Showing 48001 words to 51000 words out of 172989 words
meke damunki ?girgiza ma
ta kai tayi alamun babu komai "amman tun bayan tafiyarsu kausar na lura kike cikin damuwa idan wani abu ne ki sheida min mana ?ajiyar zuciya ta sauke da karfi tace "babu komai "to muje kici abinci ta kamo hannunta suka fito tana cewa "gsky zanen kausar ya
yi kyau idan tagani zataji dadi sosai tare da aunty suka ci abinci bata wani ci abincin kirki ba tace ta koshi ta sha ruwa ta mike ta shiga bayi ta dauro alwala ta koma d'akinta sallar ishai ta gabatar byn ta idar ta mike tana nade daddumar sallah ."
Ta ajiye a inda yake ta tsaya shiru acikin d'akinta tana jin wani irin faduwar gaba ta qarasa ta kakkabe wajen kwanciyarta sannan ta kwanta rigingine ta hade hannuwanta duka a qirji tana tunanin rayuwa ganin zata damu zuciyarta ne kawai a banza ta sauke
ajiyar zuciya ta soma karanta suratul mulk ahankali bayan ta gama karantawa ta shafe jikinta da addua ta kwanta, ahankali bacci ya dauketa cikin baccinta tayi mafarkin umma tace a daura aurenta da yaya sadam har ma ya amince da auren kiran sallah asuba ne
ya tasheta daga mafarkinta ta mike ahankali ta zauna ta zuro kafafunta kasa tare da dafe goshinsa ."
Tayi shiru tana tunanin mafarkinta addua tayi Allah ya zaba mata abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da kyar ta yunkura ta mike tsaye ta fito t
a shiga bayi ta dauro alwala ta dawo daki tayi sallar asuba duk ta rasa meke mata dadi duk da tasan mafarki ne amman sai taji abun ya tsaya mata arai cike
da raunin zuciyata ta koma ta kwanta ahankali bacci ya kwasheta aunty ce ta shigo ta tasheta tana c
ewa "bazaki gidan aunty fati bane kinfa san halinta babu hakuri sai ta d'auki abun wani iri azo ana damun rayuwarki “ numfashi ta sauke kawai tare da mikewa zaune tana dafe goshinta "ko baki jin dadi ne dan tunda kika koma kika kwanta bacci bayan sallahr
asuba to baki da lafiya tayi mika tace "kaina ke d'an min ciwo sai dai kuma .."sai tayi shiru ta kasa mgn "sai dai kuma me ?"
"Wallahi umma mafarki nayi wai umma tace a daura aurena da yaya sadam kuma har ya amince ?aunty tayi dariya tana cewa "kai p
rincess wani irin aure kuma bayan ga maganar yusif ? ta kalli aunty tana jin fad’uwar gaba mai tsanani tace “aunty ki bar maganar yusif muyi maganar mafarkina gsky banji dadin mafarkin nan ba " to ai mafarki ne mafi yawon lokuta mafarki baya zama ga
sky tashi ki sha magani kije tun karfe tara aunty fati take kiran waya "to ni me zan mata ne ?tayi magana Kmr zatayi kuka "ni wallahi bana son zuwa koina idan kaga sun nemeka to aikin wahala ne ga wannan d’an nata mai shegen maseefar kallon tsiya kamar za
i cinye mutun ".
"To ko na fad'a mata bakijin dadi bazaki samu damar zuwa ba ta kira kaulat ko Islam suje idan wani aiki zaa mata sai suyi mata ?maryama tayi shiru can tace "yanzu rashin zuwan nawa zai zama tashin hankali azo ayita kananan magana
"shiyasa nake son kije idan ma aiki ne kika ga zai miki yawa Kiyi iya wanda zaki iya ki dawo ,nifa ba aikin bane damuwata kamar matsefaffen kallon da yaya muktar yakewa mutane ".
"Babu ruwanki da kallonsa kiyi abinda ya kaiki maza tashi ki tafi dan k
i samu ki dawo da wuri “numfashi ta sauke” gsky aunty bazanje yanzu ba “ya fad’a tana wasa da yatsun hannunta “sai yaushe zaki?maryama tayi shiru ta kasa mgn “da dai kin daure tunda kinga baki da lokaci sai asabar da ladidi tsaki maryama taja kana ta
ce “wallahi ban san dalili ba hakan nan najin fad’uwar gaba kuma dai yau bana son zuwa koina “aunty ta numfasa tace “to shikenan Kiyi zamanki muje kiyi wanka ki karya ki sha maganin ciwon kai ta mike ta fito wanka tayi ta shirya ta karya aunty ta bata m
agani ta sha tayi kwanciyarta akan kujera .”
Ahankali ta rufe idanunta lokaci d’aya kwakwalu warta ta bud’e tunani ya kusantota yaki barinta ta huta duk da bata son tayi tunani akan matsalarta amman haka tunani ya mamayeta , ahankali ta dinga tunani
n maganganun yusif ,me yasa zaki damu kanki maryama already kin rigada kin yarda kin rasa yusif har abada kamata yayi kin haka rami ki binne komai ya zama tahiri arayuwarki” zanyi haka zan cire komai araina kuma zan dage da addua har na samu nasara arayuw
ata ahankali tabi
shawarar zuciyarta ta haka rami mai zurfi aciki zuciyarta ta binne duk wata matsalarta .”
tun daga wannan ranar maryama ta cire tunani da damuwar komai acikin ranta ta toshe kunnenta duk abinda ke faruwa aciki gidan tana ji kuma tan
a gani amman ta share sannna taki bari mahaifiyarta tasan halin da’ake ciki yayinda kullum sai aunty ta sheida mata sakon kiran aunty fati har sanda sati ta cika aunty ta matsa mata lallai taje taji dalilin kiran da take mata “Allah aunty bana son zuwa d
uk sanda kika fad’a min sakonta gabana faduwa yake “kiyi hakuri ki daure kije bana son tazo gidan nan “ta fad’a muryarta a raunane ganin yanayin aunty yasa ta riko hannunta “shikenan aunty zani bari na sauya kaya naje yanzu na dawo .”
“Yauwa princess
maza tashi kije Allah ya tsare min Ke “Ameen !ta furta a tsanake ta fito ahankali take taku har fito titin unguwarsu ta mike zuwa captor road tana gama garasawa bakin titi ta samu adaidai mai zuwa unguwarsu aunty fati tafiya kad'an suka yi ta sauka pen
cilima ta mikawa mai adaidaita kudi ta ta tsallako hannunta na hagu inda zai shigar daita amawo ."a natse ta shiga gidan kai tsaye bangaren aunty fati ta nufa bakinta dauke da sallama ta shiga parlour'n inda ta iske muktar da aunty fati zaune ."
Rike d
a remut tana qoqarin canza tasha a tare suka kallo kofar tare da amsa sallama .”
tun daga kasa muktar ya dauki kallon maryama ransa nayi masa dadi wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa yayin
da maryama ta had'e fuska sosai tmkr taga wani mugun abu ta qarasa ta tsugunna har kasa ta gaishe da aunty fati ,aunty fati ta amsa mata fuskarta a d'an sake wanda hakan ya dan bawa maryama mamaki domin tunda suke daita kyara da hantara tattare da zagi
né a tsakaninsu ."
Maryama ta dauke kanta tare da mikewa tsaye ta zauna tana jiran taji dalilin nemanta da aunty fati take "ke maryama baki ga muktar bane da bazaki iya bud'e ki gaishesa ba ko shi kike jira ya gaisheki ?
"murmushi ya saki yana cewa"K
insan ‘yan boko ba dai girman kai ba " wani kallon takaici maryama tayi masa daga sama har kasa wanda yasa ma kasa cigaba da magana illa ya zuba mata kwala kwalan idanusnhi masu firgitarwa ."sama da awa daya tana zaune tana wasa da yatsun hannunta sannan a
unty fati ta gyara zama ta kira sunanta .”
"maryama !
muryarta a raunane ta amsa da “na’am !"na kiraki né domin na samu labari wannan yaron yusif ya canzaki da shukura yanzu ita zai aura shine muktar yace abashi ke tunda kowa gudnki yake kinga kena
n shi zai taimaka ya aureki sai yanzu na na gane dashi kika dace ba da sauran mazan da suke zuwa neman aurenki suna guduwa , d'ago idanunta tayi ta zubawa aunty fati tana kallonta gabanta na dukan tara tara sannan ta waiga ta kalli inda muktar din yake ya
na kallonta kamar tsohon maye ."
"Karki dauka ya rasa wacce zai aura ne yasa zai aureki aa tausayi kika bashi domin yaji babu dadi aransa , yanzu me kika gani zaki auresa ko kuwa zaki tsaya jiran masu kudin da basamu zakiyi ba ?ta tambayeta tana gyara
zamanta tare da tsareta da idanunta "parlour'n ya dauki shiru na kusan mintuna goma batare da maryama tace uhm ba bare uhmm illa nazari maganar aunty fati da take da kuma tunani amsar da zata bata domin dai a halin yanzu wannan shine labari mafi muni d
aya kusanto rayuwarta muktar fa ? "ke nake sauraro !?"
Murayarta can kasa ta soma magana a tsanake "a zahirin gasky ni ina da wanda nake só kuma wanda a shirye yake da aurena idan da hali zaa iya bashi kaulat ko Islam ,ko kuma sakina amman ni dai gsky
ayi min hakuri akwai wanda muka tsaida magana dashi ."ta tsinci kanta da fad’ar haka ba dan akwai din ba sai dan tsiratar da rayuwata daga shiga maseefa”waye shi kuma a ina yake ?"maryama tayi shiru ta kasa magana hankalinta idan yayi dubu tô a tashe yak
e tayi datasani zuwa gidan amman tasan ko bata zo wannna maseefar sai ta biyota har gida "
“ke banson iskanci banza bayan nasan babu kowa a kasa shine zaki ce kina da wanda zaki aura tô ke nake son ya aura ,oh a zuwan kinfi karfin aurensa shine kika
lissafo min daidai shi ko ?"ko d'aya aunty a dai bashi cikinsu shine zai samar da kwanciyar hankali "bata son wata fitina ta kuma lura kamar fitinar ce take bibiyarta arayuwarta, ran a aunty fati a matukar bace tace "d'an ma Kinsamu zai taimaka miki maza t
ashi ki bani waje na sallameki sannan ki fara shirin aurensa dan dolenki ki auresa"
Jiki a sanyaye maryama ta mike hankalinta a matukar tashe bazata ki dan shaye shaye ba dan mahaifinta ma har ya bar duniya yana sha babu komai acikin rayuwarsu sai ma
tsala ita me kai ta saka rayuwarta cikin ha'ula'i ?kuma tasan idan ba tsanarta da aunty fati tayi ba babu yadda zaa yi tace ta auri d’anta domin ko ita take da diya kamarta tayi imani bazata dauketa ta bawa muktar aure ba mutumin da idan yayi shaye shayens
a har kwata yake fadawa haka maryama ta koma gida tana cika tana batsewa duk ranta a dagule ."
Aunty ce ta fito daga kitchen tace "lafiya kuwa naga har kin dawo yanzu ?hawaye maryama ta share tace" aunty laifin me nayi da allah ya qaddaroni cikin wann
an dangin ?basa sona basa qaunar cigabanna idan akwai wacce suka tsana a duniya tô nice suna jin kamr su kasheni wallahi suzo su kasheni su huta da muguwar tsanar da suka min na rasa me nayi masu arayuwar nan da suka tsane ni."aunty ta zauna kusa daita ji
kinta na rawa tace "me ya faru maryama ?"na gaji da wannan rayuwar aunty fati so take ta kasheni dan Allah ku barta ta kasheni ni yanzu nafi bukatar mutuwa da rayuwata akan dai ta hadani da muktar .”ta qarasa maganar tana kuka .”
“kwantar da hankali
nki kiyi min bayani da kyau ban fahimceki ba ta hadaki da muktar kamar ya ?"
"Wai ya aureni !"numafashi aunty ta sauke cikin rarrashi tace "haba maryama ki daina daga hankalinki tunda ga maganar yusif nasan baba gali zai yi mata bayanin komai maryama ta
fashe da wani sabon kuka dan ta ta’bo mata wani ciwo ne data binne "babu wannna auren bilkisu .”muryar umma suka jiyo daga bakin kofa aunty ta juya da sauri qirjinta na bugawa fiyye da kaida ummah ta gyada mata kai "haka né abinda kikaji na fada shima an
canza masa tunani har ma dana iyayensa ahankali ta tako ta dafa kafandan aunty dake kallonta a tsorace cikin tsananin tashin hankali ."
“Ummah ban gane ba me kike qoqarin fad’a min ?“abinda kika ji shi na fad’a miki balkisu yusif ya koma wajen shukur
a “inna lillahi wa inna ilahi rajiun shi kawai tayita fad’a tana maimatawa nan da nan yanayinta ya sauya ta zauna shiru taji duk wani kuzari na jikinta yayi kasa tsawon mintuna talatin sannan ta bud’e bakinta da kyar tace “shima yusif din ya koma wajensu
"Ki kwantar da hankalinki babu abinda allah bazai iya ba kuma in sha allahu allah zai kai maryama matakin da ba'a só allah yasa hakan shine mafi zama alkhairi arayuwarta ummah ta zauna ta dinga tausar aunty da maryama tana bata baki har aunty ta saki ra
nta sai dai hawaye yaki tsayawa umma ta qara da tabbatar masu duk runtse maryama bazata auri muktar ba “
Maryama ta rungume ummah ajiknta “na gode umma dan allah karki bari a aura min shi wallahi na hakura da auren ma har abada “bazaki hakura da aure
ba akan wani dalili domin duk dan sunah baya gudun aure yadda akayi aure aka haifeki in sha allahu kema zakiyi aure har ma da ya’ya da jikoki ummah ta fad’a tana shafa bayanta suna cikin wannan hali habib ya shigo aunty tayi sauri ta goge hawayenta tana
daidaita natsuwarta ganinsu haka ya fahimci akwai damuwa dan haka da hanzari ya qaraso ya riko hannun aunty cikin nashi yana tmbyarta “lafiya na ganku haka ?babu komai aunty ta basu amsa “ya babu komai ?ya kalli ummah fuskasa dauke da tambaya .”
“Me
yasa zaku boye masa yana da kyau ya sani ko babu komai zai taya yaruwarsa addua nan ummah ta fad’a masa komai “shiyasa nace ta hakura da batun wani aure ,bafa dole sai mutun yayi aure zai shiga aljanna ba “kul kar na sake jin ka fad’a haka zatayi aure mu
sa aranmu dukkaninsu babu mijin aurenta acikinsu mu godewa allah da yasa har tana masu sonta baa barta haka ba babu abinda zai zo da bazai wuce ba wata sai labari ahankali ummah ta shawo kansu suka shiga wata hirar ,”
******
Kwanakin dari kena
n da auren su maryam wanda yayi daidai da kwanakin sabain da tarewar maryam a gidan ata acikin lokacin babu wani abu da yayi sauki acikin zaman auren mai dadi a tsakanin maryam da ata duk abinda maryam zatayi domin ta cire kiyayyarta a zuciyar ata tayi
amman ko a jikinsa domin dai yaki sakewa daita ."shiyasa damuwarta ta qaru zamansu babu wani shaawa dan ata yaki rungumar marym sai ma kyma da nuna ko in kula ."
Sosai motocin jami'an tsaro guda hud'u dake gaba da bayan motar da ata ke zaune aciki
ke falfala gudu akan titi kamar suna gasar tsare baka jin komai sai jiniya mai tsanani domin a kauce abasu hanya sosai motocin dake Kan titi suka dinga komawa gefe suna basu hanya wanda adaidai wannan lokacin maryam na can tsaye acikin kitchen tana kwas
he abinci tana zubawa a kuloli ."
Bayan ta gama ta jerasu akan table duk abinda take cikin hanzari take yi kar oga ata ya shigo bata gama ba duk da ba abincinta yake ci ba sai maakatan gidan ke ciki kuma idan tayi lattin ganawa yaci ubanta ,qarar j
iniya taji alamar dawowarsa dan zaro ido tayi tare da daga kai ta kalli agogon dake manne a parlour'n karfe takwas da minti ashirin cikin sauri ta haye sama ta shiga dakinta wanda ya sha gyara gwanin burgewa. ta cire kayan jikinta ta daura towel sannan t
a nufi bayi ."
Cikin jin isa ya turo kofar parlour'n tare da shigowa babu kowa a parlour'n jakar dake hannunsa ya ajiye akan kujera da wayoyinsa sannan ya nufi sama yayinda zuwa wannan lokacin maryam ta fito tana tsaye a gaban madubi tana shafa li
p's dinta byn ta gama ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka can zuciyarta ta bata umarnin ta saka marasa nauyi tun sanda ta tare a gidan tsawon sati tara kenan atamfa da dogayen
riguna take sakawa ta sanya kaya marasa nauyi masu yanayi dana bacci yana
tsaye a dakin yaji an turo kofa bai juyo ba ."
cike da faraa ta tsaya a gabansa tana cewa "oyoyo baby sannu da zuwa "wani kallo yayi mata a dage yana sake tamke fuska tmkr yaga wani mugun abu cike da sanyin jiki ta kallesa ganin yadda yayi mata kallon
kaskanci "leave my side “ya fad'a yana nuna mata kofar fita yayi maganr cikin bacin rai bata wani damu ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa "ga abinci "bana ci kina tunanin zanci abinncikin ne ko me ?”kayi hakuri please kaci ko kadan ne na sha wahal
a sosai kafin na gama bai ce mata komai ba ya juya ya bar parlour'n.”
Wani bakinciki ta dinga ji acikin ranta "oh ni maryam me zan yiwa wannan bawa naka na canzashi?gani bata da abinda zatayi yasa taja kafafunta ta koma dakinta ."ta fad'a kan katifa
wasu hawayen bakinciki na zuraro mata nasihar sister ce ta fado mata "maryam kinsan yadda akayi auren nan hakuri zakiyi da Adam idan kina son kici riba ,auren da kayi dan soyayya ma hakuri kake yi bare wanda iyaye suka had'a zaman aure dan hakuri ,gidan au
re makaranta ce mai girma ba zaka gane hakan ba sai ka shiga, akwai darussa kala dabam dabam sai kin zauna acikinsa zaki fahimta."wasu hawaye suka qara tsiyayo mata yanzu haka zata qare rayuwarta cikin hakuri "tunda kina son shi dole zakiyi hakuri dashi .
"zuciyarta ta bata amsa da hakan .”
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai
bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da