da al'ada tazo dashi ne?,meye abun damuwar saita gana da mijin da HOTO ne kawai da TAKE na suna a bayan sunanta?.

"Ina sake jin tsoro akan abinfa na aikata domin jin dadinki akhnan,kamar ba za'a dauki tsahon lokaci ba zaki nunawa duniya ko ki gaya mata da bakinki cewa almaz ba zabinki bane".

Wani yanayi ne a fuskar mammina da yake nunawa akhnan raunin mammina da fargabar tata da gaske,sai takejin idan tayi mata hakan bata kyauta ba,bayan da qyar tasha kanta ta aminta ta zaba mata mijin auren don kubutar da ita daga fushin sultane.....bata cancanci wannan sakamakon ba,ita ta maidata cikin damuwar data kubuta ba.

"Na amince zan gana dashi,saidai ba'a wani kebantaccen guri ba......ba cikin wani kebantaccen daki ko muhalli ba,zan ganshi cikin lambu na.....zagaye da hadimai da suka saba aiki a gurin,da kuma nawa hadiman da suka saba yimin rakiya" Can qasan zuciyar mammina murmushi ne ya subuce mata. Dukkan wani tsari,dukkan wani karatu da zuciyar akhnan keyi ta gama baje lissafinsa. Kai take jinjinawa a hankali,tanason gujewa qaddararta ne.....qaddarar da ita ta riga data sani ba makawa saita sameta a kurkusa ma.....saita tilastata mallakawa almaz wannana abun....wannan tutiyar wannan alfaharin.....wannan taqamar.....mallakawar kuma zata zama matakin farko ne,zataci gaba da mallaka masa ba tare data sani ba,har xuwa lokacin da adadin data shatawa qaddararsu kan ta TSAYA!.

"Na gode da fahimtata da kikayi.....na gode da biyayyarki a gareni,zanci gaba da zama UWA wadda zata tsaya akan matsalolin d'iyarta. Duk qunci duk wuya. Duk tsanani,zanci gaba da tsaiwa dake a kowanne mataki ko rukuni na rayuwa har abada" Saita matsa a hankali tana rungume akhnan cikin jikinta,duk da yadda zuciyarta ke qyamtar hakan,gangar jikin keji tamkar tana hada gangar jikin nata ne dana safeena,kamar tana nutsa ruhinta tsakiyar abokan adawa masu tarin yawa.

Ta gefan akhnan ajiyar zuciya take saukewa,duk sanda mammina rungumeta saita ji kamar qarshen kowacce matsalarta ne yazo,tana jin wani sassauci a tare da ita,saidai still batasan me yasa wannan EMPTINESS din da takeji a ruhinta har yanzu ba wani abu da taji ya cike GURBINSA ba.

*NANAY*

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali ta shafa addu'ar data kammala bayan sallar walaha tana sauke idanunta akan saamee dake shigowa dauke da turaren wuta kamar kullum.

Tausayin yarinyar ya sake tsargawa nanay,zuwa yanzu tana jin yadda kwanakin ke qara nisa,haisam da take sanyan ran hankalinsa zai kawo kanta yayi musu nisan da basu dauka zaikai har haka ba. A hankali take karantar yanayinta,kamar ta soma sarewa,kamar ta soma cire rai daga dukkan zato da kuma tsammaninta.

Zuwa yanzu a wannan gabar kuma tana jin anya ba zata shiga maganar ba ko yaya ne?,anya ba zatayi wani yunquri ba don samawa marainiyar cikakkiyar nutsuwa da makoma mai inganci.

"Saamee" Nanay ta kirata a hankali.

"Na'am" Ta amsawa nanay din tana waiwayowa,saidai kuma tana gujewa hada idanu da ita.

"Zo nan ki bani aron wayarki in kira obbo dinku". Wani faduwar gaba tayi daga kiran sunansa kawai,yayin da nanay dake karantarta a nutse ta fahimci sauyawar yanayinta daga sanda ta kira sunansa.

A hankali take takowa zuwa ga nanay,tana kuma zuba numbers dinsa dake haddace a kanta,duk da cewa tayi saving nata a rubuce. Nanay ta zubawa hannunta idanu,tana rubuta number dinne da sauri sannan still hannunta yana rawa har sanda ta qaraso gabanta,ta tsugunna ta miqa mata wayar,nanay ta sanya hannu ta karba tana mata kuma alama data zauna.

Duban screen din wayar tayi,sunan data masa saving dashi kaman sauran yadda 'yan uwansa suke masa ne,sai ta zare idanunta tana maidawa kan saamee wadda tayi qasa da idanunta.

*HAISAM*

Kacokam ya aza idanunsa akan qunshin bayanan daya kammala tattarawa,tun daga safiyar yau zuwa yanzu yammacin ranar litinin. Abu biyu yake dagashi daga gurin sallah sai kuma dauko coffee,don ba wanda ya bawa daman shigowa dakin kwata kwata a yinin ranar.

Daidai da wayoyinsa dukka a kashe suke,sai bayan sallar la'asar dinnan ya kunnasu don ya kira masarauta yaji yanayin da ake ciki,ya kammala wayar kuma ya barta a silent don baya buqatar wani disturbance.

Wani irin kullewa kanshi yakeyi da yadda lissafinsa da bayanan daya tattara gaba daya da bincikensa suke kaishi da direction daya. Ya sanya mutane da yawa a sahu sahu saidai duk inda ya fara bin salsalar zaren kan mutum daya suke kaishi ZAITUNA/ZEENATU/MAMMINA daya gama imanin mutum daya ne da suna uku......mutum daya ne cikin gangar jiki uku.....mutum daya ne da aikin mutum uku.

"Rabbi yassir wala'ta'asir wa tammin bilkhair" Abinda ya dinga maimaitawa kenan yana zubawa allon system din idanu kaman iya aikin da aka aikoshi a yau yayi kenan cikin duniya. Idanunsa da suka nuna gajiya a fili ya janye yana maidawa saman wayarsa dake ringing,sunan nanay ne,kiran da yake jira tun kwanaki uku da suka shude,saidai yanayin rashin lafiya da kwashe wayoyin da omar yayi masa yasa dole ya daga qafa.

Jawo wayar yayi,ya yanke kiran kamar yadda ya saba sannan yabi bayan kiran. Tana ringing ya sakata a handsfree ya maida bayansa jikin kujera yayi relaxing yana jin yadda qwaqwalarsa ke ninka aikinta da wani irin gudu da sauri daya wuce iyaka,har yanajin ciwon kansa kamar yana shirin motsawa,sai ya sanya hannun nasa ya dafe kansa a hankali yana lumshe manyan idanunsa da a yau suka dan canza launi kadan.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer πŸ‡³πŸ‡ͺ*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITAπŸ‘‘*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: πŸ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*πŸ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 55*

Sallamar nanay dinne ta sanyashi bude idanunsa a hankali yana amsa sallamar gami da bude idanunshi. A nutse nanay ta miqawa saamee wayar sannan ta yunqura a hankali tana fadin

"Ki sameni a parlor idan kin gama". Kanta a qasa tana jin takun ficewar nanay din,sai ta koma ta zauna sosai saman carpet tana jin qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.

Muryar nanay yake jiran sake ji,sai yaji muryar saamee ta maye gurbinta da sallamar nan tata cikin yanayinta me sanyi.

Numfashi ya aje a hankali yana amsa mata sallamar,husky voice dinnan nashi ya ratsata ya shiga kunnenta yana motsa wani abu dake boye can saqon zuciyarta.

"akkam jirta obbo(barka da warhaka,kana lafiya yaaya)" Ta fadi a hankali tana ganin kamar xai iya jiyo bugun zuciyarta daga nan inda take zaune.

"Ani gaarii dha,akkamitti?(lafiya nake,kefa?) Ya tambayeta tana qoqarin kwatanta kyautatawa a gareta kamar yadda yasan tana qoqarin yin hakan ga nanay dinsa.

"Alhamdulillah" Ta amsa duk wani sauran magana kuma yana dauke mata gami da tsaya mata a maqogaronta. Wani irin kwarjini yake mata koda a bayan idanunta ne,ta jima da sanin shi din wani irin namiji ne daban da sai zallar sa'a zata sanya mace ta samu damar mallakarsa.

"Makaranta fa?" Yayi qoqarin tambaya don kada ta dauka ya wofantar da qoqarinta.

"Komai lafiya alhamdulillah" Ta furta a hankali,har qasan ranta tana son tambayarsa sai yaushe zai shigo jimma?....don tayi wata muguwar kewarsa,amma takejin ba zata iya ba.

"Ma sha Allah,Allah ya taimaka,nanay fa?"

"Zan kai mata yanzun" Ta fadi a sanyaye,tana sanya rai ne hirarsu ta zarta haka,tana sanya ran maganarsu ta wuce haka,amma sai gashi da wurwuri ya gajarta maganar.

A nutse ta miqawa Nanay sannan ta taka tana fita a parlor din. Nanay ta bita da kallo sanda take sanya wayar a kunnenta.

"Barka da warhaka nanay"

"Barka kade muhammad.....fatan ka yini cikin aminci"

"Alhamdulillah nanay.....komai da kowa lafiya?"

"Lafiya Muhammad,inata tunaninka omar yace wani aikin daban ka shiga,shi ya sanya ba'a samunka" Idanunsa ya lumshe a hankali yana gyada kai,cikin ransa yana jin dadin yadda omar ya boyewa nanay rashin lafiyarsa.

"Na fito alhamdulillah nanay.....ko kin samu sunan abokiyar zaman Obbolettii n ki?" Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login