Showing 45001 words to 48000 words out of 88589 words
"meye haka?"
Murmushi kawai yayi ya kashe mata ido
ɗ
aya
mumtaz na gama fa
ɗ
in saƙon ta miƙe tac
e "se anjima mummy"
Cike da fara'a mummy tace "shikenan tunda kinƙi zama, kice mata angode"
Tana fita ya Tk yayi wuf ya biyo bayanta da sauri, ko maganar da mummy ke mishi be tsaya yaji
ba yayi gaba
Sauri kawai take zubawa ta bar wajen kar ya cin
mata,
Hakan be samu ba seda ya sha gaban ta
cike da shaƙiyanci yace "ina fatan kema ana gyaramin ke yarda ya kamata?"
Ɗ
aure fuska tamau tayi ta kewaye shi tayi gaba abinta, a ranta tana fa
ɗ
in " Ɗan iska, Allah yayi
min tsari da kai"
Beyi yunƙurin b
inta ba ganin kallon da Ahmad ke mishi, duk da ya girmi Ahmad amma hakan be
hana shi jin
ɗ
an shakka ba, tunda yasan ba Allah acikin kalaman bakin shi.
BAYAN KWANA BIYU
Ya sabiha da su ya maryam da ƙyar suka shawo kan umma b ta yarda da maganar zuwan
mumtaz da najwa.
Randa ya dace su tafin, akai-akai da mumtaz ta shirya su tafi, ba abinda ya fito bakin ta se
cewa tayi "Wallahi ko waye yazo kanta bw zata je ba, ita bata son gyaran jikin tunda be zama
dole ba"
Da bayan hannu goggo safiya ta make mat
a baki, kafin tace "dan kanki tunda kin raina kowa"
Mama kam tunda tace "meyasa ba zaki je ba" tace mata "ka kurum" bata sake magana ba,
tasan sarai tana da dalilin ƙin zuwan, in akai duba da tun randa sabiha tayi maganar bata musa
ba.
Haka Amal tayi
nacin har tayi fushi ta rabu da ita,
Da dai taƙi zuwan, haka zuka tattara sauran suka tafi.
Ko da ya sabiha taga ba mumtaz a cikin su ta
ɗ
auki waya ta kirata, bugun duniya taƙi
ɗ
agawa
daga baya ma kashe wayar tayi.
BAYAN SATI BIYU, ANA SAURA SATI
BIYU ƊAURIN AURE
Kayan funitures suka iso tun daga turkey ya faruk yayi order bisa ga za
ɓ
in ko wacce a cikin su
manyan stores
ɗ
in dake gidan aka bu
ɗ
e aka shaƙare kayan duka a ciki tukun aka rufe
Duka su biyar
ɗ
in saiti
ɗ
ai-
ɗ
ai Abba b yayi musu, wan
da yaga ze ƙara ma ƴarshi shikenan
shidai yayi nashi
A sanda akayi order kayan mama itama ta yi nata order har sun so sufi wanda akayi musu duka
tsada,
A ranar da akaje ganin gidajen amaren aka ga gidan mumtaz
ɗ
aki uku ne, nan Mama tayi wa
Abba maga
na ya bada wasu ku
ɗ
in aka siya saiti
ɗ
aya.
Kamar Najwa da Bilkisu su dama dangin mahaifin su sun masu
ɗ
aya, sun tashi da bibbiyu
kenan
Ranar da za'a je jere raba tafiyar akayi
Umma babba da aunty suka tafi na mumtaz tare da ƴan'uwan mama
Mummy ta
bi wasu daga cikin ƴan'uwan umma b suka tafi na Amal
Umma ƙarama tabi wasu suma daga cikin dangin umma b
ɗ
in zuwa gidan hafsa
Mama tabi zuwa na Bilkisu, inda kuma dangin mummy duka suka
ɗ
unguwa zuwa ga Najwa.
Ganin dukiyar da aka narka ma mumtaz a
ɗ
an
madedecin gidan ta hankalin umma babba yayi
masifar tashi tunawa data yi bayan saitin da Abba ƙarami yayi musu, Abba babbar ƙananun saiti
ya ƙara musu da shi
Duk da tana basarwa, amma indai kayi mata farin sani zaka san bata cikin nutsuwar ta
Gefe taj
a bayan ta fakaici idon mutane ta
ɗ
aga waya ta kira ya sabiha tace "Duk yarda za'ayi
kar ajera saitin da Abba babba yayi musu, a samo mota a kwashe su a maida store
ɗ
in da aka
siya zatayi ciko a za
ɓ
o musu wa
ɗ
an da suka fi wannan tsada"
Cike da mamaki ya
sabiha tace "saboda me umma?, har fa mun gama da gidan hafsat mun
wuce na Amal"
Cikin fushi umma b tace "haka nake so ayi sabiha, nan da awa
ɗ
aya zan kira"
Ba ta jira jin komi ba ta tsinka wayar.
Haka suka ha
ɗ
u aka
ɓ
alle gadon aka loda su a mota
sann
an suka wuce gidan hafsa aka ciro nata suka kama hanyar store
ɗ
in da aka siya kayan
Tsabar gasa da umma ta saka a cikin ranta seda ta siya musu wanda yayi shige dana mumtaz
tukun hankalin ta ya kwanta, amma fa aljihun ta ya girgiza.
ALLAH KASA ANNABI Y
A CECE MU
🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
Ƙ
ADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg51-52
Gadan gadan shieye shirye sun fara ka
nkama,
Ta
ɓ
angaren mumtaz taƙi yarda da duk wani gyaran jiki da mama Asiya tasa azo ayi mata
Abu
ɗ
aya ta yarda da shi shine turaren jiki da ake mata, shima dan tana son ƙamshi ne, irin
ha
ɗ
in nan ne mesaka jiki yayi laushi kamar fatar jariri
Wannan bata
fashin shi, ko ba'ace tayi ba takan
ɗ
auka tayin
Ana sauran kwana goma sakina ta ha
ɗ
o yanata yanata ta dawo nan gidan, duk da ka kalle ta
zaka san akwai abu a ranta
Ganin vatayi nasara akan khalid ba yasa tun da ta iso da zaran sun ke
ɓ
e se ta fara kusar k
alid
ɗ
in
Jinta kawai mumtaz take, abinda bata sani ba khalid
ɗ
in da bakin shi ya gaya mata tayi hankali
da ita.
Fitowar su daga
ɗ
aki kenan suka iske ya faruk zaune kusa da mama
Cike da damuwa mama ke fa
ɗ
in "Memakon ka bari se bayan biki se ka tafi far
uk? ko dai wani
abunne baka sanar dani ba?"
Murmushi yayi yace "ko
ɗ
aya mama, nema ne kawai ze fitar dani"
Shiru mama tayi, haka kurin take jin wani yanayi mara da
ɗ
i a tattare da ita.
Sakina har ta kai ƙofa amma mumtaz bata tawo ba
juyowata tayi
tace "ko mun fasa ne?"
Bata san me yasa jin wani iri ba jin ya faruk zeyi tafiya
Jiki a sanyaye tace "bamu fasa ba ina zuwa"
Da sauri ta haura sama,
ɗ
akin da aka loda layan lefen ta tashiga
Bubbu
ɗ
e akwatunan tayi ta rasa me zata
ɗ
auka ma a ciki
Shir
u tayi ta zuba wa kayan ido kafin idanun ta sukai ga akwatin turaruka
Bata yi la'akari da cewa turaren mata bane, haka ta
ɗ
akko wata ƴar madedeciyar jaka ta kwashi
kusan guda hu
ɗ
u ta saka a ciki, se lip balm guda biyu
Tusa jakar tayi a hijabi bayan ta
rurrufe komi tukun ta sakko
Bata iske kowa a palon ba se sakina data gama cika
Da sauri mumtaz tace "sakina su ya faruk fa?"
Seda tayi mata kallo
ɗ
aya tukun tace "gashi a baya na"
Tsaki mumtaz taja tayi waje da sauri
Tana fita ta iske bala driver
na saka jakar shi a mota
Ƙ
arasawa tayi tace "Bala ya faruk fa?"
Yanzun nan umma babba tayi kiran shi
Jakar hannunta ta miƙa mishi tace "in ya fito ka bashi kace nace Allah ya tsare"
Kar
ɓ
a yayi ya aje a kujerar gaba sannan ya shiga ya kunna motar
S
akina na ƙarasowa suka fice zuwa neman head
ɗ
in da ze hau kayan da zata saka ranar kamu.
Seda suka isa cikin airpot sannan bala ya miƙa ma ya faruk ledar da mumtaz ta bayar
Da alamun tambaya a fuskar shi yace "na mene wannan?"
Kai tsaye yace "Mumta
z tace a baka, kuma tace nace Allah ya tsare"
Akaro na ba'adadi da yaji fa
ɗ
uwar gaba, kar
ɓ
a yayi be tsaya ya bu
ɗ
e ba ya saka a jakar hannub
shi yayi sallama da bala ya shige.
Ta duka
ɓ
angarorin kowa shiri yake ba ji ba gani
Yau ya kama saura kwana
biyar
ɗ
aurin aure, yayin da zasu fara biki daga jibi
Duka ƴammatan da suka tafi gidan ya sabiha sun dawo, ko wacce ka kalla zaka ga tana sheƙi
da ƙamshin amarci
Randa suka dawo da goggo safiya taga yarda suke sheƙi gunin ban sha'awa, aikuwa ta tasa
mum
taz tayi ta caccakar ta tana dungure mata kai
Ɗ
aya daga cikin dangin mahaifiyar mama tace "banda abinki ba wanda ze ganta yace ba tare
akai musu gyaran ba"
Da sauri ta gya
ɗ
a kai tace "ƙarya haram, hasken fata daban sheƙin ta daban, in kika ga yarda
s
uke sheƙi ba zaki ma fara ha
ɗ
a su da wannan ba"
Matan dake palon suna ta kakkare mumtaz, anayi ana dariya
Gida sosai ya
ɗ
au harama malam, saura kwana uku
ɗ
aurin aure amma zakayi tunanin ranar
ɗ
aurin auren ce.
WASHE GARI
Tunda safe wajen goma mas
u decoration
ɗ
in wajen da za'ayi kamu suka iso
Ɓ
angare
ɗ
aya na gidan aka shirya, kayan gargajiya da ake kamu dasu aka danka gunun ban
sha'awa
Ta
ɓ
angaren amaren kuwa akan gama sallar azzahar aka fara musu kwalliya
Masu kwalliya mutum biyu aka kira dan a
samu yin sauri
Hafsat aka fara ma, se najwa, se bilkisu se Amal sannan akai ma mumtaz da seda aka kai ruwa
rana kamar wacce za'aiwa auren ƙi
Ta
ɓ
angaren gidajen angwayen kuwa sun shirya tsab domin halartar taron kamun, wanda a
al'ada suke zuwa su ka
ma amarya.
Mutum shida mami ta wakilta daga
ɓ
angaren khalid
Bayan la'asar kamal da wani abokin khalid suka je
ɗ
akko su, mota biyu sukayo
Sosai sukayi shiga ta alfarma ta kuma kece raini
wajen biyar saura duka dangin angwayen suka iso, an jima da
nisa wajen farawa
Masu ki
ɗ
in ƙwarya da aka gayyata sun baje kolin su, mata na ta rausayawa
Su kansu iyayen amaren ba daga baya ba, karma ku hango shigar da mama tayi, tuni wasu da
dama suka fara raina tasu shigar alhalin suma
ɗ
in ba daga baya ba
Dangi
n angwayen ma zuwa suka gabatar da al'ada na feshe feshen turaruka da kuma sauran
abubuwa
Ana gab da kiran magariba aka tashi, na tafiya suka tafi, wanda kuma dama sunzo se bayan
biki kowa ta kama inda ya dace ta zauna.
Wajen sha biyu saura na dare
da yake gidan biki ne, bama zaka ta
ɓ
a cewa dare yayi haka ba,
shewace shewace da gu
ɗ
a da kuma hirarra ki ke tashi ta ko wani lungu da saƙo na gidan, uwa
uba ga hasken fitulu ta ko'ina
mumtaz ta ƙwanƙwasa ƙofar
ɗ
akin Abba ƙ inda take kyautata zaton maman
na nan tunda bata
a
ɗ
akin ta
Fitowar mama daga wanka kenan taji bugun ƙofar
Zuwa tayi ta bu
ɗ
e, ganin mumtaz a tsaya yasa ta matsa ta bata hanya ta shigo, sannan ta
maida ƙofar ta rufe
Kan kujera ta wuce ta kwanta bata ce wa maman komi ba
Maman ma b
ata ce ba taci gaba da abinda take
Seda ta gama tas tukun ta mayar da hankalin ta ga mumtaz da har ta fara bacci anan kan
kujerar
Kafe ta da kallo mama tayi, ta jima tana kallon ta kafin ta tashi ta fito
kitchen ta nufa, shayi ta ha
ɗ
a sannan ta
ɗ
auki ca
ke gudu uku da su Altine keta parckaging
rabon da za'ayi a gobe wajen walima
Saman ta koma, a gefe ta aje shayin tukun ta fara tashin mumtaz
"Tashi mumtaz daga ganin ki na san bakici komi ba, tashi kisha tea"
Da ƙyar mama ta samu ta tashin, ko rabin ko
fin bata sha ba tace "mama ya ishe ni"
Cike da lallami maman tace "daure ki shanye dai, ko
ɗ
aya ne kici cake
ɗ
in shima"
Tusa mata shi tayi tayi har seda ta kusa shanye shi tukun ta rabu da ita, kafin daga baya tace
"anan zaki kwana ne?"
Gya
ɗ
a kai ta
yi tace "Mutane sun cika
ɗ
akin ba wajen kwanciya"
Bata sake cewa komi ba ta juya tayi kwanciyar ta bacci yayi awon gaba da ita.
Mama kam tun ranar da aka fara taruwa ta ƙarasa rasa sukuni gaba
ɗ
aya,
Maman sakina tasha ta titsiye ta tana tanbayar ta "l
afiyar ta kalau kuwa"
Amsa
ɗ
aya ce kodayashe itace "lau" ko kuma tayi murmushi kawai
Dan ko an titsiyeta ta fa
ɗ
i meke damunta ba zata iya kwatantawa ba.
Daga baya kawai take alƙanta abin ga kewar mumtaz da zata yi.
Daga wannan saƙe-saƙen bata san sanda
bacci itama yayi awon gaba da ita ba.
WASHE GARI
Biyar saura na yamma harabar gidannan a shaƙare take da ƴan'uwa da abokan arziki, wasu
sun sha Abayoyi, wasu sun sha jalbab
ɗ
insu wasu kuma normal hijabai ne a jikin su,
Wasun su da niƙab wasun su kuma
haka nan
SHAIKA ZAINAB MAHMUD ADAM na tsaka da fara muƙaddima amare suka fara shigowa,
dukkannin su sunsha tsadaddun Abayoyin su, banda mumtaz da ta na
ɗ
e kanta da jar laffaya
me tsa
ɗ
ar gaske
Ɗ
aya bayan
ɗ
aya suka samu waje suka zauna a kujerun gaba-g
aba
Sosai shaika zainab mahmud Adam tayi shikekken wa'azi game da haƙƙin mace akan mijin ta
sosai wa'azin ke shiga dukkan mahalukin dake wajen, bama amaren ka
ɗ
ai ba, harda wa
ɗ
an da
sun jima a cikin auren dama wanda basu kai ga shiga ba
Shaika zainab
mahmud ta
ɗ
au lokaci me tsayi kafin ta rufe
Ɗ
aya daga cikin malaman da suka zo tare ta fara rero waƙa cikin harshen larabci,
Tana tafi tana waƙen,
wasu a ciki da suka iya suka hauyi suma
Anata tafi ana waƙen gunin ban sha'awa.
Note: waƙe ne da musulun
ci ya yarda dasu, don't come and attack me
😎
Sosai walimar tayi armashi, aka ƙaru sosai, wa
ɗ
an da jikin su yayi sanyi saboda tsoratarwan
datayi duk suka warware wajen waƙe da ka
ɗ
a kai.
Shima gab da magriba aka watse, bayan an gabatar da hotuna, ciye
ciye da shaye-shaye.
WASHE GARI
RANA BATA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA!!!
Tunbatsar da gidan yayi ba'acewa komi, mata ne ta ko'ina,
Tsabar cikar gidan har seda ta kawo da an bu
ɗ
e makeken gate
ɗ
in gida
Runfuna ne da kujeru ta ko'ina, karku m
ance biki ne na masu shi masu ƙubar susa
Matane hawa hawa, waccen wace wannan, wannan wace wancan
Kowa kaga fuskar shi zaka san yana cikin murna da farin ciki banda ƴan tsiraru daga ciki
Ciki kuwa harda mumtaz da mama da har shi Abba ƙarami da fa
ɗ
uwar
gaba ta same shi a
safiyar
ɗ
aurin auren
Haka zalika kalid,
Daga wayewar gari zuwa yanzu ya ƙira mumtaz a waya yafi a ƙirga, kuma in ya kirata abu
ɗ
aya
yake tambayar ta shine "Ba wani abun dai ko" har ma ta gaji da amsashi.
Sanda ya faruk ya tafi, se
washegari ya bu
ɗ
e jakar turarukan da mumtaz ta bayar a bashi
seda abun yaso bashi dariya da yaga duk turarukan mata ne
Ɗ
aya bayan
ɗ
aya ya hau shinshinar turarukan, yanayi yana lumshe ido tsabar yarda sukayi
masa da
ɗ
i
Yana tsaka da jin da
ɗ
in shi zuciyar
shi tace "Allah yasa ba satar su tayi ba dai"
Nan da na mood
ɗ
in shi ya sauya ha
ɗ
e da jin wata mummunar fa
ɗ
uwar gaba.
HMMMMM.
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU
🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR
👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
Ƙ
ADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI
WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg53-54
Tunda garin Allah ya waye mumtaz ke zauna a bedroom
ɗ
in Abba ƙ
Ita batayi wanka ba, ba ta kuma da niyar tashi tayin.
Kusan tashi uku mama na shi
gowa
ɗ
akin, a inda ta barta a nan take isketa,
Har ita maman tayi wanka ta shirya duk mumtaz na nan zaune, ta muskata nan ta muskuta can
A shigowa ta hu
ɗ
u ne mama tace "Kalli agogo fa mumtaz, sauran duk sunyi shiga ta bibbiyu
amma ke ko
ɗ
ayar bakiyi ba
, ni shin gaya min gaskiya, kodai kina da wata damuwar ne da kika
kasa gaya min"?
Sadda kanta ƙasa tayi ta kasa cewa komi, se hawaye da suka fara tsere akan kumatun ta
Jikin mama dama a sanyaye yake, nan da nan ganin hawayen
ɗ
iyar tata yasa jikin ta
ya sake
yin sanyi
Kayan dake hannunta ta aje sannan ta matsa kusa da ita
A hankali ta janyota ta rungume ta, cike da tausayi da kuma ƙauna irin ta uwa ta fara shafa
bayanta, a hankali tace "Ki gaya min ko dai kun samu matsala da khalid
ɗ
in ne?"
Tana cik
in jikin ta ta karka
ɗ
a kai,
Maman ta sake cewa "To gaya min menene?"
Cikin sheshekar kuka tace "Kawai bana jin da
ɗ
in jiki na, kuma gabana na yawan fa
ɗ
uwa
akai-akai"
Murmushin yaƙe mama tayi ta
ɗ
ago da kanta daga