Showing 153001 words to 156000 words out of 172989 words

Chapter 52 - MAR’ADAM’S COMPLETE

30 Aug 2026

40

.”ahankali ahankali take d’aga qafafuwanta har ta qaraso ta durkusa a daidai kafafun umma "umma ki daina kuka ."ta furt

a mata idanunta na kawo ruwan hawaye "umma ta d'ago idanuwanta  ta kalleta da tarin damuwa  sannan ta d'auke idanuwanta "umma nasan da wuya ki iya mantawa sadam  koni bazan iya mantawa da yaya sadam a rayuwata ba bare ke da kikayi silar zuwansa duniya amma

n dan girman allah umma kuka nan ya isa haka kar wani mummunar ciwo ya kamaki na shiga uku ,".

“ wallahi ummah ban san ina matukar son yaya sadam zuciyata ba  sai dana rasa shi zuciyata na cike da matsanancin soyayyarsa "nasani maryama allah ya jikan

sadam ke kuma Allah ya baki hakurin rashinsa  "ki daina furta hakan umma jikina na bani yaya sadam bai mutu ba tunda na ji ajikina bai mutu ba tabbas bai mutu ba zai dawo garemu ."umma tayi shiru tana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya a duk lokacin da t

aji maryam ta furta hakan ta Kan samu saukin zugin da zuciyarta keyi cike da matsanancin soyayya ta kamo kafad'an maryama ta d'agata tsaye bisa kafafunta ta rungumeta tsam ajikinta"maryama maganarki tana kwanatar min da hankali duk da nasan da wahala ace s

adam dina yana raye ."kusan minti goma suna rungume da juna kafin daga baya maryama ta zare jikinta ta tsurawa hoton yaya sadam  ido ."

A hankali ta kai hannu ta d'auki hoton ta koma kan gadon umma ta zauna tana cigaba da kallon hoton tana shafa fusk

arshi yayi matukar kyau sosai fuskarsa kwance da murmushi "umman kin tuna ranar daya d'auki hoton nan ?cewar maryama" na tuna ranar daurin auren mashkur abokinsa  ne ta fad'a tana zama kusa da maryama"yaya sadam ka dawo garemu karka  barmu zuciyar ni da um

ma na matukar qaunarka bazamu iya jurar rashinka ba dan allah ka dawo garemu ." shiru sukai gabadaya zuciyarsu cike da  tunani umma ta janyo akwatin kayansa ta fito da kayan sawarsa tana nikewa tana maidawa cikin akwatin ,maryama ta d'auki jeans dinsa ta r

ike tana kallo kafin ahankali ta motsa bakinta "karki damu umma zai dawo fa ".umma ta kalleta kawai dan ita tasan bazai dawo ba har abada mutumin da'aka binne da ransa ta yaya zaayi tunanin zai rayu har ya dawo ?"cike da sheshekar kuka tace "ya allah kabam

u hakuri rashin sadam domin zuciyoyinmu  sun gaza hakuri akansa maryama ta matso sosai ta kwanta ajikin umma cike da tsananin qauna "d'ana sadam mutumin kirki ne, d'ana sadam mai kyakkyawan zuciya ne ,d'ana sadam mai hakuri ne gashi ya tafi ya barni batare

da kowa nasa da zan kalla naji sanyi araina ba."

“shikenan na rasa mai sakani dariya na rasa mai kawar min da damuwa na rasa mai dibe min kewa."

ta qarasa maganar tana zubar da hawaye."maryam ta kai hannunta ta shiga gogewa umma hawaye tana cewa “ karki

damu umma zanyi miki duk abinda yaya sadam yake miki sannan kuma kisa aranki zai dawo garemu mu cigaba da yi miki komai tare "

"Zo zo!! ku  ga  wani abun mamaki Aunty salma ta jawo hannun baba gali da aunty hasanaa  zuwa bakin kofar d'akin umma, ka

lli ku gansu "wannan matar anyi shasha an kashe mata d'a amman dan shashanci ku kalli shirmen da take "ke yanzu wannan ne ya dameki ? baba gali  ya fad'a tare da juyawa ya samu waje ya tsaya suka biyosa suka tsya  kusa dashi suna  dubansa bakinsu  na son f

urta wani abu "salma ki  rabu dasu kawai  mu dai muyi yadda zata  dawo daidai kafin wannan yarinyar ta

gama takaba araba gado ,aunty salma ta saki murmushin jin dadi burinta zai cika "kai wallahi ina cikin farinciki saboda kaso  mai yawa zaka samu “sosai k

uwa dan kaso biyu zanci tunda ni nmj ne "ya qarasa maganar cikin tsananin farinciki wannan kuma haka ne bari kama gabanmu su kuma suje su qarata da kukansu hawaye ne yayi masu yawa" wallahi nima allah allah nake lokaci yayi araba abani kasona inji cewar au

nty hasana baba gali ya saki murmushi "ni Allah yasa a mallaka min kamfanin burodi gbdy aunty salma tasa dariya murna kmr su rungume juna a wajen ."baba gali da aunty salma suka fice suna dariya aunty Hasana ta shiga kitchen domin daurawa umma abinci dan

tun daaka nemi sadam aka rasa  kusan rabin yininta anan take yi ."

Umma ta kai hannu ta shafa sumar kan maryama  "allah yayiwa rayuwarki albarka ,allah ya qara mana hakuri, muyita hakuri da sannu allah zai mana sakayy.. “qarar wayar umma ce ta katse

ta maryama ta mike da sauri ta shiga duba inda wayar take "gashi can a karkashin pillow ta fad'a tare da d'auko wayar  ta mika mata cike da ladabi ta d'auka "assalamu alaikum, wallahi alhamdulillah mun godewa allah ya kunfan jiki Aa da kanki ai da kinyi z

amanki hjy ba sai kin wahalar da kanki ba to shikenan allah ya kawoki lafiya sukai sallama " umma waye zai zo ?granny ce "shiru tayi tana tunani , tashi muje parlour'n tare suka fito zuwa parlour umma na kiran sunan   "hassana "kanwar hajiyata na nan zuwa

in sha allahu gobe ,hasana ta fito daga kitchen tana goge hannunta tana cewa  "kai allah ya kawo mana ita lfy  ta kalli maryama ta galla mata katuwar harara "maza ki d'auke wad'an mugayen idanunki akaina  aí mu dai wannan yarinyar ki  zame mana balai a da

nginmu wai aunty yaushe zata bar bangaren  nan ne ta koma can gurin uwarta kar muma ta lashe mana kurwa ?wallah duk san dana daura idanuna akanta  ina jin kamar na kasheta ta mutu kamar yadda ta zama silar  kashe min dan danuwana dan girman allah ki sallem

a ta bar bangaren  nan mu huta da jaraba "ke dan Allah ya isa haka ina zata alhalin tana cikin takaba? wallahi hassana banason  abinda kike wa yarinyar nan yana matukar kona min rai dame kike son yarinyar nan taji ?Ko ance miki ita ta kashesa né ?Kiyi haku

ri aunty in sha allahu na daina umma ta juya mata baya tana danne hawayenta ".amman Aunty  ya kamata ki  fito da kayan sadam  tunda yanzu ya zama na magada sai bawa yara su yi amfani dashi tunda ya mutu kafin wannan mayar ta gama takaba araba gadonsa .."

"sadam bai mutu ba"maryama  ta fada da iyakacin karfinta tana juyowa ta fuskanceta  tare da dafe qirjinta "tabbas sadam bai mutu ba  ta qarasa mgnr tana kuka "yanzu ke hasana har kina tunanin abinda ya mutu ya bari sun zama na magada ku kenan ?dan kun

e magadansa sai ni da matarsa maryama nan  da  nan idanun umma  suka cika da kwalla ta shiga girgiza kai "wallahi  hasana ki bani mamaki sam banyi tunanin haka daga

gareki ba "idan ma kiyi hakuri ni da kaina zan nemi araba duk abinda ya bari domin allah ne

yace araba gado ni ban isa nayi jayayya da hukuncinsa ba amman at least kunyi hakuri   ku daina  daga hankalinku ,baku barni na huta ba baku  bar yarinyar mutane ta huta ba wai me yasa haka né ?karki manta maryama jininki ce domin kinfini kusanci daita da

n diyar yayankice uwa daya uba daya wallahi naso sadam ya rayu kodan ya kula min daita ya gatanta min ita ya bata kulawar da duk wani miji yake bawa matarsa ."ta qarashe mgnr tana kuka ".

maryam ma ta fashe da  kuka ."Umma ko zaa raba abinda sadam ya

bari dan Allah a d'an jirkinta tukun har zuwa wani lokaci saboda har yanzu police suna Kan invesgetion idan ya zamo yana raye fa bai mutu ba kuma an rigada an raba komai nashi ni dai a nawa shawarar kar a ta'ba komai nashi hatta suturarsa abarshi tukun nan

." da wani irin mugun kallo ta d'auketa dashi " yanzu ke maryama kina tunanin  yana raye ? " bai raye yana raye ya kamata  abari hukuma ta gama bincikenta alabashi komai zaa yi sai ayi amman for now abar komai gsky

Tunda tasoma magna Aunty hasana tayi sh

iru tsaye tana mka maka  mugun kallo, da ashariya daga cikin zuciyarta "kaji min tsinanniyar shegiyar yarinya suka jiyo muryar aunty salma gabadaya suka juya bayansu suna kallonta ahankali ta dinga taku har ta qaraso inda suke "lafiyarki ma kuwa maryama ?

gsky akwai  alamun kin zauce ayi hanzari akaiki asibitin mahaukata a duba lafiyar kwakwa kuwarki,"kece fa da kanki kika tabbatar mana  yaro nan ya mutu tunda a gabanki kika ce an binnesa  da ransa amman ki kekashe kasa akan bai mutu ba " wallahi aunty bai

mutu ba dan ina ..."ke jaira kiyi mana shiru anan kafin na zuciya na soma yar yar fa miki mari sadam  ya mutu kuma bazai dawo ba har abada idan ma zaki cire hkn aranki ki cire ki fara tunanin wata rayuwa."

ta fad'a tana huci “wallahi bai mutu ,kuma babu m

ai raba gadonsa hasalima babu takabarsa akaina ina nan ma tsayin matarsa har tsawon shekaru hudu “lallai hasashena ya tabbata yarinyar nan ta samu tabin hankali “to tsaya kiji da kyau duk macen da mijinta ya bata ne zatayi dakon aurensa na tsawon shekaru

hudu sannan bayan haka tayi idda idan kin haukace ne gara tun wuri musani amman rabon gado tabbas zaayisa acikin gidan nan inji cewar aunty salma .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗

     MAR'ADAMS

    

💖💖💖💖

💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

W

ATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura

wa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 28

Kwanciya maryama tayi a kasa tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya da ban tausayi  sai dai du

k wannan kukan da take sautin muryarta bata fita sosai ,tana jin ina ma sautin kukanta ya fito fili da hakan zai fiye mata sauki fiyye da rashin fitowarsa bugu da qari ko yasa yan'uwan mahaifinta sun sauko daga tsatsauran raayinsu  su tausayawa rayuwarta t

a jurewa kowance  irin jarabawar da Allah yayi mata amman ta kasa jurewa wannan  jarabawar, ta kasa jurewa jarabawar rashin miji da kuma d'anuwa gareta."meye tarin zunubina?tayiwa kanta tambayar hawaye na sake gangarowa akan kuncinta "ya Allah ka sausautaw

a rayuwata domin idan abubuwan dake faruwa akaina  suka cigaba da faruwa  zuciyata zata buga ."idanun umma dake cike da ruwan hawaye ta zubawa aunty salma tana kallonta  cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da bakincikin mummunan kalamanta ga maryama

."cike da tsananin tausayawa  maryama umma ta qaraso gareta ta durkusa ta riko tafin hannunta cikin nata cikin yanayin tashin hankali tace "kukan ya isa haka maryama  kada kanki yayi ciwo ."

     "mai yasa abubuwa suke zuwa min haka umma ?"ya zanyi d

a wannan rayuwar ? ya Allah ka d'auki rayuwata na mutu na huta da wannan duniyar da babu komai acikinta sai tarin bakinciki ya Allah ka d'auki rayuwata tunda haka rayuwar duniya take "daga wannan tashin hankali sai wannan tashin hankali meye laifina ?nan t

ake tausayin maryama ya sake ninkuwa acikin zuciyar umma tare da jin wani irin tarin qaunarta mara misaltuwa "kiyi hakuri maryama ki daina furta wad'an nan kalaman haka rayuwa take cike  da kudirorin ubangiji ,sannan dukkan rayuwa d'an adam rubutaccen al'a

marin ne daga Allah,na shafa fad'a miki duk mutumin da Allah yake so shi yake yiwa jarabawa." wani sabon kuka ta fashe dashi tana jin kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta aunty salma ta kwa'be baki tana duban umma da maryama a kaskance kafin ahankali

ta cigaba da cewa "da dai kin daina wannan kukan  munafurci da kike yi da bazai ta'ba miki maganin halin da kike ciki ba,

mutuwa ce da bakinki kika ce agabanki aka binne sadam da ransa to me kuma yayi saura ?Jin haka ya qara sa  ran umma yayi  matukar 'ba

ci  ta d'ago  idanunta cikin zafin rai ta  kira sunan aunty salma "salma !"

Yanayin yadda ta kira sunan cikin tsawa ya d'aga masu hankali gabad'aya sukai tsuru suna kallonta domin wannan shine karo na farko da suka ga tarin damuwa da 'bacin rai aciki

n kwayar idanunta,"salma  karki bari 'bacin raina ya sake ninkuwa akan wanda nake ciki ,nayi ta qoqarin na danne zuciyata akanku  amman naga alamun so kuke  sai na nuna muku  fushina da 'bacin raina"me maryama ta tsare maku ?wani irin numfashi mai zafi umm

a ta fesar kamar an tsikareta haka umma ta tashi daga gaban maryama "wallahi wallahi !!kunji na rantse akan maryama zan iya 'batawa da kowa dan haka ku  shiga hankalinku ku san irin magangun da zasu dinga fitowa daga bakinku  saboda kuma kuna da naku ya'ya

,allah yasa mata kuka haifa dayawa kusani duk mugun nufinku ga maryama kanku  ko kan ya'yanku  zai dawo domin allah baya zalinci kuma baya son mai zalinci amman nasan rashin ilimi ke damun rayuwarku domin da kusan dukkan rayuwar rubutaccen

lamari ne daga

rabbi, kilan da baku tsaya ' batawa kanku  lokaci ba gurin matsawa kanku da hassada da hankoron neman duniyar da wani ba ."

aunty salma ta kalli umma wacce  har lokacin kwayar idanunta  na kanta cike da tarin 'bacin rai sannan ta waiga inda baba gal

i da aunty hasana suke tsaye suma cike da mamakin umma .aunty salma ta daure zuciyarta da maganar umma tace "irin fatan da zaki mana kenan ?"irin fatan dai da  kukewa  kanku kenan." da sauri umma ta bata amsa da haka sannan tana cigaba da cewa  " maza ku f

ice min daga parlour bana son ganinku  kuma wannan ya zamo karo na farko dana qarshe da zaku  shigo inda nike kuyi lamarinku nayi nawa bana son ganin gaba d'ayanku a inda nake kowa ya zauna inda allah ya ajiyesa ."saboda an ta'ba miki yar so zaki fad'a ma

na haka ? Inji cewar aunty hasana "kwarai kuwa zan ma iya yin abinda yafi haka matuqar akan maryama ne aunty hasana ta numfasa kana tace "idan bake ba aunty ai murna zakiyi da abinda ake wa yarinyar nan yarinyar da ta zama silar rasa tilon d'anki  "sadam d

ai d'ana ne dana   haifa da cikina  duk kuma  wanda rashinsa zai wa ciwo a bayana yake to na barwa Allah kada wanda ya sake dawo min da hannun agogo baya kuje na sallameku bana son ganinku, yadda baku qaunar maryama nima wallahi a yanzu bana qaunarku daga

yau na yanke duk wata halaka daku ." da sauri aunty salma ta qaraso ta durkushe gaban ummah ta rike qafafuwan umma da duka hannuwanta ta soma girgiza mata kai kamar wata kadangariya tana kuka tana bata hakuri "dan girman allah aunty kiyi hakuri  bazamu s

ake cewa komai akan lamarin mutuwar sadam da gadonsa ba ki yafe mu dan Allah wallahi sai yanzu nake jin nadamar abinda nayi

in sha allahu bazan sake ba tabbas maryama tamkar diyarmu ce Allah ya huci zuciyarki wallahi bazamu sake ba ."

gwalalo idanu

aunty hasana da baba gali sukai suna kallon  makirci irin na aunty salma ,sam basu ta'ba tunanin zata aikata haka ba "lallai ta cika babba makira ta qarshe "kiyi hakuri dan Allah aunty ta sake  fad'a tana mai sakar ma umma qafafun ta kamo hannunta numfash

i umma ta sauke da karfi sannan ta samu waje ta zauna akan kujera tana runtse idanunta tare da dafe goshinta" sigina aunty salma tayiwa baba gali da aunty hassana alamun suma suce wani abu ai kuwa nan da nan suka matso kusa da umma suna mata magiya da ban

hakuri "shikenan komai ya wuce allah ya yafe muna gabadaya amman dai kusani maryama bata cancanci haka daga gareku ba ,maryama a yanzu tafi bukatar kulawa da tausayawa da soyayya tattare da rarrashi daga gareku tun daga farkon rayuwarta baku qaunaceta ba

wallahi kuji tsoron allah na rashin rike zumunci tsakani da Allah da kukayi ,wani abun mutane sunayi ne dan ganin ido wani dan zumunci zasu fake suci amana mussaman zumuncin wannan zamani amman ku babu wanda kukayi aciki kona ganin idon ma bakuyi ba bare

bayan ido amman wallahi kusani zumunci a duniya wajibi ne duk kuma wanda bai yisa a duniya ba zai yisa a lahira alahirar ma acikin wutan jahannama ta fad'a tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta ".

"wannan tabbas haka ne allah ya shireyar damu

gaba daya allah kuma ya bamu ikon sadar da zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba "baba gali ya fad'a yana mai  cike da nuna tausayawa ga maryama wacce hawaye biyu biyu ke bin kuncinta yace "diyata maryama Kiyi hakuri kinji in sha

allahu kuka da damuwarki sunzo qarshe domin a yanzu a shirye nike dana baki duk wata kulawa da uba zai bawa diyar cikinsa ."da sauri maryama ta d'ago kwayar idanunta da suka jeme ta tsurawa baba gali cike da mamakin jin furucinsa  aunty salma  tayi tsigil

tace "ki daina mamaki jin abinda babanki ya fad'a ,daa na shiga zuciyar mutun a ga abinda yake ciki da mun bude miki zukatanmu a yau kinga irin tarin nadamar da mukayi a yanzu babu wacce muke son gani cikin farinciki kamarki ki yafe mana duk da bamu dace

da a yafe mana ba saboda abubuwan da muka dauki tsawon shekaru muna yi miki "in a slow voice maryama tace "babu aunty salma komai na wuce na yafe maku ." murmushin bakinciki suka sakar mata kafin ahankali suka shiga wata hirar allah sarki umma har ga alla

h ta hakura domin ta d'auka nadamar gasky sukai ,ta sake dasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login