Showing 111001 words to 114000 words out of 188421 words
zamana cikin HASARARRU?.
Qafarsa ya buga,yana jin wani qarfin zuciyar tunkarar duk wani abu da zai masa silar rasata ko nesantata dashi komai girmansa......ballantana almaz din da ta kowacce hanya yana da qarfin ikon ruguzashi ya kuma ruguza komai cikin sauqi.
"Giwa na kiranka shugaba" Yaji an furta daga bayansa cikin girmamawa. Waiwayowa yayi ya zuba idanu akan bawan. Bawan da akayi domin ya zama photocopy dinsa,bawan daya dauka ya mallaka masa irin sunansa.
"Yaushe ta buqaci ganina?".
"Tace yanzun nan,don tana da baqin da take sallama". Siririn tsaki yaja,yana jin kamar yabi shawarar da daya sashen na zuciyarsa suke bashi,saidai yaka tuna da wani abu wanda shi kadai ne yake masa shamaki.
Kewaye yaron yayi ya fara takawa ta gabansa,shi kuma ya rufa masa baya cikin matuqar biyayya.
*MAMMINA*
Idan kaga yadda take hidima cikin jama'arta,gami da kai kawo a cikinsu,ci gaba da rabon kyautututtuka masu nauyi da girman gaske ga duk wanda Allah ya tsaga yana da rabo. Ta bude qofa sosai ga.masu son ganinta da masu son gaisheta saboda yanayin farincikin da take ciki,tana so kuma ta sake jaddadawa kowa,kowa kuma ya shaida cewa da gasken gaske tana auren diyar da tafiso duk duniya ne sama da kowaaka.
Daga yanayin giftawar yalwa ta tabbatar da isowar tamim,don haka ta miqe tana bada umarnin dakatar da ganinta har sai zuwa gobe.
A yau akwai abubuwa da yawa da takeso ta dasa harsashinsu,harsashin da zai zama wani tushe kuma sanadin da zai qarasa tarwatsa rayuwar dukkan wani mutum daya kasance ahali ko tsatson diory hamani......zai qarasa sanya giyar takaici baqinciki da bacin rai cikin ruhi da gangar jikin duk wani ahalin safeena......giyar bacin ran da zata yita bugar da kowannensu har izuwa numfashinsa na qarshe.
Yana tsaye saman qafafunsa,yana kuma goye da hannuwansa a qirjinsa,saidai takun shigowarta ya sanyashi daidaita nutsuwa da yanayinsa zuwa yanayin da suka saba.
"Zauna" Tace da tamim bayan ta zauna. Zama yayi kaman yadda ta buqata,saidai kuma zuciyarsa tana gaya masa a irin wannan lokacin kamata yayi ace darajarsa ya d'aga daga wadda yake kai yanzu zuwa mataki na gaba.....matakin daya tabbatar banda tayi masa shigo shigo ba zurfi da qudundune shine yanzu akai,ba wancan tsintaccen magen ba almaz.
"Ina fatan gidan ango ya kammala ko?" A nutse tamim ya jinjina kansa,yana jin wani abu me ciwo yana tsaye masa a wuya
"An kammala komai"
"Yayi kyau.....inajin dadin aikinka tamim qwarai da gaske......a bisa al'ada yau zataje ta kwana a gidan,gobe da asuba ya rakota da kanshi.....to amma nasan abune me wahalan gaske ta yarda da hakan,don haka na yanke shawarar fara qulla kusanci a tsakaninsu....." Saita dan dakata tana sanin murmushin dake nuna zallar farinciki.
"Zai bita Niamey a satin nan kamar yadda ta tsara zata tafi,duk da har yanzu ban yarda zai iya karbarmin ragowar kamfanin sahel ba......amma tafiyarsu tare nada tarin alfanu masu yawan gaske......a yau zan tilasta mata ganawa dashi koda ba zata shiga gidanta ta kwana ba......akwai maganganun da nakeso yayi da ita,na sanya an rubucesu a killace....duka hirar da zaiyi da ita yau a killace take a rubuce,banason ya dara daga abinda na tsara. Yana da kwanya fiye da yadda kake tunani,tabbas nasan zai haddaceta kamar yadda nakeso,kaje masa da ita,da yammaci ina buqatar a rakoshi cikin ayari.......ya zamana cikin shigar alfarma ta gasken gaske......ka tunasar dashi,kada ya nuna zalama ko rawar kai.....kada ya nuna mata damuwa ko kulawa me yawa.......a jininta ta tsani wadannan dabi'un.....amma a halittarta tanason namijin dake dasu". Mammina takai qarshe tana bashi takardar dake ajiye a gefe tuntuni.
"An gama....cikar umarninki shine muradinmu" Ya fada da zallar girmamawa yana hade hannuwansa guri guda. Murmushin farinciki ta saki tana gyada kai.
"Saura kadan na mallaka maka shugabancin gidannan tamim......yadda kayimin rana da alfanu masu yawan gaske,dole kaima ka amfana daga falalata me fadin gaske" Ta fadi da gasken gaske saboda jin dadin yadda ko sau daya bai taba jawo mata asara faduwa ko musanta umarninta ba.
Kai ya jinjina mata yana jaddada godiyarsa,saidai kuma abinda ke kaikawo a zuciyarsa yasha bambam da tazara me tarin yawa da abinda ke bayyane a zahiri.
Iska ta zuqa me yawa tana fesar da ita,har yanzu murmushi yaqi gushewa daga kan fuskarta,saita kira yalwa da dama ba nisa tayi ba.
"Ki daukomin alkyabbata,zani gurin akhnan".
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"An gama" Ta amsa mata tana fita da sassarfa.
D'ai d'ai take takawa tana kallon gidan,da yadda ko ina dokar haisam ke aiki duk da yana kwance baida lafiya. A baya qona mata rai abun yake,amma a yanzun saita saki dariya hankali kwance. Tana wassafa yadda aikinta zai sauka a kansa hankali kwance bayan ta ga tabbatuwar dinkewar alaqa me danqo tsakanin akhnan da almaz. Taci alwashi ta kumayi rantsuwa tabbas saita sanyashi ya kwashe kayansa cikin dare yabar agadez,don ko guduwar tasa bazaya iya bari kowa ya sani ba saboda munin abinda zata sanyashi ya aikata. Da wannan hasashen ta isa sassan akhnan din hankali kwance cikin tarin girmamawa da dukkan hadiman sassan suka zube suna bata.
*AKHNAN*
Kwanaki ukun nan da suka shude gaba daya bata da aiki sai kwanciya,bata da wani aiki sai kebe kanta ita kadai. Bata qaunar wata hayaniya,bata son doguwar magana ko dogon surutu. Kusan salla ce kadai ke tayar da ita,sai wani lokaci da takan bude wani sashe na balcony dinta. Shima ba kasafai ba,don bata son ganin kowa kamar yadda batason kowa ya ganta. An shaida mata saqon morsa safiyya harma da Nannie dakeson ganinta,amma tayi biris da aiken kowa,kamar yadda taqi yarda kowa ya ganta. A yadda take jinta ma gaba daya ko mammina ke son ganinta saidai tayi haquri,kawai tana qoqarin digesting din komai ne,tana qoqarin haqurqurtar da zuciyarta nema tayi accepting wai an daura mata aure......wai ta zama matar aure....mafarkin da take hangoshi da nisan gaske gashi ya cimmata a lokaci qalilan.
Tayi juyi tayi juyi,tayi tsaki har batasan adadinsa ba. Yanzun meye ribar wannan abun da sultane ya tursasa tayi?. Wannan aure da suka dage a kansa meye ne ribarsa?. Ita bata hangen komai a cikinsa sai wata irin rayuwa maras 'yanci,sai wata zallar takura da kashe dukkan burin rayuwa da yake cikin ruhi da gangar jiki. Saita maida idanunta ta lumshe tana qoqarin tsara yadda zata maida rayuwarta daidai kaman yadda take a baya.
Kai tsaye taji an murza qofar dakin nata a hankali,bata wani damu da bude idanun nata ba,saboda tasan koma waye da zai taks dokarta,ya tsallake mata doka to bazai wuce MAMMINA ba.
Bata motsa ba har zuwa sanda mammina ke takowa inda take a kwance. Can qasar zuciyarta tana mamaki,tasan da gaske taji motsinta,ta kuma ji shigowarta,amma bata motsa da nufin tarbarta ba kaman yadda ta saba?. Wani shu'umin murmushi ta saki kawai tana danne zuciyarta.
"Saura qiris ki rasa wannan gatan......saura qiris ki rasa wannan izzar.....saura kadan ki fahimci ke wulaqantacciya ce abar qyama,zaki biya dukkan wani farashi da safeena ta tafi bata biyashi ba". Ta fadi qasan ranta a fili kuma tana zama daidai qafafunta.
"Biftu?" Mammina ta kirata a tausashe. Kamar ba zata amsa ba,sai kuma ta tuna MAMMINA ce fa.....mammina dinta,wadda ke tsaiwa kaida fata wajen farincikinta,sai ta motsa labbanta a hankali.
"Na'am" Ta amsa a hankali.
"Tashi biftu" Shuru ya ratsa kadan,sannan a hankali ta juya tana miqewa,ta zauna sosai hadi da sanya hannunta tana tattare sassalkar gashinta da ya ware ribbon din yayi nasa gurin daban.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer ๐ณ๐ช*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA๐*
*HUGUMANKU CE*โ๐ฝ
[2/2, 22:22] +234 903 768 6798: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 55*
Sallamar nanay dinne ta sanyashi bude idanunsa a hankali yana amsa sallamar gami da bude idanunshi. A nutse nanay ta miqawa saamee wayar sannan ta yunqura a hankali tana fadin
"Ki sameni a parlor idan kin gama". Kanta a qasa tana jin takun ficewar nanay din,sai ta koma ta zauna sosai saman carpet tana jin qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.
Muryar nanay yake jiran sake ji,sai yaji muryar saamee ta maye gurbinta da sallamar nan tata cikin yanayinta me sanyi.
Numfashi ya aje a hankali yana amsa mata sallamar,husky voice dinnan nashi ya ratsata ya shiga kunnenta yana motsa wani abu dake boye can saqon zuciyarta.
"akkam jirta obbo(barka da warhaka,kana lafiya yaaya)" Ta fadi a hankali tana ganin kamar xai iya jiyo bugun zuciyarta daga nan inda take zaune.
"Ani gaarii dha,akkamitti?(lafiya nake,kefa?) Ya tambayeta tana qoqarin kwatanta kyautatawa a gareta kamar yadda yasan tana qoqarin yin hakan ga nanay dinsa.
"Alhamdulillah" Ta amsa duk wani sauran magana kuma yana dauke mata gami da tsaya mata a maqogaronta. Wani irin kwarjini yake mata koda a bayan idanunta ne,ta jima da sanin shi din wani irin namiji ne daban da sai zallar sa'a zata sanya mace ta samu damar mallakarsa.
"Makaranta fa?" Yayi qoqarin tambaya don kada ta dauka ya wofantar da qoqarinta.
"Komai lafiya alhamdulillah" Ta furta a hankali,har qasan ranta tana son tambayarsa sai yaushe zai shigo jimma?....don tayi wata muguwar kewarsa,amma takejin ba zata iya ba.
"Ma sha Allah,Allah ya taimaka,nanay fa?"
"Zan kai mata yanzun" Ta fadi a sanyaye,tana sanya rai ne hirarsu ta zarta haka,tana sanya ran maganarsu ta wuce haka,amma sai gashi da wurwuri ya gajarta maganar.
A nutse ta miqawa Nanay sannan ta taka tana fita a parlor din. Nanay ta bita da kallo sanda take sanya wayar a kunnenta.
"Barka da warhaka nanay"
"Barka kade muhammad.....fatan ka yini cikin aminci"
"Alhamdulillah nanay.....komai da kowa lafiya?"
"Lafiya Muhammad,inata tunaninka omar yace wani aikin daban ka shiga,shi ya sanya ba'a samunka" Idanunsa ya lumshe a hankali yana gyada kai,cikin ransa yana jin dadin yadda omar ya boyewa nanay rashin lafiyarsa.
"Na fito alhamdulillah nanay.....ko kin samu sunan abokiyar zaman Obbolettii n ki?" Kai ta gyada a hankali.
"Eh muhammad.....na samu amma da qyar,na rubuta don kada na manta,duk da nasan mantuw tayi kadan ta goge sunan azzalumin mutum irinta a kaina....."
"Meye sunan nanay?" Ya tambaya cikin tattarawa Nanay hankalinsa.
"ZEENATU" Wuta ce ta daukewa haisam na wasu daqiqu,kafin a hankali wani murmushi me cike da madaukakin mamaki ya mamayeshi. Zeenatu a Ethiopia......zaituna a agadez? Ya tambayi kansa da kansa yana kuma sake jinjina kansa.
"Matar ajani da ake zargi ZEENATU.......matar data fidda Obbolettii (sister) dinki daga gidanta ZEENATU.....ba wani alaqa tsakanin mutanen nan biyu?". Dif wuta ta daukewa nanay,tunaninta yana yin zurfi da kuma nisa.
" Ajani ya taba aure shima!.....na shekara daya muhammad kamar yadda safeenata tayi!!" Nanay ta fuusgi kalaman cikin wani irin rudani.
"Good nanay......zan iya samun wani abu game da rayuwar gidan ajani.....kaman ta hannun uwargidansa?"
"Ta rasu muhammad.....sati daya da suka wuce.....amma,bari na kira safuura" Nanay ta fadi tana yanke kiran. Ko ina na jikinta kyarma yakeyi,tanaji jikinta kamar taga Obbolettii dinta har guda biyu,tana jin kamar an gano ind sisters dinta suke,tanajin kamar an gano bakin zaren ne.
Kai kawai haisam yake juyawa a hankali,maimakon bacin rai ya mamayi fuskar nan tasa ma'abociyar Kwarjini,kawai sai wani qaramin murmushi ne yake fita a fuskarsa. Ganin komai yake tarwai.....kowanne lissafi nasa da yake sarqewa a baya a yanzun ya fara zuwa masa da warwara......yan hangen komai kamar an saka rariya ana taceshi.
Hujja daya tak yake nema da zata sake bashi tabbaci itace MATAR AJANI......hujja daya tak da yakejin a yanzu ya shirya shiga kowanne sashe kowanne lungu na masarautar agadez don ya fiddo ta. Idan ya tabbata INA MAKASHIN?.....waye wanda ya aikata kisan da shima yayi batan dabo?. Ta yaya lokaci bayan lokaci suke iya aiwatar da bazaranarsu ga motii aba jifar?,ta yaya?,su waye rassansu?,su waye mataimakansu?.
Yatsunsa kawai yake murzawa a hankali yana sake baje sabon lissafi. Kebantaccen dakin ajiyar mammina.....shi kadai ne abinda ke masa yawo a ransa da kansa....kebantaccen dakin da jikinsa ya bashi tabbacin lallai akwai BOYAYYUN SIRRIKA. TAMIM har guda biyu dake da alhakin kula dashi,da masu jin yaren oromo da yake da lissafin sunayensu yanzu haka fes dama fuskokinsu gaba daya!..
Turqashi......ya zuwa yanzu nasan me karatu yana tunanin KOMAI YAZO QARSHE......QARYA TA GAMA QAREWA......GASKIYA KUMA TA GAMA BAYYANA......SAIDAI NACE KUXO MUJE
MAJI
MA GANI
Maleek ne ya shigo a nutse bayansa daya daga cikin hadiman haisam ne. Dauke da wani kyakkyawan royal tray da aka jera masa qananun bowls masu kyau.
Idanunsa ya zare ya maida kan maleek,shima maleek din shi yake kalla.
"Ina fata wannan aikin ya kammalu?" Tashi haisam din yayi ya zauna sosai yana duban maleek sanda hadimin ya ajiye abinda ke hannunsa yana fita.
"Yadai kusa......inaso na shiga masarauta,yau zanyi kwana uku ko biyu kuma kafin na fito.....ka kira likitan nan yazo ya ciremin wannan abun" Ya fadi yana daga hannunsa dake dauke da Canular.
Kai maleek ya girgiza yana zama saman sofa.
"Amma kasan akwai ragowan drip da zaka sake sha?"
"Ya isheni haka maleek,ina buqatar kammala wani abu dole.....inaso na gama komai qasa da sati daya". Ya amsa masa yana yarfar da hannun nasa,don har yadan fara tasawa saboda zaman allurar na kwanaki a jikinsa.
"Okay " Ya fadi yana lalubar wayarsa don kiran hadiminsa da suke agadez din tare.
*TAMIM*
A nutse ya miqawa almaz alkyabbar data zama sutura ta qarshe da zai sanya a jikinsa,bayan tarin kayan ado da qawar daya fara sanyawa a jikinsa na tsadaddar suturar ALHARIR.
Shi kansa tamim din a yau yana hangen wani irin kyau da biyayya da suturar tayi a jikin almaz din,tamkar dai dama ya saba da ire iren wadannan tufafin a jikinsa. Duk da haka ba abinda ya rage qudirinsa a zuciyarsa,ba abinda ya rage kaifin abinda yakeji a zuciyarsa.....hakanan ba abinda ya sauya daga aikata abinda yayi niyyar aikatawar.
A nutse almaz ya taka cikin wani salon izza da yaji ya saukar masa,ya matsa gaban tamfatsetsen madubin dake ajiye a wani bangare na daban na dakin.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Duban kansa yakeyi cikin madubin,yana jin wani izza tana shigarsa. Tsahon rayuwarsa bai taba ganin inda yayi kyau har haka ba,koda sau daya kuwa,duk da cewa yana rayuwa cikin sutura me kyau da kuma cima me kyau,amma ba sutura irin wannan ba....ba tufafi irin wannan ba me cike da nuna qarfin izzar wanda ya sanyasu. Sosai yakeji kansa yana sake shiga charge,abinda ya qara fadada nishadin da yakeji kenan,don tun daga daren jiya ya baje dukkan kayan mayensa da aka dakatar dashi daga sha,yasha me isarsa,ya kuma dora da wani da safen nan bayan wadancan sun sakeshi. Yana jin wani banbanci da wadannan kayan da wadanda ya saba sha. Wadannan din masu taada ne sosai data sanya aka tanadar masa kwali kwali kawai don jin dadinsa,ta kuma yi masa alqawari daman,ta kuma cika,abinda ya sake saka masa nutsuwa da bin dukkan sharudda da qa'idojinta. Basa sakashi yayi mankas ya manta da abinda yakeyi,amma suna fiddashi daga duniyarsa,suna kuma fitar dashi daga ainihin duniyar da yake rayuwa a cikin ta,suna sakashi ya jishi daidai yake da kowa,yana kuma daidai da tarar kowa da komai.
Waiwayowa yayi yana murmushi yana duba tamim,abinda ya sanya tamim dauke kansa daga mummunan kallon da yakewa almaz din,kallon dake cike da hassada qyashi kishi da baqinciki.
"Wai nine almaz a haka?.....nine na mallaki matar aure d'iya mafi girman daraja a yankin africa......gida irin wanda nake mafarki da rayuwa cikin izza mulki da qasaita.......amma kasan meye tamim?" Yayi tambayar yana duban fuskarsa yana kuma takowa zuwa gaban tamim din. Qoqarin gaske tamim yayi wajen maye murmushi saman fuskarsa.
"Na rasa wanne dalili ne ya sanya uwargijiyarka ta zaboni a cikin tarin matasan qasar Ethiopia.....a baya nayi tunanin don tana mahaifiyata ne,amma a yanzu tunanina ya gagara cafko komai" Almaz yayi maganar da tarin mamakin dake ransa daya bayyana cikin muryarsa.
Murmushi tamim ya saki,yana takawa a hankali gaban wani