Showing 27001 words to 30000 words out of 172989 words
da tausayinta ba ,da sauri cikin rawar murya mrym tace"dan allah mami kiyi haquri ki daina masa kuka sai wani mummunar abu ya samesa maganarta ta katse mata kukanta saboda yadda taga tashiga tashin hankali ta zubawa fuskarta ido, kawar da kanta tayi
gefe tana qoqarin boye damuwarta dan hankalin mami ya kwanta kusan minti biyar kafin mami ta soma neman layin ata
Karfe goma daidai ya tashi wanka ya sake yi ya shirya cikin kananan kaya ya kunna wayoyinsa yana gama kunnawa kiran mami ya shigo.”
ji
ki a sanyaye ya dauka yaji tace "ni kuwa uwar data kawoka duniya ce ?wani irin tsinanne yaro ne kai ? cike da tantamar ba mahaifiyarsa bace ta kira numbersa,amman dan ta tabbatarwa kanshi sai ya cire wayar a kunnensa ya duba yaga tabbas sunanta ne sannan
ya kuma karawa a lokacin da muryarta Ke cigaba da fadin"wai ni kam sa'arka ce adamcy ? ‚lallai na sakar maka da yawa kaga gadon barcina,wallahi sai na dauki tsatstsauran mataki a kanka kamar yadda yayana suka bani shawara "jin sunan yayanta kawai data am
bata yasa shi dauke wayar daga kunnensa yana kiran sunan Allah “yau shi sweetheart ta kira da kalmar tsinuwa wani irin tsinanen yaro ne kai ?”ya sake maimaitawa kanshi cikin tsananin tashin hankali."
” tabbas akwai wani mummunar bala'i na daban dake s
on kunno kai cikin rayuwarsa ."
Yana tsaye cikin wannan tashin hankali kiran mami ya sake shigowa jiki a sanyaye ya dauka "kazo ka same yanzu yanzu ina gidan ina jiranka, sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba ,iska kawai iya fesarwa daga bakinsa ya kwa
shi wayoyinsa ya fito masu tsaronsa na ganin fitowarsa duk suka mike ya shiga mota suka fice a guje tare da jiniya cike da mutuwar jiki ya shigo parlour'n batare daya kalli inda maryam take ba dan gaba daya idanunshi na Kan mami né wacce kallo daya yayi ma
ta yasan tana cikin tsananin damuwa amman km zuciyarsa babu digon nadamar abinda ya aikata bare tausayin maryam sai ma tarin qiyayyarta data ninku acikin zuciyarsa ."
"sweetheart ta kasa ganewa tursasa zuciyarsa da take akan yarinyar Ke sake hura wutar
qiyayyarta acikin zuciyarsa ,ahankali ya samu waje ya zauan kusa da mami yana cewa "ina kwana sweetheart!dakata adamcy bana bukatar wata gaisuwarka" shiru yayi kawai yana kallonta yayinda yaji kanshi yana masa wani irin sara ,"ni zaka wa haka ko "? bai ce
mata komai ba
illa ya kalli inda maryam take zaune ya daka mata tsawa " ke tashi ki bar nan". ta mike da tsaye da sauri jikinta na rawa zata juya mami tace "Ke koma ki zauna " maryam ta girgiza wa mami kai hankalinta a tashe ."
"ni nace ki koma ki zau
an babu inda zaki , ai ya raina ne shiyasa tunda ina masa fad'a dole ya huce akanki "no sweetheart ni ba haka nake nufi ba but at least ai.. "na rantse da girman allah idan ka sake kwana a wani gida ba gidan nan inda matarka take ba babu ni babu kai har ab
ada kuma ko mutuwa nayi karkazo Kan gawata zan sheidawa ya'yana kowa ya sani "haba sweetheart Kiyi hakuri mana "nace kayi min laifi ne bare ka bani wani hakurin banza ?
"Ina baki hakuri ne dan kin janye maganrki "to bazan janye ,ba dai ka raina ni ba
to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga gana min azaba kana ganawa yarinyar mutane azaba, laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka? "wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda ya taba hadani daita ya qarasa maganar yana kallon ma
ryam"ke nace ki bar nan ko ?"ta tsaya tana kallon fuska mami ya sake mata alamar ta bar gun akaro na biyu a matukar fusace ya mike tsaye "Ke kina hauka ne ina mgn kina zaune ? ya buga mata tsawa "
"babu fa inda zata karki sake ki bar wajena matsawar b
ani nace ba "wai sweetheart me nene haka né ?ya fad'a yana sake kallon maryam dake qoqarin komawa ta zauna yace "wallahi kika cigaba da zama a wajen nan sai na canza miki kamani"maryam ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace "mami dan girman allah
kiyi hakuri ki barni na bar wajena" ai kafin mami ta sake cewa wani abu tuni maryam ta bace .”mami tayi shiru ta zuba tagumi tana dubansa kawai domin ta rasa me za tayi har kusan mintuna goma sannan yace "sweetheart kinyi shiru kina kallona "me zance tu
nda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba ,duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba ,”amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin baka cigaba da kwana a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai har abada kuma zan c
ireka acikin ya'yana sai dai ka nemi wata uwar amman bani zulai ba ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wa
nnan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a
tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 6
"Wai meye haka ne sweetheart ?"dan Allah ki daina fad'ar wannan maganar, karki manta nine fa d'anki wannan yarinyar kuma diyar wasu ce " me yasa zaki dinga fad'ar wad'an kal
aman akaina?me yasa zaki min wannan hukunci ?ya fad'a cikin tsananin 'bacin rai tunda wannan hukunci kika zartar akaina ai gara ki kasheni kawai ki huta nasan bani da gata da galihu just kill me sweetheart ko kuma ki janye wannan hukuncin naki ." yayi ma
ganar Kmr zai yi kuka ."
"Okay haka ma zaka fad'a ko ?ta daka masa tsawa yana qoqarin sake bude baki mami ta zuba masa lafiyayyen mari tana cewa "kaji magana kawai sannan kayi abinda nace kuma bazan janye kudirina ba wannan umarni ne na baka wallahi
idan ka kuskura ka sa'bawa umarnina zaka ji abinda yafi haka daga bakina."
Maryam dake tsaye akan step a tun sanda ta bar wajensu jin saukar mari yasa da sauri ta dafe qirjinta saboda tashin hankalin data tsinci kanta ciki ,ta qara taku biyu ida
nunta ya sauka akan mami da ata dake huci tmkr zakuna ,wani hawaye ne masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata ,kuka take sosai tana datasanin kiran mami datai a daren jiya ,dan tasan da bata kirata ba da hankalinta bai tsaidu akanta ba har tayi musu
diran makiya da sassafe ba ."
" wayyo allah nah ni maryam na shiga uku nah wannan duk laifina ne”. ta fad'a tana toshe bakinta da hannunwanta duka dan kar sautin kukanta ya bayyana ." cikin tsananin fushi ata yace "okay sweetheart bazan bi umarninki
akan wannan banzar yarinyar ba "ya fad'a atakaice yana furza da iska mai zafi daga bakinsa ."
"Naji bazaka bi umarnina ba amman kasani daga yau babu ni babu kai ka cigaba da rayuwarka kai kad'ai har duniya ta
nade " tana gama fad'ar haka ta nuf
i hanyar step tana kwallawa maryam kira da karfi "maryam !!! mrym ta qarasa saukowa da sauri ta tsaya cike da fad'uwar gaba tana duban mami "d'auko mayafinki muje "ina kuma mami ?tayi mata tambayar a matukar firgice ."
"gida mana dan bazan tafi
na barki acikin wannan gidan ba "kallon mami take cike da matsanamcin mamaki sannan ta waiga ta kalli ata dake tsaye taga yadda yake fidda numfashi har qirjinsa na sama da kasa wanda yake nuna tsananin tashin hankali".
cike da tashin hankali ta shiga
girgiza ma mami kai sannan ta soma magana "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni kiyi tafiyarki ni zan yi hakurin zama dashi haka ta fad'a voice dinta na rawa ".
"dan ubanki zaman me zaki cigaba dayi dashi yana wulakantaki ?maryam tayi narai
narai da idanunta tana damke hannuwanta cikin juna ,kin kuwa san babu wulakanci daya kai miji yaki kwana a gidan amaryarsa a daren farkonta zafi da ciwo ?"nasani mami dan ni kad'ai nasan halin damuwar dana kwana ciki jiya , tayi mgnr acikin zuciyarta tan
a qoqarin daidaita natsuwarta ."
"Ya wulakantanki ya tozartaki ya qunsa miki bakincikin da bazaki iya mantawa dashi ba har abada amman ki tsaya kina 'bata min lokacin" mrym ta girgiza mata kai tana mai share hawayenta "amman bake ya wulakanta ya tozar
ta ba ni yayiwa kuma na gode masa amman kisani bazan tafi na barki cikin wannan halin ba dan haka ki hau sama yanzu ki d'auko mayafinki muje an gama wannan auren". mami ta fad'a cikin tsanani 'bacin rai.”
"kiyi hakuri mami duk laifina ne dana kira
ki na d'aga miki hankali me yasa ma zan kiraki ? sannan me yasa zaki hukuntashi ? da kin barshi ni ki hukuntani mami akan abinda na aikata kina zaman zamanki na d'aga miki hankali " maryam ta fad'a hawaye na zubo mata ."you're very stupid so you're the o
ne caused all this problems ? amman dan munafurci kizo kinawa mutane kukan munafurci ."
" ina zaman lafiya da mahaifiyata aurenki ya shiga tsakanina daita sannan dan kin cika mahaukaciya ballagaza kika kirata kikace ban kwana gida ba ,dan ubanki ida
n na kwana a gidan uban me zan miki ? "ya fad'a a fusace ".?a matukar rikice tace "please am sorry I never know she wil act like this "ta fad'a hawaye na sake zubo mata, wani irin mugun kallo ya watsa mata sannan yay qoqarin qarasowa inda take mami na
gan
in haka tayi saurin taresa da hannunta dan ta lura baya cikin haiyacinsa "karka soma ta'ba min lafiyar yarinya mami ta fad'a muryarta na rawa bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba ".
"Yau sai na kashe yarinyar nan da uban daya haifeta ya fad'a cikin c
igaba da takowa cikin isa da 'bacin rai jin abinda ya fad'a yasa maryam rungume mami ta baya tana wani irin kuka tmkr qaramar yarinya "mami ki taimakeni dan girman allah "weetheart ki bani hanya naci ubanta na ganar daita kuskurenta wanda har abada bazat
a sake aikawata wani ba bare ni "ka shiga hankalinka “ita dai tashiga hankalinta “
“ adamcy banason abinda kake min dan babu laifinta ko d'aya idan hukunci ne ni dana mareka zaka hukunta."
"please sweetheart ki matsa dan babu abinda zai hanani ban
hukunta wannan yarinyar ba akanta fa sweetheart kika mareni “yana qoqarin kamo hannun maryam mami ta sake sauke masa wasu marukan ji kake tas tass !! har biyu ajere ."wannan karon kam ata daskarewa yayi awaje d'aya yana kallon mami cike da tsananin mam
aki abun yayi mugun girgiza shi "yau sweetheart dinsa ce tay masa mari har uku kuma duk akan wannan banzar yarinyar ".?
maryam kam fashewa tayi da wani sabon kuka ganin abinda mami ta sake aikatawa " matsawar ka ta'ba maryam ban yafe maka ba tana
gama fad'ar haka ta juya rike da hannun maryam sai dai abun mamaki mrym din taki biyota ta turje jikinta na kyamarrr , dole tasa mami ta tsaya ta juyo tare da zuba mata ido tana neman qarin bayani, amman mrym tayi shiru sai hawaye dake sauka akan kuncinta
"kina ganin irin wulakanci da yayi min amman da yake ke baki da zuciya zaki ki biyoni wato ke gaki mai ..."
kafin mami ta qarasa maganrta mrym ta zube kasa gabanta tana kuka tana bata hakuri .""Kiyi hakuri mami wallahi ba haka bane, ba kuma abinda k
ike nufi bane ,nayi nadama dan allah mami kiyi hakuri ki yafe masa ki daina fad'a masa kalamai haka marasa dadi ,kuma ni babu inda zan biki zan zauna a gidan mijina,da dad'i da babu zanyi hakuri dashi "tana gama fad'ar haka ta sunkuyar da kanta kasa gani
n irin kallon da mami take mata mami tayi shiru kawai tana kallonta gbdy taji kwarin gwaiwarta yayi kasa ."
Jin mami tayi shiru hankalin mrym yayi mugun tashi rawar da jikinta yake ya qaru ta d'ago kanta ahankali taga ita din mami take kallo har lokac
in muryarta a sanyaye tace "kiyi hakuri mami kece fa kike bani hakuri da kwarin gwiwar da har muka kawo matakin maaurata ,to me yasa akwana d'aya kawai da
nayi a gidansa zaki d'auki zafi akansa alhalin kin fi kowa sanin waye shi ."?
nan kuma jikin ma
mi yayi sanyi ta tsaya kawai tana cigaba kallon mrym , shi kuwa ata zuba masu ido kawai yayi yana jin zallar 'bacin rai na ratsashi yaji tsanar mrym ya sake qaruwa da mamaye duk wani sansar jikinsa "wallahi bancin mami dake tsakaninsu da shi kad'ai yasan
irin azabar da zai gana mata amman duk da haka bata tsira ba zai ganar daita Kuskurenta ,runtse idanushi yayi yana cizan lip's dinsa na kasa da karfi yayinda hawaye ke bin kuncin maryam , tsaki yaja sannan ya juya a fusace ya haye sama cikin tsananin fus
hi yake taka step ."
Yana shiga d'akin daya zamo nashi ne ya soma zariya aciki he's thinking of if someone else did what his mother did to him today da wallahi allah ne kadai zai rabasu amman sweetheart rayuwarsa ce yana matuqar qaunarta, yana son du
k wani abinda take so wajen had’in aurensa da wannan bazar yarinyar ne kawai raayinsu ya sha bam bam tsaki yayita ja tare dafe goshinsa dan wani irin sara kanshi ya cigaba da yi ."
"Maryam ta kamo hannun mami ta zaunar daita akan kujera sannan ta du
rkusa kasa gabanta "kiyi hakuri mami kema fa kinsan halinsa Kmr yadda kike cewa zai canza nima haka nasa araina wata rana idan allah ya taimakemu sai kiga ya canza, nayi miki alkwarin zan zauna dashi har tsawon rayuwata sannan kiyi min alkwarin bazaki sak
e kai hannunki fuskarsa ba sannan ki daina fad'ar kalamai marasa dadi akanshi nima kona kiraki karki saurareni akan kowacce matsala ki bani hakuri kamar yadda kike bawa sauran ya’yanki."
Mami ta qirgiza mata kai alamun bazata iya ba “please mami do t
he same thing to me “bafa zan zuba ido ba maryam ,dole nayi mgn idan ma baki fad’a min ba dole zan san komai “please!..”bafa zan zuba idanu yayi miki wulakanci daya ga dama ba domin Ke din amana ce a wajena kuma duk abinda yayi miki dole ne ya dameni ko b
akya adamcy ya aura ba dole ne nasa ido a gidansa idan naga zai cutar da ‘yar mutane bare ke da kika kasance jinina "duk da haka dai mami Kiyi min alkawarin bazaki sake damun rayuwarsa akaina ba mrym ta fad'a tana sakar mata murmushin dole wanda kana kall
o had'e yake da tarin damuwa.”
"Shikenan bazan sake ba “mami ta fad'a tana kukan tausayinta dana tilon d’anta data san haka auren zai kasance wallahi data hakura tun farko daya nuna baya so ."ahankali maryam ta
kai hannunta tana goge mata hawaye tan
a cewa "mami ki bar kuka .
zubar da hawayenki akanshi maseefa ne a gareshi "ta d'aga mata kai kawai dan batasan me zata ce ba dan kukan ne ya fiyye mata sauki akan mgnr da zatai " daga nan mrym ta cigaba da kwantar wa mami da hankali ."zuciyar mami tayi
sanyi ta sake amanna maryam itace mace d'aya da zata kular mata da rayuwar tilon d'anta."
murya a sanyaye mami tace "tashi kije ki kirashi yazo ya bani hakuri "maryam ta zaro ido tana kallon mami a matukar firgice "wallahi mami bazan iya ba he wil
beat me to the exetended sai kin koka min kina kallo fa if bancin kina nan da yanzu ba wannan labarin ake fad'a ba ."allah bazan ta'ba iya tunkarar sa ba kawai Kiyi hakuri ki yafe masa "mami am so much in love with your lovely son amman bani da wannan
kwarin gwiwa ." ta fad'a aranta hawaye na gangaro mata ."
hankali ta dora kanta akan cinyar mami tana zubar da hawaye ."tana matuqar sonshi and she don't want to loose him at all, she don't know what's happening to her brain, dan tana jin idan ya sa
keta ko idan mami ta raba auren zata iya mutuwa for real mami tace "kiyi hakuri mrym ki daina kuka nasan adamcy baya sonki shiyasa kikaga bana tuna duk wani halin da zai shiga nake yanke hukunci akanshi ta fad'a tana shafa kanta ."
"Ni kuma kinga b
ana son abinda kike masa " mrym ta fad'a a fili tana sheshekan kuka "baki so ?"mami ta tmbyeta ahankali tace "eh mami bana só ina jin ciwo a zuciyata sosai kinga sakamakon abinda kika yi yau ya qara d'aukar zafi dani tsanata ya sake qaruwa a zuciyarsa ,
mami ta sauke numfashi ,gbdy ta gama karantar maryam tana mugu mugun son adamcy ,ta kuma san muddin ya gano hk zaa qara samun matsala ne ."
"Nima baa son raina bane dan burina bai wuce na ganku tare cikin koshin lafiya da farinciki ba amman shi ada
mcy din ne zuma ne sai ancisa da wuta "haka zamuyi hakuri dashi muyita masa addua allah ya sausauta zuciyarsa ta fad'a tana sake kwantar da kanta a cinyar mami shiru parlour'n yayi baa jin motsin komai sai na saukar numfashinsu dana ac dake aiki sai kusa
n shabiyu mami ta mike tana jaddada mata tayi qoqarin ta shawo kansa yazo anjima bata hakuri ."ta qarasa mgnr tana dariyar tsokana ."
"Dan allah mami ki rufa min asiri ina ni ina tarar