Showing 36001 words to 39000 words out of 172989 words

Chapter 13 - MAR’ADAM’S COMPLETE

30 Aug 2026

52

sigarina

kafin na dawo gidan nan idan ba haka ba wallahi wallahi ki kuka da kanki “yana fita kamfani ya nufa .”

cikin hanzari suna isa ya fito.”kai tsaye ya d’auki hanyar comfrence room domin wata gagarumar matsala dake son kunno kai cikin kasuwancinsa ku

ma tunda ya sanarwa P.A dinsa yasan by this time shi kad’ai ake jira yana shiga ya iske kowa kamar yadda yayi expecting har ma da ammar da hisham cike da girmamawa manya ma’aikatan da dake zaune suka dinga gaishesa tare da qoqarin kashe wayoyinsu dan su

n san dokarsa idan yana magana baya son jin motsin kowa bare qarar waya ya mikawa ammar hannu batare da ya kalli inda hisham yake ba shima kuma bai kallesa ba .”ya samu waje ya zauna.”

sun dade suna tautaunawa da manyan ma’aikatansa domin kawowa ka

mfanisa cigaba ahankali P.A dinsa mustapha umar hassan dinsa ya mike ya kawo masa coffe karfe biyu daidai ya sallame kowa shima ya fito tare da ammar suka nufi massalacin dake cikin kamfani yana bawa direbansa umarni cikin harshen tsadadden turancinsa

su juya kan motoci fita zai yi da zarar ya fito .”Ina kuma zaka ?zanje naga

sweetheart dina “ya fad’a cike da jin fad’uwar gaban da bai san dalili ba”.

a natse suka qarasa wajen yin alwala suna magana kasa kasa ATA yace “share maganar hisham kai baka

san abinda yayi min ba muddin kaga mun dawo kamar da to naga auta kuma naga kwanciyar atare daita bayan sun idar da sallah ammar ya rigasa fitowa ya tsaya acikin wata runfa rungume da hannuwan sa a qirji yana jiran fitowar ata yana tsaye ya hango bay

an maryama idanunshi kyam akanta har sanda ATA ya qaraso ya tsaya kusa dashi yana cewa “me ya d’auki hankalinka da kayi concentre haka ?zubin halitta mai kyau nake kallo ”ya bashi amsa da haka kana ya cigaba da magana “ kalli can abokina ka gani tsayuwar

ta ma kawai abun burgewa ne .”

ATA yaja tsaki yana cewa “nonsense ! ba tsaki zaka já ba ka kalla ka gani kai kanka zaka fahimci abinda nake nufi, yarinyar da nake fada maka ce, ata da yayi niyyar kallonta ya fasa ya cigaba da kallon ammar fuskar tash

i nan babu wani annurin kirki sai dai bugun zuciyarsa ya qaru sosai fiyye da duk wani tunanin mai karatu ” maryama mai kyau !Ammar ya kira sunanta “saurin juyawa ATA yayi yanayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba, maryama kuwa juyowa tayi ahankali sanye cik

in kanki bautar kasa ta nade kanta da qaramin hijab kayan sun matukar yiwa jikinta kyau “ mr ammar ta hango tare da bayan wani tsaye .”

“Mai kyau qaraso mana mu gaisa “ tayi murmushi wanda yake qara tafiyar da imaninmu mutun “ahankali ta soma takowa

zuwa inda suke tsaye tana wata irin tafiya da mutane suke ganin tsabar yanga ce tayi mata yawa nan kuwa rashin kibar da bata dashi né ya janyo haka “kalleta abokina gashi tana nufomu zaka fi qare mata kallo sosai wallahi yriyar ta had’u” bazan kalleta ba t

unda ta had’u ka aureta mana ,duk kabi ka damu mutane Kmr wanda bai ta’ba ganin mace ba “bai fi sauran taku biyu ta karaso zuwa inda suke tsaye ba ATA ya soma d’aga kafafunsa bai tsaya akoina ba sai a inda motarsa take tun kafin ya qaraso masu tsaronsa sun

zagayesa .”

Murmushi kawai ammar yayi yana d’auke idanunsa daga kallon bayan ATA “mr ammar barka da rana ya fama da jamaa ?tayi mgn a natse cikin sanyayyar muryarta “na kusan sumewa da wannan murya fa “ maryama ta d’an zaro ido tana cewa “wace ni dan

allah ka rufa min asiri kar madam tasamu wannan labarin na shiga uku na “mu shi uku dai “ya fad’a had’e da murmushi, cikin marairaicewa tace “kaji ba ashe kaima tsoronta kake ji “yasa dariya adaidai lokacin da motocin ata suka fice yayinda ammar ya ciga

ba janta Kmr yadda ya saba .”

kai tsaye abdullahi estate ata yace a wuce dashi ana gama daidaita parking ya fito ya nufi gidan mami tana daga zaune taji ana yunkurin bude kofar ta tsaida idanunta akan kofar dan ko baa fad’a mata ba jikinta ya gama ba

ta d’an lelenta ne ke tunkarota “a natse ya turo kofar ya shigo kana ya maida kofar ya rufe akan mami idanunshi suka fara sauka bayan ta kallesa ta dauke idanunta akanshi zuwa wani gefe tana jijiga kafarta tayi tmkr bata ji dadin ganinsa ba alhalin kuwa wa

ni farinciki ne ya mamayeta domin tun da ta gansa tasan tayi winning yazo ban hakuri ne .”

Ahankali ya tako zuwa inda take zaune akan kujera wanda zuwa lokacin tunin ta runtse idanunta durkusawa yayi a gabanta yana sauke numfashi tare da d’auran hannu

wansa akan gwiwowinta “Kiyi hakuri sweetheart ki yafe min nasan ban kyauta miki ba ,ban san abinda yasa na aikata haka ga mahaifiyata ba wacce bani da kamarta ,duk duniya itace take dani nake daita.”nan da nan hawaye ya jike gashin idanun mami “yanzu zagin

wad’an da suka manyanta a zamaninku ya zama wani abun ado shiyasa kayi min son ranka kuma agaban matarka , me kake tunani idan ba maryam ka aura ba ? “kaga kenan ka siya min raini ne a wajenta ko kuma nuna mata kofar yi min abinda ta ga dama .”



sweet heart na aikata hakan ne abisa kuskure amman kiyi hakuri dan allah “ ta d’aura hannunta a saman nashi kawai batare da ta sake cewa komai ba tana jin tsananin qaunarsa .“Kiyi hakuri kiyi min addua sweetheart ko allah zai sa min son diyarki a zuciyata

ko kad’an ne , sweetheart har yanzu na kasa manta mafarkina ina tsananin sonta gashi bansan inda zan sameta ba sannan duk yadda naso na cireta araina na manta daita na kasa manta komai nata .”bugun zuciyarta, numfashinta fuskarta da kamshinta idanuwan

ta murmushinta hawayenta sautin numfashinta sweetheart bazan boye miki ba na sha saduwa daita acikin mafarkina .”

Mami ta tsura masa idanunta tana kallonsa “na fara shan sigari duk dan saboda ita haka zalika a qoqarin na manta daita ne na fara shan g

iya ina danne zuciyata akanta ,nayi iya yina domin na manta daita amman wallahi sweetheart abun yaki aiki har yanzu koina na juya ciwo nake ji acikin zuciyata “mami tayi shiru zuciyata cike da tsananin tunani abu daya ne yayi mata dadi acikin magangunsa

shine rokon adduarta na allah ya saka masa son mrym ko kad’an ne wannan abu ya sanyaya zuciyarta kuma daman tana wannna adduar .”

“Sweetheart nifa abun tausayi ne abun a tausayawa ne akwai ciwo mai zafi acikin qirjina bana buqatar tausayawar kowa

sai taki kece kawai zaki tausaya min domin kece kawai kika san ciwona kuma kece kawai kike sona tsakanin da allah.“mami ta

numfasa tana cewa “adamcy nah ina tsananin sonka da tausayinka kai ma ka sani ..”“na sani sweetheart amman akan yarinyar nan kin c

anza min koma nace kinfi sonta akaina,mami ta kallesa kawai “sweetheart ki janye maganarki akaina zan cigaba da rayuwa daita Kmr yadda kika bukata amman batu na samammarta farinciki babu shi domin ni kaina zuciyata baa cikin farinciki take ba dan haka d

an Allah ki janye magarki akaina .”

Ta girgiza kai alamun a’a “sweetheart kin janye dan idan nayi kuskure kin bin umarninki wani abu zai faru dani idan kuma wani abu ya sameni kece kike da asara sam ita ba asararta bace kina ji kuma kina gani zata ko

mawa wani ta bar miki d’anki da rayuwar daya tsinci kanshi .” muryarta a sanyaye tace “babu abinda zai sameka adamcy kuma Ina rokon Allah ya kawo maka saukin abinda Ke damunka "ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka .



“why sweetheart me yasa zaki min asarar hawayenki bayan kin min addua?”addua nafi bukata daga gareki kuma kinyi min na kuma gode Kiyi haquri don Allah ki daina kuka ni dai kin janye furucin ki akaina “na janye kai ma kuma kayi min alqawarin bazaka

takura rayuwar maryam ba .”dan allah ka barta tayi farinciki a gidanka wallahi bancin mutane zasu zageni da na raba aurenku kowa ya huta“

“sweetheart babu mai zaginki kuma da zaki min haka wallahi da naji dadi da samun kwanciyar hankali “uhmm adamcy ta

a girgiza masa kai “kayi hakuri kawai adamcy zan maka addua kamar yadda ka bukata ya sauke wani numfashi yana mikewa ya zauna gefenta ya zauna yana kiran sunanta .”

“sweetheart!”

“ina jinka adamcy “ina son zan qara aure“bazan hanaka qara aure ba adam

cy amman dan allah ka bari zuwa nan gaba kad’an dan bazan ta’ba yarda ka shigo da wata gidanka ba alhalin diyata bata da matsayin komai a wajenka “why sweetheart “?mu bar wannan maganar adamcy muyi wata dan bana son jinta for now shiru kawai yayi yana m

ai runtse idanunshi shi kad’ai yasan zafin da ciwon da zuciyarsa keyi .”

“Sweetheart cikin satin nan in sha allahu zan bar kasar nan zuwa holland “da sauri mami ta kallesa sam maganar bata mata dadi ba ,kuma tasan dan ya nisanta kanshi da maryam ne “zak

a bar kasar nan saboda maryam ko ?tayi maganar kamar zatayi kuka “ko d’aya sweetheart “saboda me zan yi tafiya saboda ita ?”kema kinsan tafiye tafiye yana cikin tsarin aikina” mami tayi shiru ya riko tafin hannunta cikin nashi “sweetheart!”ta sake kallon

sa “ki kwantar da hankalinki nifa banki na daina tafiya zuwa koina ba saboda ke “wa na ajiye a inda zani ?”

“Me zakaje yi a hallond?yayi shiru yana kallonta “naga duka yaushe maryam ta tare da zaka tsiro tafiya gsky nidai idan son raina ne ka bar tafiya

r nan ka wakilta wani ka d’an zauna da maryam “shikenan sweetheart “ya bata amsa da hakan cikin halin damuwa ya mike tsaye yana mata sallama murmushi ta sakar masa amman gida zaka wuce ko ? ya gyada mata kai kawai “to allah yayi maka albarka ka gaishe mi

n da maryam anjima manu direba zai kawo maku abinci “to !kawai ya fad’a a takaice sannan yasa kai ya fice daga parlour’n massalacin ya nufa domin gabatar da sallar laasar .”

Hisham zaune akan kujera yana waya da nuzla “eh har yanzu ina office , alla

h kuwa da gaske nike amman bari nayi sallar laasar na tura miki babu mamaki ma idan na tashi aiki zanzo na gaki kafin na wuce gida , sosai kuwa ya fad’a yana murmushi kmr yana gabanta ,ahankali yaji ana Knocking din kofar office dinsa amman ya share ya

ki bada umarni shigowa ya cigaba da waya da nuzlah har kusan mintuna shabiyar sannan yace wa nuzla “bari zan kiraki nan da minti biyar acan bangaren nuzla cike da shagwaba tace “a’a ban yarda ba “okay to shikenan zakiji komai da zanyi “yana gama fadar ha

ka ya bada umarni shigowa ga diyar aminin abbansa dake aiki akarkashinsa .”

Zakiya ta tura kofar office din ta shigo ahankali ta tsaya agabansa amman bai d’ago ya kalleta ba ya cigaba da wayar da yake .”a tsanake ta bude bakinta ta kira sunansa “hi

sha…yayi saurin d’aga mata hannu yana cewa alamun tayi shiru dan da yasan itace bazai bada umarnin shigowa ba “a’a abdull ne ya shigo akwai maganar da zamuyi dashi shiyasa nace ki bani minti biyar “okay naji da zarar na gama dashi zan kiraki ya katse kir

an sannan ya kalli zakiya yace “yaya akayi ?sai data numfasa kana tace “akwai matsala fa “me ya faru “ya budurwa zata zauna ta dinga tayar maka da hankali haka?” nifa abokiyar aikinka ce kuma kusan yaruwarka wacce ko matarka tasan da zamana bata ta’ba nu

na damuwarta ba sai wata can .”

“aa dakata zakiya banason haka matsayin nuzla dabam a wajena tana sama da kowacce mace a wajena ba wai wata bace kin fahimta ko ?“ kana nufin har matarka ?“eh bakiji nayi generalizing ba nace kowa , tafi kowace mace

dan haka bana had’a maganarta data kowa ki kyaleni ke bani ma abinda ya kawoki ki bar min office menene ma ya kawoki “

? ”mr Ibrahim yace ka tura masa idan ka gama “tô naji zaki iya wucewa please ya fad’a yana nuna mata kofar fita da yatsun hannunsa .”

Ta juya ranta a matukar bace yace “idan kina shiga harkata zan iya sallamarki aiki , akwai wata mace ne bayan nuzla acikin zuciyata da zaki zo kina wasu surutan banza ?tsaki yaja ya fara duba file din data ajiye agabansa .”tana fita

daga office din

hisham office din abdull ta shiga tana kiran sunansa “abdull !! “menene ?ya tmbyeta tare da barin abinda yake ya dago ya zuba mata ido “wai me abokinka ya taka akan wannan banzar yarinyar nuzla ne da zai iya ciwa kowa mutunci akanta wai me tafi sauran mat

a ne ?kaga irin wulakanci da yayi min yanzu saboda suna yin waya daita “kinsan me ?ta girgiza masa kai alamun tana jinsa “hakuri zakiyi zakiya dan wannan yarinyar itace muradin ransa dan ko matarsa baya sakewa daita akan wannan yarinyar kuma bata son yana

muamula da kowace mace “ai kuwa wallahi tayi kadan dan bata isa ta hanashi muamula da kowa ba .”

“Ita din me ? sannan akan me ?to sai dai idan a gidinta zai tare ko kuma ya cicibota ya dawo daita office dinsa inyaso duk abinda yake tana gani ko kuma t

a dinga binshi duk inda za shi .”yayi murmushi yace “ko dai kina kishi daita ne naga duk kin damu ?”“kishi ?meye tsakanina da hisham da zanyi kishi akanshi bayan aiki da kuma dangantar dad dinsa da nawa ?”kawai dai wallahi naji ina tausayin matarsa ne yari

nyar kirki ce ga hankali ga ladabi shine kawai nake tausaya mata saboda nasan duk lokacin daya auri wannan banzar yarinyar ina tausayawa rayuwar matarsa duk da nasan yarinyar nan bazata yarda ta auresa ba wata manufa gareta .”

“Me yasa kika fada haka

?ince guduwa tayi lokacin da zaayi aurensu dashi sannan yanzu ta dawo masa ai kasan akwai abinda take nufi dashi wallahi , wakilla haushi taji dan ya auri nana hauwa’u kawai ta dawo ta hanashi zaman lafiya da matarsa kuma tasan idan batayi amfani da karf

in soyayyar da yake mata ba bazata yi galaba akanshi ba shi kuma dake qaramar kwakwaluwa ce dashi yake wani biye mata yarinyar daya kamata yaci ubanta laada waje “.

Abdull ya sake yin murmushi wanda dagani na takaici ne “ kinsa me ? kije kawai Kiyi aikink

i zai fiyye miki amman hisham kam bai ji bai gani akan nuzla bancin nasan gidansu nuzla basa biye biye da ni kaina nace anyi masa wani abu ne “.

“gsky kam amman ni matarsa nake ji ka duba kaga ranar d muka je gidansa baka ga yanayinta ba kamar tana ji

n tsoronsa komai a dar dar take yi shi kuma ko kallon biyayyar da take masa baya yi sai ma wayar da yake da wannan banzar yarinyar ina ma ni ya samu da naci ubansu daga shi har ita “gsky nana hauwa’u bazata iya ba Ke dai zai fi kiyi abinda Ke gabanki sark

in shiga abinda babu ruwanta “kana ji ko abdull “dan allah Zakiya kije na gaji da mgnr hisham nayi masa mgn har na gaji idan zai canza ya canza idan bai zai canza ba tare dani allah zai wa hukunci ba daga haka bai sake cewa kala bata juya ta bar office d

in cike da takaici .”

Qarfe biyar daidai motocin ata suka shigo gidan yayinda maryam ke zaune a parlour’n kasa cikin tsananin tashin hankali tana waya da nana hauwa’u “wallahi sister duka fa kwanaki biyu ne kawai nayi acikin gidan nan amman ji nake tamk

r a makabarta nike zagi kuwa acikin kwanakin nan sai dai kawai nace Alhamdulillah ,shi kawai baya ganin abubuwan da yake min kuskure ne shi kawai kanshi ya sani eh ko jiya ya sha yanzu haka ma cikin matsala nike dan daren jiya na kwashe kwalin sigarin na

zubar a shara ashe da saura aciki kuma yace lallai sai na dawo masa da abunsa ,ni yanzu tashin hankalina na aika a siyo masa sigarin baa samo exactly irin wanda yake sha ba ….”

“Shiru tayi sakamakon turo kofar parlour’n da akayi idanunta data zub

awa kofar suka sauka akanshi sanda yake qoqarin takuwa ,sosai ya dauki hankalinta koda yaushe fuskarsa tashi a daure take kallo daya yayi mata ya janye idanunshi akanta “sannu da zuwa” ta fad’a a matukar tsorace tana qoqarin mikewa ta bar parlour’n tun k

afin ya soma cin ubanta , bai amsa ba yace “me na fad’a miki ?bana ce karki sake na dawo na ga wannan fuskar ba ? ya qara taku biyu taja baya da sauri “dan allah kayi hakuri ta fad’a cikin tsananin tashin hankali“.ina sigarina ?”

Mmn sudais

💗💗

💗

💗💗💗

MAR'ADAMS



💖💖💖💖

💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan

  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login