Showing 63001 words to 66000 words out of 188421 words

Chapter 22 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

86

cikin cin alwashi. Wannan alwashin nata ne,ba wani daya isa yayi mata shiga hanci da qudundune ta qyaleshi!.....ko wayeshi!.

"Kada ka yarda irin haka ta sake maimaituwa......duk qanqantar zartarwa ina buqatar ta fara wucewa ta gaba na"

"An gama"

"Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani motsi da ba'a amince masa ba?". Shuru tamim yayi,kafin ya girgiza kai a hankali.

"Banga komai ba......saidai wannan kwarjinin nasa daya cika gurin gaba......"

"Tamim.......akwai wani me kwarjini ne sama da nawa?"

"Babu" Ya amsa mata cikin qanqan da murya

"Yaushe idanunka suka fara ganin hakan?"

"Ayimin aikin gafara" Ya fada yana rusunawa,abinda ya haifar da shuru kenan.

"Zaka iya wucewa,ka tuntubi bulama ko akwai wani sabuwar alama ko sabuwar masaniya?". Ta fadi tana jin ranta yayi jagulewar da bazata iya ganin bulama bama.

"An gama Allah ya baki nasara" Ya fada yana miqewa,ya sake kai gaisuwar ban girma sannan ya juya yana fita.

Iska ta fesar,tana son ta riski akhnan don auna gwargwadon matsayar tunaninta,tanason kuma ta samu layin tafisu,don tana son shirya komai na auren akhnan ta fanni biyu. Bangaren akhnan din da almaz da takeso kowanne motsi ya tafi da babban motsin da zai ajiye alamun GIRMA cikin dukiyar aure shigarsa da cikar kamalar da zata masa jagorancin samun KARBUWA a zukatan kowa da kowa.

*MORSA SAFIYYA*

A nutse ta amsa sallamar nanny tana ajiye carbin dake hannunta a gefanta saman lallausan kujerar da take zaune a kai.

Daya daga cikin palukanta na alfarma dake sassanta,wanda ke dauke da wani irin sassanya kuma nutsatstsen yanayi. Iya nutsuwa da tsarin sassanta kawai zai gaya maka adadin tata nutsuwar data wanzu har saman fuskarta,duk da tarin ciwuka da firgici tsoro da take boyewa cikin fitowar kowacce rana zuwa faduwarta,amma qarfin riqonta da addu'a ya sanya nutsuwa takan mamaye dukkan wani fargaba da tsoronta.

Cikin girmamawa ta marabci nanny kaman yadda suka saba. Ta zauna suna maganar su Aeera data samu daga falon farko sun gwagwgwafe ana musu lalle.

"Haka kawai don rigima falaak ta tashi kira da neman a kira mata me jan lalle.......wai sun karanta cewa sunnah ce me qarfi......tanaso lallai tayi koyi da abinda annabi ya umarci mata su dinga yi". Kai nanny ta gyada tana murmushi.

"Sosai sheikh yake da qoqari.......ban taba ganin matashin da nutsuwa tayi masa hijabi ba irin malamin nan nasu,ko yanzu bamu dade da gama maganarshi da babansa ba sultane" Ta fada tana murmushi,murmushin daya sanya morsa itama sakin nata murmushin.

"Komai na falaak ya canza,nutsuwarta ta sake yawa,abubuwa da dama sun sauya tattare da ita,duk wansa ya sameshi a matsayin d'a ko suruki dole yayi alfahari da hakan". Morsa safiyya ta fadi tana sakin murmushi,har cikin zuciyarta tana jin dadin sauyin falaak din. Hakan yana sake tabbatar mata da girman tasirantuwa da mutanen kirki da mutanen arziqi. Daidai nan hadiman morsa safiyya suka gama cika gaban nanny da kayan ciye ciye sannan suka janye.

"Ai dama sun jira......basuyi wannan lallen ba,bata hannuwansu zasuyi,su dake da biki a nan kusa" Nanny ta fada tana murmushi. Maganan ya danja hankalin morsa safiyya,ta daga idaunta tana duban nanny din ba tare data tambaya komai ba.

"Daga qarshe dai akhnan ta fidda miji.......in sha Allah kuma sultane ya sanya daurin aurenta sati na sama". Nanny ta fadi alamun farinciki yana wanzuwa saman fuskarta.

Wani irin duba na mamaki morsa safiyya takebin nanny dashi,maganar tayi mata mugun zuwa a bazata. Idanunsu ya hadu guri daya,abubuwa da yawa nanny din ta fuskanta tattare da morsa din.

"Ta fidda miji?,a yaushe?,a 'yan tsukakkun kwanakin nan?,kuma har ta iya gabatarwa sultane?" Tayi tambayar dukka ga nanny wata irin shakka tana ratsata. Kai nanny ta gyada

"Nima nayi mamakin juyewa da sauyawar ra'ayinta haka cikin qanqanin lokaci......saidai shi Allah ba yadda baya iya sauya al'amuransa a yanayin da yaso,a kuma lokacin da yaso" Shuru morsa safiyya tayi,tana jin wuta tana dauke mata. Kowanne sashe na jikinta yana gaya mata wannan ba ra'ayin biftu bane......ba ra'ayin akhnan bane. Fuskar mammina ta gilma ta cikin idanuwanta,ta lumshe idanuwanta a hankali ba tare data iya furta komai ba.

Cikin kunnenta ake mata busa da kamar kalaman.

"Tayi nasara a kanki" Wani sashen na zuciyarta kuma yana kokawa da hakan......yana kuma qaryata abinda takeji daga qasan ranta.

"Safiyya" Nanny ta kira sunanta tana karantar yanayinta. Bata amsa ba illa bude idanunta da tayi tana duban nanny.

"Na roqeki don Allah......karki zargi komai,kada kisa komai cikin qasan ranki,komai Allah yana shiryashi ne daidai da tsarinsa,ki bita da fatan alkhairi da dukka gudunmawar da zaki iya bata don samun ingantaccen aure me dorewa......sultane kansa ya rufe maganar,yace dukkan wanda zai dawo masa da hannun agogo baya zai iya fuskantar fushi da kuma bacin rai......banason ranki ya baci safiyya.....banason wani abu mara dadi.ya gilma tsakaninki da sultane dalilin kishi". Idanu ta zubawa nanny shuru yana dan ratsa gurin,sai kuma ta saki wani siririn murmushi.

"Kishi?" Morsa safiyya ta maimaita kalmar,saita jinjina kanta a hankali

"Koda nace miki toh.....koda nace miki ba komai to tabbas kema kin sani qarya nakeyi. Na rasa idanuwa irin nawa cikin agadez da zasu dinga ganin kalar abinda ni nake gani......na rasa hankula da zuciyoyi irin nawa SAK!. Akwai tarin duffai daya kamata ace sun yaye.....ban sani ba,ko lokacin yayewarsu ne baiyi ba?,amma a cikin jikina zuciyata da gangar jikina suna bani lokacin yana dab da yi......koda bani da abinda zan yiwa khadeeja......amma akwai kyakkyawar alaqa tsakanina da ubangijina.......akwai sauran fili me yawan gaske da zan gurfana gaban ubangijina,ya kuma saurareni da dukkan rahamarsa da jin qansa,komai tarin buqatu da qorafe qorafe na.......bazan iya hana kowa aikata komai akan akhnan ba......amma kuma nima ban manta ba......addu'a tana sauya qaddara mara kyau izuwa me kyau......addu'a tana sauya tarin qaddarori...." Takai qarshen maganar tana jinjina kanta cike da tarin yaqini da tabbaci da wani irin gamsuwa da takeji har cikin qasan ranta da zuciyarta.

*MAMMINA*

sai data gama shiryawa tsaf cikin wani silk material na hareer me tsadan gaske sannan ta koma saman stool ta zauna tana sake gwada kiran tafisu.

Ajiyar zuciya me sanyi ta sauke sanda tafisun ke mata sallama cikin qasqantar da murya.

"Daga yanzu......zaki tafiya ta qarshe wadda ta haura zagayen agadez.......zaki kasance a kurkusa kuma a duk sanda ba buqaceki".

"Duk yadda kikeso shine abinda zai faru.....duk yadda kikeso kuma haka za'a yishi.....fansar lokacina raina da lafiyata a gareki". Wani qasaitaccen murmushi ta saki,tana jin ta gama samun dukkan wata dama ta duniya......an gama hore mata sarrafa dukkan wani mutum dake kewaye da ita,burika qwaya biyu kadai sune abinda suis rage mata cikarsu.

"Yayi kyau......inaso a gobe ki kasance cikin masarauta.......ina buqatar kowanne shiri ya fara gudana na bayyanar almaz a matsayin surukin masarauta.......sannan ina buqatar kowanne shiri ya zama a tsare,irin shirin da akewa bikin kowacce d'iya ta gata. Inaso a shirya dukiyar aure mai gigita hankali da tunani,inaso a gabatar da gaisuwar aure kalar wadda ba'a taba gani ba......inaso girma da izza su nuna kansu,inaso a siyawa almaz mutunci martaba da kwarjinin da ba'a taba ganinsa tattare da dukkan wanda ya taba zuwa neman auren akhnan ba.......komai inaso ya wanzu bayan tafiyar me martaba umara kafin kuma dawowarshi".

[1/19, 19:45] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 30*

___________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

___________________________

A kansa ta fara ganin mutumin da tana zaune saman kujera shima yana zaune. A kansa ta fara ganin mutumin dake iya duban qwayar idanunta yayi magana da ita a tsanake. A kansa ta fara ganin mutumin da sam batayi masa wani kwarjini ba ko daya......tarin jaran gwanon wadannan abubuwa suke sanya mata wani yanayi na daban a kansa.

Bawai a kansa malamai suka saba baquntar gidan ba,amma kowa yana rayuwa ne a qarqashin ikonta,gwargwadon yadda takeso ya rayu bisa tasarrufinta.

"Ki nema tamim duk inda yake kice ina buqatar ganinsa a yanzu".

"In sha Allahu.....ki huta lafiya,da fatan za'a gafarceni" Yalwa ta fada ta yunqura ta miqe tana ficewa.

Da idanu tabi yalwa din har sanda ta bacewa ganinta. Ta sauke hannayenta data rungume qirjinta dashi tana jan siririn tsaki. Ta tsani yadda takejin wani fargaba da razani suna ratsata......ba halinta bane batason kuma dabi'ar ta soma keta jininta. Tana da tarin abubuwa da takeso ta aiwatar,wadanda suke buqatar JARUMTA da RASHIN TSORO,abubuwa masu yawan da raguwar zuciya ba zata aikatasu ba.

Tsam ta miqe ta isa ga freezer din dake ajiye tana aikinta,ta bude da kanta ta zaro ruwa me sanyi sosai. Tana neman abinda zai sanya kanta ya huce......tana neman abinda zai sanyaya mata tunaninta ko kwanyarta zata dawo aiki da kyau.

Tana dora gorar saman freezer din sanarwar isowar tamim ya marabceta.

"Zan fito yanzu......bulama ya jirayi tafiyarsa tukunna" Ta fada tana komawa mazauninta na dazu.

Alkyabbar data shigo da ita ta sake maidawa,ta kuma maida yanayinta cikin izzarnan da bata yarda ta gushe daga gareta,ta fara saukowa cikin takun isa da nutsuwar da bata jin takai mata har cikin zuciya.

Har qasa yakai gwiwoyinsa kamar yadda ya saba,bai kuma gyara ba har sai data samu guri ta zauna.

"Ya ake cikin cikin qasar can?" Ta tambayeshi a izzance. Zamansa ya gyara sosai kanshi a qasa.

"Na sanya dukkanin wasu matakai da zasu zurfafa bincike,kuma sun dauki adadin wasu kwanaki akan zasu bani cikakken bayanin dana buqata.....kwanakin ba zasu haura goma sha hudu ba......"

"Suyi qoqari kada su dara sama da haka.....ko nawa suke buqata za'a biyasu......bayanai kadai nake buqata,sautin motsin kowanne me rai.....kowanne dan adam da ya shiga cikin da'irar buqatunmu......ban dauke kowa ba,yaro ko babba,mace ko namiji.....shugaba da mabiyi!"

"Yadda kikeso hakan za'ayi Allah ya qara miki nisan kwana" Tamim ya furta da yaren oromo da yakanyi amfani dashi kadai idan suka kebe irin haka......a muhallin daya tabbatar ba wani mahaluqi da zai iya jinsu.

"Wanne sakaci ke shirin faruwa cikin gidannan qarqashin jagorancinka!" Mammina tayi magana a gaba ta biyu cike da kausasawa me yawan gaske.

Qasa yayi sosai da kansa cikin neman afuwa daya sabawa kanshi kafin yakai ga jin wanne kalar laifi gareshi?.

"Akwai dama wani me zartarwa da tsara wani abu cikin gidannan ba tare dana sani ba?.....ba kuma tare dana sahale ba?,har kuma ku mara masa baya?" Tayi tambayar tana jin wani sabon bacin ran yana motsa mata sama dan dazu.

"Tuba muke giwa.....tuba muke uwarmu maganin kuka mu......taron yazo ne a bazata......lokacin da kika fita a gidan,ba damar neman izini ko sanarmiki......sannan duban matsayinsa a gurin sultane daya sahale masa aiwatar da komai,sultane ya shaida mana umarninsa daidai yake da nashi,haka girmamashi daidai yake daka girmamashi.....shi din d'a ne a gurinsa halak malak......"

"Ya isheni haka tamim!" Ta fada tana daga masa hannu.

"Kuskure na farko da zaku fara yi kenan,ku yadda ku daidaita matsayina da nashi......saidai nan gaba kadan zan cire masa wannan girman daka zuciyar dukkan wanda yake ganinsa da girman!" Ta fadi cikin cin alwashi. Wannan alwashin nata ne,ba wani daya isa yayi mata shiga hanci da qudundune ta qyaleshi!.....ko wayeshi!.

"Kada ka yarda irin haka ta sake maimaituwa......duk qanqantar zartarwa ina buqatar ta fara wucewa ta gaba na"

"An gama"

"Akwai wani abu ne daya haifar da rashin aminci ko wani motsi da ba'a amince masa ba?". Shuru tamim yayi,kafin ya girgiza kai a hankali.

"Banga komai ba......saidai wannan kwarjinin nasa daya cika gurin gaba......"

"Tamim.......akwai wani me kwarjini ne sama da nawa?"

"Babu" Ya amsa mata cikin qanqan da murya

"Yaushe idanunka suka fara ganin hakan?"

"Ayimin aikin gafara" Ya fada yana rusunawa,abinda ya haifar da shuru kenan.

"Zaka iya wucewa,ka tuntubi bulama ko akwai wani sabuwar alama ko sabuwar masaniya?". Ta fadi tana jin ranta yayi jagulewar da bazata iya ganin bulama bama.

"An gama Allah ya baki nasara" Ya fada yana miqewa,ya sake kai gaisuwar ban girma sannan ya juya yana fita.

Iska ta fesar,tana son ta riski akhnan don auna gwargwadon matsayar tunaninta,tanason kuma ta samu layin tafisu,don tana son shirya komai na auren akhnan ta fanni biyu. Bangaren akhnan din da almaz da takeso kowanne motsi ya tafi da babban motsin da zai ajiye alamun GIRMA cikin dukiyar aure shigarsa da cikar kamalar da zata masa jagorancin samun KARBUWA a zukatan kowa da kowa.

*MORSA SAFIYYA*

A nutse ta amsa sallamar nanny tana ajiye carbin dake hannunta a gefanta saman lallausan kujerar da take zaune a kai.

Daya daga cikin palukanta na alfarma dake sassanta,wanda ke dauke da wani irin sassanya kuma nutsatstsen yanayi. Iya nutsuwa da tsarin sassanta kawai zai gaya maka adadin tata nutsuwar data wanzu har saman fuskarta,duk da tarin ciwuka da firgici tsoro da take boyewa cikin fitowar kowacce rana zuwa faduwarta,amma qarfin riqonta da addu'a ya sanya nutsuwa takan mamaye dukkan wani fargaba da tsoronta.

Cikin girmamawa ta marabci nanny kaman yadda suka saba. Ta zauna suna maganar su Aeera data samu daga falon farko sun gwagwgwafe ana musu lalle.

"Haka kawai don rigima falaak ta tashi kira da neman a kira mata me jan lalle.......wai sun karanta cewa sunnah ce me qarfi......tanaso lallai tayi koyi da abinda annabi ya umarci mata su dinga yi". Kai nanny ta gyada tana murmushi.

"Sosai sheikh yake da qoqari.......ban taba ganin matashin da nutsuwa tayi masa hijabi ba irin malamin nan nasu,ko yanzu bamu dade da gama maganarshi da babansa ba sultane" Ta fada tana murmushi,murmushin daya sanya morsa itama sakin nata murmushin.

"Komai na falaak ya canza,nutsuwarta ta sake yawa,abubuwa da dama sun sauya tattare da ita,duk wansa ya sameshi a matsayin d'a ko suruki dole yayi alfahari da hakan". Morsa safiyya ta fadi tana sakin murmushi,har cikin zuciyarta tana jin dadin sauyin falaak din. Hakan yana sake tabbatar mata da girman tasirantuwa da mutanen kirki da mutanen arziqi. Daidai nan hadiman morsa safiyya suka gama cika gaban nanny da kayan ciye ciye sannan suka janye.

"Ai dama sun jira......basuyi wannan lallen ba,bata hannuwansu zasuyi,su dake da biki a nan kusa" Nanny ta fada tana murmushi. Maganan ya danja hankalin morsa safiyya,ta daga idaunta tana duban nanny din ba tare data tambaya komai ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Daga qarshe dai akhnan ta fidda miji.......in sha Allah kuma sultane ya sanya daurin aurenta sati na sama". Nanny ta fadi alamun farinciki yana wanzuwa saman fuskarta.

Wani irin duba na mamaki morsa safiyya takebin nanny dashi,maganar tayi mata mugun zuwa a bazata. Idanunsu ya hadu guri daya,abubuwa da yawa nanny din ta fuskanta tattare da morsa din.

"Ta fidda miji?,a yaushe?,a 'yan tsukakkun kwanakin nan?,kuma har ta iya gabatarwa sultane?" Tayi tambayar dukka ga nanny wata irin shakka tana ratsata. Kai nanny ta gyada

"Nima nayi mamakin juyewa da sauyawar ra'ayinta haka cikin qanqanin lokaci......saidai shi Allah ba yadda baya iya sauya al'amuransa a yanayin da yaso,a kuma lokacin da yaso" Shuru morsa safiyya tayi,tana jin wuta tana dauke mata. Kowanne sashe na jikinta yana gaya mata wannan ba ra'ayin biftu bane......ba ra'ayin akhnan bane. Fuskar mammina ta gilma ta cikin idanuwanta,ta lumshe idanuwanta a hankali ba tare data iya furta komai ba.

Cikin kunnenta ake mata busa da kamar kalaman.

"Tayi nasara a kanki" Wani sashen na zuciyarta kuma yana kokawa da hakan......yana kuma qaryata abinda takeji daga qasan ranta.

"Safiyya" Nanny ta kira sunanta tana karantar yanayinta. Bata amsa ba illa bude idanunta da tayi tana duban nanny.

"Na roqeki don Allah......karki zargi komai,kada kisa komai cikin qasan ranki,komai Allah yana shiryashi ne daidai da tsarinsa,ki bita da fatan alkhairi da dukka gudunmawar da zaki iya bata don samun ingantaccen aure me dorewa......sultane kansa ya rufe maganar,yace dukkan wanda zai dawo masa da hannun agogo baya zai iya fuskantar fushi da kuma bacin rai......banason ranki ya baci safiyya.....banason wani abu mara dadi.ya gilma tsakaninki da sultane dalilin kishi". Idanu ta zubawa nanny shuru yana dan ratsa gurin,sai kuma ta saki wani siririn murmushi.

"Kishi?" Morsa safiyya ta maimaita kalmar,saita jinjina kanta a hankali

"Koda nace miki toh.....koda nace miki ba komai to tabbas kema kin sani qarya nakeyi. Na rasa idanuwa irin nawa cikin agadez da zasu dinga ganin kalar abinda ni nake gani......na rasa hankula da zuciyoyi irin nawa SAK!. Akwai tarin duffai daya kamata ace sun yaye.....ban sani ba,ko lokacin yayewarsu ne baiyi ba?,amma a cikin jikina zuciyata da gangar jikina suna bani lokacin yana dab da yi......koda bani da abinda zan yiwa khadeeja......amma akwai kyakkyawar alaqa tsakanina da ubangijina.......akwai sauran fili me yawan gaske da zan gurfana gaban ubangijina,ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login