Showing 21001 words to 24000 words out of 188421 words
naki dole ki warwareshi......dole ki fuskanta kibi dukkan abinda yake tsarin sultane.......mun fara kaiwa wata gaba dashi......gab'ar dana fuskanci sai munyi da gaske zamu b'ulle......sai da takatsantsan zamu sha a hannunsa,saboda tunaninsa a yanxu ba nashi bane shi kadai.....ba shi kad'ai yake tunaninsa ba".
"Amma mammina........me yasa?....."
"Ya isa akhnan" Mammina ta furta a hankali tana canza yanayin fuskarta,sai kuma ta miqe tsam tana zame jikinta.
"Bazan yarda naci gaba da baqinjini ba......bazan bari aci gaba da yimin mummunan kallo ba......aci gaba da fassara tarin alkhairaina zuwa wani abu na daban ba.......kiji kiyi tunani da kyau.....amma karki manta......ko da zabinki ko babu zabinki kina iya zama rabon me rabo,kamar yadda sultane ya tsara hakan......yanzu dukka ragowar aikin yana hannunki......na gama nawa aikin" Mammina ta fadi a nutse sanda takai dab da qofar fita daga parlor din.
Bata motsa ba.....batayi kuma yunqurin fita ta bita kota dakatar da ita,don a karan kanta takeji duk wata kafa ta tunaninta ta toshe ta kuma tsaya mata cak.
Lallai tana buqatar nisan tunani da kuma nisan nazari......lallai tana buqatar kebancewa,tana kuma buqatar qure duk wani nisan tunani da zatayi akan MEYE MAFITARTA?.
★Idan tace zata iya wassafa adadin abinda takeji a jiki da zuciyarta tasan tabbas tayi qarya. Wani irin yanayi ne dake d'auke da wani irin tsukewa qunci da tashin hankalin da batasan ta ina zata bullo masa ba.
Abu guda daya ta sani shine.......ba zata taba bari zaituna taga rauninta ba,ba zata taba qyaleta ta fahimci tayi rauni tattare da ita ba.
Iya boye yanayin da zaituna ke jefata a ciki wani kalar tashin hankali ne da ta tabbatar qarfin jarumtar dake yawo a jininta ne kawai yake tallafarta ta wannan bangaren.
*_"BA'A QWACEMIN ABINDA YAKE NAWA NE NA ZUBA IDO NA QYALE,BA'A SHIGA GONATA BA TARE DA NA DAUKI FANSA BA......BAN IYA KAWAICI KO HAQURI BA......DUK WANDA YA SHAYAR DANI MADACI SAI NA SHAYAR DASHI GUBA.......DUK WANDA YA DANDAMIN ZAFI SAINA D'AN D'ANA MASA RADAD'I MAFI CIWO KODA YANA KWANCE CIKIN KUSHEWARSA......SHEKARU KO DADEWAR ZAMANI BASA HANANI KO SU MANTAR DANI AIWATAR DA FANSATA_*
Maganganu ne da suka zauna mata daram a cikin kwanyarta......cikin daren farkonta data soma kwana cikin masarautar agadez......ta kuma zama MATA mallakar sultane Muhammad.
Daren da ta fara sanya zaituna a idanunta madadin sultane......daren da kowanne ango shike marabtar amaryarsa....a daren zaituna ce ta marabceta........bayan ta sanyata ta dole ta amsa sunan AMARYA......duniya dukka sun kalleta da wannan sunan a madadin GIRMA DA MATSAYI na uwar gida da take dashi a qa'idance.
RABOn falaak ta tabbatar shi yayi rantsuwar daya tilastata a wannan daren ta tare a masarautar da sunan matar SULTANE. Banda wannan rantsatsen rabon......tako ta ina....ta kowacce fuska bata ga ta inda zata iya kutsen shigowa ba.
Har yau har kwanan gobe zaituna bata daina qoqarin binne sunan falaak......ta daina amsa sunan 'YA ga sultane ba......tana d'aga daraja tare da sunan akhnan BAWAI DON TANA SON HAKAN BA.....SAI DON FIR QARFINTA DA WATA SALON QADDARA TAYI.
Taba qofar da akayi shine abinda yaja hankalinta kadan,ta waiwaya tana ajiye ajiyar zuciya,idanunta ya sauka akan falaak.
Kamar ko yaushe,cikin suturar data suturce jikinta ko ina,rungume da daya daga cikin litattafanta na makaranta. Dubanta ta maida ga fuskar falaak din,kullum qara wani cika take da nutsuwa da haske. Tun daga sanda malamin ya shigo rayuwarsu taketa noticing canje canje sosai daga falaak din,saidai akwai wata fargaba kadan qasan zuciyarta dake sake fadada a ranta duk sanda ta kalli yadda falaak din take sake canzawa daga dabi'u zuwa halayenta. Bataso falaak din tayi SON MASO WANI......batason falaak din ita kuma qaddararta da jarrabawarta tazo ta wannan fannin.......
Kacokam ta canza course dinta na makaranta ta koma bangaren addini,wanda ada ba wannan ne zabinta ba.
"Momma.......nannie ca takeson magana dake" Ta fada tana duban idanun momma din. Kai ta gyada mata a hankali tana dauke dubanta daga falaak din,saidai maganan da falaak din ta qara yi ya dakatar da ita daga qoqarin daukan mayafinta da takeyi.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/5, 19:10] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 12*
_________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________
"Momma.......nace idan ba damuwa.....me zai hana a dinga aikawa da sheikh haisam abinci?" Waiwayowa tayi tana duban falaak din.
"Shi yace yana buqata?" Kai ta girgiza a hankali.
"Aah.....hasalima naga me wada da daya daga cikin masu girkin sultane yakai masa shi......sannan lokaci lokaci tare sukanci abinci da sultane din.....kawai dai naga ya dace ne,kuma kaman girmamawa ce a matsayinsa na baqo na muhimmanci a wajenmu" . Idanu ta dan zubawa falaak din,tanaso tace mata aah......to amma tana ganin kamar barinta zai iya zama wata hanya ta alkhairi a nan gaba.
Ta aminta da nutsuwarta,dari bisa dari ba zata aikata abinda bai dace ba.....kaman yadda takeji akan sheikh haisam.......ta jima bataji wata irin nutsuwa me tarin yawa da tasiri akan wani dan adam.ba bayan shi.
"Ba kullum ba falaak.....lokaci lokaci".
"Kamar juma'a juma'a?" Ta tamba morsa safiyya cikin wani irin yanayi na zumudi.
"Ba laifi" Ta amsa mata tana kewayeta ta fice,zuciyarta kuma na sake bata tabbacin abinda take zargi.
Lallai akwai wani al'amarin cikin zuciyar falaak din,saidai bata sani ba,ita kanta ta fahimci hakan ko bata fahimta ba?. Koma meye zata kasance jajiryacciyar uwa da zata saita d'iyarta,ba kuma zata bari tayi wani abu da zai zubda kimarta da martabarta ba dama martabar gidansu gaba daya.
Da sallama cikin nutsuwa ta qarasa tana zama gefan nanny din. Ta amsa mata itama tana duban morsa din.
"Me yasa ana tsaka da magana zaki tafi safiyya?" Nanny ta fada tana duban morsa safiyya. Bata iya cewa komai da ita ba,don batasan me zatace matan ba. Bataso kuma ta buda baki abinda bai kamata ba ya fita a bakinta. Nanny tana da wani irin kima a idanunta......ba kuma zata iya manta qauna da kulawar data bata ba......bama ita din ba.....SAFEENA wanda qaunar data yiwa safeena ce ta gutsirar mata kadan daga cikin ta.
"Banyi tunanin haka daga gareki ba safiyya.......na sanki.....mutum ce ke me rama halasci da halasci.....mutum ce ke me tsananin girmamawa da kyautatawa........amma kuma karon farko kina nema ki manta ki take dukkan alkhairan da mammina tayi miki?......kinsan ciwon da gorin haihuwa yake dashi kuwa?". Ta fadi maganan tana duban morsa safiyya.
Idanunta ta lumshe sannan ta girgiza kanta a nutse,still bata iya cewa komai din ba,wannan ya bawa nanny daman ci gaba da magana.
"Akwai ciwo.....akwai kuma zafi me yawa safiyya....ko bare wanda baki sanshi ba ban zaci zaki iya masa haka ba ballantana matar data dauki jininki FIYE DA KANTA.....Duk duniya ta shaida haka......ta mata riqon da ko kanta akace ta riqe iya abinda zatayi kenan,saidai wasu kusakurai 'yan kadan da basu kai ayi mata hukunci dasu ko ko a qyamaceta saboda su ba......da kuma rufewar idanuwa da soyayya kan iya jawowa kan ko waye ma". Wani abu me tauri morsa safiyya ya hadiye da ya wuce ta maqogoronta da qyar.
Tana hange tana hasashe tana kuma ji a jikinta kamar akwai wani gagarumin yaqi dake tunkarota a gaba.......tana jin kamar akwai wani gagarumin abu da zai iya faruwa a gaba......wanda batajin tana da qwarin gwiwa ko qwanjin tallafarsa da iya nata qarfin.
Sake Imani takeyi,tana kuma sake gasgatawa gami da nutsewa cikin mamaki,da gaske MAMMINA TA ILLATA KOWA A GIDAN......MAMMINA TA YIWA TUNANIN KOWA ILLA......bata ji a jikinta shirunta na shekara da shekaru yana nufin komai daidai yake tafiya cikin masarautar........nuna kishinta tsakanin ita da ita da kwantaccen salon da ba wanda zai fahimta kawai bata tunanin ya GAMSAR da zuciyar zaituna.......ya kuma bata irin nutsuwar da takeso,ko kuma ya cike wannan ramin....wannan zuciyar da kuma wannan rurutacciyar wutar fansar data gani kwnace cikin idanunta tun a ranarta ta farko.
Murmushi ta saki a hankali,cike da wata nutsuwa da zata sanyaka kayi tunanin har zuciyarta abinda ke wakana kenan.
"Ko kadan......ban qyamaceta......ban toxartata ba,ban kuma hukuntata ba......koda karen daya rayu tare da safeena yafi qarfin wulaqanci a gurina.......kawai abu daya na sani......bana bari a wafce abinda yake haqqina ne a gudarmin dashi xuwa muhallin da komai zai iya kasancewa.......bana kuma iya zuba idanu haqqin JINI ya toxarta......bana kuma iya tozarta alqawura mafi girma da aka dauka a lokacin da ruhi ke bankwana da gangar jikin data kasance mafakarsa ta shekara da shekaru,yake kuma bankwana da iskar data kasance mahadinsa tsahon wanzuwarsa a duniya........zaituna zataci gaba da kasancewa UWA ga akhnan kamar yadda ta tsara hakan ya kasance.......amma hakan bawai yana nufin na koma baya bane ya shige na kuma saje da 'yan kallo da wadanda suka saki ragamar sarrafuwar tunaninsu a hannun wani........taci gaba da amfana da wannan damar......taci gaba da zama UWA ga akhnan......saidai kuma akwai guguwar da idan ta taso a nan gaba kadan......ba wasu hannuwa da zasu iya tareta.....na gode sosai da karamcinki nanny....ke din 'yar uwace ta gari ga d'an uwanta.....xan qoqarin yiwa zuciyata saiti amma a sanda ya kamata".
Ta sani....nanny din ta sani,akwai zaurance kalmomi masu harshen damo masu damar gaske cikin maganganun morsa safiyya.......saidai saninsu fahimtarsu ko warwaresu basu take buqata ba....salaama take buqata da wanzajjen zaman lafiya don dorewar shugabancin da mulkin sultane cikin nutsuwa da kwanciyar rai.
♣️★Wannan nazarin......da wannan nutsuwar da take buqata sune suka kwashe mata darare biyu cif ba tare data iya sarrafa tunaninta ta fidda maslaha guda daya a cikinsu game da hukuncin sultane ba.
Tana jin kamar kota ina a daure take.........bata sakeji daga mammina ba......bata kuma sake yo aike daga sashenta zuwa nata ba.....sai takejin komai kamar baya tafiya daidai,saita fara jin kamar ta rasa wani bango da zata jingina dashi......ba jimawa kuma ta fahimci mammina itace qarfinta......itace jigonta......itace qashin bayanta. A hankali ta sake tabbatarwa tana buqatar mammina a kowanne hali......tana buqatar shawararta......ita daya ce tayi imanin zata samar mata da mafita. Da wannan tunanin a wannan daren ta shiga wanka,ta kuma wanke kanta da hair gel dinta ma qamshin strawberry.
Maimakon ta busar dashi da tarin nau'ikan drayers din da take dasu kusan kala goma.....kawai sai taji a daren iska take buqata me kyau data fuskanci ita ke kadawa ta hanyar buda curtains din windows din dakin,iskar kuma dake tashi da wani dadaddan yanayi na qamshin qasa daga farkon damina.
Tanason yanayin,amma kuma tana tsoron damina......tana tsoro ruwan sama ya tabata da yawa,ta sani iska irin wannan tana bata wani irin nishadi,tana kuma rage mata nauyin zuciya sosai.....don haka sai kawai ta shirya kanta cikin wata cotton night gown fara qal,wadda tsananin haskenta yake kashe idanu.
Har qasa take,ta kuma suturce jikinta sosai,hakanan hannunta yakai har gwiwar hannu,saita dauki comb kawai bayan ya fesa turare ta kuma shafe tsadajjiyar fatar nan tata da designer cream dinta na dindindin.
Kyawawan idanunsa ya sake zubewa dukkaninsu saman screen din system din dake gabansa. Wanda ya dauki a qalla awa daya zaune cikin balcony din yana qoqarin zana abun hannun nata exactly kamar yadda ya ganshi. Baya son koda qwarzane daya daya gani a jikinsa ya canza idan aka tashi qerashi,tun daga adon dake jiki da kuma nau'in color dinsa girma da fadinsa yanaso ya kasance daidai da yadda ya ganshi.
Qaro hasken system din yayi,abinda ya sanya ya qara masa yawa a ido,dole ya sanya hannu qasan foldable table din daya dora system din,ya zaro farin glass din da yakanyi using lokaci lokaci idan hasken na'ura ya fara damunsa,ko buqatar sakashi ya tashi a wasu lokuta,musamman da eye glasses din ya kasance na musamman,don yana iya connecting nashi da wayarsa yayi receiving call ba tare da kowa ya gane waya yakeyi ba.
Idanun nasa ya janye yana lumshesu guri daya ganin komai ya zanu kaman yadda yakeso,relaxing bayansa yayi jikin kujerar yana jin yadda gajiya ke saukar masa saboda dadewar da yayi a zaune din. A hankali ya furxar da sassanyan iska daga bakinsa,a lokuta da yawa irin wadannan idan ya gaji,karatun qur'ani ne kawai ke bawa zuciyarsa dama gangar jikinsa wani irin hutu da nutsuwa,don haka a hankali yayi bismillah,cikin muryar nan tasa me zurfi dake kamanceceniya data sheikh afif muhammad taj ya soma karatu da sassauqar murya cikin surar da yafi so cikin suroron qur'ani.
A hankali take takowa zuwa farfajiyar veranda din saman nata,tana sanya hannunta tana warware gashin nata da suke sarqafe da juna. Sautin karatun da taji irinsa kwanaki ya fara sauka cikin kunnuwanta a hankali,saita ci gaba da takawa tana jin yadda karatun ke shigarta a hankali da wani irin yanayi.
Shuru tayi tana ci gaba da wara gashinta cikin wata irin mutuwar jiki data saukar mata daga shigowarta gurin,wadda bata shigo da ita ba,ta tabbatar daga fara sauraron karatun dake mata wani irin mugun dadi ne yanayi ya fara ratsa gabbanta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"What a beautiful sound" Ta furta can qasan ranta da qaramin turancinta da yaren faransanci ya rinjayeshi,saita taka a hankali zuwa saman daya daga cikin kujerun hutawa na alfarma dake wajen,zaman nata kuma a wajen sai ya sake kusanto mata da sautin sosai kusa da ita.
A nutse take sauraron karatun,kamar bata qaunar wani harafi ko daya ya subuce mata. A hankali zuciyarta ke wani irin sanyi,kamar bacewar walqiya ta dinga ji tunanikan dake cunkushe a kanta suna bajewa. Nutsuwa da daidaito yana samuwa cikin dukkanin tunaninta da zuciyarta.
Ta nutsu sosai ta kuma shagalta wajen sauraron sautin karatun tare da mamakin daga inda sautin yake fitowa. Daidai lokacin yakai qarshen surar ya kuma yanke karatun a hankali kamar daukewar ruwan sama,abinda ya sanyata daga kanta da sauri kaman me neman wani abu nata daya bace mata.
A nutse ya ware idanunsa,ya miqe ya zauna sosai jin sautin alamun shigowar saqo ta system din nasa,abinda ya bashi tabbacin duba saqonshi na zanen bracelet din daya tura ga SHAKUR shakur din yayi,sai ya zauna sosai yana maida idanunsa ga system din,saidai kuma idanunsa fadawa sukayi side line na system din nasa dake daukar masa duk wani motsi dake gaban ginin hagu da kuma damansa.
Yanayin motsin daya gani daga gaban veranda din nasa ya sanya jan arrow din ya dora saman camera ta farko ya budashi sosai,take ta bayyana tsaye cikin veranda din nata. Sassalkan gashinta da bai kammala bushewa ba ya kwanta sosai daga gaban goshinta kafadunta zuwa bayanta. Rigar ta zauna a jikinta sosai,saita maidata kamar wata 'yar tsanar roba da aka zauna aka yiwa kyakkyawan qira da zabin halitta me daukan hankali.
Juyawa tayi zuwa baya sannan ta sake juyawa zuwa gaba,abinda ya bashi tabbacin akwai abinda take nema kenan. A hankali ya zame idanunsa daga saman system din ba tare daya motsa komai nasa ba banda idanun ya maidashi kan ainihin veranda din nata direct. Cikin wani nutsuwa idanunsa suka sauka a kanta,sanda ta sanya hannunta tana tattare tulin gashinta tana daureshi tsakiyar kanta,waiko hakan zai bata daman sake jin sautin da qilan zai mata jagorar da zata fahimci daga inda karatun yake fitowa.