Showing 69001 words to 72000 words out of 88589 words
hanamu cutar da
ɗ
an kowa albarka annabi muhammad"
Kai jama'a tun kafin lauje ya warware daga cikin
na
ɗ
i umma babba tayi la'asar fa
Haka kawai take ji acikin jikin ta akwai wani ƙulli me girman gaske a lamarin.
Sanda labari ya iske Amal cewa aure ya koma kan ya faruk tayi matuƙar shiga ru
ɗ
u
bama ita ka
ɗ
ai ba, harda sauran amaren da suma al'ajabi be
barsu ba
Duk wanda suka tambaya kanun zancen sedai yace "haka kawai khalid
ɗ
in ya sake ta aka
mayar da auren akan ya faruk"
Abun mamaki sanda hafsat ta kira umma babba dan taji dalilin hakan,
umma babba ta tsinci kanta da kasa fa
ɗ
in komi game da mumt
az, abu
ɗ
aya tace "Sauyin
ubangiji ne kawai hafsa".
Kusan hakan maganar take a kunnen kowa, takamaimai ka titsiye mutum kace meye dalilin da
yasa aka mayar da auren mumtaz kan ya faruk,?
Sedai suce "Ikon ubangiji ne".
TO HAKA UBANGIJI YAKE ABUN SHI, I
N YA RUFA MAKA ASIRI TO BABU WANI MAHALUKI
DA YA ISA YA TONA SHI
SHIYASA AKO DA YAUSHE MUKE ROƘON UBANGIJI DA YA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA
LAHIRA, YA HANE MU AIKATA AIKIN DANASANI.
Goma saura na dare su Abba babba suka tara matan su da kuma ƴaƴan su kaf
dake ma'aura,
da kuma wanda kenan cikin gidan banda wanda aka kai jiya,
Mumtaz na ra
ɓ
e jikin mama taƙi yarda ta bu
ɗ
e ido sam tsabar tsoro da kuma abinda take
tunanin ze kai ya kawo
Ƙ
afa
ɗ
aya kan
ɗ
aya umma babba ta
ɗ
ora tana zaune a gefen Abban ta dama,
umma ƙarama
kuma na gefen shi ta hagu
Mama na kusa da Abba ƙarami da shima zaka ga annurin fuskar shi ya da
ɗ
u,
Uncle ƙasim ma aunty na kusa da shi.
Unccle Abbas da shima da ƙyar ya yarda ayi zaman yana zaune kuaa da mummy
Goggo safiya na daga gefe.
Y
aran duka suna zaune a ƙasa
Ƴ
aƴan ta mata gaban su na ta fa
ɗ
uwa dan sun san umma babba ba ƙaramin shiri tayi wa
zaman ba
Da addu'a Abba babba ya bu
ɗ
e taron, sannan ya fara da ban haƙuri ga wanda suke tunanin
ba'ayi musu daidai ba
Nan Abban yayi nasi
ha me ratsa jiki kafin ya waiga ga umma babba yace "a matsayin ki na uwa
nasan ban kyauta ba da ban baki damar ki ba, amma ina me baki haƙuri"
Ido
ɗ
aya umma ƙarama ta kashe wa uncle Abbas da gaba
ɗ
aya hope
ɗ
in su itace umma babba,
botsarewar ta kawai suke
jiran ji
Amma ga mamakin su da Abban ya kai ƙarshen maganar shi, se ji sukayi umma babban tace
"ai kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah ya bashi ikon riƙe ta da gaskiya da amana, ya tsole
idon maƙiya"
JAKAR UBAN CAN
😳
ALLAH KASA ANNABI YA CE
CE MU
🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
Ƙ
ADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg73-74
Tsit palon yayi, wan
ɗ
anda kansu ke a ƙatsa duk
suka
ɗ
ago tsabar yarda kunnuwan u suka kasa
gasgata abinda suka ji
Bama yaran ka
ɗ
ai ba, kaf iyaye matan da mazan mamaki ne kwance a fuskokin su
Mama kam sakin baki tayi bilhaƙƙi da gaskiya tana kallon umma babba da tai mirsisi da
idanuwan ta
Ƴ
aƴan umm
a babba kaf idanun su ciccikowa da ƙwalla sukayi jin irin bazatan da mahaifiyar tasu
tayi musu
Abba babba shi kanshi maganar umman tayi mugun bashi mamaki, ta wani fannin kuma a take
yaji ƙimarta na da
ɗ
uwa a zuciyar shi, ko ba komai bata kunyata shi ba
A
hankali mama ta maida kanta ga ya faruk dake gefe yayi folding hannayen shi ga ƙirji
A fakaice tayi mishi jinjina da hannun ta, dan ta san ba aikin kowa bane inba shi ba, duba da
sanin kafaffen hali irin na umma babba.
Mumtaz kam banda raba ido babu abi
nda take, dan ita har ga Allah bata yarda da abinda umma
b tace ba
Hajiya umma ƙarama kuwa ƙiri-ƙiri zaka hango rashin nutsuwa a tattare da ita, ga uwar zufa
data ke ta fama gogewa a fakaice
Goggo safiya ta gyara zama duk da itama mamakin ne kwance a f
uskar ta tace "To se muyi wa
ubangiji godiya,
Nasan yarda nake cikin bazata haka kowa yake a nan" ta maida kallon ta ga umma babba da
har yanzu ƙafarta
ɗ
aya na kan
ɗ
aya tace "Kin kyauta ƙwarai da gaske hajiya Nabila haka
akeson babba ya kasance kullum ciki
n fahimta da fawwala ma ubangiji komi, wallahi dole mu
fa
ɗ
a kin mana bazata, Allah yayi riƙo da hannayen ku wajen riƙe amana"
Da "Amin" kowa ya amsa, fuskar kowa da fara'a da annuri banda uncle Abbas da yayi mutuwar
zaune tunda yaji furucin umma babba
Ga
Tk da ya gama ƙullin shi shima zaune, idanuwan nan kamar zasu fa
ɗ
o ƙasa saboda
muguwar hararar da yake aikawa ya faruk.
Cike da farin ciki uncle ƙasim yace "magana ta ƙare anjima se a sada ta ga
ɗ
akin mijin ta"
Ba wanda ya ankare se ji sukayi Tk yace
"wallahi da sake babu wanda kuma ya isa ya sake
titsiye ni yace na saki matata alhalin warda ake jira aji ta botsare bata botsare ba"
A firgice umma ƙarama ta dafe bakin ta,
Uncle Abbas kuwa cikin zafin nama ya sauke ma Tk tagwayen maruka, cikin tsananin
fushi me
ha
ɗ
e da tsoro yace "Baka da hankali ne Tk, iyayen ka na magana kana magana, kodai kaje
kasha abinda ke maka saƙe-saƙe a cikin kai ne?"
Umma ƙarama na ganin hankalin kowa ya koma kan Tk ta samu ta sa
ɗ
a
ɗ
a ta bar palon ta nufi
ɗ
akin ta.
Abba
babba da yafi kowa zafi shima yace "Ku rabu da shi, maimaita abinda kace Tukur"
Ƙ
unƙuni ya hauyi, ya kasa magana
Tsintsinkewa kawai zuciyar Uncle Abbas keyi, karon farko da tsoro me tsanani ya kamashi
Tsawar da Abba babba ya daka mishi yasa shi fa
ɗ
in
"Ina nufin nima a anso min tawa matar
tunda kowa ana maganar shi amma anyi shiru da tawa"
A kusan tare umma ƙarama dake la
ɓ
e suka sauke ajiyar zuciya ita da uncle Abbas da ya silale
ya koma ya zauna
Sedai abinda basu sani ba shine ba ƙaramin yaro kaf a p
alon, maganar Tk ta farko abar
tunanice a ƙwaƙwalwa
Yarda umma babba ta zauna tana fasa maganar a kanta abun se ya baku mamaki
Daga haka dai iyayen maza suka sallami kowa ya rage se su ka
ɗ
ai se kuma goggo safiya.
Ba ƙaramin mamaki umma babba ta shiga
ba ganin yarda manyan ƴaƴan nata ke murna, masu
raguwar zuciya daga cikin su harda kuka
Nan ma zuciyarta ta sake yin sanyi
A nan palonta ta barsu su duka ta shige bedroom
Seda ta kulle ƙofar tukun t zauna tana sake fasa maganar da Tk yayi
Can data gama
fasata ta kuma
ɗ
auko maganar da ya faruk yayi mata a
ɗ
azu ta ha
ɗ
a, se ta ga
abun ya bata ma'ana
ɗ
aya
Ta jima sosai a zaune tana nazari har lokaci yaja bata sani ba, daga ƙarshe a bayyane tace
"Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI a maganar shi".
Abba ƙarami
ne ya amshi maganar Tk da niyar gobe Ze kira aminin nashi ya sanar mishi da
zasu zo su
ɗ
auki amarya sakina.
Da wannan maganar ta Abba ƙarami aka rufe taron, bayan fa
ɗ
a me zafi da Abba babba yayi
masa.
Umma ƙarama data shiga
ɗ
aki waya ta
ɗ
auka ta kir
a uncle junaid da shima jarabar maman
sakina tasa ya kulle kanshi a
ɗ
aki
Jiki na rawa umma ƙarama tace "wallahi junaid asirin mu na gaf da tonuwa, nidai na kasa
sukuni gaskiya ku kira malam kusa shi ya rufe mana bakin kowa gudun jin kunya"
Shiru uncle
junaid yayi kafin yace "Baya
ɗ
aukar wayata daga jiya zuwa yau, tuntuni naso ya
rufe min bakin sakina da mahaifiyar ta kafin mu samo bakin zaren"
Dogon tsaki uncle junaid yaja sannan yace "duk wannan wawan ne da ya sako mana
ɗ
anshi a
tafiyar, wallahi ba da
n ya sako sakaran
ɗ
anshi ba da babu yarda za'ayi mu rinƙa shiga tashin
hankalin da ze sa har a farga da yanayin da mutum ke a ciki ba"
Still gaban ta na fa
ɗ
uwa tace "kuyi magana da Abbas
ɗ
in dai, shi ya kwatanta kiran shi, in ma
be
ɗ
auka ba dole aje a sam
e shi a daren nan kar wanki hula ya kaimu inda bamuyi tsammani
ba junaid"
Daga can uncle junaid yace "Bari nayi trying shi".
Ƙ
iri-ƙiri uncle Abbas na ganin call
ɗ
in uncle junaid yaƙi
ɗ
agawa, haka ya ƙaraci kiran shi har ya
haƙura.
A daren ranar bay
an tashi daga zaman da akayi a palon Abba babba, ya faruk ya
ɗ
auki
maganin da ya amso daga wajen Alramma ya nufi sasan mama
Ta can ƙofar baya ya shiga, har sama ya haura
A palo ya iske maman da goggo safiya se inna hassu da su ka
ɗ
aine sukayi saura a ƴan
biki
Zama yayi suka gaisa da inna hassu, itace dama basu gaisa ba tukun ya matsa kusa da mama
yayi ƙasa da murya yace
"Mama na kar
ɓ
o maganin tun
ɗ
azu, ya kamata ta sha kar tayi wasa dashi kamar wancan"
Hankali kwance mama tace "shiga tana
ɗ
akin ta"
Ɗ
an
jimm yayi ka
ɗ
an kafin ya miƙe ya nufi ƙofar da zata sada shi da
ɗ
akin nata.
Mumtaz na kwance ta kifa cikinta akan gado,
daga ita se ƙaramin baƙin wando da be wuce tsakiyar cinyar ta ba se vest fara ƙal da bata
ƙarasa rufe mata cibiya ba
Ga gashin ta
da yasha gyaran biki ta baje shi, yarda take kwance haka gashin yabi lafiyar pilon
shima, kusan rabi ya rufe mata gefen fuska,
Wayar goggo safiya ce a hannunta, ta ƙuƙe se typing msg take
Gaba
ɗ
aya hankalin ta da nutsuwar ta yana kan wayar, baka jin ƙar
ar komi a
ɗ
akin se na
madannan wayar
Ya faruk ya turo ƙofar ya shigo bakin shi
ɗ
auke da sallamar da bata kai ga fitowa ba ta koma
inda take
Tunda ya shigo ya ƙame a wajen kamar wanda aka dasa
Gaba
ɗ
aya bugun zuciyar shi ya sauya daga yarda take, ta ko
ma bugawa da sauri-sauri
Yarda yake a tsayen nan babu wani abu dake motsi a jikin shi se idanuwan shi dake bin ko ina
da ina na jikin ta da kallo.
Seda ya gama ƙare mata kallo ya sa
ɗ
a
ɗ
a a hankali yakai hannu ya fizge wayar dake hannun ta
A firgice tace
"wayyo Allah na" tana waigowa da sauri
Tana ganin waye a tsaye ta miƙe a guje ta sauka daka kan gadon ta
ɓ
oye a bayan abun saƙale
jakunkuna ta tsaya
Fat-fat haka ƙirjin ta ke duka
Leƙo da kanta tayi taga ita yake kallo ko me, ga mamakin ta gaba
ɗ
aya han
kalin shi na kan
screen
ɗ
in wayar da ya fizge daga hannun ta
Da sauri ta dafe ƙirji tunowa da tayi khalid fa take rubuta ma saƙo
Aiko mancewa tayi da kayan data saka ta fito da sauri tayi wuf zata ƙar
ɓ
e wayar
Cikin zafin nama ya damƙeta da hannun shi
ɗ
a
ya sannan yaci gaba da karanta dogon saƙon
data rubuta ma khalid
ɗ
in
Wutsil wutsil ta hau yi tana son ƙwacewa daga riƙon da yayi mata
Seda ya gama karancewa tsaf tukun ya maido da idon shi kanta
Jinjina kai yayi ha
ɗ
e da
ɗ
aga gira
ɗ
aya yace "ohhh ashe ha
r haddace number guntun can
kikayi"?
Zum
ɓ
ura baki tayi sannan tace "Akwai no
ɗ
in ai a wayar"
Ɗ
alle mata maki yayi da
ɗ
ayan hannun sannan yace "dan akwai number a wayar shine ya baki
damar yin magana da shi?"
Banza tayi da shi
Jin tayi shiru yasa ya sak
e matseta sannan yaja kumatun ta da
ɗ
an ƙarfi yace "kin mance akwai
auren wani a kanki ko?"
Nan ma shiru tayi, tayi ƙwalƙwal da ido kamar me shirin yin kuka sannan tace "Haƙuri na bashi,
kuma na gaya mishi ni ba fasiƙa bace, bayan sata babu wani abu danak
e wanda be dace ba"
Nan da nan maganar datayi yasa yaji wani iri ha
ɗ
e da tausayin ta na da
ɗ
a kamashi
A hankali ya samu gefen gadonta ya zauna, sannan ya janyota ta zauna akan cinyar shi
Seda ya
ɗ
auki mintoci kafin yace "daga yau daga rana irin ta yau ba
na so na kuma jin kince
kina sata
Kuma kar na sake ganin ko da wasa kin sake
ɗ
aukar waya da sunan zaki ma wani wawa da be
cancanci sanin ki ba sam msg, ki rabu da kowa"
Robar maganin da ya shigo da ita ya
ɗ
akko, da kanshi ya bu
ɗ
e murfin ya kai maganin bak
in ta
Gintse baki tayi taƙi bu
ɗ
ewa,
Ware mata manyan idanun shi na gado yayi sannan yace "bu
ɗ
e bakin ki kisha"
Duk da
ɓ
ata ran da take haka ta bu
ɗ
e ya tuttula mata shi, seda ya tabbatar da tasha ya kai
adadin daya dace tukun yacire ya kulle
Jiki a sany
aye yace "da izinin ubangiji kin bar ƙara sha'awar kayan kowa daga yau"
Gaba
ɗ
aya kunya ta rufeta
Hannayen shi nata zagaye a bayan ta kusan mintoci kafin ya sake cewa "gaya min abun wa da
wa kika
ɗ
auka, kuma in kin
ɗ
auka me kike yi da shi?"
Shiru tayi k
anta a ƙasa, duk a takure take jin kanta
Seda ya sake maimaita tambayar tukun tace
"Tsaya in saka kaya to"
Bu
ɗ
e idanun shi yayi sosai a kanta kafin yace "wannn su ba kaya bane?"
Banza tayi da shi, ta miƙe daga jikin shi
Shi kam be ma da energyn da ze
iya hanata tashi, yana kallo ta
ɗ
auki zumbu
ɗ
e
ɗ
en hijabi ta
saka sannan ta koma kan stool
ɗ
in gaban mudubi ta zauna
Gyara zama yayi ya
ɗ
an kishin gi
ɗ
a a gefen gadon sannan yace "ina jin ki gaya min"
Kanta a ƙasa tace "agogunan Abbana nafi
ɗ
auka, se na w
ani malamin mu guda
ɗ
aya, se
agogon khalid da abun hannun mamanshi, se carbin umma babba, se kuma naka agogon"
Tana gaba fa
ɗ
a ta sadda kanta ƙasa
Tashi zaune yayi yace "meyasa abun maza kawai kika fi
ɗ
auka?"
Jiki a sanyaye tace "nima ban sani ba"
Gya
ɗ
a
kai yayi, a ƙasan ranshi yace "shima wannan akwai lauje cikin na
ɗ
i kenan"
Bayan
ɗ
an shirun da yayi, can yace "to me kike da su in kin
ɗ
auka?"
Still kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannun ta tace "Ba abinda nake da su, ajiyewa kawai
nake"
Bata gama maga
nar ba ta tashi daga inda take zaune ta bu
ɗ
e wata jaka madedeciya ta miƙa
mishi
Ba musu ya kar
ɓ
a, ya duba, a hankali tace "na baka naka, yanzu agogon khalid dana malamin
mu se kuma na Abbana ne kawai a cikin nan"
Hannu ya saka ya ciro carbin umma, kafin
yace komi tayi sauri tace "se kuma carbin umma
babba"
Kallon carbin yayi yana tuna sanda ya ganshi ya fa
ɗ
o daga jikin ta
Gya
ɗ
a kai yayi ya miƙa mata jakar "ungo ajie, zuwa gobe in nazo kawo maki maganin ki se in
tafi da su"
Gya
ɗ
a kai tayi
Ɗ
aukan magani
n yayi ya nufi ƙofa,
Jiki a sanyaye ta bi bayan shi da kallo,
Kallo ne me ma'anoni da dama
Gaf da ze fita ya waigo karaf suka ha
ɗ
a ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa
Murmushi yayi yace "Nafi wancan guntun kyau ko?".
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU
🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
Ƙ
ADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg75-76
Seda ya faruk ya jera kwana hu
ɗ
u cif se bayan isha
zezo da kanshi yabama mumtaz maganin
ta
A kwana hu
ɗ
un nan shaƙuwar da ita kanta bata san ta yaya hakan ya faru ba ta shiga tsakanin
su.
****BAYAN SATI ƊAYA
Tsaf an gama gyaran gidan ya faruk inda mumtaz zata zauna
Ha
ɗ
a
ɗɗ
u kuma tsadaddun kayan
ɗ
aki
Abba ƙarami ya zuba wa mumtaz tunda yaji labarin
abinda dangin khalid suka ce game da kayan
Dan kanshi yace a rabu da su kar wanda ya sake binsu.
Ƴ
an tsirarun dangin mama da kuma