Showing 15001 words to 18000 words out of 172989 words
ba ta fito hannunta rike da qaramin
cup ta durkusa gabansa ta mika masa tana kallon cikin kwayar idanunshi cike da tashin hankali sakamakon rashin sonta da take hangowa acikinsu ."
Yaki amsa ta kai hannunta ta kamo laulusan tafin hannunsa ta saka cup din ciki ,yaki amsa ya cigaba da k
allonta "kayi hakuri kasha zaka ji sauki zugin da zuciyarka take maka "na sani akwai zafi akwai radadi da ciwo sosai abaka wanda baka so ,ka sani ni nana hauwa'u bazan takura maka ba bazan hanaka abinda kake so ba ,idan ma ta kama ka auro nuzla ka had'amu
kana da damar yin haka bazan damu ba ."
Idan kuma bazaka iya had'amu ba zaka iya sakina ka zauna daita kad'ai na yarda na amince idan kuma zaka iya cigaba da zama dani shima na yarda na amince koda baza kayi komai na aure dani ba, abu daya kawai nak
e so daga gareka shine ka bani kwanciyar hankali." tsareta yayi da oly eye's dinsa masu firgitartata a yanzu , hakan yasa tayi saurin kawar da kanta gefe tana danne kukanta."
Bin jikinta da kallo yayi yana mamakin jin abinda ta fad'a ,hakan nan yaji t
ausayinta ya mamaye jinin jikinsa tana da matukar saukin kai sannan bata da yawon damuwa da fari ta tayi qoqarin tsaida mutuncinsa dana iyayensa har ma dana dangi gabdaya domin auresa, sannnan tayi qoqarin karesa a wajen mahaifiyarsa daya fita yanzu kuma t
ana tayasa murnar dawowar masoyiyarsa har ma da albishir din ya aurota "kai sakarai ka dawo cikin haiyacinka bata son kaga dole zata fad'a haka ,kai ba haka bane to me yasa taki fad'awa mumy komai bayan taji wayarka da zaka fita .?"
Wani zazzafan numf
ashi ya sauke yana cewa" idan ni kuma bana raayin aurenta fa? ya fad'a tare da amsar cup din hannunta yana sauke numfashi "bazai ma yuwu kace baka son aurenta ba wannan ma ba abinda hankali zai dauka bane nuzla fa zuciyarka ce ta fad'a tana qoqarin mikewa
tsaye zata juya taji ya hard'e mata kafafu nan da nan gbdy ta juyo ta zubo jikinsa a gigice take kallonsa duk da tasan shine ya hard'eta amman hakan nan ta tsinci kanta da bashi hakuri ."
"Ka..Ka... kayi haku... "shiiiii! ya fad'a yana kai cup din hannu
nsa ya ajiye akan table din dake gefensa ya tsura mata ido suna shakar numfashi juna yayinda ita kam tuni ta runtse idanunta dan bazata iya jurar kallon ba dan duk yadda take jin numfashinsa na saukar a fuska da wuyanta hakan bai sa ta bude idanunta ba ."
laulausan tafin hannunsa ya kai saitin wuyanta sakamakon zafin da yaji ajikinta yayi wani abu yaji ya tsarga masa da sauri itama ta bude idanunta suka tsurawa juna ido muryarsa a
rauni yace baki da lafiya ne ."?numfashi ta sauke da karfi sannan ta mik
e daga jikinsa ta zauan a gefensa tana cewa "lafiyata lau nima haka naji yanayin jikinkina ya sauya."
"Okay yanzu mu ajiye maganar wasa da gaske kin amince na auro nuza ?ta gyada masa kai alamun eh ! ya gyara zamansa yana kai cup din madara bakinsa "n
ima zan miki abinda kike so amman sai kin shawo min kan mumy ta amince na auri nuzla idan kika min haka zan baki duk wani kwanciyar hankalin da kike bukata daga gareni ".
shiru tayi tana tunanin kafin daga baya tace "dan wannna mai sauki ne zan mata m
agana kuma in sha allahu nasan mumy zata amince ."shiru Kawa yyi "gsky nana hauwa'u tana da kirki da hakuri dan kwata kwata bai ta'ba tsamanin zata amince ba tunda itama bata sonka ai dole ta amince zuciyarsa ta fda masa haka tsaki yaja domin sai ya sake t
sintar kanshi da jin haushi "muje ka kwanta ka huta dare nayi bai ce uffan ba ya mike ya nufi kofar d'akinsu itama tabi bayansa ."
Kai tsaye suna shiga d'akin ya fara zare rigar jikinsa bathroom ya shiga ita kuma ta kakkabe inda zata kwanta ta kwanta
tana kokuwa da numfashinta duk da bata son yaya hisham amman bazata so wa kanta kishiya acikin kwanakin da ko goma batayi a gidan miji ba ,hassalima bata tare agidanta ba zuciyarta banda rawa da bugawa babu abinda take wasu siraren hawaye suka gangaro mata
ta fara sheshekan kuka tana jin motsin fitowarsa tayi saurin danne kukanta tana share hawayenta ."
Numfashi ta dinga saukewa sama sama ya dawo gabanta ya tsaya daga shi sai 3 qauter dake jikinsa duk wani zati dake jikinsa mai daukar hankali ajikinsa
ya bayyana wani tsoro ne qarara ya bayyana akan fuskarta dama zuciyarta gbdy wanda yasata saurin runtse idanunta gam ji tayi ya kwanta jikinta har tana jin saukar numfashinsa ya kai hannuwansa ya d'an matsar daita "ki koma wajen baccinki sannan kukan me Ki
ke yi wa mutane ?"
"Ba kuka nake yi ba " ta fad'a muryarta na rawa "uhm shi wannna kuma ya sunansa?ya fad'a yana kwanciya "qoqari tayita ta danne kuka ya fuskanceta sosai "alokacin da numfashinta Ke sama da kasa ya kai hannu daidai qirjinta inda ya su
ka sauka akan dukiyar fulaninta wani abu yaji alokaci daya yadda numfashinta Ke sauka da kuma tsarga wa wani abu da yaji mai kama da shoucking "
"Kina jina zuciyarki tayi nauyi sosai da alamun akwai abinda Ke damunta "ta lumshe idanunta tana sauke numfa
shi kuma har lokacin bai dauke hannusa ba "na rashin son hisham ne ?ta
girgiza masa kai alamun a'a "to na meye to?bana komai bane "okay yanzu ki bude baki kiyi kuka mai sauti domin ki rage nauyin da zuciyarki tayi aiko kamar jira take ta bude zatayi kuka d
an har sautin muryarta ya soma fitowa taga ya zaro ido tare da bude bakinsa ba zato ba tsanani yaji saukar laulausan lip's dinta akan na nashi .."
"Tsura mata ido yayi batare daya sake cewa komai ba illa kwayar idanunshi daya zuba mata yana jin wani iri
n sauyi ajikinsa tmkr wanda ake jona masa wutar lantarki cikin lokaci kankani komai ya birkice masa bai san yadda akayi ba ya had'eta da jikinsa still bakinsu na manne cikin juna , sai fidda numfashi nana hauwa'u take cikin jin wata irin kunya sam bada wat
a manufa tayi hakan ba gudun abinda zai fad'a ne dan yanayin yadda ya zaro ido babu sauki zai iya yin komai ."
Da ba dan period din da nana hauwa'u take ba da babu abinda zai hana hisham saninta ya mace a daidai wannan lokacin wannan shine abinda ya h
ana komai faruwa amman murza kam ta sha gbdy ya manta wata kiyayya jin dadinsa kawai yake da jikinta ita kuwa babu abinda Ke fitowa daga cikin kwayar idanunta sai ruwan hawaye tare da mugun tsoronsa tana son hanashi abinda yake tare da sheida masa bafa ita
bace zabinsa amman tsoronsa ya hanata ."
"Yau ne kawai shima nice na jawo ta fadawa zuciyarta hakan, in sha allahu hakan bazai sake kasancewa ba ,ita dai bata jin wanzuwar tsanarsa ko kiyayyarsa acikin zuciyarta idan ya shirya yin rayuwar aure daita za
ta bashi dukkanin farinciki idan kuma zai cigaba da nuna tsanarta ne zata janye jikinta sosai hisham yazo hannu gashi babu damar aiwatar da komai lumshe idanunshi yayi tare da komawa gefe ya kwanta yana mayar da numfashi bai san meke damunsa adaidai lokaci
n ba domin kuwa idan yace yasani yayi karya ."
Bayan ta juya masa tana rufe rabin jikinta ya dan waiga ya kalli bayanta wanda hakan yasa shi jin wani irin ajikinsa gabansa ya dinga tashi tsurawa bayanta ido yayi shape dinta mai matukar kyau da d'aukar
hankali,duk da yasan jikinsa na da taushi amman sai yaji nata kamar yafi nashi soft kai everything ko dan bambamci halitta ne jikin ,nuzla ya tuno wanda yasa tunaninsa ya koma kanta itama fa masha allah tana da sura mai kyau da taushi uwa uba kuruciya dan
nana hauwa ta girmeta da kusan shekaru hudu zuwa biyar ya dauki kusan mintuna talatin a haka bai motsa daga inda yake ba yana kuma jiyo saukar numfashinta ,numfashi ya sauke ya canza hasken d'akin zuwa mara nauyi sannan ya zame ya kwanta ya d'an janyo gef
en bargon data rufa dashi ya rufe jikinsa ."
Washegari hisham ya bude ido bai ga nana hauwa'u ba ya kunna wutan dakin tare da kai idanunshi ya sauke akan agogon dake ajiye akan table it was 9:44tsaki yaja tsaki sannan ya mike ya shiga bathroom ,bath
tube ya shiga yayi wanka ya fito black boxcer da black singlet ya saka sannan ya daura kaya akai ya fito fuskarsa a hade ya gaishe da abbansa dake zaune rike da jarida sannan ya shiga dakin mumy domin ya gaisheta ko kallonsa batayi ba bare ta amsa sallamar
sa, ahankali ya qaraso har inda take zaune juyar da kanta gefe tayi alamun bata son ganinsa "momy Kiyi hakuri nana hauwa'u ma da kike fushi akanta bata damu ba ."
maganarsa ta sake bata haushi "mumy ina magana "a shake ta juyo ta kalleshi "maganarka bat
a da wani amfani agareni fitar min a daki kar na qara ganin ka shigo min daki sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba korosa tayi daga dakinta ." ya fito sami abban yana masa complain shima da farko abban bude masa wuta yayi amman ganin yana bashi hak'uri
da janyo masa ayoyi akan masu hakuri da yafiya ya hakura shima ya daura da yi masa nasihohi yana janyo masa ayoyi da hadisai akan irin tanadin da Allah yayiwa masu hakuri da biyayya ga iyaye ."
bayan ya gama ya riko hannunsa zuwa dakin da mumy take
ya mata nasiha sosai akan hakuri da yaya nan mumy tace "naji na hakura amman ka fad'a masa kar na sake ji ko ganin yaje wajen nuzla idan ba haka ba zaka sha mamakina zaka haddasa gabar da baa san ranar qaresa ba akan nana hauwa'u kuwa zan iya tsine maka "h
isham ya dan saci kallon mahaifiyarsa Kmr zai mata kuka "wai momy me yasa yanzu kike yin haka ne ?."abinda bakya yi da
"yanzu ka canza shiyasa nima na canza idan ka só abinda nike son zaka cigaba da ganina a yadda kasani sabanin haka kuwa matsaloli zam
uyita samu da kai sha sha mara hankali "Ke dai kiyi hakuri ki bar mgnrsa da nuzla raayinsa ne idan yana sonta ya qara daita tunda allah ya halasta masa ajiye mata sama da daya "a ina ?ba dai wannan yarinyar ba sai dai wata dabam kai watan ma ba dai ina ray
e ba mu iyayensa mu ishesa misali tunda muka haifesa ya taso mu biyu kawai ya gani ya koyi example daga garemu ".
Abba yayi murmushi yana cewa "wannan raayinmu ne ta yuwu shi kuma bashi da wannan raayin "mumy zatayi mgn abba yayi saurin dakatar daita
ta hanyar cewa "abar maganar haka yanzu dai ki sanya masa albarka tare da kyakkywar addu'a da kuma fatan alkhairi acikin rayuwarsa " mumy ta numfasa kana tayi Kmr yadda abba ya umarceta ,hisham sam bai ji dadin kalaman mumy ba ya tashi ya fito ransa a bace
ya shiga d'akin baccinsa ."
Nana hauwa'u na gyaran daki taji an shigo ta dan juyo ahankali domin ganin wanda ya shigo , yaya hisham ta gani a tsaye fuskarsa babu alamun fara'a ya sha kunu tamkar bai tab'a dariya ba,tana kallonsa ya qarasa inda dur
owar mirrow yake yana dube dube ta bar abinda take ta qaraso ina yake ta tsaya gabanta na wani irin bugawa da karfin gaske "me kake nema ?shiru yayi har sai data sake maimaitawa, fuskasa a hade yace "ai Kinsan abinda nake nema ki dauko ki bani "babu musu t
a nufi inda ta ajiye wayoyinsa guda biyu da wallet dinsa daman da zata goge saman durowar ne ta canza masu wajen ajiya ta dawo ta mika masa tana cewa "fatan ka tashi lfy?bai amsa ba ya fice daga cikin dakin yana jan tsaki tabi bayansa da kallo ."
lums
he idanunta tayi tana jin damuwa cike da sanyin jiki ta gama abinda take ta fito yana zaune a falo ."Kusa dashi taje ta zauna tana wasa da yatsun hannunta "abinci fa yayi ready ? a qalla ya kusa minti goma sannna yace "bana da raayin ci "tayi shiru ta rasa
me zata sake cewa" oh allah ban ta'ba tunanin zan yi irin wannan rayuwar ba ,sai yanzu take ganin gskyr maryam akan yayanta aure ba abu ne da zaka iya sadaukar da rayuwarka akanshi ba domin abune da mutuwa ce kawai take rabawa tashi yayi ya nufi wata kuje
rar yana dane dane a wayarsa ."
daren ranar da kuma wunin safiyar data waye duk a cikin k'unci nana hauwa'u tayisa har izuwa yanzu cin abinci kawai ke fito da'ita shima bisa takurawar mumy ce ."dan kar mumy tazo ta tarar daita a d'aki tana kuka bayi t
ake shiga taci kuka har ta godewa ubangiji, idanuwanta sunyi jajir kamar barkono, da dare ma da mumy tazo zata d'auketa domin kaita gidanta sai da mumy tayita rarrashinta dan ji take gara ta cigaba da zama dasu akan zamanta da yaya hisham mumy ta fito tana
bata kwarin gwiwa sai da abba ya sake masu wasu nasihohi masu ratsa zuciya da kuma gangar jiki sannan yaya hisham ya d'aukesu suka wuce direban mumy na biye dasu abaya domin shi zai dawo daita ."
Har suka isa gidan nasiha mumy take masu shi dai yaya
hishsm bashi da wani kuzari saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa amsarta dan bai jin zai iya mata irin son da yake wa nuzla yayinda nana hauwa'u itama jin momy kawai take amman har a zuciyarta tasan yaya hisham bazai bari su zauna lafiya ba sai 9 na dare sa
nnan direba ya dawo da momy ta barosu su kad'ai acikin makeken gidansu. d'akin take kallo a tsanake komai yayi mata kyau most especially parlour'n wanda aka qawata shi da kayan zamani masu kyau".
Karfe tara da minti shabiyar daidai wayarsa ta soma rin
ging ya d'auka ya duba, ita kuwa tunda wayar ta fara ringing ta
tattara gabad'aya hankalinta kacokan akanshi , bata san dalili ba taji wata irin muguwar faduwar gaba ,ta dan saci kallon inda yake a zaune a tun sanda suka shigo ,bata dauke kwayar idanunta a
kanshi ba har sanda ya dauka yana cewa "wallahi nuzla rigimarki tayi yawa dare fa yayi okay shikenan ganin nan zuwa yana gama wayar ya fice batare da yace mata komai ba ."
wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauke tana dafe qirjinta tare da fashewa
da kuka ,ahankali ta durkusa kasa ta cusa kanta cikin qafafunta tana kuka tare da kankame jikinta ,sai da tayi kuka mai isarta sannan ta mike ta shiga bayi wanka tai ta fito ta bude wordrobe dinta shiru tayi tana kallo babu abinda babu hatta kayayyakinta n
a gida an kawo mata ta
saka kayan bacci wondo dogo da riga mai long sleeve butter colour touch of brown ta saka hijab sannan tayi sallar shaf'i da witiri tayi addua akan Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi a tsakaninta da yaya hisham ."
sai d
ata rufe kofarta da key ta kashe fitilun dak'in tayi shirin kwanciya bacci , koda ya dawo ya tarar har tai bacci yana murda kofar d'akin yajita gam nan da nan yaji ranshi ya 'baci meye abun kulle kofa tsaki yaja ya juya ya shige d'akinsa ."
Washe gari
tana farkawa daga bacci tai sallah sannan ta fito ta wuce kitchen, had'adden breakfast ta had'a masu naji da gani bayan ta kammala sannan ta d'auka ta kai dining, d'akinta ta koma tai wanka ta shirya cikin doguwar rigar abaya bak'a mai ratsin ja tai rolli
ng kanta da mayafin abaya sannan ta saka takalmi silifas ja , ta feshe ilahirin jikinta da turare tayi kyau sosai abunka ga farar mace ta d'auki phone d'inta ta fito zuwa falo ."
tana fitowa shi kuma yana fitowa daga d'akinsa sanye da jallabiyya brow
n , cikin sakin fuska ta masa barka da kwana ,wani kallo yayi mata mai hade da harara sannan yaki amsa tsabar bakinciki "meye jiya zaki wani rufe daki ?tayi shiru "me kike tunani akaina ?"still dai shiru tayi masa tare da sunkuyar da kanta kasa "ko gidan n
an naki ko kuma da kudin wani naki aka gina shi ?shiru tayi tana nazarin maganarsa ,a wannan shirun datayi ta fahimci inda maganarsa ta dosa yana son ta'bo yayanta ne abinda bazata d'aukar masa ba kenan muddin baya son zaman tashin hankali daita ya tsaya i
ya kanta kar ya ta'bo mata wani nata ita dai zata jure komai akanta amman akansu bazata iya ba ."
Numfashi ta sauke tace "ga breakfast can akan dining idan ka tashi ci ".ta fada haka né dan kawo qarshen maganar sai dai bata kai ga k'arasa rufe bakinta b
a yayi saurin cewa "to baa
ci ina miki magana kina min maganar wani abinci d'an yunwa kika dauki ne ko me ?" yadda yayi maganar sai da ya gigitata "na fahimci haushin nuzla kike ji a zuciyarki "idan har fahimtata gsky ne wallahi kiyi maza ki cire a zuciyar
ki daman munafurci ne yasa kikace kin amince idan zan aureta na aureta well idan na tashi aurenta ba amincewarki nake nema ba ."
A natse ta durkushe a gabansa tana kuka "karka min mummunar fahimta bazan iya bacci ba matsawar na bar kofar a bude tunda ko
far shigowa falo a bude take amman kayi hakuri bazan sake ba maganar nuzla kuma wallahi babu ruwana ko mata goma zaka aura byn ita kana dama "saboda ga dan iska ba ?"ka rufa min asiri ba abinda nake nufi ba kenan yaja tsaki ya juya a fusace shifa ba lalla'
ba yake son tayi ba so yake