Showing 39001 words to 42000 words out of 188421 words
saro wasu ba tare da takurawa ko saka takunkumi daga wajen mammina din ba.
Daga nesa can suka baro mutum biyun da suka zamo amintattunta na gaske gaske,wadanda ta sanya suka musu tattaki cikin shigar da ba zaka gane daga ina suka fito ba. Tayi hakanne saboda daren daya soma yi,daren yayi nisan da fitar zata iya zame musu qalubale,duk da cikakken yaqinin amincin da yankin nasu yake dashi.
*HAISAM*
Sanye yake da long sleeve hoodie shirt a jikinsa baqa wadda ta dace da yanyin sanyin da yake busawa a gari ta kuma dace da skinny jeans din jikinsa.
Saman kansa baseball cap ne wanda ya lullubeta da hular dake maqale da rigar jikinsa.
Boots ne a qafafunsa masu tsananin daukan idanu,duk kuwa da duhun daren da kuma kalarsu da suka kasance baqaqe. Dukka hannunsa zube yake a aljihun wandonsa saboda sanyin da yake kadasu,idan ka ganshi a lokacin ba zaka taba dauka shine sheikh haisam ba. Dressing dinsa baqo ne da sam ba kasafai ya fiya yinsa ba,amma yana tsananin fidda wani irin sirrin kyau tattare dashi gami da bayyanar da zallar quruciyar dake yawo cikin jinin jikinsa.
Sosai wannan tsahon nasa ya fito,tsahon da dole ka kirashi da GIANT kai tsaye a iya kallon farko kawai,tsahon ya dace da yanayin cikar jikinsa da kuma murjewarsa,wanda kai tsaye wasu lokutan zaka iya kiransa gabjeje saboda yawan motsa jiki da qarafuna da injina masu nauyi da yake yawaita yi.
Ko a yanzun daya kasance wani irin dare me yawan shuru,cikin nutsuwar nan data zame masa dabi'a yake takawa abinda,kai bakace ya dauki duhun dare ko nisansa a bakin komai ba. Ba wani tsoro ko firgici a tattare dashi,daga fuskarsa har zuwa zuciyarsa,zuciyarsa dake motsawa can qasan qirjinsa tana kuma maimaita ayoyin qur'ani da maimaitasu din ya zama wata dabi'a ta ruhi da zuciyarsa a duk sanda ya samu kansa cikin shuru da kadaicewa kaman haka,ayoyin shafi na biyun qarshe na cikin suratu al_imran,wanda ke bayani akan halittar sammai da qassai da kuma jujjuyawar dare da yini,tsarkake girman ubangiji kan yadda ya halitta ya kuma tsara komai. Bayan haddar qur'ani gaba dayansa da Allah ya azurtashi dashi......akwai tafsirinsa daya kammala tun yana da shekaru goma sha takwas a duniya zuwa sha tara,don haka a duk sanda yake karantashi yana jin kamar yarensa yake magana dashi saboda fahimtar fassara da ma'anar kowacce aya,don haka ko a yanzun da yake karanta ayoyin yana sake girmama zatin Allah daya halicci dare,daren kuma ya zama mahutar kowanne bawa.....mahutar kowacce irin halitta. Shuru yakan mamayi ko ina,zirga zirga tana taqaita a bisa dole,jikkuna suna kusantar makwancinsu zuwa ga bacci,baccin da yake tamkar dan uwan mutuwa saboda karbar ruhin kowa da Allah yakeyi. Yana dawo da ruhi da rayukan wadanda yaso suci gaba da rayuwa,ya kuna riqe ruhikan wadanda kwanakinsu suka qare a duniya.
(Fahimtar ma'anar qur'ani a sanda kake karantashi abune me wani irin gard'i da ba zaka fahimta ba sai in kana gane ma'anoni da fassarar ayar,kuyi qoqari yaranku su fahimci hakan,zai taimakawa hankulansu imaninsu da tarbiyyarsu,hakanan BACCI abune daya kamata a kiyaye ladubban yinsa,akwai addu'o'in da sukazo na bacci kala kala,a cikinsu kuma akwai wadanda suke dauke da addu'ar neman gafarar Allah idan daga wannan baccin rai yayi halinsa,shi yasa akeso kafin ka kwanta ka cika da aiki me kyau,kamar nafila ko karatun qur'ani istigfari da sauransu,da yawa cikin novel nasan muna qoqarin saka nafila yayi sannan ya kwanta ko shafa'i da wuturi,duka muna qoqarin nuna muku kafin ya kwanta ko ta kwanta wani aiki me kyau tayi,do bakasan zaka tashi ba ko ba zaka tashi ba,Allah ya bamu cikawa da kyau da imani).
K'irjinsa cike yake da jiran sakamakon abun hannun da ya tura a qera masa,a yanzun tunaninsa yayi nisa zuwa ga yadda zai fidda asalin abun hannun daga ma'ajiyarsa zuwa gurinsa don gudanar da binciken da zai zame masa mabudi na farko kuma tsani na farko da zai fara takawa zuwa ga inda mai laifinsu yake.
Zuwa yanzu ya gama karantar tsari da yanayin unguwar gaba daya,kusan ya gama da komai daya shafeta cikin dararen da yake fita. Ya gama sanin manyan mutanen dake rayuwa a cikinta,adadinsu sunayensu dama ayyukansu.
Idonsa ya sake daukewa daga sararin samaniyar da yau sam ba alamun hadari sai taurari data bar musu,yana sauke dubansa a gabansa,daidai sanda ya sake ganin gilmawar mata biyu.
Mata biyu kamar wancan karon,kamar wancan lokacin,da irin suturar daya gani a wancan lokacin,saidai banbancin kawai a yanxun ba wata mota daura dasu,da qafafunsu suke shiga layin.
Da wani irin hanzari ya jawo baseball cap dinsa da hoodie dinsa ya rufe fuskarsa da kyau,da wani irin kuzari kuma ya nufi layin da yaga sun shiga din cikin kula da takatsantsan da motsinsa.
Sanda ya isa babu su ba alamarsu,ya qarasa a hankali qasan wata matashiyar bishiya data bada rassa ba masu yawa ba,wadda aka dasata daga farkon layin,ya jingina sosai da ita yana sake sajewa a jikinta.
Da dukka wannan fikirar da basirar yake bin gidajen dake jere cikin layin da kallo cikin nutsatsen nazari. Layi ne da yake jerin sahun layikan da suke dauke da manyan mutane sosai fiye da kowanne layi......layi ne kuma da yafi kowanne qarancin zirga zirga na jama'a koda kuwa da rana ne.
Ci gaba yayi da kallon gidajen,kowacce qofa a rufe take,ba wata qofa guda dake a bude,abinda yaso cakuda hankalinsa kenan ya kuma so kauda tunaninsa ya gaza sanyawa kowanne gida a ciki wata ayar tambaya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kai ya girgiza a hankali,ko kadan bazai yarda da kwanyarsa a lokacin ba,lokaci ne daya kamata tayi aikinta yadda ya dace. Ganin gilmawar wasu mata sanye da uniform na gidan sultan of agadez......a dare irin wannan daya zama doka ce ta hana shiga da fita cikin lokaci irin wanna har sai safiya tayi. Da wani salo da yanayi na tafiyar da batayi daidai da tafiyar da ake yinta bisa qwarin gwiwa gaskiya da rashin tsoro ba. Yayi nisa......akwai tazarar da zai zamana zai wahala ace kusanci ne ya kawosu unguwar.....ko cudanyar maqotaka,unguwanni ne dake maqotaka ada juna,saidai kuma mabanbanta ne.
Da cikakken kuzarinsa ya miqe daga jikin bishiyar,ya kuma tsaya qyam da qafafunsa yana sake zube hannuwansa a aljihun wandonsa sosai yana sake zube idanunsa akan gine ginen.
Iska sosai ya zuqa yakai hunhunsa sannan ya furzo da ita daidai sanda lissafinsa yazo kan gida na shida.
Idanunsa cak ya tsaida akan gidan yana qare masa nazari. Kowanne gida dake layin yana da sassauqan fenti da bai tsufa ba bai kumayi sabunta da yawa ba,amma shi wannan gidan sabon fenti gareshi. Kowanne gida akwai sassauqan haske dake nunawa kadan,alamun wani girin fitilunsa a kashe suke,wani gurin kuma a kunne,amma wannan gidan dundum yake,ba wani alamun haske komai sirantarsa a tattare dashi.
Akwai mazubin shara gaban kowanne gida don inganta layin,amma daya lura sosai babu mazubin sharar a gaban wannan gidan......
Sake zagayawa yayi da idonsa sauran gidajen kafin ya sake maida dubansa gaban gidan. Daga alamunsa daga waje yana da yalwa da wadatar da za'a iya shigar da mota cikinsa kamar sauran dukkanin gidajen unguwar da layin,amma motar tana fake a waje ita daya qwallin qwal......
So samu ya qarasa jikin motar,ya duba wadanne lambobi ne a jiki,duk da motar daya taba gani anbi diddigin lambobin jiki,saidai duk zurfin binciken da sukayi basu samo komai a kanta ba,hasalima plate numbers din isn't valid a region na agadez dama nijer gaba daya.
Saidai kuma a tsari irin na aikinsa yasan hakan zai iya zama da hadari......takawa koda d'ani guda ne daya inda yake tsayen zuwa gaba,komai zai iya faruwa,wanda inda sabon ma'aikaci ne shi ko maras gogewa yasan abinda zaiyi kenan,saidai a aiki irin nasu......akwai wasu damarmaki da kana ji kana gani zaka barsu hakanan su wuce su subuce maka saboda wani dalilin da yafi wannan qarfi da amfani.
Sake bin layin yayi da kallo,akwai dan kiosk qwara biyu tal,wanda a binciken layukan da yayi na wancan lokacin dukkaninsu suna saida qananun abubuwan da shiga kasuwa zai zamewa mazauna unguwar wahala. Sai ya janye manyan idanunsa da suka rusuna kadan,ya saka yatsansa cikin kunensa,take wani red light yayi blinking na wasu sakanni sannan aka fara magana.
"Ina buqatar beeno yanzun nan,a bunu street,banaso ya haura mintuna biyar don ina hanyar barin layin.......gida ne number ta shida.......ya zama shine target din" Ya qarasa fada yana kuma gimtse kiran kai tsaye.
Ya samu iya abinda yake buqata a nan din,yanaso yayi gaba kafin wadanda suka wuce din su dawo ko zai samu nasarar sake samun wani abun da zai bashi haske daga hanya har zuwa cikin gidan sarautar,sai ya maida hannayensa zuwa ga aljihun wandonsa ya soma takawa a nutse da kuma lura yana barin gurin.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
[1/9, 19:37] +234 903 555 3736: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 20*
*MAMMINA*
Tun daga farfajiya ta biyu take iya jiyo sautin almaz cikin hargagin data tabbatar tashin hankali akeyi dashi. Idonta ta lumshe kafin ta budeshi cikin bacin rai gami da jan qaramin tsaki.
"Kamar muryar yaron nan nakeji" Mammina ta fadi don samun tabbaci.
"Shine......ba shakka shine" Ta fisu ta fada tana jinjina kai. Shuru ya biyo baya,tamkar mammina din ba zata ce komai ba kafin ta sake magantuwa.
"Banda target ne cikin rayuwarsa gaba daya......banda wata shiryayyar qaddararsa ce data ahalinsa ke tunkararsa wadda ba makawa saita samesu......tabbas da na canza yaron nan". Wani murmushi ta fisu ta saki
"Dabi'unsa zaki canza bawai shi din zaki canza ba,aikinmu na yanzu shine mu canzashi zuwa yadda mukeso din,mu canzashi zuwa kalar mijin burin AKHNAN.....abun harinmu shine ya mamayi rayuwarta ta soshi fiye da yadda takeson SULTANE dole muyi sadaukarwa me yawa akan hakan don tabbatuwar wannan MANUFAR don samun zuri'a daga garesu cikin sauri kaman yadda buri da mafarkinki suke......ki barni dashi" Tafisu ta fadi suna buda qofar da zata sadasu da ainihin gidan,don tuni sunsan da zuwanta,anbar komai kuma ta yadda zata samu daman shiga ciki ba tare da kowa ya fito ko yazo ya bude mata ba.
"Na rantse idan baka bani ba......zan kubce muku irin kubcewar da ba zaku taba samoni ba!!!" Ya fadi da wata tsawatacciyar muryar data sanya wata mummunar faduwar gaba saukarwa mammina......muryar ta cilla can qololuwar cikin tunaninta,ta lalubo wani sauti da yayi sak da sak da wannan sauti da muryar da almaz.
"Akwai wani dan tasirin kamanceceniya a sanda yake magana cikin fushi?" Ta yiwa kanta tambayar data saka zufa tsatstsafowa a goshinta.
"Tafisu.....banaso ya sake magana cikin fushi.....banaso na sakejin yanayin sautinsa yana fita cikin fushi"
"Na fahimta" Tafisu ta fada tana jinjina kai wani kalan murmushi na fita saman fuskarta. Wannan murmushin wani kalar abune da a wasu lokutan yake bawa mammina mamaki. Duk yadda takai ga iya wasan kwaikwayo cinye firgici da damuwa.....maye gurbin tsananin tashin hankali da sassanyan murmushi tafisu ta fita iya buga wasa ta wannan bangaren.
"Amma kuwa da ka yiwa kanka da kanka asarar tulin arziqi......tulin jin dadi maras yankewa da yake jiranka....." Muryar tafisu ta ratsa hargagin almaz da wani irin murmushi.e taushi saman fuskarta tana dubansa.
A fusace ya waiwayo,suka zubawa juna ido shi da tafisu suna yiwa juna kallon kallo har sai daya janye dubansa yana furzar da iska daga bakinsa,wannan ya bawa tafisun daman isa gabansa. Zamewa tayi cikin salo na sarauta ta durqushe a gabansa cikin tsananin girmamawa tamkar tana gaban sultane
"Ranka ya dade....... Kai da kake shirin zama suruki ga qasaitaccen sarkin africa irin sultane?.....kai da kake shirin mallakar da jagorantar gurin da yafi ko ina kawo maqudan kudade kaf dukiyar surukinka?......kai da kake shirin zama mutum me qololuwar martaba?....ina kai ina wadannan tarkacen a yanxun?......" Idanu ya zubawa tafisu yana jin wani abu me kama da girma girma yana sauka saman zuciyarsa.......tasirin girman ya soma danne tasirin fushinsa,yana saukar da wani sassauci a dukka zafin da zuciyarsa da jikinsa ma ya dauka. Ta fahimci hakan tafisu,bama ita kadai ba hatta da mammina din,saita dan dago a hankali.
"Inda zaka nutsu ka kwantar da hankalinka......ka bamu aron nutsuwarka da kamalarka na wani dan lokaci......gaba kadan daki guda zaka mallaka na dukka kalar kayan da kake kwadayin sha kakejin labarinsu kuma baka taba samunsa ba......ko daga wacce qasa yake kuma ko daga wanne yanki ake kawoshi sarrafashi ko nomashi......amma fa lallai sai kayi haquri na wani dan taqaitaccen lokaci". Idanunsa ya dauke,yana jin wani girma yana saukar masa.
Karon farko da cikin dabi'arsa yakeso da buqatar wannan girmamawar da bai taba samunta ba,a yanzun sai tazo masa da wani irin yanayi da yaji kome akeso yayi zaiyi,indai zaici gaba da samun wannan girmamawar,don haka ya koma ya zauna dabas saman daya daga cikin tsadaddun sofas din dake masa dadin kwanciya sosai tun xuwansa gidan.
A sace ta kalli mammina,mammina din ta jinjina kai cikin tsananin mamakin yadda tafisu ta iya sarrafa komai cikin qasa da mintuna biyu kacal. Almaz din dake da wahalar sha'ani,tsananin taurin kai da rashin jin magana,kafiya da tsaiwa cak akan abinda yasa kanshi amma ta iya cinsa da yaqi haka da sauri?.
Qarasowa tayi ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa tana dubansa. Yayi fresh yayi kyau a kwanakin kamar yadda ta buqaci ganinsa haka,saita dauke idanunta ta maida kan tamim dake tsaye,wanda tunda suka shigo bai sake cewa komai ba.
"Kana iya komawa masarauta,yau a ciki zaka kwana,akwai yiwuwar sultane ya nemeka da safe koda asubahi" Kai ya jinjina yana rusunawa cikin girmamawa,sannan ya juya yana nufar hanyar fita zuciyarsa tana matsewa guri guda.
Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,kafin ta fisu ta matso tana ciro wata jaka daga qugunta. Wareta tayi ta fito da wasu takardu da kudade ta zubesu saman table din data jawo zuwa tsakiyarsu.
"Muna maka murna......zaka samu 'yanci fiye da yadda tsuntsun dake shawagi a sararin samaniya ke samu".
Kalmar 'yancin da tafisu ta ambata itace taja hankalinsa har ya dago da kansa da a dazu suke kallon sama. Yanci itace kalmar da yafi buqatar ji,yasha gwada yin nisa da rayuwarsa dama duk mutanen da ya sani don yayi rayuwar tasa a yadda yakeso cikin sakewa.......amma baya nisan zango yake sake tsintar kansa cikin wadannan mutanen dai da yake tunanin ya yiwa nisa. Duk inda ya motsa rayuwarsa kamar ana monitoring dinta ne.......rayuwar sa tana zagaye ne da wadanda keda iko a kansa wanda ba kasafai ya fiya banbancesu ba.....kamar yadda yake rayuwar ba tare da sanin hagunsa ko damansa ba,daidai da rashin daidai dinsa ba.......saidai ba abinda ya gane daga qarshe illa KUDI.
Ya fahimci sune suke da ikon sarrafawa mutum komai yadda yakeso.......ya fahimci sune suke da qarfin ikon sawa ayi koda ba'aso,a kuma bari koda ba'aso ba,don haka har ransa yakejin ya karbi tayin wannan aikin don kaiwa ga buqatarsa,wannan ya sanya ya miqe ya zauna sosai yana duban bayanan da tafisu ta soma masa kan takardun da adadin abinda zai iya zama nasa.
Murmushi kawai yakeyi yana jin mafarkansa suna budewa zuwa reality. Aikin duka ya masa wani irin sauqi,don tako ina ribarsa yake hangowa ba wata faduwa