Showing 57001 words to 60000 words out of 188421 words
ba tare data ankare da haka ba?.......sai a yau ta sake yadda ta kuma tabbatar da gaske ne sultane YA D'IYANTAR DASHI......da gaske ne da sultane yace YA MAIDASHI D'ANSA da gaske yana nufin abinda ya fada din......iya yau kawai ta tabbatar mata da haka.
Amma kuma tana raye?.....ta yaya zata bari haka ta faru?.....ta yaya zata bari haka ta kasance?. Ta kasa haifawa sultane MAGAJI kamar yadda ta hana kowacce d'iya mace haifa masa magaji sai magajiya qwalli biyu da take jinsu kamar wutar dake cin naman jikinta a kowacce safiya idan ta kallesu. BAI KAMATA TAYI SAKACIN DA WANI ZAI HAURO ta saman kanta ba......ya rusa duk wani matsayi kusanci da martaba da tayi shekaru tana tattalinsu ba.....bai kamata ta bari wani ya fado tsakiyar wannan kakkauren zaren data debi shekaru tana saqashi ba ya tsinkashi. Waninma da har yanxu xuciya da gangar jikinta ke alamta mata DANGER a duk wani kallo da zata aza idanunta a kanshi ba.
"Bappi......bayan dukka wanzuwar su kawu mammani dake raye?". Akhnan ta samu kanta da furta tambayar tana duban sultane da wani irin sanyin mamaki daya daketa.
Kai tsaye yake duban idanunta shima,sannan ya jinjina kai.
"Bakisan MATSAYIN D'A a wasu guraben ya haura na DAN UWA BA?......Bakisan kuma matsayin D'A wajen yin waliccin auren qanwarsa ya zarta na kawunnanta ba?" Maganar tasa ta fito da wani nauyi me yawa daya sanyata maida kanta qasa kawai. Banda tauri da kafiya gami da tsaiwa da zuciyarta ke dashi.......banda tattalinnan da takewa GIRMA da IZZARTA ba abinda zai hanata fashewa da kuka a yanzun nan.
"Amma ranka ya dade......Allah ya taimakeka.......bai kamata kafin ka yanke rana da komai ka tsaya gana da yaron ba?......kasan wayeshi da asalinsa?" Tayi maganar da sanyin murya da sanyin zuciya,sanyin daya sanya haisam tattarasu dukka ya aza saman ma'auni daya.
"Ba buqatar hakan......indai ta iya gabatarmin dashi......ta sani ya dace da dukka wani tsarinta ne......ku shirya komai,zata zama matar aure nan da kwanaki goma masu zuwa.....kaji abinda na fada muhammad?" Ya maida dubansa da tambayarsa kan haisam da yayi kaman baya wajen.
"Indai wannan din umarni ne daga gareka zan cikashi in sha Allah"
"Umarni ne haisam.....umarni ne muhammad" Ya furta cikin nuna girman umarnin nasa da gasken gaske.
"Ranka ya dade......ba kuskure kuwa?,.......ya kamata a duba.....muna neman alfarma,aure ba wasa bane.....diyarka mafi daraja zaka miqa......."
"Zaituna ya isa haka......na rufe wannan babin har abada,na rufe matsalan akhnan akan aure har abada......bana son wani ko wata su sake tayar da ita......yin hakan zai iya sawa mutum ko waye ya fusakanci mummunan hukunci daga wajena kai tsaye kuma"
Runtse idanunta tayi tana jin kamar jiri na shirin kayar da ita daga zaunen da take. Ta gaji da zama a gurin,tanaso ta shaqi wata iskar daban bayan wannan,tana jin kamar wannan iskar ta gurbace da yawa,don haka ta miqe cikin girmamawa.
"Na gode bappi......" Ta iya hada kalmomin da qyar
"Madalla" Ya amsa mata a taqaice yana kauda idonsa daga dubanta,wani abu yana cakar zuciyarsa.
"Tafiyar zata yuwu?" Sultane ya sake tambayarsa,tambayar data aza masa wani tarin nauyi ta kuma sake jan hankalin mammina cike da mamakim wacce tafiya sultane din zaiyi wadda ita bata da labarinta?.
Tafiya da sultane wani abune da zaya bata tsarin aikinsa gaba daya......dukkan wani plan nasa na kammal aikinsa cikin wata daya zuwa wata daya da rabi yana jin zai iya samun naqasu ko koma baya. Amma kuma ta yaya zai fito ya gayawa sultane haka kanshi tsaye?.
"Na fahimceka muhammad......kada ka damu,zamu wuce da babban limamina......zan iya barin kulawar masarauta a hannunka?,sati biyu kacal da jagorancin wazeer hamza?". Wani nauyin ya sakeji sultane ya aza masa,amana komai qanqantarta tana masa nauyin gaske,baya qaunar dukkan wata amana da za'a bashi ace ya riqeta,idan kuwa har aka bashin yana qoqarin cikata da dukkan iyawarsa......da duk wani qarfi nasa daidai da yadda yasan yana da abun fada gaban Allah. To amma a yanzun idan yace zai riqe wannan amanar......yayi imani a jininsa yana jin SARAUTARSA zata iya motsawa......zata iya bayyana kanta da kanta daga lungun da yaje ya ajeta......zata danne matsayin da yaketa qoqarin daidaita kansa a yanzu......zata iya murqushe siffarsa ta MALAM ZALLAH ayanzun ta fito da siffar da har yabar agadez bazai yarda a sanshi a cikin ta ba wato SARAUTA.
To amma bai kamata ya wofantar da komai da sultane yazo masa dashi ba,don haka ya motsa kadan.
"Zanyi iya abinda dama da iko suka bani,bani da alaqa da mulki ko sarauta irin naku.....bansan ya komai zai tafi ba" Maganarsa ta harba wani abu saman zuciyar mammina daya tilasta murmushi fita saman fuskarta. DAMA ce wannan din da idan tayi amfani da ita da kyau zata zame mata silar samun abubuwa masu yawan gaske.
"Na yarda dakai,na kuma aminta dakai,nasan zakayi iyakacin iyawarka da dukka qoqarinka.....Allah yayi maka albarka,ya sakawa uwayen da suka kawoka duniya da alkhairi....."
"Ameen" Ya amsa yana lumshen idanunsa,addu'a da ya yiwa motii da nanay yana jin sun biyashi a komai.
Abinda ya kawota ya kammala,ta samu kuma sama da abinda take buqatar samu,don haka ta miqe tsam cikin girmamawa.
"Ina neman izinin zuwa babban asibiti......zan duba maras lafiyanmu da hari ya ritsa dashi a jiya,da sauran majinyata dake asibitin" Sirrintaccen murmushi ne ya kubuce daga can qasan zuciyar haisam
"Good job maher" Ya furta can qasan ransa. Shi ya buqaci maher da ya buqaci ganinta.....kuma kafin zuwanta an gama tsara yadda komai zai kasance. Yana buqatar fitarta daga masarautar koda na awa daya ne.....wannan space din yake buqata don isa ga abun hannun nan.
[1/15, 20:08] +234 903 555 3736: ๐ *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*๐
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 28*
Murmushi kadan sultane yayi,duk da cewa baya cikin yanayin. Wani kyakkyawan dabi'arsa da haisam yayi noticing shine,yana da son farantawa iyalinsa da sauraren ra'ayinsu,dabi'ar da tayi kamanceceniya sosai data motii dinsa. Qoqarin shiga sahun mazan da manzan Allah yace sune mafi alkhairi a duniya...wato mazan da suka kasance mafi alkhairi ga iyalansu,wadanda suka samu shaida me kyau game da iyalansu kenan.
Dabi'un mammina da yawa suna burge SULTANE.....cikin su harda yadda ta zama me sakakken hannu da nuna damuwa ga mutanenta tsananin damuwa. Morsa safiyya hakan take itama,saidai nata da banbanci,tana duba abinda ya cancanta a yiwa hakanne,wanda bai cancanta ba tana dauke idanunta daga kai. Ba komai take bari a bayyana ba na alkhairinta.....sabanin mammina da takan bayyana motsinta na alkhairi komai qanqantarsa,takance tana yin hakanne saboda sauran masu sukuni suyi koyi da ita,su taimaki wanda baidashi....wanda ya gaza dame nema,hakan kuma sai sultane yaji shima hujja ce.
"Allah ya bashi lafiya shida sauran majinyata,masarauta zata ganshi in sha Allah".
"Giwa na godiya" Ta amsa cikin tsananin ladabi sannna ta juya tana takawa a nutse ta fice.
*HAISAM*
Jikinsa yaji yana mutuwa a hankali sanda yake baro sassan SULTANE. Akwai mintuna ashirin kafin lokacin sallar azahar. Sosai yaji gilmawar mutum daga bayansa,gilmawar da baka isa ka gane an wuce din ba idan ba irin mindset dinsa kake dashi ba,saidai shi yaga inuwar,yaga kuma wucewar ta inuwar gabansa,saidai yanayi zubi siffa da tsarin wanda yake kyautata zaton ya wuce din bai masa kama da suffa da zubin bulama ba........sai ya dauko qididdigar jikkunan TAMIM guda biyu. A tamim qarami lissafinsa ya tsaya,yadan maida tunaninsa baya kadan akansa kafin ya samu guri ya ajiye nazari a kansa zuwa lokacin da zai zama free,don yanzu akwai abinda yakejin yafi masa komai muhimmanci da ya aiwatar dashi.
Daga saba'in xuwa saba'in da biyar yaji ya sake matsar da matakin mammina. Ta shirya komai kuma ya faru kaman yadda taso shine abinda zuciyarsa ke faffasa masa shi. Tafi kowa sanin halin sultane,tafi kowa kuma karantarsa.....idan ranshi ya baci akan abu baya doguwar magana a kansa......tayi nasara,saidai tata nasarar shi ta zame masa wani.mabudin aikinsa.
A yau dinnan yakeso ya fara dasa masa tarakuna har guda biyu......don haka ya wuce Kai tsaye zuwa ga sassansa yana sanar da yaron gidansa qasa da mintina ashirin yana buqatar dukkan wasu masu alhakin kula da tsaron gidan dama wanda ke kula da kowanne sashe na gidan,hadimi da hadima,babba ko yaro,mace ko namiji a babban filin dake ajiye a bayan ginin masarautar daya tabbatar zai daukesu gaba daya,ya kuma aikewa da omari saqon karta kwana da dukkan tsarikan da yake ganin zai amfani dasu.
Dukkanin nazarinta da nutsuwarta ta hada guri daya,tana kuma sake zurfafa tunaninta gaba daya akan komai daya faru tsakanin jiya da yau din.
Tana jin wani iri da qyashin yadda sultane ke shirin miqa ragamar komai a hannunsa,a hankali kaman yana raunana power din kowa.......kamar yana son fara juya ra'ayin sultane da fara sarrafa tunanin sultane din. Kamar ya fara aiki da wani abu me qarfi da batasan meye ba wajen sarrafa sultane din da tunaninsa gaba daya.
Riqon qwarya wa fada da kuma damqa waliccin auren akhnan a hannunsa?. Wani siririn murmushi ya qwace mata,ta gyada kanta a hankali. Tana jin kamar lokaci ne wannan na samun cikakkiyar damar da zata sake wani abun fashewar,abun fashewar da take kyautata yaqini da zaton zai iya tashi harda shi,ya kuma zame masa mummunan bala'in da zaiyita binsa har qarshen rayuwarsa.
Can qasan zuciyarta kuma zafi takeji,zafi takeji sosai na yadda sultane ya yanke hukuncin damqa ragamar masarauta da auren akhnan a hannunsa. Da farko ta tashi a yau da zummar ta jashi a jiki don sarrafashi kaman yadda take sarrafa kusan duk wani me fada aji cikin masarautar.......to amma tana kokwanton yiwuwar hakan,don wani abu take hange tattare dashi da yasha banbam da wanda take gani gurin sauran mutane. Juyawa tunaninta yayi ga Maher......ta jima tana ganin matashin cikin gidan,tana kuma da haske a kansa kan baida matsala da kowa. Irinsa take so,irinsa ne kuma kewaye da ita,wadanda sukan iya sadaukar da rayukansu da rayuwarsu saboda ita,ba shakka ya cancanci ta duba wani gurbi ko muhalli kusa da ita tayi masa mazauni.
*HAISAM*
Cikin qanqanin lokaci ya kammale dukkan wasu masu tsaro na gidan. Hadimai ne bayi ne da sauran ma'aikata da masarautar ta qunsa,ya kuma yiwa taken laqabi da taren wayar da kai.
Qofofi hudu yasa aka fitar na shiga gurin taron. Uku na shigar mata,biyu na shigar maza. Kowacce qofa kafin ka shiga sai ka sanya sunansa saman takardar dake ajiye a bakin qofa a hannun manyan hadimai na gidan,ciki kuwa harda tamim babba da qarami da kuma bulama. Yana sane ya basu wannan aikin na tsaiwa kan kowa ya rubuta sunansa,hakan shine zai riqe masa su a gurin,ba wata dama ko hanya da musayen aiki ko matsawarsu a gurin har sai an kusa tashi a taron.
Duk wani hadimi da hadima dake tsaron sassan mammina an tsara rukunin zamansu a can ciki,yadda fita daga dakin taron zai zame musu long process,baya ga haka ya kasance doka ta zama dakin taron har zuwa sanda za'a kammala taron.
Shi da kansa yaso ya jagoranci shiga sassan mammina,saidai yana da wani irin fikira da tsananin hangen nesa. Bacewarsa a gurin zai iya zama babbar ayar tambaya ga duk wanda yasan wani plan daya shafeshi komai qanqantarsa. Duk da bai sani ba,amma yana jin a hankali wani abu me kama da ana ci gaba da babiyar kowanne motsi da daga qafa tasa.
Cikin hikima qwarewa da sanin makamar aiki yake hada ayyuka biyu. Aikin farko shine monitoring na shigar abdii sassan mammina,tun daga qofar farko da zaka taras ta shiga sassanta har zuwa gurin da suka nufaci zuwa. Camera ne qarama da ya sanya abdii maqalewa daga gaban rigarsa,ta yadda zai dinga ganin komai tamkar tare suke shiga gurin dashi.
Bai taba tunani ko kawowa a ransa zai bawa abdii wannan aikin ba. Amma yadda yaron ya tsaya a gabansa da wani irin confidence yaji a ransa bari ya gwada.
Ya dafa kafadarsa bayan ya gama shirya abdii din da yanayin shigar da yakeso ya shiga gurin.
"Wannan ba muhallin wasa bane abdii,wannan din wani gagarumin aiki ne mafi hatsari da zakayi......faduwa ko nasarar dukka ni zatafi shafa kai tsaye......rayuwar motii rayuwar nanay rayuwar oromia gaba daya". Da wani kalan murmushin nutsuwar da bai taba gani ba saman fuskar abdii din yake kallonsa.
"Obbo......nayi maka alqawari.....zan cikashi,zan kuma baka mamaki" Abinda yace da haisam kawai kenan. Musayar kallo suka yiwa junansu na wasu daqiqu,haisam din ya dan daki kafadar abdii sannan ya ya juya a nutse yana ficewa.
Kamar a yanzun da suke gurin,ya rarraba aikin zuwa ga mutane daban daban,duk da basu da yawa,amma yana saka ran qaro wasu cikin mutanensu uku da suka rage suna rayuwa cikin agadez din tun kafin isowarsa qasar.
Beeno da salawi suna cikin hadiman,sun saje sosai dasu suna karantar reaction din kowa. Bayason bayyana fuskar dukkanin mutanensu,saboda hakan zai zama wani hadari ne na daban,kuma zai zama wata hanya ta rashin security.
Omari yana tare dashi amma ta bayan fage,yana tayashi monitoring motsin abdii da ya soma nisa cikin sassan mammina din.
Zuzzurfan muryar nan tasa dake dauke da wani irin amo ya sanya duk wani dake gurin nutsuwa da tattarar hankalinsu guri guda a kansa. Kusan ba wanda a gurin baisan sheikh muhammad haisam ba,musamman hadimai mazan dake cikin gidan,wanda dukkaninsu sun samu sanarwar nad'ashi a matsayin D'A,sanarwar da ta zauna cikin kwanyar kowanne hadimi na gidan take kuma aiki tamkar sauran dokoki cikin gidan.
Har cikin jinin tamim yakejin wani abu yana tsarga masa game da yanayin muryar haisam din,wani irin yanayi da ya saukar masa da wata mummunar kasala a dukka gabobinsa. Yana jin wani abu daban tattare dashi,yana jin wani yanayi na daban a muryarsa......kamanninsa dama tsaiwarsa gaba daya.
A nutse ya koma da baya bayan kammala jawabansa ya bawa ME WADA guri. Shine kusan dukkanin shugaban hadimai maza dake gidan,wanda haisam ya zauna dashi na mintuna goma sha biyar kafin su shigo nan din,ya kuma bashi tsarin abubuwan da zai gabatar musu.
Akwai sabbabin dokoki da tsare tsare daya shirya gabatarwa daga sanda sultane ya tashi zuwa umra. Sai a yanzu yake jin kamar wata dama ya samu da zai bude wuta akan aikinsa ba tare da tunanin sultane zai hango komai daga gareshi ba. Sabbin dokoki ne da zasu zama wajibi akan kowa dake rayuwa cikin gidan,yanaso kuma ya gabatarwa da sultane su ya sanya hannu a jimlace su zama TABBATACCIYAR DOKA da zai rarrabata tsakanin dukkan hadimai da bayi na gidan.
"Be fast abdii" Haisam ya furta qasa qasa yana duban tsakiyar tafin hannunsa da na'urar ke maqale,wanda zaka dauka tasbihi yakeja.
"Na kusa qarasawa ainihin muhallin da take kebancewa" Ya fada cikin qwarewa da takatsantsan da dukka motsinsa,duk da taswirar hannunsa da haisam ya tsarata tsaf tana nuna masa kowacce hanya daya kamata kayi.
Qofar glass din ya zuge gefe daya,ya kuma shiga a hankali. Tafkeken parlor dinta daya zama na musamman ne ya soma bayyana,wanda yake dauke da wani irin nau'in ado da yaja hankalin haisam din.
"Obbo......oromian....."
"Dakata!" Haisam ya tsaida abdii.
"Ba wani hatsari?" Abdii ya tambaya saboda tsayuwar data zama ta ba zata.
"Turn to your left side" Ya bashi umarni yanason ganin wani abu da yaga gilmawarsa. Yadda haisam din ya fadi masa hakan yayi,take tafkeken frame din dake dauke da wani nature drawing ya bayyana.
Sosai haisam ya zubawa frame din idanu,wasu abubuwa suna dawo masa akai. Wasu shekaru can baya da wasu memories da suka ja hankalinsa sosai.
"Ka dauki hoton frame din ka turamin......kafin ka shiga ciki.......kaje ka duban dining table na sassa......idan baka samu komai ba a nan ka qarasa store da yake manne da babban kitchen dinsu".
"An gama obbo" Abdii ya fadi yana ciro wayarsa yayi snapping frame din sannan ya soma laluben bangaren dining.
Ba jimawa ya sameshi,tun bai qarasa ba ya hangeshe sheqi da kwanukan abinci na alfarma da suka janye hankalinsa. A yanayinsa kamar anci abinci ba jimawa a wajen.
"Inason ganin kwanukan da kyau.....da abincin dake cikin kowanne......ka hanzarta,don kowanne lokaci hankalinta yana iya karkatowa gida" Haisam ya