Showing 90001 words to 93000 words out of 188421 words
kadan ya daga ya kalli maleek din,sannan ya miqa hannu ya karbi towel din,sai maleek ya sakar masa ba tare da yace masa komai na,shima ya karba yana juyawa a nutse ya nufi toilet.
Ajiyar zuciya me nauyin gaske maleek ya saki,ya jinjina kai a nutse ya tsugunna ya kwashe kayan haisam din. Yaga abinda yakeson gani din,wani irin fushi ne kwance cikin idanun haisam,irin fushin da akan samu jikin jinin SARAUTA saboda wata dabi'a ta rashin son raini dake tattare da wannan jinin wanda irinsa ne a jikinsa shi da haisam. Wannan ya sanya sau tari yafi kowa saurin fahimtar haisam.....saboda wasu irin dabi'u da jini kusan irin daya ke zagayawa a jikinsu.
Abinda yake gani a idanun haisam a yanzun me zurfi da girma ne,irin abinda bai taba gani ba a idonsa akan kowa. Ya tabbatar dukka shurun da yayi da qoqarin kaucewa hada ido da kowa yana yine cikin yunqurin controlling kansa fushinsa da kuma bacin ransa. Yayi imanin inda ba tasiri na ilimin zamantakewa da addini a tattare dashi......akhnan din zata gane girman kuskuren data tafka Kai tsaye. Yana YAKANA yana da DAUKE KAI......amma a duk sanda qura takai bango yana da wahalar sarrafuwa yana kuma da wuyar sha'ani. A mganganunta yasan ta tabo abu mafi girman da yafi tsanar a taba masa ADDININSA,dole yasan fushinsa yana iya fin haka ma. Yana kammale masa kayan ya taka a nutse yana ficewa a dakin don ya bashi daman shiryawa da daukan adadin lokutan da yaga sunyi masa.
Bai jima ba sosai ya fito ya fara shiryawa,yana shiryawan yana ambaton sunan Allah don neman agaji da samun sassaucin dacin da yakeji tun daga harshensa zuwa cikin maqogoronsa. Yanata qoqarin manta maganganunta,amma koda ya cillasu baya saisun dawo masa cikin kansa.
"Subhanallah" Ya fadi a hankali lokacin daya kammala fesa wannan mayen turaren nasa ya ajiye bottle din saman madubi. Tafin hannunsa ya sanya ya shafa qirjinsa har sau uku yana furta addu'ar sassauta fushi da bacin rai. Baisan me yake samunsa ba a kwanakin nan.....baisan me yasa a kanta fushinsa yake yawa ba.....baisan me yasa kome tayi yake bata ransa fiye da yadda ya kamata yaji ba.
Yayi iyakacin bakin qoqarinsa na kaucewa kowanne shirgi nata,don ba dominta ya shigo AGADEZ ba,ba zamanta yakeyi ba.....bata kuma cikin lissafin mutanen da yake hangen bincikensa zai iya wucewa ta kansu,amma kuma baisan me ya sanya lamuranta ke sake shiga cikin rayuwarsa ba.
Duk yadda yakai ga yakicewa da dojewa amma sultane yana sake jawoshi da sakashi cikin al'amuranta......banda girmamawa ga sultane sam baiga hadinsa da karbar sadakinta da kuma zamowa waliyyinta har ya daura mata aure ba.
Komawa yayi ya zauna a hankali gefan sofa bed din yana sake maimaita addu'ar. A hankali a hankali yaji yanayinsa yana daidaituwa,fushin kuma yana raguwa,sai ya miqe a hankali ya soma takawa bayan ya sanya flip flops dinsa masu tashin gaske,don kawai fitowar ta zama dole saboda maleek da omar da yasan ba gidan zasu kwana ba.
"Nifa na kasa jurewa......batasan gonar da take shiga bane?......inda a Jimma ne tana zaton shekara daya ma ta isheta ta samu daman tsaiwa kawai a gabansa......iya tsaiwa kawai obbo maleek,bare harta samu daman fadin maganganu masu zafi?" Abdii dake balbalin fada ya fadi yana nuna yatsarsa ga maleek dake zaune hankali kwance yana shan coffee dinsa,da alama kuma ya tattara dukka hankalinsa akan abdii din daketa zirya yana fada.
Murmushi omar ya saki yana ajiye remote din hannunsa daya dauka don kashe Ac din parlor din
"Ina hakaitota ni kaina cikin masarautar jimma........rashin sani yafi dare duhu,inda cikin jimma ta fadi wadannan maganganun data zama nama".
"Da ba zata sake rashin kunya a duniya ba.....da tasan ba'a tabawa oromian prinsii dinsu.....amma nan gaba sai......". Cikin tarin nutsuwarnan tashi ya saki gyaran murya sannna ya zagayo yana zaban kujerar zama.
Tuni abdii ya kama kanshi,kai kace ba shine yaketa surfa bala'in nan ba. A hankali ya zauna saman kujerar a lokaci guda kuma yana aikewa abdii wani kallo daya sanya abdii din diriricewa,lokaci guda kuma ya miqe yahau hadowa haisam coffee ba kuma don ya buqaci hakan ba,sai don nauyin da idanu da kuma kallon da haisam din ya jefeshi dashi ya sanyashi qaramar rudewa.
Parlor din ya dauki shuru,cikinsu ba wanda ya sake cewa komai,har zuwa abdii ya kammala hada coffee din ya kawo gaban haisam din yana cewa.
"Obbo....."
"Zauna nan" Haisam ya fadi kai tsaye cikin salon umarni. Bai musa ba ya zauna din,saidai ya kasa hada idanu da Haisam din kai tsaye.
"Morning flight evening flight or night flight......wanne ka zaba don komawa Ethiopia kuma jimma?". Idanu abdii ya zaro yana qoqarin duban haisam da yakai cup din coffee bakinsa a nutse
"Obbo......ni bance zan koma gida ba,idan nabar niger obbo tare dakai ne".
"Kace mana abdii?"
"Lakki(a'ah)" Abdii ya fada yana girgiza kai.
"Meye alaqarka da dabbar da ba ita ka shigo farauta ba daji?,koda zata yita bibiyarka a baya?" Ya jefa masa tambayar yana ajiye mug din hannunsa.
"Babu obbo"
"Ergamni keenya maali?(meye mission dinmu?)"
"Obbo......zaqulo mutumin daya kashe ajani,sannan mu kaishi gaban hukumar binciken sirri qasar Ethiopia kuma ta hukuntashi" Kai ya jinjina a nutse yana lumshe idanunsa gami da budesu.
"Daga sanda kaji a ranka ka fara sauka daga wannan ra'ayin,to daga ranar ka siyi tikeetii(ticket)na komawa Ethiopia....banzo AGADEZ don susan waye ni ba......na yarda na zama mutum mafi qasqanci a idanun kowa muddin hakan zai zama tsani zuwa ga cikar burinmu......"
"Kamar ba komai zaka iya dauka ba kaima daga gurin yarinyar ba.....kamar tana jin kanta tana da Kyau......maza suna layin mutuwar sonta tana wahalar dasu....."
"Omari,Dhaabadhaa(stop it)" Yatsunsa ya saka yayi zipping bakinsa alamun yayi shuru,sai ya kalli maleek yana daukan nasa mug din ya zauna gaba kadan dasu yana fadin.
"buna keessan xumurree,nuti ni deemna(idan ka gama shan coffee din sai mu tafi)".
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kamar kowacce magana ta qare,amma can qasa maleek ya zare mug dinsa daga bakinsa yana duban haisam.
"Rayuwarta na kewaye da hatsari haisam.....daidai ne ka kauda kai?" Maleek din bai zaci samun amsa daga gurinsa da wuri ba,amma kafin ya maida cup dinsa bakinsa sai yaji yana fadin.
"Ani lubbuu namoota koo fi warra koo baraaruuf qofa dhufe(nazo nan ne kawai don ceton rayuwar jama'ata data iyayena)......haqqin kareta ko daukar nauyinta ba'a wuyana yake ba" Ya qarasa fada yana dire mug din gami da daukar remote ya fara canza tasha.
"But she's so strong fa.... Omari ka kula kuwa?" Ya kira sunan omar din yana kanne masa ido daya.
"Indeed......" Omar ya fada yana qoqarin qara wani abu,saidai haisam.ya kira sunansa da sound dinnan da dukkaninsu sunsan idan yayi irin wannan kiran me yake nufi. Hannayensa zube a aljihun trouser din jikinsa,still idanunsa kan TV da suke program kai tsaye da sheikh Dr zaakir naikh.
*MAMMINA*
Kai kawo kawai takeyi tsakanin falukan nata guda uku tana duban agoguna manya guda biyu dake tsaye a kusurwoyin parlor din. Har cikin jikinta tana jin yadda jininta ke tafasa......tana kuma iya jin yadda kaf dokokin haisam din sukayi mata wani irin dabaibaiyi,dabaibayin daya sake tabbatar mata cewa YA SANYA KOWACCE DOKA CE SABODA ITA. iya tuna wannan kawai idan tayi yana sanya wani zare daga tsakiyar cikinta kadawa,wanda bata sani ba,hanji ne.....zuciya ce ko wani abu na daban dake neman sanya mata tsananin tsoro,yake kuma tuna mata da ZEENATU. Zeenatun data kasance haifaffiyar Ethiopia data shafe rayuwa me tsaho a can,zeenatun da ko sunanta mammina batason tunawa ballantana ta tuna WACECE ITA?. Zeenatun da har yau ta zama silar kasa yarda aminci da sakin jiki cikin dukkan rayuwa daqiqa da awannin da zasu shude mata a rayuwa.
Idan har ya sanya wadannan dokokin da suka tabata har haka,arashi ne ko kuma YAQINI?. Idan ba yaqini bane KAKKAIFAN ZATO ne?.
A irin wannan daren,akwai tarin sirrika da suka kasance nata kebantattun dake gudana gabanin fitowar kowanne haske da zai bayyanar da dakushewar duhun dare,amma a wannan daren komai yana neman tsaiwa cak!. Komai ya kasa gudana yadda ya saba saboda wadannan banzayen dokokin nasa?.
Duk da yalwa ta fado mata parlor din da wata irin ba zata amma hakan bai kada hankalinta sosai ba,saboda abinda takeji cikin jini da jikinta,firgici dake neman ratsa naman jikinta yakai ga jinin dake harbawa zuwa zuciyarta tana jin yafi kowanne firgici girma da nauyi.
"Kiyimin aikin gafara......bulama ya qaraso.....saidai a yanayin dana ganshi ina me tabbatar miki ba lafiya.......kamar!"
"Kika barshi a waje bayan kinsan tulin dokar dake yawo cikin gidan?". Mammina ta fadi tana goye hannayenta a baya gami da sassauta bugun zuciyarta da kuma qoqarin hana halittar TSORO wanzuwa a qirjinta.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/27, 19:22] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 44*
Ko kammala rufe bakinta mammina batayi ba yalwa ta miqe da hanzari don yiwa bulama iso.
Sanye cikin kalar suturar daya daya cikin hadiman sassanta wanda zai wahala ga mara zuzzurfan nazari ya zaci cewa d'a namiji ne cikin yafen da ya lullube ilahirin jikinsa dashi.
Hannu yasa ya yaye lullubin,take fuskar bulama data qara wani baqi da maiqo ta bayyana,saiya sulale ya zube a gabanta yana tallafe da hannayensa da yakejinsu kamar ba'a jikinsa ba.
Kasa magana mammina tayi saboda yadda qirjinta ke bugawa,tabi hannun nasa da kallo wanda duk motsi guda daya da zaiyi dashi yana jin azabar can tsakar kansa.
"Ki yafemin......ki rufan asiri,ina neman sassauci ki janye aikin da kika doramin........bazan iya ci gaba da karbar ragamar aikin nan ba" Ya fada da wani matsanancin tsoro da mamaki da har yau ya kasa barinsa.
"Ka bude baki kayimin cikakken bayani......bani da lokacin bata lokaci!" Mammina ta fada cikin tsawar dake cakude da fargaba da tarin tunani iri daban daban.
Sosai yayi qasa da kansa,yana jin asarar dukkan wata garabasa,qarin matsayi da alfanu da zai samu baya kammaluwar aikin wuna sulalewa,saidai sulalewar aikin daga hannunsa yafi masa sauqi akan ci gaba da yinsa gami da fuskantar abinda ke tunkaroshi. Abinda ya gani ya kuma hanga tattare dashi......abinda ya gani ya hanga cikin idanunsa wani irin yanayi ne daya sanya tsoro ya tsarga masa yake shirin tsaga zuciyarsa gida biyu.
"Duk da tarin qwarewata ta shekara da shekaru........duk da tarin nasarorin dana samu cikin ayyukan dana kwashe shekaru ina miki ba tare da samun matsala ko tangarda koda sau daya ba.......a yau ina me bakin haquri na janye daga wannan aikin......don ya riga ya ganni,ya kuma bani saqo da gargadi me girman gas......." Ya fara kaiwa qarshen maganar yana mata nuni da hannunsa.
"Ina fata sunana baiyi kuskuren fitowa daga bakinka ba?!" Ta tambayi bulama cikin wata sabuwar tsawar tana jin wani yamutsi yana haduwa tsakanin qirjinta da kwanyarta ba tare daya damu da bi ta lafiyarsa ko bin ba'asi ba na mugun nadin da hannunsa yasha dake alamta kyakkyawar karaya ce ya samu.
"Koda za'a sanya kaina gabas a yanka bazab iya aikata hakan ba......saidai akwai abinda ke nuna yuwuwar yasan wani wanda yayi.kama da wanda ya aikeni zuwa gurinsa". A wannan karon hannun kujera mammina ta samu ta zauna tana jin saman kanta ya mata nauyi kaman an jibga mata wani abu,saidai duk da haka wannan bai iya kawar da izzar da takeji ba.
★Dukkan wani shirin aure da uwa kanyi akan d'iyarta na wajibi da wanda bana wajibi ba mammina din yinsa takeyi. Ga duk wanda ya kalleta a sannan kai tsaye zai fahimci da gaske shirin aurar da d'iyar gata takeyi.
Kudi kawai take zubdawa,ta kowanne fannin don ganin komai ya tafi daidai da yadda ake gudanarwa......sannna sama da abinda ya zama anayi a al'ada. Tana maimaitawa a gaban kowa cewa,aure ne na d'iyar da ba'a taba me gatanta ba a fadin qasar agadez dama niger gaba daya,dole komai yasha banbam dana sauran yaran da duniya take ganin su din qurewa ne matuqa gurin gata da girma da martaba da kuma isa.
Wani irin gida ta zuba kudi me girma da daukan hankali ta siyawa almaz wanda ta mallaka komai a hannunsa a madadin nasa ne......sa'annan ta jibge kayan alfarma da dukkan nau'in abinda tasan ya kasance mafi soyuwa a zuciyar akhnan cikin gidan da take da yaqinin zasu burge akhnan din zasu kuma iya zama mataki na farko da almaz zai fara samun wani fili koda qarami ne cikin zuciyarta da har za'a cimma gaci a qurarren lokacin da takeso ya zama SANADI na tabbatuwar ragowar mafarkinta daya rage.
Komai yana tafiya mata daidai ta fannin shirin biki......saidai ta kowacce kusurwa tana jin wani rashin TSARO a tattare da ita. Ta kowanne bangare tana iya riskar yadda SABBIN DOKOKIN cikin gidan suke sake tabbatuwa a kanta kowacce safiya.
Kamar yadda ba wata daqiqa da zatazo ta shude bata tunasar da ita sunan HAISAM ba,da tarin yaqini da fatan ta maida aikin ragamar kula da duk wani motsi nasa hannun qwararre kuma amiñtaccen da bata da irinsa wato TAMIM.
Wani irin mamaki ne yake kasheta a kowanne second a duk sa'in data tuna BULAMA ya gaza aiwatar da aikinsa?. A duk tarin shekarun daya kwashe yana hidima a gareta......tarin ayyuka masu hatsari da muhimmanci da yasha aiwatar mata,ba wani yanayi da yayi kama da alamu na rashin NASARA sai yanzu a kansa?......akan malamin da baisan komai ba sai alqalami da tawwada?.....malamin xa take da yaqinin koda cikakken sunansa zai wahala ya iya rubutashi?.
"WAYE SHI?" Tambayar da take kwashe darare tana yiwa kanta ita kenan,ba kuma don saboda tana qirqirar tambayar a karan kanta ba.....aah......tana ji kamar ana tunkudo mata tambayar ne daga wani sashe daban na zuciyarta.
Cikin kwanaki qalilan ta kammala komai,ta kuma sake jajircewa da raba hankalinta gami da zurfafa nazarinta akan komai. Duk da sadarwa da yawa ta yanke mata cikin gidan.....duk da saqonni da yawa sun dakata da shigo mata,amma ta zama calm tana manage da ragowar hanyoyin da suka rage mata a bude,tare da tabbatarwa kanta zata WARGAZA kowacce sabuwar doka da taci karo da muradinta da kuma cikar burikanta.
★★
Dukka tafukan hannayenta guda biyu ta shafa saman fuskarta bakinta na fidda sautin
"Alhamdulillah" Ta sauke hannun nata zuwa qirjinta sannan ta masa ma'ajiya saman cinyarta.
Shuru tayi tana fidda numfashi a hankali,tana mamakin yadda nutsuwa ke cika ruhinta da zuciyarta bayan shafe tsahon kwanakin da tayi tana addu'a akan lamarin akhnan.
Daga randa nanay ta fita a sassanta bayan sanar mata da kwanakin da suka rage na auren akhnan,daga wannan ranar bata qara kwanciya tayi bacci a rabin daren da a baya take kwanciya tayi bacci ba bayan ta gama ibadunta.
Tun asali ita din tana cikin jerin sahun mutanen da ba wani dare dake kufce musu,koda cikin jinya ko lalura take,zata daddafa ta tashi,wannan kuma tayi imani yana daya daga cikin makamai na nasararta a masarautar AGADEZ. Tayi imanin yana daya daga cikin garkuwarta daya hana zaituna ta cimmata.......yana kuma cikin manyan hijbai data tabbatar Allah ne kadai ya sanyashi tsakaninta da mammina.
Ta yarda dari bisa dari sallar dare garkuwarta ne.....rigakafinta.....kuma itace qashin bayan daidaituwar dukkan al'amuranta
(Kina da matsala?,kina da damuwa?,me zai hana ki gwada lazumtar sallar dare?,zakisha mamaki......kina da dare.....kina da lokacin da ubangiji ke saukowa da kansa yana tambayar ina me buqata na biya masa,ina me tambaya na amsa masa.....me ya hadaki da malaman tsubbu da bokaye?).