Showing 174001 words to 177000 words out of 188421 words
system din nasa gami da qoqarin kiran kowa a cikinsu. Idanu kawai ya lumshe,gwara ya barsu suyi iyayinsu,ba lallai su fahimci komai ba......ba kuma lallai yayi musu bayanin komai da komai ba.
Bayaso su kalli lamarin da wani idanu daban,shuru shi yafi dacewa ya zama amsa......koda kuwa hakan yana nufin zasu amince da cewar SHI YA ZABOTA.....shi yake sonta.
Wani irin aminci ne a tsakaninsa da zai wahala wani yaga kiran wani ya share,don haka cikin qaramin mintuna ya hadasu gaba daya,sai gasu sun cika su bakwai cif harda haisam da omar da maleek din dake guri daya a gari daya.
"Me yake faruwa da mr lowering gaze?". Naseeb dake zaune ciki parlor din gidansa yana shan fruit da alamu ke nuna matarsa ce a gefe tana yankawa tana miqa masa ya fadi,ganin har suka gama zama online dukkaninsu haisam bai motsa ba bai kuma ce komai ba.
Murmushi da yafi kama da dariya maleek yayi,irin wanda sunsan ba dabi'arsa bace. A cikinsu dukka shida haisam dinne keda wannan jinin sarautar a jikinsu,so izza wani lokacin zuwa musu kawai takeyi. Dariyar maleek taja hankalin kowa,don Omar gabadaya ya kurumce,bayajin yana da bakin bayani,yayin da ta wani gefe kuma zuciyarsa ta kasa gasgatawa da kuma yarda da inganci da sahihancin auren.
"Lowering gaze ya qare daga yau......mr man aure zaiyi,nan da kwanaki uku masu zuwa kawai". Dariya suka sanya gaba daya,kowa da irin abinda zai fada,abinda ya sanya haisam zama sosai yana ware idanunsa da suka dan sauya launi a kan screen din,wannan ya basu daman ganinsa sosai,sai kuma kowa ya fara komawa nutsuwarsa. Shuru ya ratsa ko ina,ya bude baki da nutsuwar nan da suka sanshi da ita.
"Da gaske maleek yake gaya muku.....ruwanku ku yarda.....ruwanku kuci gaba da duban abun ta fuskar wasa" Yana kaiwa nan ya sake relaxing abinsa,saidai kunnuwansa suna tare dasu,duk da qasa qasa yake kallon screen din da salon kallon da zaka dauka bacci yakeyi. Maganan ta saukarwa kowa a bazata.
"Haisam dinnan da baya iya kallon mace sai biyu?......guys a duba maganan nan fa?" Amjad ya furta sounding so amazing.
"I'm serious" Ya fada da wata murya kaman mejin bacci,yanayin dake nuna musu ya gundura da yadda suketa avoiding labarin.
"Wacce jarumar?.....wacce kuma me tsananin sa'ar ce?" Mutallab ya tambaya cikin son jin wadda tayi nasarar.
"Akhnan" Omar ya amsa wannan karon kai tsaye yana tallabe da kumatunsa,irin mamaki ya masa kisan mummuqe.
Yadda suka kama sunan kusan lokaci daya ya sanya haisam sake girman idanunsa yana jifan omar da kallo. Da alama akwai wani labari nata da suke dashi?. Tambayar data girmi tambaya a wajen haisam saidai qarin tabbaci,don kowa maganan naseeb ta tabbatar masa da haka.
"Akhnan?......the princess of agadez?.....stubborn and silly girl?" Naseeb ya jero gaba daya. Maganan ya sakashi qarasa bude idanunsa gaba daya ya azashi kan omar. Omar din da yaqi yadda ya kalleshi.
Komai kenan da yake fadi akan yarinyar akan kunnen omar ne?,komai omar yana hankalce dashi kenan?,komai omar ya labartawa su khadeem.
"Amma Captain......waye ya tilastaka.......gaya mana sai inda qarfinmu ya qare" Mutallab ya fadi yana matsowa dab da screen din gami da lowering muryarsa irin sirrin nan za'a gaya masa. Yadda mutallab din yayi ya sakasu dukkaninsu kwashewa da dariya,banda haisam daya murmusa kawai yana bin fuskokinsu da kallo daya bayan daya.
Har abada ba abinda zai sauya wannan amincin.....wannan yardar.....wannan damuwa da lamuran junan dake tsakaninsu,sirrin dayansu na kowane a cikinsu,saidai wannan SIRRIN nasa ne shi kadai.....wannan SIRRIN na hukumarsu ne kawai.....wannan SIRRIN kareshi yana jin ya zama tamkar wani abu na dolensa.
"Babu.....ba kowa my guy" Haisam ya amsa da muryarsa data qara dadi saboda laushi data sakeyi.
"Gangan kenan.....kaima ka fadi ne kawai khadeem,banda haka......captain ne fa?......ka manta?.....dama akwai wani abu da yake tsoro a rayuwarsa?.....akwai abinda ke razanashi?.....ka manta da forest din da kowa zai kasa shiga ya koma amma saboda yanayin weather na gurin shi dayanshi yake shiga yayi abinda ya kaishi ya dawo?". Amjad ya furta yana tuna musu lokuta masu dadi na rayuwarsu.
"I remembered" Ya amsa wa Amjad yana girgiza kai da qarfi.
"Duk da haka komai yana da dalili......meye boye a bayan wannan auren da wuri haka?.....ko dama can da wani abun kuka boye mana yaa omar?" Naseeb daya ajiye qaramar wuqar hannunsa ya fada yana sake fuskantar screen din sosai.
Da hanzari omar ya daga hannuwansa dukka biyun sama,kamar me surrender,alamun ba ruwansa,bai kuma san komai ba. Sai maleek ya gyada kai yana sake tabbatar musu da reaction din omar.
Shuru kadan ya ratsa,kafin ya motsa da cikakken nutsuwarsa yana duban fuskokinsu still. Shi ya sani,ba komai bane zai iya boye musu ba,kamar yadda suma bass iya boyewa junansu komai. Duk da cewa ba'a rasa jituwa me qarfi tsakanin wani da wani a cikinsu,kamar yadda maleek ya zama mafi qarfin jituwa shida omar a tsakaninsu,saboda gidan da suka fito shida maleek din,daidaito da kamanceceniyar jini da rayuwar yau da gobe da suka tashi a ciki me shigen kama da juna.....saidai hakan bai sauya wannan AMINCIN dake tsakaninsu ba.
Akwai dalili.....tabbas da akwai dalili.....saidai dalilin wani dalili ne da bazaiyuwu a yanzu na fadeshi ba" Ya furta a nutse. Ya riga ya barwa ransa kansa da zuciyarsa.....a gefe guda kuma yana jin dole ya kare MARTABARTA koda ba zata shiga rayuwarsa don ta wanzu har abada ba.....hakanan dole ya kare martabar sultane shima saboda AMANA ba abinda yakai girma da qarfinta.
"Hakan yana nufin ba don SOYAYYA bane captain?" Naseeb ya fadi cikin yanayin hankali da nutsuwa irin ta wanda ya ajiye iyali.
Idonsa ya lumshe sannan ya budesu lokaci daya akan naseeb din.
"Ba ko yaushe bane soyayya yake zama dalilin yin komai naseeb" Shuru ya sake ratsawa,kowannensu da nazarin da yakeyi,saidai dukkaninsu sun fahimci da gaske akwai dalilin,ba kuma soyaya bace.....amma tunda har baiji ya kamata ya fadi dalilin ba,suma ba wani hurumi ko dalili na matsa masa. Dukkansu sun yarda da haisam,dari bisa dari,yana da wani irin hankali da dattako cikin dabi'u halaye da kuma jininsa,tun sanda suka hadu a haka yake.....har yanzu kuma ba abinda ya sauyashi.
"Idan da rai....idan da rabo komai yana iya canzawa.....kabi a hankali.....wataran zaka iya b'urmawa cikin soyayyarta". Naseeb ya fadi cikin bashi tabbaci.
Murmushi ya saki kadan,can qasan ransa yana basu uzuri da RASHIN SANI.
"Bazaiyuwu bane na sota.......bana planning din son kowacce diya mace a rayuwata.....don zata iya zame min BARAZANA......zata iya kuma zama itace RAUNINA.....samun RAUNI ga ma'aikacin security intelligence kuwa barazana ne ga rayuwarsa......ka auri wadda ke sonka.....wadda kawai zata yarda ta sadaukar maka"
"Ba'a yiwa so iyaka.....ba'a yiwa so irin wannan dabarar" Naseeb ya fada yana girgiza kansa sosai.
"Inaji kamar akai naseeb,saboda banga kuma banji muhallinsa ba sam sam" Yana kaiwa qarshe qarar wayarsa ya dauki hankalinsa. Ya aje dubansa a nutse,sai yaga motii ne yake kiransa. Hakan ma ya masa,don yasan a bakunansu,maganganu ne fal tarin tambayoyi da kuma qalubale masu yawa. Da hannu ya basu uzuri,ya miqe kuma anutse yana haurawa zuwa sama,yayin da dukkaninsu suka bishi da kallo had ya bace,sai kuma tattaunawa ta koma tsakaninsu.
Duk wani magana da yayi akan auren suka ajiye gefe,suma tashin nasa yayi musu,sai kawai suka fara tsara yadda komai zai gudana,koda kuwa bazaiso hakan ba,amma sunsan bata yadda za'ayi captain sheikh din zai daura aure koda sadaka za'a bashi matar subar komai ya tafi a haka. Koda ba a ranar da za'a daura auren ba,dole suyi wani abu da shi kansa zaisan YES aure zaiyi.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
[2/13, 12:26] +234 903 555 3736: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 83*
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
"Assalamu alaikum warahmatullah" Haisan yayi sallamar da cikakken nutsuwa sanda yake zama saman stool din dake gaban madubin.
"Wa'alaikumussalam" Motii aba jifar ya amsa muryarsa dauke da wannan tarin dattakon kamala da kuma kamewar.
"Barka da warhaka ranka ya dade" Haisam ya furta da yaren oromo yana rusunawa tamkar motii aba jifar yana gurin.
"Barka kade muhammad". Cikin asalin girmamawar da yakewa me martaba aba jifar ya soma gaidashi,cikin tsananib kulawa da tarin girmamawa. Shuru ya ratsa na sakanni,yanajin nauyin abinda zaice da motii dinne,yana jin kamar baiyi abinda ya kyauta ba. Aure rana tsaka?,aure kuma a kwanakin da duka duka ko bakwai basu kai ba?. Sai yakejin nauyin motii sosai,abinda kuma ya hanashi kiran nanay kenan,don baisan da yadda zai mata bayani ba.
Kamar me martaba aba jifar yasan tunanin dake ran yaron nashi,sai ya kira sunansa da wani irin nutsuwa qauna fahimtar juna da girmamawa.
"Muhammad"
"Ranka ya dade" Haisam ya fadi da harshe na girmamawa yana rusunar da kansa kamar yana a gabansa.
"Naji saqo daga bakin bobbo......na kuma karba dukka bayanai daga bakinsa,na kuma fahimci komai,kuma koda baimin kalar wannan bayanin ba......ni nasan yarona bazai taba tozartani ko ya kunyatani ba......ko kuma ya aikata wani abu na ba daidai ba......na amince na kuma yarje maka ka auri diyar Muhammad hammud......domin kuwa shi din mutumin kirki ne,tsohon aboki daya kasance amintacce,kuma ma'abocin halaye da kuma dabi'u masu kyau. Na aminta bazan bayyana ga muhammad hammud ba saboda yanayin tsarin aikinku.....zan bada goyon baya dari bisa dari......saidai kuma abu guda daya da zan gaya maka muhammad....." Me martaba ya fada yana dan dakatawa.
"Muhammad" Ya sake maimaita kiran sunansa
"Na'am me martaba"
"Kaji tsoron Allah......aure ba wasa bane,nasan ka fini kusan sanin hakan,domin kai me karantarwa da nusashe da mutane ne akan hakan........kada ka yarda koda wasa ka qudurta a ranka zaka auri d'iyar hammud don ka fake a bayanta......don ka cimma wata manufa taka......koda sultane ya roqi ALFARMAr ka auri diyarsa.....kada ka manta hakan bazai canza MARTABA KIMA DARAJA DA TATA ALFARMAR BA......koda yace GARKUWA kawa yakeso ka zame mata......bafa hakan yana nufin yayi wasarere da ita da qaunar da yake mata ba,don haka kaji tsoron Allah,ka tsarkake niyyarka" Sosai maganganun motii ke masa yawo saman kai,sai ya tuna masa da maganganun sultane a jiya.
"Na gode sosai muhammad.......na gode daka martabani.....ka karramani ka kuma karbi qoqon barata hannu bibbiyu.....ko iya haka ya isheni muhammad,ka kuma nunamin halascin D'A na halak.....don Allah na roqeka.....koda baka zamo miji cikakke ga akhnan ba kaji tsoron Allah kada ka cutar da ita.....koda baka zamo miji cikakke gareta ba.....ina nema mata ALFARMA ka zame mata GARKUWA......ka zame mata GATA ka zame mata SUTTURA"
Dukkaninsu kalamansu idan aka tattarasu abu guda suke nunawa. Dukkaninsu kalamansu idan aka tattarsu guri daya zasu hadu,sai yakejin kamar sunason sauya masa manufar komai a zuciyarsa ta qarfi da yaji.
"Ina fata komai yana tafiya lafiya?" Haisam ya tambayi motii bayan sun gama maganan data shafi auren.
"Komai lafiya Alhamdulillah.....bisa dafawar ubangiji da qoqarinka". Kai ya jinjina a nutse,a duniya to su waye yake dasu sama dasu din?. A koda yaushe yana nan ne amma hankalinsa yana can jimma. Abu daya yanzu da yadan sake saka masa nutsuwa,gano anihin kan matsalar,sanin wacece ZAITUNA ya sauqaqe masa abubuwa masu yawan gaske,ya sake saka qarin saka idanu sosai a kanta da wata irin boyayyar matsin lamba da ita kanta batasan da ita ba.....abu daya ya rage masa a yanzu........iya adadin rassan da take dasu a Ethiopia......iya adadin idanunta a Ethiopia din.
"Ma sha Allah......"
"Ranar juma'ar nan ma da izinin Allah zanje na duba al'ummata na qauyen Dass" Motii ya fada a nutse yana duban nanay data shigo wanda tun dazu ya nemi ganawa da ita.
Sam abun sai yaji bai kwanta masa ba,ya miqe a nutse yana duban fuskarsa a madubi.
"Amma motii.....wakilci kawai bai wadatar ba?" Kai ya girgiza yana murmushi.
"Ambaliyar ruwa aka samu......lamarin yafi qarfin wakilci muhammad,ina tsoron ranar da Allah zai tsaidani ya tambayeni ne nayi akai?,wacce gudunmawa na basu?" Shuru haisam yayi.....su din rainon me martaba aba jifar ne,wannan ya sanya zukata da ruhika suke da wata irin nutsuwa.
"Hakanma yayi motii,amma da zaka iya jinkirtawa,zan aiko da wasu qari da kuma musaye na masu tsaron lafiyarka daga hukuma" Kai motii ya girgiza yana sanya hannunsa cikin na nanay daketa kallonsa
"Babu wani abu da zai faru damu sai abinda Allah ya rubuta masa,ga Allah ne kadai muminai suke dogara" Kansa ya gyada,motii na sake zama masa wani role model a rayuwarsa,tun daga quruciya har kawo yanzu.
"In sha Allah motii.....in sha Allah".
Sauke wayar me martaba aba jifar yayi daga kunnensa yana duban khadeeja data zuba masa idanu. Mace daya tamkar da dubu a gurinsa.....uwar gidansa kuma uwar dukkanin 'ya'yansa......matar da har yanzu ba wata mace daya taba jin zuciyarsa tanaso koma bayan ita.
Murmushi ya saki a hankali yana ajiye wayar a gefansa.
"Irin wannan kallon kamar ranar da muka fara haduwa?" Ya fadi yana kashe mata ido daya. Qaramar dariya ta saki,tana jin kunyarsa kadan tana saukar mata. Duk tsahon shekaru da kuma haife haifen da tayi ba abinda ya sauya tsakaninta da IBRAHIM. Har yanzu wannan kallon qauna rahama da soyayyar yana nan a inda yake,takan kalli haisam a yawancin lokuta,tana kuma rayawa a ranta tana yiwa diyar duk data sameshi a matsayin miji murna,musamman idan ya dauki halayen mahaifinsa. Wannan dalilinne ya sanya take tsananin yiwa saamee sha'awarsa,ko don maraicinta,ko don kuma nata nutsuwar da kuma hankalin.
"Allah yasa ba wani laifi nayi ba ake tuhumata da idanu.....abu daya dana karanci a gurinki muhammad haisam ya gado" Sake sunne kanta tayi a nutse tana murmushi.
"Ko daya Allah ya baka yawan rai,....ina na isa na tuhumi mijina haka?" Murmushin ya maida mata shima yana dan jan hannunta.
"Magana nakeso muyi Allah yasa aban aron hankali duka da tunanin a nan"
"Ba aro za'a baka ba,domin kuwa hankalin tunanin da wadda ta mallakesu dukka naka ne"
"Na sani,na gode da aka sake tabbatarmin" Ya furta yana murmushi.
"Khadeeja....." Ya kirata da sunanta na asali.
"Sanin kanki ne komai muqaddari ne daga Allah,sannan sanin kanki ne muna rayuwa ne akan rubutacciyar qaddararmu......sannan sau da dama akwai abinda muke hanga ga yadda zai kasance sai Allah ya canzashi ya kasance daban da yadda muke tunani.....duk Allah yana yine don zaba mana maslaha da kuma abinda xai dace damu....wasu suna shiga rayuwarmu a sanda bamu zacesu ba,wasu kuma suna fita a sanda bamu tsammacesu ba.....haka rayuwa take. Ka marabci dukkan wanda Allah ya kutso dashi rayuwarka don bakasan dalili ko manufar haka ba....kada ka koreshi kada ka qyamci kalar qaddararsa.....hakanan duk wanda ya zabi fita daga rayuwarka kada ka tsaidashi,.......bakasan manufar Allah na koreshi daga cikin rayuwarka ba,wataqila bai cancanci zama da kai ba......wataqila wanzuwarsa a rayuwarka matsala ce" Kai ta jinjina a nutse tana jin jikinta yana sanyaya,hankalinta kuma yana gamewa guri daya.
"Kin tuna sultane hammud na yankin sahel?" Ya tambayeta yana duban idanunta. Nazari kadan tayi sannna ta girgiza kai da sauri tana murmushi.
"Wanda yazo barkar haisam?.....yace in sha Allah shi din babban malami ne da ba'a taba irinsa ba?.....ga sarauta ga ilimi.......dan gatan malami.....isa takai isa kenan malamin dake da sarauta" Sosai murmushi ya qwacewa motii,ya sani zai wahala nanay ta manta sultane ko don saboda wadannan kalaman. UWA bata manta wanda yayi KYAKKYAWAN FATA ga yaronta.....kamar yadda bata manta wanda yayi mummunan fata a gareshi. Lokaci lokaci takan tambayeshi ina hammud na sahel?,saidai shi kansa bayace ba,don baisan ainihin sunan qasar ba har suka rabu,sadarwa ta yankewa kowa a cikinsu,tun a Egypt.
"Yana ina kuwa?,har yanzu ba wani labarinsa?"
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ya dawo khadeeja......ya dawo rayuwarmu ta hanyar bawa haisam auren diyarsa me sunanki khadeeja......auren da zaa daurashi nan da kwana biyu ko uku a madeena". Wani iri taji xancan,kwata kwata saita gagara fahimta,ta zubawa motii idanu tana neman qarin bayani.
Murmushi ya saki,ya miqa hannu yana lakace mata hanci.
"Dauke idanuwannan ma'abota kwarjini.....irin idanun sheikh muhammad haisam sak" Tare murmushi ya qwace musu,tana kallonsa ne bawai don bata aminta dashi ba,ta yarda da mijin nata dari bisa dari,da wata irin yarda da d'a yakewa iyayensa.
"Bani labari motii" Ta fada cikin son jin yadda wannan bahagon al'amarin ya kaya. Nutsuwa yayi sosai yana sake riqe hannunta cikin nasa.
"Gidan sultane haisam ya sauka,acan kuma yame gudanar da bincikensa,saidai cikin binciken ya samu gidan sultane a hargitse......ya samu