Showing 30001 words to 33000 words out of 188421 words

Chapter 11 - LU'ULU'U COMPLETE

Unknown   

27 Aug 2026

100

Taci gaba da irga takun akhnan,gami da hasashen saukarta daga stairs din zuwa qasa. Bata bude idanunta ba,bata kuma dakata da lissafa takun ba har sai da ta lissafa taku talatin da biyar cif......abinda yayi daidai da isarta dab da sassan nanny sannan ta juyo da sassarfa ta mara mata baya,so samu ta hada da kiran sunanta.......amma abune da zai zama wani irin cikin birnin iko da mulkinta,don haka sassarfar kawai ta hada da ita,tana da tabbacin zata cimmata a daidai inda lissafinta ya tsaya.

Kusan duk inda zata gifta duk da darene kauce mata hanya suke,sannan su sadda kansu cikin girmamawa da ganin yadda giwar sultane din ke tafiya da salon sassarfa.

Sai da idanunta suka fara hangota sannan ta fara kiran sunanta,kiran daya isa kunnen akhnan din,ya kuma sanyata tsaiwa cak duk kuwa da cewa so samu ta wuce ba tare data tsaya sauraren kira mammina din ba.

Dab da zata isketa nanny ke fitowa daga nata sassan,da alama ziyarar data saba fita a daidai wannan lokacin zataje,saita dakata tana duban akhnan,kafin ta maida dubanta ga mammina dake qarasowa gurin d wani irin sauri daya fita daga al'adar tafiyarta.

Kafin mammina ta iso tuni nanny ta sallami dukkan hadiman dake tare da ita,ta kuma sanyasu su tsaida wucewar kowa ta gurin har sai sun bar gurin,ta maida dubanta ga akhnan. Ita takeso ta fara tambaya.....amma ta tabbatar a yanayinta ba zatace komai da ita ba koda zasu shekara a gurin,don haka ta maida dubanta ga mammina.

"Lafiya zaituna d'iyarki take?". Kai mammina ta juya cike da zallae alhini tana duban nanny. A hankali ta sake sanya qafarta gaba tana barin gurin,b wanda ya sake tsaidata tsakaninsu sai kallo da suka bita dashi,kafin mammina ta tattara idanunta akan nanny

"Rigimar biftu na neman zautani nanny......ban sani ba ko ke zaki iya fahimtar da ita?" Kai nanny ta girgiza tana duban akhnan data fara nesa kadan dasu kafin ta sake kallon mammina.

"Duk wani abu da kika kasa fahimtar da biftu bana tunanin akwai wanda zai iya......bana tsammanin akwai me ita sarrafata".

" So take lallai lallai ta azamin nema mata mijin auren daya dace da ita.....ki duba wannan girman al'amarin nanny,indai ba baqinjini takeson qaramin ba?" Mammina ta fada da wata kwantacciyar murya dake nuna karaya sosai cikin sautinta.

Murmushi nanny ta saki tana dafa kafadar mammina.

"Indai don wannan ne.....banga wani aibu a ciki ba,idan ana lissafin wanda yafi kowa sanin ciwo da zafin haihuwar biftu idan aka cire safeena kece ta daya......hakan da tayi ya nuna ita din d'iyace 'yar gaske da tasan girman halacci......maza kiyi hakan indai shine zai daidaita tsakaninki da d'iyarki". Idanu mammina ta zubawa nanny,a saman fuskarta shakka kokwanto da rauni suna yawo,can qasan zuciyarta kuma wani shimfidadden farinciki ne zallah gami da taya kanta da kanta murnar samuwa da kuma tabbatuwar nasararta.

Nanny ta fahimci kamar maganan bata gama zaunawa mammina ba,don haka ta motsa tana yiwa shema'u hadimarta alama da hannu ta qaraso.

"Kibu biftu,ki shaida mata ta dawo zuwa ga sassan mammina.....injini".

" Zan sameta nanny......ta dauki zafi,rabu da ita" Mammina ta fadi tana soma takawa tana bin gwadaben da akhnan ta wucesun.

Da kallo nanny ta bisu,murmushi yana fita a fuskarta. Bata taba ganin qauna irin ta mammina da akhnan nan ba....qaunar da zata iya rantsewa koda tsakanin wasu 'ya'yan da iyayensu na asali da suka haifesu babu ita.

Batasan adadin abubuwan data saqawa zuciyarta ba zata aiwatar daga daren yau zuwa gobe ba. Ta riga ta zartarwa kanta a goben zata bar agadez zuwa Niamey,kuma ba zata sake lamuncewa kowa ya ganta ba. Koda sultane dinne,koda ita mammina din ce.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Dafa kafadarta da taji anyi shi ya tsaidata. Tasan mutum daya ce tak ta isa tayi hakan a gareta,don haka tana waiwayo ta fada jikinta ta rungumeta tana sakin kuka.

"La....la....la,wanne irin abun kunya kike shirin bari?,hawayen sarauniyar agadez haka a fili a araha?" Mammina ta fada tana goge mata fuskarta dake kwance saman kafadarta. Wani qwarin gwiwa taji yana hauro mata kamar yadda ta saba ji.......tabbas mammina itace qwarin gwiwarta. Duk wani pattern da take rayuwa akai tsarin mammina ne. Ta nuna darajar matsayin da Allah ya bata,ta nuna mata girman da take dashi......ta karantar da ita cewa ITA TA MUSAMMAN CE.....tana da banbanci da sauran yara......tana da banbanci da sauran duk wani halitta dake rayuwa cikin masarautar. Wannan motsa mata izzar tata da tayi ya sanya ta hadiye kukanta,ta kuma bi mammina wadda ke riqe da hannunta tana takawa da ita zuwa wani kebantaccen guri dake da tarin kima a gurin mammina dama duk mutumin da zata gana dashi a gurin.

Hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana nazartar gurin cike da tarin mamaki. Yana da kusan dukkan map na gidan amma bai taba lura da wanzuwar gurin ba.

A yanzun da yake nazartar gurin da idanunsa da zaka dauka a rufe suke.....yana iya hangen yadda gurin zai iya linking nasa da wancan kebantaccen dakin ajiyar da ya zama guri na biyu da yake buri da muradin shiga ya duba wasu abubuwa da jikinsa ya jima yana bashi akwai bayanan da zai iya buqata cikin gurin.

Lokutan da agogo ke bashi yakeso yayi amfani dasu a tsakanin lokutan,ya tabbatar yana cikin lokutan da dan bibiyarsa ba lallai ya sake kasancewa dashi ba har zuwa awa daya a gaba. Zai iya ci gaba da kasancewa dashi daga awa dayar har zuwa awannin biyun da zai samu tabbacin ya kwanta......daga nan kuma zai dora aikinsa ne bayan ya tabbatar asubahi tayi,wadannan sune hasashen jadawalin lokutan daya tabbatar zaiyi amfani dasu gurin bibiyarsa. Bazai dawo nan kusa ba saboda yayi motsin da ya fuskanci yaja hankalinsa har ya miqe ya maida qofarsa ya rufe A ZATONSA baisan cewa TARKO bane kawai haisam din ya D'ANA MASA don tabbatar da cewa sun fara aiki da umarninta?.

Motsin sawayen da yaji ya sanyashi sake nutsuwa da kyau......muryarta kuma ta zama abu na farko daya fara shiga kunnensa.

"Kin taba ganin inda uwa ta iya qyale yarinyarta tasha wahala?.....kin taba ganin inda d'iya tayi fushi da uwarta?". Ya haddace muryarta da kyau,sautinta yana da banbamci da sauran sautukan da yake ji cikin masarautar,duk da yadda yake qure qoqarinta gurin daidaita harshenta dana kowa su saje a ma'auni guda daya......ma'aunin da sai kana da qwaqwalwa da fikira irin tasa zaka iya sansani banbance banbance a tsakanin abinda aka gauraya guri daya.

Ta ganshi a ranar nan,a yanzun kuma bazai zama lokacin daya dace ta sake ganinsa ba,don bai shirya ajiye zargi ko kokwanto a kansa a zuciyar kowa ba,don haka ya taka a hankali ya shiga tsakanin bishiyar dogayen yaro masu tsahon gaske guda biyu dake gurin.

Wayarsa ya zaro a hankali jin alamun shigowar saqo,ya rage hasken sosai yana duba saqon daya shigo masa. Bobbo muhammad dawud ne,ya sani akwai tattaunawa da zasuyi,duk da ta chart ne ta kebantacciyar manhajar da sukanyi musayar tattaunawa,amma bai dauka zai nemeshi haka da wuri ba. Tsaiwarsa ya gyara yana maida hankalinsa kan wayarsa,ya soma maida messages din bobbo din,duk da ba hakan yaso ba,yaso yana daki a nutse,amma idan yace zaya jira kaucewar kowa baisan yawan tsahon lokacin da zai dauka ba.

"Zauna a nan ki saurareni da kyau" Mammina ta fada tanawa akhnan nuni da daya daga cikin kujerun dake ajiye a gurin.

A nutse ta qarasa ta zauna,sannan mammina din ta taka itama zuwa kujerar dake daura da ita.

Dukkanin hannuwan akhnan ta kama ta aza saman cinyarta,ta sanya idanunta sosai cikin nata.

"Inaso ki saurareni sosai da kunnen basira......inaso ki bani duk wani hankali naki da kike dashi" Kai ta gyada a hankali,batajin akwai wani sauran abu da mammina zata buqata daga gareta ta kasa yi mata shi.

zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*

*Safiya musa abdullahi*

*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261

KO

08187255862

*Al'ummar qasar nijer ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช*

*2349166221261*

*Safiya musa abdullahi*

*NITA*

*CFA 500*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*

09166221261

*SHAIDAR BIYA*

09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA๐Ÿ‘‘*

*HUGUMANKU CE*โœ๐Ÿฝ

[1/7, 19:49] +234 903 555 3736: ๐Ÿ’Ž *L U'U L U'U*

*_(The diamond)_*๐Ÿ’Ž

*H U G U M A*

*BOOK 02///PAGE 16*

___________________________

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX

__________________________

"Kisa a ranki ni din tamkar mahaifiya nake a gurinki ba UWA ba.......ba wani tsanani da zaizo da zan iya juya miki baya.....to amma dole wataran kaza take taka d'anta badon bata sonshi ba.....aah,saidai kawai ta bashi wata tarbiyya.....idan nace a komai na rayuwarki zanci gaba da zaqewa.....zanci gaba da kasancewa a gaba gaba hakan zai iya zame mana matsala......" Takai qarshen maganar tana sauke numfashi.

"Duk wank hukunci naki da zabi naki ina tare dashi biftu......duk wani kalan abu da zai saka rayuwarki a nishadi ina tare dashi biftu.......zakiyi aure kamar yadda sultane yake da buqata.....zaki aure amma zaki auri mijin da zai zamana qarqashin juyawarki umarninki da kuma haninki......zaki auri mijin da kece zaki shirya ki kuma tsara kalar rayuwar da kike buri da mafarki......mijin da bai isa ya sakaki ko ya hanaki ba,zai kasance qarqashin sarrafawarki". Idanu akhnan ta lumshe tana sake budesu lokaci guda hade da wani irin lafiyayyen murmushi.

Lallai ba shakka duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi.......duk wanda ya girmeka ya girmeka har abada. Abadan duk duniya bata da wani masoyi daya d'ara mammina.....a wannan gabar har cikin tsakiyar zuciyarta da ruhinta tana jin cewa koda sultane SAI YA JIRA a soyayyar mammina a gareta......ta sake gasgata cewa idan ba MAMMINA babu ita AKHNAN.....tabbas ba zata taba kai labari ba idan ba mammina na gefanta ba.

To wai me yasa tun baya ita batayi irin wannan tunanin ba?......namijin da zai zama miji a idanun sultane kawai amma cikakken HOTO a idanunta da bazai hanata aiwatar da komai da ta tsara cikin kundin rayuwarta ba?.

"Kina jina?" Muryar mammina ta dawo da ita daga tunanin data fara nisan zango a cikinsa. Kai ta gyada mata tana sauke blue eyes dinta da rashin wadataccen haske ya sake sanyawa ya zama wani me qyalli da daukan idanu.

Sama ta daga kanta mammina din,saboda digar yayyafi da taji cikin jikinta gami da haskawar walqiya,alamu ke nuna ruwan saman farko zai sauka kenan da yardar me duka yau a qasar agadez. Idanunta ta mayar kan akhnan,wadda yayyafin ruwan bai sanyata ta qifta idonta daga kan mammina ba.

"Ki nemo mijin ki kawo......zan tsaya don tabbatuwar dukka wadannan sharud......"

"Mammina manaaaa......" Ta furta da wani sassanyan yanayinta daya fusgi hankalinsa daga inda yake tsaye,inda hankalinsa yayi nisa sa maganganunsu ya tura dukka hankalinsa da nutsuwarsa zuwa ga bobbo muhammad dawud.

Kyawawan idanunsa ya daga yana kallon gabanshi,duk da bai iya ganin komai sai alamunsu a mazaunin dake gaba kadan dashi. Tafin hannunsa ya sanya yana goge yayyafin ruwan daya sauka saman screen din wayar nasa yana kuma qoqarin hanashi ci gaba da sarrafa wayar saboda yadda yake dan qara yawa.

Baisan me yasa sautin nata ya fusgi hankalinsa ba.......sai ya sanya tafin hannun nasa yana yiwa wayar rumfa da xummar rage saukan ruwan saman screen din,saidai a wannan karon kunnuwansa sun gaza kaucewa daga tsintar maganganunsu.

"Da gaske nake mammina......na baki wuqa da nama......ki kawo duk wanda kikaga ya miki.......fatana na rayu cikin 'yanci,irin 'yancin da kowacce mace maras igiyar aure a kanta zata rayu dashi......ban taba sha'awar soyayya ko tarayya da kowanne namiji ba.....don har yanzu bana zaton an halicci irin ajina daya dace da MARTABATA".

Har cikin jinin dake harbawa a jikinsa yakejin zancansu bai shefeshi ba,burinsa su matsa shima ya wuce ciki kafin ruwan yakai ga bata masa waya ko katse muhimmiyar maganar da yakeyi da bobbo......amma a wannan gurbin baisan sanda yaja wani siririn tsaki ba.

Haka kawai yakejin wani bacin rai kadan kadan yana tasiri a ransa. Banda girman kan dake dawainiya da ita yana tunanin akwai tasirin jahilci. Wacce irin uwar goyo ya rabauta da ita wadda ke goyon bayan duk wani shirin shirme nata maras ma'ana?.

"Zai kasance ni na zaboshi......amma ki koyawa kanki nunawa duniya cewa shine zabinki......idan hakan bata faru ba,bana tunanin zan sake zama cikin matsalolinki irin wannan har abada". Kai ta girgiza sanda ruwan ya fara damunta saboda yanayin saukarsa daya qara yawa.

"Komai zai kasance kamar yadda kika buqata mammina ta......na gode da kasancewarki cikin rayuwata" Ta furta sanda suka miqe a tare,ta kuma matsa tana rungume mammina din sosai da tarin soyayyarta danqare cikin zuciyarta.

A hankali mammina din ta zareta daga jikinta tana sakar mata murmushi.

"Nan da kwana uku kawai zan gabatar miki da duk wanda nake ganin zaibi umarninki ne kawai".

" Ba buqatar hakan......koda zamu qare zamanmu ban ganshi ba bana buqata mammina.......buqatata daya na amintar da sultane.....na fita daga fushinsa"

"Idan har kikayi hakan kowa ma zai iya fahimtar komai" Amsar data bawa akhnan kenan ta soma takawa don barin gurin duba da yadda ruwan yayi qarfi lokaci daya.

Idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda bishiyar ta gaza rufe saukar ruwan duka cikin kansa,duk da ta tare wani kaso da bai taka kara ya karya ba.

Maganganunsu na qarshe ne suka maimaita kansu cikin kansa,yayin da zuciyarsa ta yunquro da wani qaqqarfan yunquri tana gaya masa.

"Not your business haisam......not your business". Kansa ya gyada a hankali,har cikin zuciyarsa yana jin hakane,zuciyarsa gasiya ta gaya masa,wani sashen kuma na zuciyar tasa tana cike da wani irin yaqini da zargi me qarfi akan MAMMINA.

Yanajin tana sake cika dukkann wasu sharuddan zargi da zato me qarfin gaske a tattare da ita......yana jin a duniya a yanzu itace bakin zaren ZATONSU ta farko.......a jikinsa yake jin akwai wani abu binne.

Sultane ne kawai ya gilma cikin tunaninsa da idanunsa......yana ji da dukkanin yaqininsa akwai wani abu da ba daidai ba......amma kuma yana gayawa zuciyarsa da kansa cewa ba huruminsa bane......BINCIKE YA KAWOSHU AGADEZ.....aiki yazo yi kawai ya koma,aikin da yake sanya rai yake kuma jin cewa kwanakinsa qalilan suka rage. Ya rage baccinsa......ya hana kansa jin dadi walwala da tafiye tafiyen da yakanyi don kawai sake gane girman buwayar Allah saboda aikin kadai. Ya kasa samun nutsuwa na tsahon shekaru....baccinsa yakan yanke idan ya tuna koda kowanne lokaci rayuwar MOTII zata iya fuskantar barazana.

Barazanar dake gabansa.......aikin dake gabansa yafi gaban wannan abun da yake gani a yanzu.....bayajin kuma yana da sauran abunyi akai.....abu daya ne yasa hankalinsa yake kaiwa gurin,jikinsa yana bashi matar itace zata zame musu tsani na samun wani abu ko yaya ne game da AJANI AHMED.

Sauka ruwan yake da wani irin yanayi daya tayar da qamshin qasa. Sassanyar iska dake kadawa da walqiya me tsananin haske tsakanin zubar ruwan da iskar. A haka yake takawa cikin cikakkiyar nutsuwarsa,kamar ba ruwan sama ke sauka saman kanshi ba. Abu daya kawai yayi.......zare kewayayyar hular dake saman kansa,ya riqeta a hannunsa,wannan ya bawa ruwan damar sake kwantar da sumar dake kansa me yawa da kuma sulbi.

Ruwan farko kenan da ake sanya ran ya kasance tafe da tarin albarka,yaci gaba da takawa yana furta ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN da kyawawan jajayen labbansa masu sulbi.

Yanayin ya tuna masa ne da jimma........tana da wani irin dadi a yanayin damina irin haka. Kyawawan shukoki da tsirrai,guraren da zaka kebe kanka cikin nutsuwa wanda yake sanyashi nishadi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login