Showing 87001 words to 88589 words out of 88589 words

Chapter 30 - Lauje-Cikin-Nadi-Book-Compeletx

ya sadda kan shi ƙasa

Jiki a sanyaye tace "nasan hu

kuncin ba da

ɗ

i ze maka ba yaro na,

mu barsu da aniyar su, mukuma gode wa Allah da ya taƙaita mana abun, ko a haka aka tsaya

Allah ya warware mana kaikaifen LAUJEN da ke CIKIN NAƊI"

Bece komi ba sema sake jin wani tausayi da ƙaunar ta a cikin ranshi.

Gya

ɗ

a kai goggo safiya tayi itama tace "hakane abinda zahra'u tace faruk, koda amanar

zumunci da suka ci aka barsu ya ishe su"

Umma babba ta

ɗ

ora da "mugunta kuma ai fitsarin faƙƙo ce, suje can su ƙarata da matsalar

dake a tsakanin su ma ta ishe su"

Aunty ta

ce "Allah yayi mana maganin abinda bamu iyawa"

Haka suka ha

ɗ

u sukai ta ba ya faruk baki da kalami masu da

ɗ

i har sanda su Abba babba da

uncle ƙasim suka fito da niyar zuwa duba Tk dake kwance shima har yanzu.

Gaf da azzahar aunty da umma babba suka wuce g

ida aka bar goggo safiya da mama se

mumtaz da ke bacci tunda ta samu ta shiga ta gaida Abba ƙ ta bi lafiyar

ɗ

ayan gadon da mama

ke kwana a kai ta kwanta

Ba wanda ya tashe ta aka barta tayi baccin ta.

***Sosai ya faruk ya fuskanci mus'ab da Ahmad yace

"Ku saurare ni da kyau kuji, tunda har su Abba suka yanke wannan shawarar to babu yarda

za'ayi mu ja da su, abinda zamuyi yanzu shine, zan yi write up akan uncle Abbas da uncle

junaid harma da umma ƙarama akan cin amanar da sukayi, mu ya

ɗ

a su a duniya"

Tu

n

ɗ

azu se yanzu mus'ab yayi murmushi, dan gaba

ɗ

aya wannan tunanin bezo mashi ba sam

Ahmad yace "yes, shiyasa nake alfahari da kai ya faruk"

Murmushi ya faruk yayi sannan yace "zamu ha

ɗ

a duka da pictures

ɗ

in su, yarda har fita ma

seta gagare su saboda

kunya, sannan ko su Abba sunji zamuce bamu san yarda akayi ba"

Dariyar farin ciki mus'ab da Ahmad suka saka ha

ɗ

e da rungumar ya faruk dake ta murmushin

jin da

ɗ

i shima.

BAYAN SATI ƊAYA

Khali na kwance yana ta scrolling a facebook yaci karo da dogon rub

utu me

ɗ

auke da hoton

umma ƙarama da uncle Abbas da kuma uncle Junaid

Ganin fuskokin su da kuma rubutun da akayi da manyan baƙi daga sama ya sa shi miƙewa

zaune da sauri ha

ɗ

e da ƙurama rubutun ido, inda ka rubutu "MACIYA AMANA UKU"

Tiryan-tiryan khalid y

a karanta labarin tas, inda babu wani abu da aka

ɓ

oye akan irin cin amanar

da sukayi, har da asirin da akayi wa Abba ƙarami na sata da be kamashi ba ya kama ƴarsa

mace

ɗ

aya tilo

A sukwane khalid ya fito ya hau kiran sunan "mami" da ƙarfi

Mami na zaune it

a da aunty hajara suna firarsu sukaji mahaukacin kiran da kalid ke kwa

ɗ

a mata

A firgice har suna rige*rigen fitowa

Mami tace "lafia khalid"

Fuska sha

ɓ

e-sha

ɓ

e da hawaye yace "mami na cuci kaina, na shiga uku, ni dama nasan

mumtaz mutuniyar kirkice wallah

i"

Kallon kallo mami da aunty hajara sukayi kafin mamin tace "me yafaru kake kira ma kanka

shiga uku?"

Cikin kuka kamar wani ƙaramin yaro ya miƙa mata wayar

Hannun ta har rawa yake wajen ƙoƙarin ƙar

ɓ

a

Shiru tayi tabi wayar da kallo, bata san mutanen da

ke cikin hoton ba, amma content

ɗ

in saman

yaja hankalin su ita da aunty hajara har suka tsunduma cikin labarin

Tun kan mami ta kai ƙarshe take furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!"

Aunty hajara kanta jikin ta yayi sanyi tana tuno fuskar mumtaz

Ku

kan da khalid keyi ya karyar musu da zuciya, se ga mami itama sha

ɓ

e sha

ɓ

e da hawayen

nadama da danasani

(SHIYASA BINCIKE YAKE DA KYAU KAFIN KA YANKE HUKUNCI

KUMA GAGGAWA AIKIN SHEƊAN CE)

Ranar haka khalid da mami suka yini cikin juyayi da danasani.

K

amar yarda kalid yaga wannan rubutu game da su incle Abbas, haka ya kara

ɗ

e lungu da saƙo

na ƙasar.

Uncle ƙasim na gani yayi murmushi, a fili yace "Nasan ba kanwar lasa bane kai faruk, kayi

ƙ

oƙari"

Gaba

ɗ

aya fita ta gagari uncle Abbas da uncle junaid, g

a tsiyar dake tsakanin su data kunno kai

me zafin gaske.

Umma ƙarama kam tun sanda Abba babba ya bata tikitin sallama taƙi yarda ta sanarwa da

iyayen ta abinda tayi

Seda wannan rubutu me

ɗ

auke da hotunan su ya bayyana aka san komi,

Abin duniya suka taru

sukai mata yawa, ga tsana daga wajen ƴaƴan cikin ta, ga kuma tsana

daga nasu gidan, rana zafi inuwa ƙuna kenan.

Abba ƙarami tun yana hospital yasa aka gyara mashi

ɗ

aya daga cikin maka makan gidangen

shi

Kai tsaye yace "ya gama zama da kowa, nesa nesa

tafi"

Hakan kuwa ba ƙaramin da

ɗ

i yayi wa mama ba, dan sanda ya sanar da ita kasa

ɓ

oye murnar ta

tayi seda ta rungume shi.

Haka ya faruk yayi ta up and down har seda gidan ya shirin gidan ya kammala sannan aka

sallami Abba ƙarami

Direct sabon gidan suka

wuce

Seda aka kwana

ɗ

aya tukun mama taje can gidan

Ta kwasa abinda take so daga nan, ta rabar da wanda bata so.

Duk da ƴan'uwan nasa basu ji da

ɗ

in huƙuncin da Abba ƙ ya yanke ba, amma hakan besa sun

hana shi ba, sanin irin haƙurin da yayi da kuma

ɗ

awa

iniyar da yake kan yi dan ba denawa yayi

ba.

BAYAN WATA TARA DA ƳAN KWANAKI

Ya faruk na kwance waya kare a kunnen shi suna magana da mus'ab da ya fita shigo da wasu

kaya na

ɗ

aya daga cikin companyn Abba ƙ dashi ke managing yanzu a maimakon uncle Abbas

Mumtaz na zaune akan darduma tayi zaman tahiya ga uban tirtsetsen cikin ta a gaba haihuwa

yau ko gabe

Ta gama karatun tahiyar tana so ta miƙe tsaye amma ta kasa,

Ya faruk hankalin sa na can kan wayar da yake

Hannun ta tafa alamar magana

Shiru beji ba

Sake tafa hannuwa tayi a karo na biyu sannan ya faruk ya farga da tafin nata

Sallama sukayi da mus'ab ya taso ya matso kusa da ita yace "menene"

Alama ta sake yi mishi da hannu,

shiru ya faruk yayi ya bita da ido dan har ga Allah be fahimci me take nuf

i ba

Da dai mumtaz taji kamar bayanta ze

ɓ

alle tace "Ai se ka

ɗ

aga ni tunda kasa na

ɓ

ata sallah ta"

Kwashewa da dariya ya faruk yayi ganin yarda har idonta sun cika da ƙwalla

Seda ya miƙar da ita tukun yace "yanzu dai in kin huta kiyi sallar a zaune tun

da in kin yi sujjada

baki iya

ɗ

agowa ta da

ɗ

i"

Banza tayi da shi ta wuce can gefen gado ta zauna tana maida numfashi.

Kallon ta yayi cike da so da ƙauna ha

ɗ

e da tausayawa yace "in sha Allah kin kusa sauke su ki

huta kema, Allah yayi maki albarka matata!"

Lumshe ido tayi, a koda yaushe ya faruk na sata jin nutsuwa a rayuwar ta

Ko kallon shi tayi takan tsinci kanta cikin farin ciki ha

ɗ

e da godiya wajen ubangiji

cike da shauƙin so ta

ɗ

ora kanta a kafa

ɗ

ar shi, shi kuma ya zagayo da hannun sa kan ƙaton

cikin

ta yana shafawa.

A GURGUJE.

Mom Asiya data samu ta anshi nata tikitin daga wajen incle junaid taje ta maka Tk a kotu tana

nemar wa ƴarta saki

Haka akaita tafka shari'a har Allah ya basu sa'a ta samu sakin, sedai ba'a jima da sakin ba cikin

Tk ya bayy

ana a jikin sakina

Hankalin sakina ba ƙaramin tashi yayi ba, haka sukai ta fama wajen ganin bayan cikin nan,

amma da yake duk abinda Allah yayi niyar halitta babu makawa seyayi haka suka haƙura har

ƴ

ar Tk tazo duniya ba dan ransu yaso ba.

ALHAMDULILLAH!!

!

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI

NAGODE WA ALLAH DA YA NUNA MIN FARKO DA ƘARSHEN LITTAFIN "AKWAI LAUJE

CIKIN NAƊI" ALLAH UBANGIJI YASA MU AMFANA DA DARASIN DA KE CIKI, KUSKUREN

CIKI YA YAFEMAN, YASA MUYI TARAYYA A LADAN!









GODIYA DA JINJINA TA MUSAMMAN GA MIJI NA ABIN ALFAHARI NA, ƘAUNAR KA TA

DABAN CE A RAINA, ALLAH YA BAKA KARIYA ADUK INDA KAKE

JINJINA GAREKU IYAYE NA, ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKAIRI.

SANNAN INA MIƘO GAISUWA DA F

ATAN ALKAIRI GA DUK WANI MAKARANCIN LITTAFI NA



😊

MUSAMMAN ƳAN CIKIN GROUP ƊINA, ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA HAƊA MU A BOOK

Ɗ

INA NA GABA DA ALKAIRI

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU

🤲

30/5/2023

ZAINAB FALALU

08145225540

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login