Showing 117001 words to 120000 words out of 188421 words

Chapter 40 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

80

ta gyada a hankali.

"Eh muhammad.....na samu amma da qyar,na rubuta don kada na manta,duk da nasan mantuw tayi kadan ta goge sunan azzalumin mutum irinta a kaina....."

"Meye sunan nanay?" Ya tambaya cikin tattarawa Nanay hankalinsa.

"ZEENATU" Wuta ce ta daukewa haisam na wasu daqiqu,kafin a hankali wani murmushi me cike da madaukakin mamaki ya mamayeshi. Zeenatu a Ethiopia......zaituna a agadez? Ya tambayi kansa da kansa yana kuma sake jinjina kansa.

"Matar ajani da ake zargi ZEENATU.......matar data fidda Obbolettii (sister) dinki daga gidanta ZEENATU.....ba wani alaqa tsakanin mutanen nan biyu?". Dif wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin zurfi da kuma nisa.

" Ajani ya taba aure shima!.....na shekara daya muhammad kamar yadda safeenata tayi!!" Nanay ta fuusgi kalaman cikin wani irin rudani.

"Good nanay......zan iya samun wani abu game da rayuwar gidan ajani.....kaman ta hannun uwargidansa?"

"Ta rasu muhammad.....sati daya da suka wuce.....amma,bari na kira safuura" Nanay ta fadi tana yanke kiran. Ko ina na jikinta kyarma yakeyi,tanaji jikinta kamar taga Obbolettii dinta har guda biyu,tana jin kamar an gano ind sisters dinta suke,tanajin kamar an gano bakin zaren ne.

Kai kawai haisam yake juyawa a hankali,maimakon bacin rai ya mamayi fuskar nan tasa ma'abociyar Kwarjini,kawai sai wani qaramin murmushi ne yake fita a fuskarsa. Ganin komai yake tarwai.....kowanne lissafi nasa da yake sarqewa a baya a yanzun ya fara zuwa masa da warwara......yan hangen komai kamar an saka rariya ana taceshi.

Hujja daya tak yake nema da zata sake bashi tabbaci itace MATAR AJANI......hujja daya tak da yakejin a yanzu ya shirya shiga kowanne sashe kowanne lungu na masarautar agadez don ya fiddo ta. Idan ya tabbata INA MAKASHIN?.....waye wanda ya aikata kisan da shima yayi batan dabo?. Ta yaya lokaci bayan lokaci suke iya aiwatar da bazaranarsu ga motii aba jifar?,ta yaya?,su waye rassansu?,su waye mataimakansu?.

Yatsunsa kawai yake murzawa a hankali yana sake baje sabon lissafi. Kebantaccen dakin ajiyar mammina.....shi kadai ne abinda ke masa yawo a ransa da kansa....kebantaccen dakin da jikinsa ya bashi tabbacin lallai akwai BOYAYYUN SIRRIKA. TAMIM har guda biyu dake da alhakin kula dashi,da masu jin yaren oromo da yake da lissafin sunayensu yanzu haka fes dama fuskokinsu gaba daya!..

Turqashi......ya zuwa yanzu nasan me karatu yana tunanin KOMAI YAZO QARSHE......QARYA TA GAMA QAREWA......GASKIYA KUMA TA GAMA BAYYANA......SAIDAI NACE KUXO MUJE

MAJI

MA GANI

Maleek ne ya shigo a nutse bayansa daya daga cikin hadiman haisam ne. Dauke da wani kyakkyawan royal tray da aka jera masa qananun bowls masu kyau.

Idanunsa ya zare ya maida kan maleek,shima maleek din shi yake kalla.

"Ina fata wannan aikin ya kammalu?" Tashi haisam din yayi ya zauna sosai yana duban maleek sanda hadimin ya ajiye abinda ke hannunsa yana fita.

"Yadai kusa......inaso na shiga masarauta,yau zanyi kwana uku ko biyu kuma kafin na fito.....ka kira likitan nan yazo ya ciremin wannan abun" Ya fadi yana daga hannunsa dake dauke da Canular.

Kai maleek ya girgiza yana zama saman sofa.

"Amma kasan akwai ragowan drip da zaka sake sha?"

"Ya isheni haka maleek,ina buqatar kammala wani abu dole.....inaso na gama komai qasa da sati daya". Ya amsa masa yana yarfar da hannun nasa,don har yadan fara tasawa saboda zaman allurar na kwanaki a jikinsa.

"Okay " Ya fadi yana lalubar wayarsa don kiran hadiminsa da suke agadez din tare.

*TAMIM*

A nutse ya miqawa almaz alkyabbar data zama sutura ta qarshe da zai sanya a jikinsa,bayan tarin kayan ado da qawar daya fara sanyawa a jikinsa na tsadaddar suturar ALHARIR.

Shi kansa tamim din a yau yana hangen wani irin kyau da biyayya da suturar tayi a jikin almaz din,tamkar dai dama ya saba da ire iren wadannan tufafin a jikinsa. Duk da haka ba abinda ya rage qudirinsa a zuciyarsa,ba abinda ya rage kaifin abinda yakeji a zuciyarsa.....hakanan ba abinda ya sauya daga aikata abinda yayi niyyar aikatawar.

A nutse almaz ya taka cikin wani salon izza da yaji ya saukar masa,ya matsa gaban tamfatsetsen madubin dake ajiye a wani bangare na daban na dakin.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Duban kansa yakeyi cikin madubin,yana jin wani izza tana shigarsa. Tsahon rayuwarsa bai taba ganin inda yayi kyau har haka ba,koda sau daya kuwa,duk da cewa yana rayuwa cikin sutura me kyau da kuma cima me kyau,amma ba sutura irin wannan ba....ba tufafi irin wannan ba me cike da nuna qarfin izzar wanda ya sanyasu. Sosai yakeji kansa yana sake shiga charge,abinda ya qara fadada nishadin da yakeji kenan,don tun daga daren jiya ya baje dukkan kayan mayensa da aka dakatar dashi daga sha,yasha me isarsa,ya kuma dora da wani da safen nan bayan wadancan sun sakeshi. Yana jin wani banbanci da wadannan kayan da wadanda ya saba sha. Wadannan din masu taada ne sosai data sanya aka tanadar masa kwali kwali kawai don jin dadinsa,ta kuma yi masa alqawari daman,ta kuma cika,abinda ya sake saka masa nutsuwa da bin dukkan sharudda da qa'idojinta. Basa sakashi yayi mankas ya manta da abinda yakeyi,amma suna fiddashi daga duniyarsa,suna kuma fitar dashi daga ainihin duniyar da yake rayuwa a cikin ta,suna sakashi ya jishi daidai yake da kowa,yana kuma daidai da tarar kowa da komai.

Waiwayowa yayi yana murmushi yana duba tamim,abinda ya sanya tamim dauke kansa daga mummunan kallon da yakewa almaz din,kallon dake cike da hassada qyashi kishi da baqinciki.

"Wai nine almaz a haka?.....nine na mallaki matar aure d'iya mafi girman daraja a yankin africa......gida irin wanda nake mafarki da rayuwa cikin izza mulki da qasaita.......amma kasan meye tamim?" Yayi tambayar yana duban fuskarsa yana kuma takowa zuwa gaban tamim din. Qoqarin gaske tamim yayi wajen maye murmushi saman fuskarsa.

"Na rasa wanne dalili ne ya sanya uwargijiyarka ta zaboni a cikin tarin matasan qasar Ethiopia.....a baya nayi tunanin don tana mahaifiyata ne,amma a yanzu tunanina ya gagara cafko komai" Almaz yayi maganar da tarin mamakin dake ransa daya bayyana cikin muryarsa.

Murmushi tamim ya saki,yana takawa a hankali gaban wani babban glass cup daya cikashi da tataccen lemon inibi wanda ya cakudashi da sinadarai daban daban.

"Kaidai ungo wannan kasha mu tafi.....yanzu ba lokaci bane na tunanin wannan.....tunda harka yadda ka shiga cikin masu sa'a ai shikenan,ba abinda ya rage maka saika zuba idanu kaci gaba da irgen lokutan sa'arka". Dan shuru almaz din yayi,kafin kuma ya saki murmushi yana miqa hannunsa ya karbi lemon hannun tamim din.

"Inason lemon nan sosai,inajin dadinsa" Ya furta a hankali sannna kuma yakai cup din bakinsa.

Tas ya shanye lemon a kurba daya,sannan ya miqawa tamim cup din yana cewa.

"Kamar zai bani freshness din da nakeso,na gode tamim" Ya damqa masa cup din yana juyawa. Da wani kalar shu'umin murmushi yabi almaz din,rabin aikinsa ya kammala saura rabi,yana duban takunsa da yakeyi cikin wani yanayi daya bayyanar da b'urbushin qasaita.

"Matsiyaci ya samu guri,wai har ya iya yanayi na masu mulki da saruta" Ya fada a fili can qasa yana jifan hanyar da almaz yabi da harara.

Jerin gwanon motocin alfarmar guda shida ne cass suka takewa motor din da almaz ke ciki baya. Ya saki wani irin murmushi sanda dukkan wani hadi dake cikin lemon ya fara zagaya sassan jikinsa,ya kuma soma jinsa a sama,uwa uba yadda yaga manyan motocin alfarma irin wannan na take masa baya sai ya sake sanya yanayin yabi jikinsa sosai

"Shege almaz,yau shine kamar gomna?" Ya tambayi kansa da kansa yana dariya. Sam a rayuwarsa ya rayu cikin wani madaukakin yanayi ba burinsa bane,damuwarsa daya shine ya rayu cikin 'YANCI. Bayason UMARNI,yafison ya rayu cikin sakewa da kuma zabawa kansa duk kalar rayuwar da yakeso,ba tare da an bashi umarni ba,ba tare da an sanyashi ko an hanashi ba. Ya sani......yanajin wata izza da girma a cikin jininsa da baisan wacce iri bace,wannan ya sanya sau tari yafi zabar kebance kansa tare da qin amincewa ya shiga taron jama'a.

Duba daya tamim yayi masa ya tabbatar ya fara fita daga hayyacinsa,ya fara buguwa,sai ya gyara zamansa sosai yana dubansa.

"Kasan meye almaz?" Kai ya girgiza yana duban tamim da idanun nan nasa da tamim din yake ganin suna masa kama da wasu idanu.

"Akhnan matarka.....tana da tsananin girman kai....bata girmamawa kowa saboda tana ganin mahaifinta shine sarki a wannan yankin....."

"Ashe?" Almaz ya fadi da wata irin murya yana bude idanunsa da kyau. Kai tamim ya jinjina cikin bashi tabbaci da son isar da saqonshi

"Qwarai da gaske.....kai baka lura ba?,a matsayinka na namiji kuma mijin dake aurenta.....ta taba gaidaka?,kota taba zuwa gurinka nemanka?,kota taba nemanka din koda a waya ne?" Shuru almaz yayi,wasu abubuwa suna cakudewa cikin kansa tsakanin maganganun tamim da kuma abinda tamim din ya bashi yasha. Gefe daya wata izza tana huruwa cikin ransa,yana jin kansa yana girma da fadi.

"Ba ko daya" Almaz ya fada muryarsa tana kaduwa da wani irin yanayi na wanda ya fara buguwa.

"Ahto....to kai kuma saika bari aci gaba da tafiya a haka?"

"Inaaaa......daga yau zan fara nuna mata ina da iko a kanta" Ya fada yana ji a ransa dole ya zama tsayayyen namiji.

A hankali tamim ke buda masa wasu abubuwa,yana kuma sake karanta masa abubuwan da ya tabbatar zasuyi tsananin tasiri a kansa game da akhnan din. So samu komai ya fada jagule musu a yau,shi yasa ya fara da horashi da kadan daga cikin kayan mayen dana tanada,wanda wannan shine zai bashi damar dorawa kan tsarinsa d'od'ar ba tare da sunansa ko alamar ayar tambaya ta hau kansa ba.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 56*

Yanaji a ransa,daga sanda auren almaz ya sauka daga kan akhnan,daga sannan zaiyi dukkan me yuwuwa don ganin ya mallaketa,koda meye zai faru a shirye yake,idan ta kama ma yana jin cewa a shirye yake ya dauketa cancankat ya rabata da ganin kowa ya kaita wata duniya ta daban,inda zai samu damar mallakarta ba tare da wani tarnaqi ba.

*AKHNAN*

Tana tsaye ne kawai tana jin yadda birra ke shiryata cikin wasu qawatattun kaya na alfarma da mammina ta aiko dasu. Iya akwatin da aka sanya kayan kawai abun kallo ne ballantana akai ga kyansa da kuma tsadar da suke da shi. Tana ji ne kamar ta sanya hannu ta ciro zuciyarta daga qirjinta,tana jin wani irin qunci da suya da zuciyarta takeyi kamar zata babbake.

Maganganun mammina kawai suke bata dauriya da qwarin gwiwa.....addu'ar da sultane ya kirata jiya yayi mata wadda ta bata tabbacin ya huce da ita.....yana kuma dab da maidata BIFTU dinsa kamar yadda take a baya,su kadai ne abinda suka sanya take iya tsaiwa da qafafunta a yanzu haka. To amma yaya rayuwar zata kasance?,ta yaya zata iya carrying identity na matar aure da mutumin da shi da ZERO daya suke a wajenta.

"An kammala ranki ya dade" Birra ta fadi cikin tsananin girmamawa tana komawa baya. Batako waiwaya ta kalli kanta a madubi ba kamar yadda ta saba ba ta fara matsawa inda birra ta ajiye mata takalmanta ta fara zurawa.

Falaak ce tayi sallama a nutse tana shigowa,fuskarta qunshe da murmushi tana duban akhnan din. Ita kanta idan ta kalli akhnan.....ta tuna a yanzu tana amsa sunan matar aure ne saita dinga jin abun wani abu na daban. Wani al'amari ne da dukkaninsu basu kawo wanzuwarsa a kusa ba.

"Ya biftu" Ta qaraso gabanta tayi kiranta da yanayin kira irin na tsakanin qanwa da yayarta.

Kyawawan blue eyes dinta da kwallin da birra ta zizara mata ya qara yiwa kyau ta daga ta dubeta.

"Yayanmu ya qaraso.....zan iya shiga sahun 'yan rakiya?" Ta tambaya tana dage dukka girarta sama.

"Yayanmu?" Ta maimaita sunan cikin kanta,saita ware idanunta akan falaak

"Me yasa kike da rawar kai har haka falaak?,yaushe ya zama yayanki?" Tayi maganar haka kawai tana jin furucin falaak din yana tabata. Bata wani damu ba,zuwa yanzu halayen akhnan din duka ba baqinta bane,sannan uwa uba tana sanya ran lokaci yayi da akhnan din zata sake janta a jiki,don zata tafi gidan aurenta ne,zata fara wata rayuwa ta daban ba wadda sukeyi ba a yanzu,dole komai zai canza.

"Tunda kina nuna min careless,na sani koshi zai daukeni a matsayin qanwarsa ta gaske,irin abinda na rasa a tare da ke" Sosai maganan ya ratsata,amma duk da haka saita dauke idanunta daga kan falaak din taci gaba da sanya takalmanta a hankali,kafin ta soma nufar qofa,birra buhaina bushira barratu bara'atu dama falaak suna biye da ita.

*HAISAM*

Yau din tun daga nesan nesa da gidan ya sanya salaana ya ajiyesu. Akwai nazari da yakeso ya sakeyi na unguwar duka dama anihin ginin katangun masarautar. Tare da maleek suke takawa,wanda dukkaninsu suna maqale ne da Bluetooth suna hira a tsakaninsu ta conference call din da suka hada da mutallab....khadeem....amjad.....naseeb. Duk da maganarsa qalilanne cikin hirar tasu,amma hakan bai hana masa jin dadin hirar ba,wadda ta gauraya da yanayin garin daya bada lullumi na hadari. Jikinsa har yanzu bayajin qwarinsa sam,amma kuma hakan dai bai kauda wannan jarumtar qarfin halin da qarfin zuciya da qawazucin dake tattare dashi ba.

Surutu ko dogon magana ba dabi'ar maleek bane,suna dan kamanceceniya ta wannan fannin,duk da wani lokaci maleek idan da zurfin sabo tsakaninku yana dogon hira,kamar dai a cikinsu su bakwai din,to amma yau tunda suka taho yake basu labarin agadez.

"Nan kusa zakuzo guys....don nikam har nayi farin kamu" Maganan yaja hankalin haisam,amma sai baice komai ba da wannan salon basarwar tasa,yayi kaman baiji ba,yaci gaba da takawa abinsa yana nazarin ginin katangar masarautar da suka fara cimmata.

Yanajin ihun khadeem,dan rud'u ne na gasken da kusan yafi kowa rudu a cikinsu,wannan ya sanya yafi kowa tara 'yammata.

"Me nakeji kana fadi maleek?,yau kuma an biyo ta kanka?" Idanu maleek ya lumshe yana shafa qirjinsa murmushi yana qwace masa.

"Wata princess tayi wuf da zuciyata daga shigowata......kuma bazan tsaya kallon ruwa ba kwado yayimin qafa.....zan zauna,zan jira mahaifinta ya dawo na nema aurenta da kaina Allah khadeem" Still haisam yaji maganan ta masa ba zata,duk da cewa yayi hasashen haka dama tun wancan ranar,amma kuma issues din da suka sakoshi a gaba ya sanya bai maida hankali ba akai.

"Amma mutumina.....ya akayi ka riga dan gari yin farinjini?" Naseeb ya fadi da alamun yana danne dariya qasan ranshi.

Sarai maleek yasan da waye yake,saiya saci kallon haisam sannan ya janye idanun nasa da sauri kafin ya masa wannan kallon nasa yana dariya qasa qasa.

"Ya qaryata zuciyarsa ne kawai.....ina kuma masa fatan kada nan gaba kadan na sake kiranku kuzo kuyi jinyar me ci......" Qit! Haisam ya yanke kiran gaba daya,kowannensu take wayarsa tayi disconnecting,abinda ya sanya kowa dariya a cikinsu daga shiyyar da yake. Sunsan halinsa,sunsan aikinsa ne,kuma shi daya yake iya musu wannan yankar qaunar idan hira batayi masa ba,don shi kadai ne a cikinsu ya karanci sanin ilimin sanin na'ura ciki da bai dinta.

Harara yadan watsawa maleek sannan yace

"Ashe dama ba don Allah ko zumunci kace zaka zauna ba?....."

"Ba haka bane captain......"

"Haka ne.....kuma zanga waye zai baka auren....badai falaak ba?" Hannu maleek ya dora saman qirjinsa yana marairaicewa haisam.

"Tsaf zaa maidawa motii ni unconscious.....a haka ma nayi kara ne ban tareta ba,inaso nabi komai bisa tsarin addini.....mahaifanta kafin ita" Kai haisam yake jinjinawa,ya sani dukkaninsu har yanzu ba wanda ya sauka daga kan tarbiyya mutunci kima da martabarsa,saidai isowarsu bakin babban qofar shiga masarautar ya sanya suka aje zancan a nan.

Duk wani hadimi dake bakin kowacce qofa da zai wuce zuwa hanyar ciki rusunamasa yakeyi cikin GIRMAMAWA. Irin girman da sultane ne kawai ya cancanceshi,abun har ya fara bawa maleek mamaki.

Su kansu wani jin dadin dawowarsa sukeyi,hakanan sukejin rashin karsashi na gabatar da aikinsu,da wani irin salam da gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login