Showing 135001 words to 138000 words out of 172989 words

Chapter 46 - MAR’ADAM’S COMPLETE

30 Aug 2026

49

baka jin magana na kiraka yafi sau babu adadi wayarka akashe ,mai yasa baka jin magana “kiyi hakuri heartbeat wani abokina b

ello ne bashi da lafiya shine gabday nida sauran abokanmu mukaje dubasa to kuma babu wanda zai kwana awurinsa shine nida atiku muka tsaya” okay ! ta fad’a tana sakin fuska “gsky wannan abu ne mai kyau nasan dole zaka rama bacci da ganin idanunka bacci ba

i isheka ba, dan allah ka dinga kiyayewa karka daukowa mahaifiyarmu magana ka dai ga yanayinmu dan Allah ka rufa mana asiri karka bari abokai su koya maka shaye shaye ,domin shaye shaye shine abinda mutun zai yi ya gurbata rayuwarsa dan shi da samun kwa

nciyar hankali har abada “in sha allahu zan dinga kiyayewa amman fa yau ma acan zan kwana babu damuwa ai taimako ne amman ka kiyaye dan Allah ,ya shiga dakin mahaifiyarsu ta sake yin mika ta shiga dakinta .

Bai samu aunty a daki ba dan haka ya f

ito ya nufi kitchen adaidai bakin kofa suka hadu ya gaisheta male ki dafa min

indomi amman a soya” kai kuma daga ina haka amman ba gidan nan ka kwana ba ?ta fad’a tare da bin gefensa ta wuce tana rike da kular shiru yayi “a ina ka kwana ? uhmm aunty

laifina ne da ban fad’a miki ba dan ya fad’a min bazai samu damar kwana a gida ba “wai a wurin abokinsa bello zai kwana a hospital maryama ta bawa mahaifiyarsu amsa tana karba kular hannunta “wai mai yasa aunty bakya bari na miki aikin komai ne byn

na iya ?ai sai na sangarce naje gidan mijin na kasa yiwa mijina komai “ ai kina aiki kuma ma girki ai na safe kawai nake “babu wata matsala da zaki samu dan kin kware in dai wurin girki ne maryama tayi murmushi farinciki samu nasarar kare danuwanta d

a tayi “kai aunty banda yabo fa kar azo aji kunya ta fad’a tana ware idanunta “.

babu wani yabon kai ai gsky na fad’a bazanji kunya ba matukar akan girki ne kai dama komai ma “wannan gsky ne male muna alfahari dake ,nima ina alfahari daku yarana

shiru sukai gbdy har habib suna tunani maryama ta dubesu yau fa a lissafina sauran sati day’a a daura min aure gashi har yanzu aunty bakiyi maganar zuwa wajen yanuwanki damu ba “kai heartbeat kina son damun kanki akan wad’an nan mutanen idan mu bamuje

ba su me yasa bazasu zo nememu ba ?”kawai ki sharesu mu cigaba da rayuwarmu cikin qaddarar rayuwar iyayenmu tare da yiwa mahaifinmu addua ,muje muyi breakfast suka zauna kusan atare suka saka aunty a tsakiya sannan suka fara breakfast maryama na cin abi

nci taji shigowar sako wayarta ta dauka ta duba tare da yin shiru ta dafe goshinta da hannu daya ta shiga dogon tunani “ya’akayi naga kinyi shiru ina tunanin yadda zan bar gida ne na rigada na saba da danuwana ,muyi hira tare muci abinci tare muyi kuka

tare muyi dariya tare in fact komai ma “gara dai kiyi aurenki shine kwanciyar hankalinmu gbdy inji cewar habib maryam ta dungure masa kai” tana cewa “kenan bazakayi missing dina ba ?” zanyi mana ni ne ma zan fi kowa kewarki amman ya zanyi tunda aure za

kiyi kuma zamu dinga ganin juna a duk lokacin da muka so kinga ai banga abun damuwa ba zamuyi komai Kmr yadda muka saba ya fad’a yana kallonta komai dai menene zan fi jin kewarka sosai .”

“ karki damu heartbeat idan ma kikace mu tattara kayanmu mu d

awo gidanki mu zauna tare zamuyi tunda nasan yaya sadam ba mai damuwa bane inji cewar habib wani sako ne ya sake shigowa wayarta ta duba tana gama dubawa taja tsaki” yakayi princess ya kikayi tsaki “ wani kafanin ke son nayi aiki dasu na tura masu ya

nayin zane na tun da dadewa to basu tashi bukatata ba sai yanzu , at the same time ga wani sako daga ogun state wai suna son naje har kamfaninsu dake ogun state nayi masu zane , ni bama zanen bane damuwata ba yadda kmr yadda date din da zaa masu za

nen ya zamo date din daurin aurena bari kawai na tura masu bazan samu dama ba su kuma wad’an can zan tura masu sako nan da qarshen wata zan zo

na fara aiki dasu .“ fine daidai kenan amman zuwa ogun state din ma ai ba damuwa bane ta dubi habib taya zaka

ce ba damuwa bane ?Ko nace zanyi hankalina bazai kwanta ba ,”zaki iya zuwa Kiyi bayan an daura aure idan kin dawo sai ki cigaba da hidimar bikinki tunda abun kwana daya ne “ ni dai gsky ban yarda kije har ogun state ba aunty ta fad’a gara ki hakura id

an ba haka ba bazaki samu natsuwar hidamar yin biki ba daga yau hankalinki zai rabu gida biyu shiru sukai gbdy can maryama tace “ gsky kika fad’a “ni dai ina son kike ki fad’awa yaya sadam sai ya rakaki kuje tare “okay bari zan yi masa mgn muji me

ye raayinsa Kiyi masa mgn idan ya amince sai kuje tare .”

Bayan kwanaki uku

Tsaye yaya sadam yake a d’akinsa muryarsa can qasa qasa yana waya da nadiya “haba nadiya nasani nasan ban miki adalci ba amman kema Kinsan yadda nake mutuwar sonki ,soy

ayyar shekaru biyar fa ni kad’ai nasan me nake ji ajikina tabbas nasan laifina ne da ban shigo da maganarki da wuri ba har aka zartar da wannan hukunci ,No bazan iya cewa mahaifiyata haka ba . zan dai san abun yi ki kwantar min da hankalinki ki saurareni a

t anytime .a natse ya fito cikin jallabiya ruwan qasa kawai yaga maryama zaune ita kad’ai a falon .”sai daya zauna sannan suka kalli juna shi da maryam gano yanayin maryama kamar tana cikin damuwa ya matsota sosai har suna iya shakar numfashi juna dan a t

unaninsa ko taji wayarsa ne ahankali ya kamo yatsun hannunta wanda yasa taji wani irin zirrr a sansar jikinta nan da nan tayi qoqarin zare hannunta bai damu ba yace “lafiya na ganki haka ?daman magana nake son muyi “ina jikin me zaki fad’a min ?”amm amm

daman akan wani aiki ne daaka kirani nace na fad’a maka nan dai tayi masa bayanin komai ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta “kinji abinda naji kuwa ?wani irin aiki ne har ogun state kuma a ranar daurin aurenmu ?nan da nan jikin maryama ya kama rawa “kayi h

akuri bansan mgr zata bata maka rai ba na hakura ba sai naje ba na cigaba da aikina anan daman ba wai zasu d’auke bane aiki ne na lokaci zuwa lokaci kuma ba aikin kwana bane amman kayi hakuri karkayi fushi dani ta qarasa mgnr muryarta cike da rauni .”

ya kalleta cike da tausayinta sakamakon yadda take magana cikin sanyin murya da tsoro ,ita kanta a yadda take maganar tana jin babu dadi har cikin ranta “shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu me kike ganin zamuyi ?”ya tambayeta cikin sanyin rai “tô wai

idan ka amince sai muje tare da kai ,idan kuma baka amince ba wallahi babu komai na hakura allah ya zaba min abinda yafi zama alkhairi murmushi ya sakar mata yace “shikenan karki damu amaryata zamuje tare ai ni yanzu duk abinda kike so ina so ko bangon

duniya kika ce zamuje tare allah ya nuna mana ranar nan da nan murmushi ya bayyana

a fuskarta “amman naji dadin amincewarka wallahi baka ta’ba sakani farinciki irin na yau ba na gode sosai allah ya jikan iyayenmu Allah yasa suna aljanna Allah ya saka maka

da alkhairi Allah yaja da kwanan ummah ,Allah ya bamu zaman lafiya a arayuwar aurenmu “Ameen Ameen ya Allah Allah ya nuna min kin haifa min yara masu yawa tasa hannu tana rufe fuskarta nan suka cigaba hirarsu.”

Ranar lahadi 14 ga watan October shekar

a ta dubu biyu da bakwai aka daura auren maryama da yayanta sadam .ana gama daurin aure suka fara shirin tafiya ogun state wanda kusan yaya sadam ne yayita matsa mata ta d’auko kayan aikinta tare suka shiga wajen ummah lokacin tana tare da yan’uwanta dana

mijinta tayi masu fatan alkhairi fuskarta dauke da farinciki maryama ta zama mallakinta gabdaya lokacin da zasu wuce aunty hassna tace “yanzu dan lalacewa aunty har da murna kike tun baaje koina ba an mallake miki d’a “cak maryama ta tsaya cike da sanyin

jiki “me zanyi hassana matarsa ce kuma ya amince tunda ya amince meye nawa aciki ?kunga kuyi maza ku kama hanya Allah ya tsare min ku suka sa kai zasu fice har sun kai bakin kofa umma tace “sadam ya juyo daga inda yake “ka kular min da maryama da kyau ,A

llah ya tsare hanya “to ni ummah bazakice ta kular miki dani ba ?tayi murmushi shikenan “maryama ki kular min dashi Allah yayi maku albarka suka ce “ameen suka fito suka shiga mota suka d’auki hanyar ogun .”

Cikin sauri sauri ATA ya fito daga dayan b

edroom dinsa cikin wasu had’ad’den kanana kaya bakake ajikinsa ,ya  shiga dayan dakinsa wanda kusan abubuwansa masu mahimanci anan suke, yadda jikinsa ke fitar da kashin turarensa reed akoda yaushe haka dakin Ke dauke da kamshin turensa, cikin sauri ya

dauki farin glass dinsa   ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya dauki agogo baki ya daura a tsintsiyar hannunsa ya bude bedside  ya dauki  wallet dinsa ya tura cikin ajihunsa ya daura facing cup yayi mugun kyua ya fito sanyayyen kamshin tura

rensa na binsa cikin sauri yake taka step cikin . a zaune ya iske mami tana waya ya d’an tsaya yana kallonta dan ga dukkanin alamun da wannan yarinyar take waya gyaran murya yayi yana sham kamshi ta waigo tana dubansa “ina zuwa kuma ? wani aiki !ya bata a

msa atakaice yana had’e gira sama data kasa dan kar ma tayi masa mgnr mrym “naga yau weekend ce ?eh ogun state zani zan iya dawowa a yau watakilla kuma sai gobe dan aikin nada matukar mahimanci .”yana gama fad’ar haka ya nufi kofar fita .”

To adamcy

mami fatan nasara

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗

     MAR'ADAMS

    

💖💖💖💖

💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantas

hi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTub

e.

             Page 25

         Tafiyar awanni hud'u ta kawosu maryama ma'aikatan ATA dake jahar ogun state yaya sadam yayi  parking din motarsa acikin haraban ma'aikatan sannan suka fito atare yana gyara zaman farar shaddar jikinsa yayinda maryam

a ke qoqarin neman layin mr  segun kira d'aya mr segun ya d'aga sukai magana na second biyu sannan ta fuskanci yaya sadam fuskarta kwance da annurin  farinciki mara iyaka tace "kad'an yi hakuri yanzu za'a yi mana iso zuwa ciki " yaya sadam ya gyad'a mata k

ai kawai alamun babu komai yana sakar mata tsadaddaden  murmushinsa ,suka  tsaya suna magana kasa kasa kafin ayi masu iso .wani matashin saurayi ne ya sauko  sanye da bakaken kaya ya shigar dasu ciki .

a wani dogo office aka shigar dasu wanda gabad'aya ns

a glass ne dan ana iya hango duk wanda yake ciki ,basu d'auki cikakken mintuna goma ba mr segun ya shigo yana tmbyr saurayin daya shigo da

su maryama "niyi ina bakuwar  daka shigo daita ?

"sir itace  a gabanka zaune”  mr segun ya d'an ware idanunshi ak

an maryama dake zaune yana mata barka da zuwa yana mai sake  masu iso  zuwa wani office din dabam wanda daga shi sai wanda ATA yake cikin zaune zaman jiran qarasowarta  .

   

     "kusa da maryama yaya sadam ya samu waje ya zauna kamar zai mata numfas

hi "madam ya hanya ?"

mr segun ya tambayeta cike da kulawa yana kallonta "alhamd sir tunda gamu mun samu mun qaraso lfy amman fa  da kyar dan hanyar nan taku bata da kyau tafiyar da ya kamata ace one to two hour's ne ya kawomu shine ya d'aukemu har four h

ours

amman alhamdulillah "wannan gsky ne mutane na yawon complain akan hanyar nan tamu amman dai  alhamd tunda kun qaraso lafiya tun  mai gida bai gaji da zaman  jiranki  ba dan awaninsa biyu da qarasowa bari nasa akawo maku abun sha, idan kin gama wancan

office din dake kallonki zaki shiga kafin nan ma zaki same aciki "yana gama fad'ar haka ya fita da d'an sauri ya barsu zaune maryama ta zuba ma yaya sadam ido har sanda aka kawo masu abun sha ta d'auka ta tsiyaya masa a glass cup ta mika masa ."

ahankali

yasa hannu ya amsa cup din hannunta ya kur'bi kad'an yana mai lumshe idanunshi sannan ya ajiye cup din hannunsa yana dubanta a tsanake "ya naga duk kinyi wani iri ?"naji yace idan na gama na shiga  ni kuma nafi son mu shiga tare da kai banason na barka kai

kad'ai zaman jirana "

Gajiyayyun idanunshi ya ware sosai akanta kafin ahankali ya hadiye wani abu daya tsaya masa a makoshi sannan yace "karki manta aikinki  kika zo ,kuma kema Kinsan ke kad'ai zasu bukaci  gani banda ni  ?" duk da haka idan a son ra

ina ne mu shiga tare "ta fad'a tana mai tsareshi da narkakkun idanunta ." suna zaune wnn saurayin da yayi masu iso  ya  shigo yana cewa "madam ki shiga ke kad'ai mai gida yake jira "ok but dan allah ko zamu iya shiga mu biyu ?cike da jin haushin maganarta

yace "tare zakuyi aikin ne ?no ni kad'ai ce !to ke kad'ai ake buqatar gani aciki dan mai gida baya son hayaniya "ya qarasa maganar tare da ta'be baki sannan ya fice ya shige wani office ."

hankalin maryama ya tashi matuka dan har ga allah haka nan taji ba

ta son shiga ita kad'ai qarara damuw ta bayyana acikin kwayar idanunta da shi kad'ai yaya sadam yake iya gani har ya fahimci halin da take ciki ,ahankali yaya sadam ya tsiyaya mata drik ya miko  mata ta girgiza masa kai alamun bazata sha ba ,"why ?! ya tmb

yeta yana sake tsareta da idanunshi dafe goshinta tayi tana cewa "bana jin shan komai a yanzu ,tun daya ga haka yasan ko me zai yi 'bata lokacinsa  kawai zai yi dan bazata kar'ba ba, dan haka ya mike tsaye suka fito tare tana gabansa yana take mata baya ha

r suka fito dogon hanyar da zata kai su office din ATA wanda alokacin yana tsaye  acikin tangamemen office dinsa  ya hard'e  hannuwansa duka a faffad'an qirjinsa idanunsa kyam  akan maryama da yaya sadam ta cikin glass door ,har  ta fara taku domin qarasow

a zuwa  inda office dinsa yake yaga ta tsaya  ta koma baya kad'an tana magana da wani da bai san ko waye ba ,sai dai idanuwanta  yana kansa ,kwakwa luwarta na hasko mata fuskarsa daga nesa kamar tasan fuskar yayinda shi din ma  kallonta yake cikin shigarta

ta mutunci kamar ranar farko daya fara d'aura kwayar idanunshi akanta ."doguwar riga ce sanye ajikinta har qasa  mai dogon hannu  da qaramin hijab dinta mai zip a gaba,sai  nikaf kalar hijab din da take sanye dashi wanda iya kwayar idanunta kad'ai ake iy

a gani ,tsaki yaja da karfi fuskar nan tashi babu wani annurin kirki dan babu abinda ya tsana arayuwarsa kamar 'bata lokaci ,yana wasa da komai arayuwarsa amman baya ta'ba wasa da lokacinsa ,ita kuma

abinda ya fahimta kenan daga gareta  tana da matukar was

a da lokacinta da kuma damarta  ".

"ya kuma kika tsaya  madam bayan  an fad'a miki ke kad'ai mai gida yake jira ?"ta jiyo sautin muryar segun  daga bayansu ta juyo a natse idanunta kyam akan  yaya sadam sannan tace  "yanzu zan shiga na d'an tsaya mu

na magana da mijina ne "miji kuma alokacin aiki ? yayi mata tambayar da mamaki akan fuskarsa dan shi a tunaninsa bata da aure tunda ta amsa gayyatarsu a weekend mutumin daya gansu tare kuwa ya d'auka d'an rakiya ne ko kuma saurayinta ."a natse ta gyad'a ma

sa kai tana cewa "Eh mijina ne kuma yayana ne   ". ATA wanda yake tsaye yana ciza lip's dinsa da karfi  cikin zafin rai  bai san wainar da'ake toyawa ba amman haka nan yake jin matsanancin bugun zuciya da kuma 'bacin rai mara misaltuwa "any way kiyi sauri

ki shiga kiyi abinda ya kawoki dan mai gida baya wasa da lokacinsa ,akan lokacinsa zai iya aikata komai kafin ta bashi amsa  yaya sadam yayi murmushi ya matso kusa daita sosai tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihu wondonsa fuskarsa a sake  "karka damu

yanzu zata shiga  kuma zata maku abinda kuke so "ya fad'a masa haka sannan ya maida hankalinsa kan maryama  kamar zai mata numfashi"k'anwata kuma amaryata karki wani damu da jiran da zan miki ni kad'ai abinda  nake so dake ki  natsu sosai kiyi abinda ya ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login