Showing 45001 words to 48000 words out of 172989 words
mahaifiyarta take mata ."
"Kece yar wahala daga nace ina son shi sai Kiyi min mummunar fata in sha allahu akanki zai qare "aunty salma taja hannun shukura zuwa cikin d'akint
a tana cewa "manta da sakina muyi abinda Ke gabanmu "ta saki hannunta ta qarasa gaban wasu kwanuka
ta bud'e d'aya daga ciki ta d'auko tandun kwalli ta mikawa shukura tana cewa "ungo nan shukurata maza ki shafa wannan kwallin à idanunki" shukura ta ka
r'ba ta soma qoqarin shafawa yayinda aunty salma ta juya da sauri ta sake d'auko wani qaramin gwan gwani wanda Ke d'auke da wani bakin magani ta sake dawowa inda shukura take tsaye ta miko mata hannunta d'aya tana cewa "bani kwalli ki bani tafin hannunki
idan yasan wata ai bai san wata ba zai san dani yake ".
Cike da farinciki shukura ta mika mata tandun kwallin sannan ta mika mata tafin hannunta kamar yadda ta buqata cikin sauri ta zuba mata bakin maganin tana cewa "ki fad'i sunansa sau uku sannan
ki fad'i duk abinda kike son yayi miki idan kin isa gabansa ina mai tabbatar miki bazai sake miki mutsu akan komai ba sai akan abinda kika fad'a masa zai yi aiki dashi kuma zai bi umarninki ."
nan da nan shukura tayi abinda aunty salma ta umarceta
"ki lashe kije zaki ga irin tarbar da zai miki sannan zaki ga irin tarbar da zai yiwa maryama zabinsa ,matsawar kika ga tarban da yayi miki bai miki ba ko ya had'a da tozarci ko cin fuska karki 'bata ranta ki dawo kawai amman kuma wallahi wallahi sai nayi
masa abinda sai ya wulaqanta akan soyayyarki sai ya dawo yana kuka akanki, ke sai yayi sambatu akanki sai ya fifitaki akan uwar data kawo shi duniya ".
"yauwa mamana shiyasa nake mugun sonki allah dai ya bar min mamana ."maza kije garesa cike da Ka
mala da mutuntaka da kamewa ki shirya duk wasu kalamai masu sanyi da sanyaya zuciya da zakiyi amfani dashi allah ya bamu sa'a wani irin numfashi shukura ta sauke tare da rungume aunty salma ajikinta tana furta "ameen !sannan ta saketa ta juya da sauri
ta bar d'akin ta nufi d'akin da yusif yake ."
ahankali ta shiga d'akin bakinta d'auke da sallama yana nan zaune kamar yadda suka fita suka barshi sai dai idanunshi a runtse suke suna kallon saman d'akin sallamar daya ji anyi ne yasashi bud'e idanu
tare da sauke idanuwanshi abakin kofar d'akin suka sauka akan shukura dake tsaye tana kallonsa fuskarta cike da fara'a do cikin ido suke kallon juna ."
Wasu abubuwa ya dinga ganin suna fitowa daga cikin kwayar idanunta suna shiga nashi nan da nan ya
gyara zamansa sosai yana cigaba da kallonta cikin wani irin farinciki mara misaltuwa tamkar lokacin ya fara ganinta arayuwarsa cike da tsananin farinciki yace "ya kika tsaya qaraso gareni zuciyata Ke take muradin son gani "cike da karairaya shukura ta d
inga taku har ta qaraso ta zauna kusa dashi ya zuba mata ido kawai yana sakar mata tsadadden murmushinsa cikin shukin qaunarta daya ji daga sama "yaya yusif !"
Ta kira sunansa cikin wata irin murya idanuwanshi kawai ya zuba mata batare da yace mata k
omai ba " akace daya daga cikinmu zata maye maka gurbin maryama a wajenka me ka gani
."?murmushi yayi kawai "gabanta ya shiga fad'uwa amman data tuna irin tarban da yayi mata a yanzu sai taji wani sabon gwarin gwiwa ya shigeta "ina son na maye gurbin ma
ryama acikin zuciyarka me zaka iya cewa ?"ai wannan ba komai bane na amince dake dan ma kin fita dacewa dani ".
ta lumshe idanunta kana tace "amman kace domin maryama kawai kazo gidan nan ba dan wasu yan iska ba ?tayi masa tambayar tana mai kafesa
da idanunta yayi shiru yana kallonta qirjinsa na wani irin bugawa da karfi "maryama kad'ai zuciyarka ke muradin son gani bamu marasa kamun kai ba ?ya kai hannusa ya riko hannunta gam cikin nashi yana matsewa "yaushe na fad'i haka ?ni babu wacce zuciyata
ke muradin gani sai ke murmushi tayi kawai aranta tace "aiki yayi tasiri kanan "ta qara damke hannunsa dake cikin nashi "baka ci komai da'aka kawo maka ba".
"na koshi domin ganinki ma kawai ya kosar dani "ya fad'a a daidai lokacin da kausar ta shigo h
annunta rike dana maryam ."wani irin bugu zuciyar kausar yayi da karfi sakamakon ganin yanayinsu dan ita maryama daman ta rigada ta cire samunsa acikin ranta ganinsu haka ma bai d'aga mata hankali ba ."
cikin wani salon jan hankali shukura ta tsura masa
ido tana kallon kwayar idanunshi tana jin wani irin shaukin sonshi na ratsata yayinda maryama ta zame hannun ta cikin na kausar ta samu waje ta jingina bayanta da bangon d'akin Tare da sunkuyar da kanta kasa tana kallon zara zaran yatsun kafafunta dan ba
ta son ganinsu bancin darajan kausar ma da ko hanyar d'akin bazata biyo ba ."
cike da tashin hankali kausar tace "yaya meye haka kuma ?"mai nayi kausar ?shima ya tambayeta yana jin kamar ana soka masa allura a gabad'aya ilahirin jikinsa "jikin ma
ryama ya qara yin sanyi rauninta ya soma bayyana idanunta suka fara ciccikowa da ruwan hawaye "shikenan shima an gama dashi "ta fad'a acikin zuciyarta "dan Allah malama ki sakar masa hannu"kausar ta fad'a tana zabga mata harara shukura tayi murmushin mugu
nta tana zare hannunta cikin nashi tsaki kausar taja sannan ta soma zayyane masa duk abinda maryama ta fad'a ".
Amman da mamakinta sai ji tayi yace "sai me idan ta fad'a miki haka ?ta sake kallonsa a matukar tsorace tana cewa "yaya me kake nufi da f
ad'ar haka ?ina nufin yanzu shukura nike so kuma ita zan aura "ya salam yaushe wannan alamarin ya faru ?amman ko akan hanyarmu ta zuwa nan babu wannan tsarin a zuciyarka ? maganar maryama kake tayi babu tsarin auren wata shukura arayuwarka "to yanzu na ca
nza raayina ita nake so
kuma ita zan aura " a kan me ma zan auri wannan yarinyar? ya fad'a yana nuna maryama da babban yatsan hannunsa ."
"kausar ta rikice ta gigice ta waiga ta kalli maryama dake tsaye shiru tana ciza lips dinta na kasa "haba yay
a me yasa zakayi haka ?me yasa zaka sa'ba alkwarin da kayiwa mumy ?me yasa ka furtawa maryama cewar kana sonta zaka aureta yanzu kuma kazo da wata magana da hankali bazai d'auka ba "why why !!? yaya dan allah karkayi haka,ka dawo haiyacinka karka yiwa mary
ama haka tayi maganar cike da tashin hankali idanunta na kawo ruwan hawaye ."
"Duk yanzu na daina jin komai akanta sai dai ko a cikin masu mana aiki a gidanmu zan bawa wani shawarar ya auri wannan yarinya,amman yanzu sai shukura itace zabina a hali
n yanzu ma na kagauta na d'auketa daga wannan gidan dan ta fi karfin zamansa ita din ta dabance acikin zuciyata Ina kallonta ina jin farinciki araina "
hawaye dake makale acikin idanunta maryama suka zubo akan kuncin tayi sauri tasa hannunta t
a goge yayinda zuciyar shukura tayi mata sanyi ta qara tabbatarwa kanta aikinsu yayi tasiri akanshi ta d'auko ruwan lemu ta tsiyaya a cup ta mikawa yusif tana cewa "ungo sha kaji sanyi aranka "yasa hannu ya kar'ba yana sakar mata murmushi cikin tsanani
n tashin hankali kausar tace "karka sa'ba alkwarin daka d'auka ,da maryama kawai kafi dacewa ba da wata shukura ba ka bud'e idanunka da kyau please ."
cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa maryama tace "kausar karki d'aga hankalinki dan bay
a cikin hankalinsa da natsuwarsa hasalima bazai ta'ba fahimtarki ba a halin yanzu ,kiyiwa danuwanki addua dani da shukura duk abu d'aya ne bazan ta'ba bakinciki dan yusif ya canza ni da shukura ba fatana allah ya basu zaman lafiya tana cikin fad'ar haka
taji an fasa kuka abayanta mai kukan tana fadin" lahaula wala kuwwata inna lillahi wa inna ilahi rajiun wannan wani irin massefa ne haka ?
Duk suka juya umma suka gani tsaye cikin matsanancin tashin hankali "Shukura me maryama tayi miki kike shiga
rayuwarta ?amman Kisani allah baya bacci kuma zai saka mata da kyakkyawan sakayya Ke kuma zaki ga muguwar sakayya dake da uwarki "idanu kawai yusif ya zuba mata ya kasa cewa komai "kiyi mata na malam yahuza ta hakura ta bar miki shi yanzu kuma yusif din ki
ke so ?".
"umma gashi nan ki tambayesa bani nace ina sonshi ba shine da kanshi ya canza dani " yi min shiru munafukar allah daga Ke har uwarki zaku girba abinda kuka shauka ,da izinin allah sai maryama ta samu wanda yafi yusif komai kausar ta bukaci
umma tayi mata qarin bayani akan mlm yahuza batare da 'bata lokaci ba ta zayyane mata komai ."
"uhmm lallai maryam kina cikin tashin hankali allah ya fitar dake kawai zan iya cewa sannan ta cire wayarta daga cikin fost dinta ta kar6i mukullin mota da
ga hannun yusif ta fice waje tana neman layin mumy yusif ya cigaba da yin shiru maryama ta juya jiki a sanyaye ta bar d'akin tana goge hawaye haka zalika umma kasa cigaba da tsayuwa tayi zuciyarta na tafarfasa ta shige d'akanta tana kuka ."
yaya
sadam dake tsaye yana waya ya hango fitowar maryama tana tafiya tana goge hawaye ya bita da kallo Kamar ya tsaidaita yaji damuwarta sai kuma ya rabu daita da zumar zai nemeta daga baya ya cigaba da wayar da yake cikin haka kiran umma ya shigo wayarsa d
aman what's app call yake ."ya katse kiran domin ya d'auki kiran ummah kiran ya katse ya lalubo qaramar wayarsa yayi mamakin ganin missed call dinta dayawa ashe a silet yake "
ya kirata dan baya son ya shiga sai ya gama wayar da yake ,tana d'auka ya
ji muryarta can qasa tana kiran sunansa ya amsa yana tambayarta "lafiya ummah naji muryarki haka ?tace sadam kana ina ne ?ina cikin gida " tace ka shigo yanzu yanzu "okay! kawai ya fad'a ya soma tafiya cikin sauri ya shigo d'akinta."ya garasa inda take z
aune yana cewa "lafiya umma meke damunki kamar ma kinyi kuka ?."
wani sabon kukan ta fashe masa dashi tana zayyane masa abinda ya faru yace "ikon allah anya kuwa lafiya ?ina fa lafiya sadam kai ma kasan ba lafiya ba ,"yanzu dai sai a kira abba aji me
zai ce ,ai wad'an nan mutanen abun nasu babu imani ai bazasu bar iyayensa ma haka ba duk abinda zasuyi dan su juyar da hankularsu zasuyi ."
jikin yaya sadam yayi sanyi ya kasa cigaba da magana "wallahi da ina da inda zan kai maryama ta cigaba da ray
uwarta da nayi dan ina son taji dadi, maryama tasha wahala a hannun mutanen gidan nan sam sam basa son ganin cigabanta .""Kiyi hakuri umma komai zai wace babu abinda yafi karfin addua maryama malama ce nasan zatayi addua ."ban ta'ba shiga tashin hankali i
rin na yau ba domin har ga allah naso auren maryama da yusif amman da izinin allah bazasu ci bulus
ba duk abinda sukai mata bazai tafi a banza ba sai allah yayi mana maganinsa ."
bayan fitarsu maryama yusif ya tattara hankalinsa kacokan akan shukur
a ita kuma sai faman zuba masa surutu take ,acikin zuciyarsa baya jin dadin hirarta amman kuma zahiri abun ba haka bane murmushi kawai yake sakar mata yana biye mata ."karfe biyu daidai suka fito tare da shukura sai ga baba gali ya shigo ."yana ganin yusi
f tare da shukura ya washe hakora yana cewa "a'a yusif ashe dai kazo?yusif ya gaishesa , baba gali ya amsa yana tmbyrsa "ina ita maryama take dana ganka da shukura ?yusif ya d'an tsotsa keyarsa yace "yanzu ta wuce tana kuka wai dan nace shukurace zabina
ita zan aura "shukura kuma yusif ?yayi mgnr Kmr bai san komai ba "kwarai kuwa baba ita zan aura dan haka da zarar na koma gida zan sheidawa dady da mumy agaugauta azo a nemar min aurenta ta zama mallakina ".
"Ikon Allah haka kuma abun ya kasance ?k
ai kuwa yusif me yasa zakayi haka?" idan wani abu tayi maka sai ka sanar ayi mata magana bawai ka canzata da shukura ba ya fad'a haka a fili amman a bad'ani murna yayi yace abu yayi kyau aikin salama yayi tasiri daman yasan zata iya fiyye da hakan muddin
akan biyan buqatarta ne "babu laifin da ta min kawai dai bana sonta ne yanzu shukura zan aura "to to shikenan allah yayi maka albarka Allah yasa ayi damu ."
Yasuf ya amsa da "ameen !ya tura hannunsa cikin aljihu ya ciro bandir din yan dubu ya mika
wa baba gali "ga wannan baba "kai yusif har da wata hidima ai da ka barshi ni murnar auren shukura ma da zakayi ya wadatar dani sukai sallama da baba gali ya wucesu yana murna yasuf ya kira kausar tana dauka yace "Ke kina ina ne ?ina tare da maryama ne
" ta bashi amsa da haka "to ni zan wuce idan kin shirya ki fito mu wuce idan kuma na wuce ne na barki to ?ok minti biyu kawai na baki tare da maryama suka fito tana kwantar mata da hankali "
kausar kenan karki wani damu dani fa idan da sabo maryama
ta rigada ta saba kawai Kiyi wa dan'uwanki addua in sha allahu nima zan tayaku yi masa addua ki gaishe min da mum kice ina matukar qaunarta "tana gama fad'ar haka ta juya ta soma taku a natse kausar ta bita da kallo hawaye na zubo mata ."tunda maryama ta
juya hawaye ke turereniyar zubo mata qirjinta banda bugawa babu abinda yake ta kasa shiga bangarensu ta wuce bayan d'akinsu tana kuka tun daga kasan zuciyarta " ko kallon shukura kausar batayi ba ta fice daga gidan cike da tausayin maryama suka wuce ."
alhamdulillah aunty salma ta furta cike da yalwataccen farinciki wannan magana itace mafi dadi acikin zuciyata "wallahi mama kin gama min komai arayuwata kinga yadda ya rikice yace ma nan kusa zaa daura auren "haba wa ai ni din bata wasa bace ai mudd
in baku auru ba to wallahi babu mai zuwa ya kwashe wannan banzar yarinyar.""baba gali yace "ai baki ta'ba faranta min rai ba kamar yau na dauka fa abun bazai yuwu ba ashe shi yafi komai sauki a wajenki dan allah kisa ayi aikin da zaayi auren kamar yadda ya
fad'a "kai dai ka zuba ido kawai kayi kallo wannan auren kamar anyi an gama ."
"Kinga bari na kira fati na sheida mata ta soma shirinta "ya fad'a yana lalubo wayarsa "wani shiri kuma gareta ?aunty salma ta tambayesa "ai muktar dinta ke mutuwar son ma
ryama tun kwanaki dana je gidanta take sheida min nace ta d'an jinkirta muga me zai faru kinga yanzu dama ta samu",lallai kam dama ta samu daman shine daidai da aurenta" aunty salma ta fad'a tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya zaa qare auren dan gi
ya " kai salama baki da dad'i wallahi bakaji dadin da naji ba ai nan duniya bana qaunar maryama yarinyar kamar aljana ga kyau ga shiga rai suje su karata da muktar, shi din ma bazata auresa ba sai ya'yana sun bar gidan nan ."
Cike da murna da
farinciki baba gali ya kira aunty fati ya sheida mata komai ai kuwa tayi murna dan muktar din ma ya dameta kullum bashi da magana sai na maryama hatta shaye shayen da yake yace zai daina muddin zaa bashi aurenta" da kyar maryama taja kafafunta ta shigo pa
rlour'nsu tana mai danne damuwarta sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana d'an cikin damuwa aunty ta dubeta tace "Kuna fita aunty fati ta kira waya wai kizo gobe da safe tana son ganinki "to !kawai maryama ta fad'a ta shige d'akinta dan bata son tay
i doguwar hirar da har zai sã mahaifiyarta ta fahimci wani abu duk da tasan dan dole tasani amman ba da wuri haka ba "safa da marwa ta shiga yi acikin d'akin tare da cure hannuwanta waje d'aya" tsawon shekaru aunty salma na bibiyar rayuwarta ."
"laif
in me tayi mata ? me ta tare mata? idan wani laifi tayi mata ta fad'a mata ta nemi yafiyarta ta barta ta huta "? wasu hawaye masu ciwo suka gangaro mata a yanzu ba kanta kad'ai take tausayawa ba har da mahaifiyar yusif da yaruwarsa dan ita tsakaninsu das
u aunty salma da baba gali da ya'yanta allah ya isa ne bazata ta'ba yafe masu ba ,domin cirewa kanta damuwa Kan kujerar zanenta ta nufa ta zauna ta zaro farar takarda ta ajiye agabanta ta d'auki pencil ta tura cikin bakinta ta fara tunanin me zata zana ?"
.
Babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai fuskar kausar murmushi mai hade da damuwa ya bayyana akan fuskarta "kausar zan zana domin dai nasan shikenan ni da ita kuma sai wani ikon allah ."ahankali ta soma bada shape din fuskarta tunda ta zauna bata
tashi ba sallah laasar né kawa ya tashita koda ta idar ma Kan aikinta ta koma ta cigaba ranar a d'akin maryama ta qarasa niyyinta da misalin karfe bakwai aunty ta shigo d'akin ta isketa tana gabatar da sallar magrib ."
Ta qarasa gaban table din k
ayan zanenta nan idanunta yaci karo da hoton kausar har da kalar kayan data zo dashi yau din nan aunty ta saki murmushin jin dadi tare da cewa "lallai princess an fad'a soyayya ko da yake yarinyar tana qaunarki ta qarasa mgnr adaidai lokacin da maryama
ta sallame ta mike jiki a sanyaye take kallon aunty dan wallahi sai take jin kamar bata kyauta mata ba tunda ta tabbatar kota fada mata kuka kawai zatayi tayi hakuri sannan ta kwantar mata da hankali "
"kinyi shiru kina kallo