Showing 111001 words to 114000 words out of 172989 words
cikin yanayi na tashin hankali maryam ta sauke numfashi tana jin sabon tashin hankali na shigar
ta "abinda basu sani ba ai wannna had'uwar itace kusan ta biyar a tsakninsu dashi har bakin mota ta raka aunty shahida tana karfafa mata gwiwa ta bud'e mata gidan baya ta shiga ta zauna "allah ya tsare min aunty nah zaki shigo gobe né ?sosai kuwa zan z
o gobe ai idan ban zo ba wannan muskililin zai iya kiran likitansa kuma zai iya gano komai allah ya kai mu gobe aunty shahida ta wuce gida ta barsu duk da taso tayi magana da adam amman ganin yanayinsa akwai tsananin damuwa koma tace haushinta yake ji .
Acan d'akin kuwa a hankali ATA ya runtse idanunshi tare da motsa labbansa "princess you want to kill me ba ?kina son sonki ya kasheni ba ?duk tsananin soyayyarki ne ya hanani yiwa mahaifiyata biyayya why kika kasa bayyana min kanki a zahiri gashi kom
ai zanyi sai da tunaninki ".ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare ya tuna lokacin da yake saduwa da maryam karfin tunaninta ne yayi tasiri a zuciyarsa har mazakun tarsa ta mike if not da bazai iya aikata komai daita ba "nima ina sonka sosai
zuciyata da gangar jikina kai kad'ai suke jira saboda zuciyata da gangar jikina mallakinka ne har abada ,yaji sautin muryarta acikin dodon kunnensa suna masa kuwa ahankali ya bud'e idanunshi yana kallon d'akin .wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana fu
rta "why princess ?ina son na ji sautin muryarki a zahiri kullum sai dai naji a bad'ini ya fad'a da wata irin murya kamar tana tare dashi ya dade zaune har goshin asuba sannan ya zare hannunsa cikin na mami ya fito ya nufi d'akinsa kamar ya d'an kwanta ya
huta dan wani irin sara kanshi ke masa amman yasan ko ya kwanta bazai ta'ba iya runtsawa ba saboda halin da mahaifiyarsa take ciki ."
kai tsaye hanyar bathroom ya nufa ya tura kofar ahankali ya shiga domin tsarkake jikinsa bayan ya zare jallabiyarsa
wanka tsarki ya soma alokacin da ruwa ya fara sauka ajikinsa zuciyarsa ta fara hasko masa komai daya faru a awanin da suka gabata "sweet heart kinga irin matar da kika za'bawa rayuwata ko ?" Kin aura min mazinaciya ,kin aura min macen data gama zubar da m
utuncinta a waje “Ko adadin maza nawa ne suka kusanceta ?yayiwa kanshi tamabayr yana furta kalmar subhallah acikin zuciyarsa "a gaskiya sweetheart baki kyauta min ba ,shiyasa raina yaki amsarta zuciyata taki sonta, babu shakka wannan dabi'ar ce yasa zuci
yata ta qasa amsarta amatsayin mamata "nan da nan zuciyarsa ta fara tafarfasa yana jin tuttukin bakinciki sakama kon yadda yaji maryam akan gado "sweetheart kin sadaukar da rayuwarki akan mazinaciya batare da kinsani ba wani zazzafan numfashin ya fesar k
ana ya cigaba da wanka da wannan tunanin yayi wankan tsarki Ya gama ya d'auro alwala ya fito ya sauya wani jallabiaya mamadin ya kwanta ko ya zauna sai kawai ya tsinci zuciyarsa da són gabatar da nafila "gara ya koma zuwa ga ubanginsa ko zai fita daga cik
in maseefun da yake ciki na tsawon shekaru ."
Cike da tashin hankali maryam ta shiga d'akinta ta samu waje ta zauna tana duban mami "wani irin soyayya mami take mata haka ?ta furta a saman lip's dinta tasan mami na matuqar qaunarta amman bata ta'ba t
unanin zata aikata haka akanta ba ,kanta ta kifa a daidai hannun mami hawayenta na zuba "allah sarki mami kina sóna da yawa ,kina son cigabana ta kowani hanya kina nan kina shirya min yadda zanji dadi a gidan d'anki ni kuma mahaifiyata tana nan tana shir
ya yadda zan cutar da d'anki domin kuwa da magungunan da sukai masa sunyi tasiri sai abinda tace masa zai yi amman duk runtse duk wuya bazata ta'ba barin yaya adam ya juya wa mami baya ba idan sukai nasara akanshi sake kwantar da kanta tayi tana tunanin
irin kallon da ATA yake mata wanda ke d'auke da tambayoyi kuma tasan duk akan yadda ya sameta ne ."hakika maryam kinyi gaugau wa arayuwarki "ko a wani matsayi yaya adam zai dauketa fatanta allah yasa yau né cikin zai shiga dan kuwa idan ya shiga kafin y
au akwai kutirin bala'i a gidan ."
sosai tayi zurfi cikin tunani qarar wayarta ce ya dawo da ita daga tunanin da take ta yunkura ta mike da kyar ta d'aga tana duba screen din wayarta sunan mahaifiyarta ce ta kalli agogon wayarta tana mamaki kiran me
take mata adaidai wannna lokacin ? kamar bazata d'auka ba sai kuma ta kara wayar a kunneta ta shige bayinta tana magana qasa qasa ."ummah lafiya ?okay to shikenan amman karki aiko da komai sãi mami ta wuce “bayan ata ya idar da nafila ya zauna yana add
ua tare da neman zabin allah arayuwarsa ,wannan shine karo na farko da yayi wannna tunanin da kuma addua wa mahafiyarsa yana zaune har aka kira sallah asuba ya mike yayi alwala ya fita zuwa masallaci ya gabatar da sallah sannan ya dawo bai
shiga d'akinsa
ba ,ya shiga d'akin maryam domin duba mami wanda alokacin itama mrym tayi sallah tana kwnace abayan mami tsaki yaja tare da jan qafarta d'aya ."
firgigib ta bud'e idanunta ta mike zaune tana shafa idanunta bai tsaya wata wata ba yaja hannunta hany
ar waje yayi daita ,maryam wanda keta rokonsa ya barta a kusa da mami amman bai kulata ba yana kaiwa waje yayi fillinging daita ta zube qasa tana dubansa "yayinda shi kuma yake jifanta da wani mummunar kallo,"bai ce mata komai ba dan idan ma ya nuna mata
yaji ciwon rashin samunta a cikakkiyar budurwa zata iya cewa kishinta yake wanda shi kuma har ga allah ba kishinta yake ba, kawai yadda ta munafurci mahaifiyarsa ta nuna mata cewar ita din mutuniyar kirkice yafi damunsa "kiji abinda zan fad'a miki kar na
sake ganinki a kusa da mahaifiyata domin ita din mutun ce mai tsarki "hannuwanta duka ta d'aura bisa kanta tana kiran "wayyo allah na shiga uku dan ko bai fito fili yayi mata dalla dalla ba ta fahimcesa fiyye da haka "shiiiiii ! karki kuskura ki tasa mi
n uwa daga bacci idan ba haka ba wallahi kinji na ranste sai na d'agawa uwarki da ubanki hankali kin dai san halina, Kinsan abinda zan iya yi dan haka stay a way from my mum ."yana gama fad'ar haka ya juya ya koma d'akin ya zauna kusa da mami yana kallon
yadda take sauke numfashi normal ba kmar d'azu ba ."
Maryam kam komawa tayi Kan step ta zauna ta raku'be jikinta waje d'aya tana tunani yadda zatayi "wani hanya zanbi ni maryam ya fahimci shine mutum na farko da ya fara sanina ya mace ?"babu wata h
anya tunda rashin hakurinki ya janyo kika mallaka masa kanki baya cikin haiyacinsa zuciyarta ta bata amsa da haka “amman kuma ai kina da sheida ?tabbas kina dashi sister itace sheidata ta d’an ji natsuwa kad’an amman duk da hk hankalinta ba’a kwance yak
e ba .a hankali ta mike tsaye ta fara tafiya kamar mara laka ajiki jikinta ba qaramin sanyi yayi ba ganin irin kallon zargin da yake mata duk yadda taso taji haushinsa ko kuma taga laifinsa zuciyarta ta kasa kar'bansa amatsayin mai laifi ko wanda zataji ha
ushi sai ma taga kamar ya fita gaskiya kuma kowaye dole irin kallon da zai mata kenan . idanunta taga suna ganin duhu akan kujera mai zaman mutun uku ta zube ta kwanta tana runtse idanunta ."
Karfe takwas saura maryam ta farka ta sauke idanunta akan
agogo bata sake yunkurin komawa bacci ba ta tsaya ta gyara ko'ina tare da shiga kitchen da yin abincin da zasu yi breakfast dashi sai dai har lokacin zuciyarta cikin dar dar take ta kasa jin sukuni dan hango katoton matsala wa rayuwarta take . Karfe go
ma gabdayansu ya'yan mami suka harllara a gidan kuma a dakin maryam .maryam din ce kad'ai bata cikinsu tana parlour’n qasa cikin jimami yayinda ATA ke gabana mami yana magana cikin tsananin damuwa "dan allah
sweetheart ki bari na fitar dake zuwa kasar Í
ndia a duba min lafiyarki murmushi iya baki mami tayi tana cewa "adamcy kenan baka son na mutu ko ?mami tayi masa tambayar idanunta na kanshi "wallahi banaso sweetheart!"Yayi maganar kamar zai yi kuka kallonsa kawai mami take without saying a word to him
sai dai wani irin tausayinsa ne ya mamayeta da sauran yanuwansa tabbas ta yarda kuma ta amince d'anta na mutuqar qaunarta damuwar dake yawo cikin rayuwarsa ne ya hanashi yi mata biyayya runtse idanunta tayi sai ga hawaye sharr yana sauka akan quncinta ".
hannunta ya riko gam cikin nashi yana cewa "why sweetheart?me yasa zaki zubar da hawayenki "ki daina kuka please idan wani abu kike so ki fad'a min am ready do anything for you sweetheart idan kuma tafiyar ne bazakiyi ba wallahi na hakura bazan takur
a miki ba amman dai bana son na rasaki, dan a yanzu idan kika mutu ba iya yan'uwana ba hatta mutane gari ma sai sun min gori akan rayuwata aunty shahida ta kallesa tasan sarai daita yake maganarsa ."an waye gari wai yar'uwata ce da kanta tamin gori sweet
heart a karon farko naji na tsani kaina duk da nasan tayi min né akan abinda nake miki ,nasan na sakaki cikin damuwa sweetheart ki yafe min lafifukan da nayi miki abaya da wanda zanyi a gaba nasan kina sona da wannna yarinyar ne yasa kema kike takura min
amman dan allah ki yafe min tsanar da nake fad'a miki inawa yarinyar a gabanki nasan tana sakaki cikin tsananin damuwa "wallahi sweetheart na sha fad'a miki Kiyi min addua ko allah zai saka min soyayyarta acikin zuciyata amman har yanzu shiru babu wata a
lama ta qaunarta "ya qarashe maganar muryarsa na rawa mami ta kallesa idanunta cike da ruwan hawaye tace "tabbas yawon fadar tsanar da kakewa maryam tana bata min rai amamn adamcy na yafe maka duniya da lahira burina allah ya had’a hankulanku waje d'aya
."
d’aya bayan daya yan'uwansa suka baro d’’akin zuwa parlour suka had'u gabadayansu suna hira har da maryam nan aunty shahida take basu labarin abinda ya faru "kai auntynmu dan allah da gaske ?wallahi ga maryam ku tambayeta "gaskiya auntynmu kin
gama da yayanmu "inji cewar zabiba maryam ta mike tana mai jin tsananin farinciki yadda yan'
uwanta kuma dangin mijinta suke matuqar qaunarta aunty khadija tace "ai gara da,aka gama dashi baki ga yayi laushi ba duk ya canza kala kamar bashi ba ,yaro sai
shegen taurin kai da fadin ran tsiya ai ni wallahi mami tayi min daidai ai da mun san d'an wannan shirin film din zai dawo dashi haiyacinsa da tunin an dade da wuce gurin aunty khadija ta qarasa maganar tana miqawa zabiba hannu suka tafa ."
“Allah dai ya
sa buqata ta biya." nana hauwa'u tayi murmushi tare da mikewa tana cewa “in sha allahu ta biya sai fatan alkhairi ta shiga kitchen inda maryam take qoqarin gama tuwon shinkafa da
miyar agushi .”
tun daga falo kamshin miyar ke shiga hancin nana hau
wa'u har sai da yasa yawunta tsinkewa "matar yaya wannan kamshi haka kamar zaa tafi gasar abinci "kai sister yau kuma tsiya zaki min "?”ke mu bar wannan maganar yaya had’uwarku da yaya ta kasance daren jiya ?"nan da nan yanayin maryam ya sauya idanunta
suka canza kala alamun zatai kuka "babu wani jin dadi sister yayanki wani kallo yake min wanda bazan iya fitowa na bayyana shi ba .nana hauwa'u ta dafa kafad’anta "karki wani daga hankalinki ko sarewa "me yasa zaki fad'i hka wallahi sister a matukar tso
race nake "ba gani ba meye abun tsoro ?nana hauwa ta fad'a cike da kulawa maryam bata san sanda ta rungumeta ajikinta ba tana share hawayenta ."shadaya da rabi daidai ata ya sauko ya fita daga gidan kuma alokacin maryam ta gama komai har da miya suna tsa
ye suna hira da nana hauwa’u inda nana hauwa’u take fad’a mata ciki gareta wani ihu mrym tayi ta rungumeta “gsky sister am very happy for you Allah ya hada miki komai da komai “kema sister kiyi ahankali fa dan baki sani ba ko ciki gareki mrym ta zaro ido
waje “sister ina jin tsoron abinda zai biyo baya “ina nufin an samu a daren jiya “allah yasa ai da ni kad’ai nasan irin farinciki da zanyi dan ko baya so zan rike abina bare ma da gudu zai kwace suka dariya basu gama rufe bakinsu ba kawai suka jiyo sauti
n muryar ATA cikin hargagi da tashin hankali .”
"ku yanzu daku zaa had'a baki ayi min haka "? a she yadda nake qaunarku ku ba haka kuke qaunata ba ?"daman na dade dasanin haka ,na gode allah ya saka da alkhairi ku tashi ku bar min gidana gabandayank
u bana son ganin fuskokinku” ya qarasa maganar adaidai lokacin da su maryam suka fito rike da hannun juna a bakin kitchen suka ja suka tsaya jikin maryam banda rawa babu abinda yake ".dan kwata kwata bata son ganinsa cikin tashin hankali
“Ya kalli inda
maryam suke tsaye ya nunata da yatsan hannunsa “kema bazan qara zama dake ba ki tattara duk abinda kikasan naki ne acikin gidan nan ki bar min gidana na sake ki saki u…”cike da tashin hankali aunty shahida tayi wani Irin qarasowa inda yake ta rufe masa
baki tana girgiza masa kai tare da nuna masa yatsanta d’aya alamun d’aya zai furta maryam kuwa tun kafin ta gama ji ta d’aura hannuwanta duka bisa kanta tare da shiga wani sabon tashi hankali"wani laifi suka masa haka ?ta jefawa wankakkiyar kwakwaluwarta
tambayar ."
inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda nana hauwa'u ta shiga furtawa tana maimatawa wanda yasa maryam ta kama tana yi bakinta na rawa wannan wace irin maseefa ce inji cewar aunty khadija dan gabadayansu babu wanda jikinsa bai d
’auki rawa ba maryam kuwa tashin hankalin da take ciki ya hanata kwakwaran motsi a inda take tsaye magana take son yi
koda kalmar hakuri ce garesa amman ta qasa furta komai numfashi kawai take ja ta bakinta tana fitarwa dashi da kyar .”
alamarin ATA ya gi
rmi tunanin yan'uwansa suna kallonsa ya buga ma aunty shahida razananniyar tsawa bayan ya cire hannunta “cikin tsananin tashin hankali da fad’uwar gaba take rokonsa "Adam ba’a saki cikin fushi idan kuma ya zama dole sai kayi kayi d’aya wani mugun kallo
yayi mata yana mai janye jikinsa daga nata ya sake maida kallonsa ga maryam “tsayuwar me kike yiwa mutane maza ki fara qoqarin bar min gidana ,kuma haka banason ganin kowacce acikinku wallahi na tsaneku sannan na cire kaina acikinku aunty khadija ma tayi
karfin halin qarasowa inda yake yayi saurin ja baya "bana son jin komai kawai kuje tunda kunfi son farincikin yarinyar nan akaina shekara nawa ina fama da zazzafar qaddara amman acikinku ko sau d'aya babu wacce ta zaunar dani ta fahimceni amman dan rashin
Imani irin naku daku aka had'a baki na kusanci wannan guntuwar yarinyar wallahi kun cuceni .””ai tun daga zuwa d’auko shahida ya kamata ace na fahimci akwai wani abu a qasa amman babu komai kuje na gode .”
mamaki da matsanancin tsoro suka kama mary
am “daman akan ya kusanceta ne ya zartar da wannan hukuncin akanta? ganin maryam bata da niyyar bar masa gidansa ya qarasa inda take ya kamo hannunta yana ja bata iya ce masa komai ba sai ma binsa da take har ya kai bakin kofa ya bud'e tare da hanka d’ata
waje ya maida kofar ya rufe da karfi wasu hawaye masu zafi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta tana gogewa wasu na sake biyowa kuncinta ."ATA na gama juyo idanunshi ya sauka akan mami tsaye ,cikin tsannain tashin hanakali take kallonsa muryata na
rawa tace "me ka aikata haka adamcy ?yanzu sweetheart har za’a had’a baki dake a cutar da rayuwata ?ban shirya yin rayuwata da wannan yarinyar ba saboda me zaa min karya da ciwonki ?numfashi mami ta sauke tana kallonsa "dan haka na saketa saki uku dan b
azan qara zama daita ba gabad’aya babu wanda bai furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ba har mami dan kam sai data dafe qirjinta dan wani luguden bugu yayi .”
nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud’ewa da rawar jiki ta riko hannunsa ya
fixge "har ke ban cireki acikinsu ba kuyi rayuwarku nayi tawa tunda bakwa sona nima na hakura daku har abada zabiba ta bud'e baki ta soma magana cike da in ina "ni ..ni dai yaya wallahi banda ni dan ba dani aka shirya komai ba hasalima yau din nan nasa
n komai aunty kahdija ta ta'bata alamun tayi shiru amman ta zame jikinta "dan allah yaya karka mana haka wallahi muna tsananin sonka muna qaunarka ta durkushe kasa tana jan gwiwowinta zuwa garesa ya tsaidaita ya juya ya haye sama a matukar fusace yake taka
step ."wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke atare "mami ta kallesu daya bayan tace "garin yaya kuka yi wannan kuskuren ?yaakayi kuka bari yasan komai ? tayi masu tambayar
ajere cikin tsananin tashin hankali,gbdynsu sukai shiru dan basu da bakin
magana ta sake sauke ajiyar zuciya "ina maryam take ? tana waje ! nana hauwa’u ta bata amsa cikin kuka kai tsaye kofar mami ta nufa ta bude inda taci karo da maryam durkushe tana zubar da hawayen mami ta kai hannunta ta d'ago ta ta