Showing 60001 words to 63000 words out of 172989 words

Chapter 21 - MAR’ADAM’S COMPLETE

30 Aug 2026

28

daura kwayar idanuna akanta “wallahi Allah mami jiya kasa bacci nayi saboda zan zo na

ganki sai kuma gashi naga yan’uwana gabad’aya .”allah sarki maryam nima nayi kewarku sosa

i .”

Tayi murmushi mami ta cigaba da kallonta “tunda sister ta fad’a min zamu zo tare nake murna sai naga gari kaman da gangan yaqi wayewa don kada inxo na ganki” to gaki ga maminki kinganta cikin koshin lafiya “wallahi gashi na ganki kuma naji dadi

sosai ai ni ina ganin ma na dawo kenan bazan koma wannan gidan mai kama da makabarta ba sai na kwana biyu “.nana hauwa’u ta zungurinta kan tayi shiru amma ina maryam bata fuskantarta ba mami ta miqe tsam ta basu waje dan tasan dole zasu tautauna a tsakani

nsu .” mami na fita nana hauwa’u ta zubawa maryam duka a cinya wallahi ki rufa min asiri baki isa ki kwana a gidan nan ba yadda na dauko ki haka zan maidake gidanki “.

wajen da nana hauwa’u ta daketa take sosawa tana dariya tace “wallahi babu inda zan

i “kamar zaki iya bayan kina tsananin sonshi ? “kai nana hauwa’u ban da sharri wa ya fad’a miki son 'ya'yan take?inji zabiba ta fad’a tana murmushi nana hauwa’u tace “ai ni tuni na san da wannan ga tanan kuma idan ta isa ta karyata ,sister ban da sharri fa

auren daaka samu na amince da kyar zaki zo kice ina son shi nana hauwa’u ta sake qara mata wani dukan maryam tace “babu komai wallahi koda da zafi ni banji zafin ba, dan bakya laifi ko kin kashe dan masu gida wani dan masu gida ?”yayanki ! dariya suka bus

he da ita gabad’aya su Aunty zabiba tace "Kefa sabon iskancin mai lasisi kikaje kika koyo a gidan yaya “barta dole tayi iskanci da alamun taga gadon baccinsa shima yaya naga ya canza kwana biyu da alamun ya angwance inji cewar zabiba “.

wallahi ku dai

na fad’ar haka kar sautsayi ya shigo dashi mu shiga uku “ku dai shiga uku amman mu ai yayensa ne dole ya daga mana kafa dariya maryam ta saki har da tafa hannu “wannan kanin naku ai mami kawai yake d’agawa kafa hira suke sosai yayinda maakatan gidan suka c

ika gabansu da kayan marmarin da abinci da abun sha aunty khadija ta dubi auta “da alamun kin samu lafiya “alhamdulillah Aunty khadija rayuwar aure is not easy amman haka zamuyita hakuri har allah ya kawo mana sauki Ameen “ kefa maryam yaya zaman naku da u

ban shegu ?uhm ta numfashi “to da sauki zance amman ni matsalata mai girma ce kuma ban san ranar da zan fita ciki ba” ta qarasa maganar kamar zatayi kuka .”

Gabad’aya suka zuba mata ido cike da tausayawa “ita fa siater matsalarta mai sauki ce ba kamar

ni ba da ko muryata baya son ji baya cin abincina kona girka sai dai masu gadin gida suci bani da kwanciyar hankali matukar yana gida , sister kuwa nuzla ce matsalarta amman ni zanyi maganinta “ki rabu daita

huce haushi take akan hisham shi kuma rashin ga

newa ne idan ba haka ba ko sauraranta ma yayi “inji cewar aunty khadija “allah ya kyauta daga nan Suka cigaba da hirar matsalolin rayuwa wani suyi dariya wani suyi jimami cikin haka aunty abida ta shigo daman ita tana yawon shigowa ko dan taji halin da ata

yake ciki a wajen mami diyana da rukkaya suka shigo su kuma nana hauwa’u ce ta kirasu kusan duk yammatan gidan suka shigo aka sake bud’e habin hira banda nuzla har karfe shida ta buga suna tare ana hira .”

Ahankali motocin ata suka shigo haraban esta

te dinsu sakamakon kiransa da mami tayi suna gama daidaita tsayuwar motocin ya fito kamar ance ya kalli kofar gidan baba babba hisham ya gani tsaye tare da nuzla ya zuba mata ido kamar zai mata numfashi .”shiru yayi yana mamakin karfin halinsa ko bai ji ku

nyar kowa ba ai ya duba mami bare tsakaninsa dashi” ahankali nuzla ta kalli inda yake kallo d’aya tayi masa ta d’auke idanunta tana jin farinciki dan yanzu bata jinsa aranta haka ne ma yasa take son dandanawa jininsa wahala kuma har ga allah tana son ta au

ri hisham yanzu dan hishsm miji ne bancin yana kawo mata uzurinsa akan mahaifiyarsa da yanzu ta dade da kasamcewa a gidansa .”

daya daga cikin masu tsaron bakin get din ya dagawa hannu ya taho da sauri ya tsaya a gabansa cike da girmamawa “daman hisha

m na zuwa wajen nuzla ne ?Eh !ranka ya dade kusan kullum yana zuwa shiru yayi kafin daga bisani yace “okay zaka iya tafiya “ya juya ya koma bakin aikinsa shi kuma ya nufi kofar gidan mami yana kiran mb ,yayan mami suna shirin mikewa su kama gabansu har nan

a hauwa’u dan ita maryam mami tace ta zauna ATA zai zo sai su wuce tare suka ga mutun ya shigo kamar wanda aka jehoshi yana huci “gabad’aya suka mike tsaye suna kallonsa .”bai ce masu komai ba ya samu waje ya zauna akan kujera yayinda kannensa suka gaishes

a amman yaki magana ya soma waya da yaya Ibrahim .”

Hankalin mami ya tashi ta qaraso garesa ta dafa shi tana tambayarsa “lafiya adamcy naga ka shigo wani iri ?still shiru yayi yaki magana ganin haka aunty shahida ,aunty khadija da zabiba har da nana

hauwa’u sukai ma mami sallama zasu wuce muryarsa a kausashe ya soma magana cikin tsananin fushi “auta kar naga kin fita daga gidan nan kin dawo gida kenan .”gabad’aya suka dawo cikin tsananin tashin hankali suna dubansa “akan wani dalili kenan adamcy ?aunt

y shahida ta tambayesa “yayi shiru yana huci tamkar zaki “ka barta ta koma gidanta tayi zaman aure tunda suna zaune lafiya da mijinta “inji wa yace miki haka ?ya fad’a a zafafe yana fesar da hucin numfashi “zaku iya wucewa amman ita babu inda zata mami kam

shiru tayi ta kasa magana “mami kice wani abu mana kinyi shiru kina kallonsa “aunty khadija ta fad’a tana dubanta “zaku iya wucewa zanyi magana dashi “

Suna shirin fita mb ya shigo dole tasa suka tsaya kallo d’aya yayiwa abokinsa ya fahimci akwai dam

uwa ya qaraso kusa dashi ya zauna yana cewa “yaakayi friend ! kace nazo yanzu yana qoqarin bud’e bakinsa yaya Ibrahim ya shigo “ya fesar da numfashi sannan ya soma mgn “mb daka shigo yanzu kaga hisham tare da nuzla ko baka gani ba ?“na gansu amman.” dakata

mb “an tabbatar min kullum yake zuwa wajenta kuma nasan yana yin hakan ne saboda ne “.juya can ka kalli auta da kyau “haka aka kai masa ita ?yau zaa yita ta qare gidan nan laifin mai tayi masu ?idan laifi ne ,ni ne nan nayi saboda naki amincewa da soyayya

r nuzla kuma nasan shine sila da dalilin son a kuntatawa auta tunda ni babu abinda zaa iya min ,dan haka yau zan kashe wannan aure .”mami ta sauke numfashi sannan ta mike ta bar wajen.”dan tasan halin d’anta wani irin murdaden mutun ne mai wuyar shaani ”

Yan’uwansa ma numfasawa sukayi domin wannan karon fad’an gasky yake da son kwatarwa kanwarsa ‘yanci amman sunyi mamaki wannan shine karo na biyu da ya nuna kulawarsa akan nana hauwa’u amman duk da haka bazasu bari ya kashe mata aure ba .”maryam ta kall

esa taga yadda hankalinsa ya tashi akan yaruwarsa ya manta irin azabar da yake gana mata ,ya manta cewar itama diyar wani ce yake quntata mata hawaye ya cika idanunta tausayin kanta ya kamata ta kalli nana hauwa’u taga itama hawaye take ta kalli ata cikin

sa’a idanunsu ya tsarke cikin juna tayi kamar zata girgiza masa kai amman wata katuwar hararar daya zabga mata mai had’e da kallon banza yasa ta d’auke idanunta akanshi ,tana mai share hawayenta da hannu ta qaraso kusa daita nana hauwa’u ta riko hannunta z

uwa gefe “sister kinji hukunci yayanki dan allah karki yarda ya kashe miki aure saboda ya hisham mutumin kirki ne nuzla ce matsalarki .”

“bani da zabi sister bazan iya ce masa a’a ba duk abinda yake son ya zarta akaina na amince ni mai biyayya ce a ga

resa ,maryam ta rungumeta ajikinta “bakya son yaya hisham ne ?”to bazan ce bana jinsa araina ba , amman idan yayana yace na koma gidansa zanyi idan yace a’a babu inda zani “wallahi sister kina son mijinki “ta fad’a tana zare jikinta a nata ta tsura mata id

o tana kallonta hawaye ne kawai yake fita daga cikin idanunta qirjinta har wani sama da kasa yake “ta riko hannunta tana cewa “ shi bai rike nashi auren ba zai kashe auren wasu muje ki fad’awa mami kina son mijinki nana hauwa’u taki binta ta zare hannunta

ta rakube gefe tana share hawayenta dole tasa maryam ta dawo ta tsaya kusa daita tana share mata hawaye .”

mb ya kira layin hisham cikin kankanin lokaci sai gashi ya shigo yayi mamakin ganin mutane cike ya tsaya yana kallonsu

d’aya bayan d’aya sai da

i bai ga matarsa acikinsu ba , wani mugun kallo ata yayi masa sannan ya qaraso gabansa ya tsaya tare da jin kai ya zuba hannuwansa duka cikin aljihunsa “baka son auta shiyasa ka zabi ka dinga quntata mata ta wannan hanyar ko ?hisham yayi shiru yana mai sun

kuyar da kanshi kasa dan jin kunya “kasani nasani kowa yasani ban bada goyon bayan auren nan ba dan har yanzu bana son aurenku daita “cool down ata mb ya fad’a yana dafashi ya buge masa hannu yana qoqarin cukumar wuyan hisham yaya ibrahim ya shiga tsakanin

su “dan girman allah ka matsa “ babu inda zani ka samu waje ka zauna ayi magana ta natsuwa “idan har kaga na zauna to ya miko min takardar sakinta dan bazata qara zaman aure daahi ba har abada ya saketa yaje ya auri wacce yake so .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗

   MAR'ADAMS

  

💖💖💖💖

💗💗💗💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi  byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan ac

count number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

       Page 12

Jin abinda ATA ya fad'a ya

sa  maryam duk ta rud'e sai zufa take fitarwa hankalinta yayi matukar tashi gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa domin tasan halinsa tunda ya furta zai raba auren lallai zai aikata hakan "ta fashe da wani irin kuka mai karfi , haka ma nana hauwa'u kuka take sos

ai , yadda maryam ta rud'e haka matan dake tsaye a wajen suka rud'e gashi babu damar yin magana .mazan  kuwa sai faman bashi hakuri suke yana fixgewa mb ya fuskancesa sosai yana cewa "haba ATA ka kwantar da hankalinka abi komai ahankali "kasan allah muddin

ina raye sai na kashe wannnan banzar  auren ."

qanqame maryam nana hauwa'u tayi ajikinta suna mai fashewa da wani kuka cike da tashin hankali maryam ta soma magana muryarta na rawa "sister ke kad'ai ce zaki kawo karshen wannan matsalar "nana hauwa'u

ta zare jikinta ta tsura mata ido ,idanunta na sake cika da ruwan hawaye . saboda babu mai fad'a ma yaya adam yaji sai ke a yanzu idan kika nuna masa kina matukar son mijinki shikenan magana ta qare dan dole zai hakura ya barku "nana hauwa'u ta girgiza ma

ta kai "dan allah sister karki bari ya rabaku yaya hisham mutumin kirki ne ki tashi kiyi wani abu ta karashe mgnr tana kuka numfashi nana hauwa'u ta sauke tana share hawaye "bazan iya ba sister duk abinda yayana ya zaba min shine daidai ."haba sister haba

sister !! karkice haka mana kiyi hakuri kiyi wani abu mana ta qarashe maganar tare da qoqarin mikar daita tsaye "

da kyar nana hauwa'u ta mike tsaye bisa kafafunta ta soma tafiya jikinta na rawa rawa taku biyar tayi ta tsaya cak ta kasa cigaba da

tafiya hawaye na sake wanke fuskarta yayinda ata da hisham suka tsurawa juna ido kowannensu zuciyarsa na zafi cike da tashin ahankali ." hisham ya janye kwayar idanunshi cikin nashi ya tsurawa nana hauwa'u yana mai shafa kanshi abu d'aya zuwa biyu ne suka

tsarga masa a tsayen da yake a gabansa ,abu na farko farinciki yadda Adam yaji zafi da ciwo acikin zuciyarsa ,abu na biyu kuma mahaukaciyar soyayyar nana hauwa'u da yaji yana bin jinin jikinsa tare da huda duk wani tsoka dake sansar  jikinsa ,cikin wani i

rin sauri zuciyarsa ta dinga tsalle tana bugawa da matsanancin karfi kamar zata fito daga cikin qirjinsa  hannuwansa duka ya miko mata alamun tazo garesa dan bazai iya rabuwa daita ba ."

   ta kalli yayanta dake tsaye rike da kugunsa, ta waiga ta ka

lli yan'uwanta sannan ta kalli hisham da har lokacin yake miko mata hannunwansa gabad'aya nana hauwa'u ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga sakamakon fad'uwar gaban data risketa ,haka ne ma yasa jikinta ya cigaba da rawa gashi yaya

hisham yaki d'auke kwayar idanunshi akanta wanda yayi sanadiyyar da suka fad'a kogin tunani hankalinsu ya bar duniyar da suke ciki ya lula dasu can wata duniyar . "friend kayi hakuri ka kwantar da hankalinka hisham bazai ta'ba cutar da auta ba ,sannan huku

ncin da d'auka akanshi daidai ne ko yanzu ka taka rawa aciki rayuwar aurensu wannan zai zama kashedi ne mai karfi kayiwa hisham".

"shi kansa bai san yana son matarsa ba sai yau haka zalika itama auta tana son mijinta ka duba ka gani yanayin da suke

ci

ki na damuwa a yanzu "ATA ya sauke hannunsa dake rike da kungunsa ya juyo yana kallon mb a kallon da yake masa ya fahimci ransa ya kai kololuwar tashi da maganar da yayi masa ahankali ya kalli inda hisham yake tsaye yana mikowa nana hauwa'u hannu ranshi ya

qara 'baci cikin tsananin fushi yace "wallahi wallahi idan kika kuskura kika isa garesa sai na balballa ki "Jin sautinn muryarsa yasa nana hauwa'u tai saurin dawowa haiyacinta tana mai sunkuyar da kanta kasa ."

A rud'e maryam tace "me yasa yaya ada

m "! ta matso gabansa ta tsaya tana dubansa hawaye na sauka daga idanunta "me yasa zaka kashe mata aure alhalin tana son mijinta ?ya kamata kayi masa uzuri saboda kai kanka kasan yaya hisham mutumin kirki ne wallahi bazai ta'ba cutar da sister ba duk duniy

a a halin yanzu sister bata da kamarsa idan ka tsaya domin kwatar mata 'yancinta nifa ?"nida kake min fiyye da abinda yake mata fa"? sai da gaban kowa dake wajen ya bada wani sauti bugu mai karfi

Wani mugun kallo yayi mata da tsumammun idanunshi yana nun

a da yatsan hannunsa "wacece ke da ina magana zaki saka min baki ?ya fad'a tare da d'auketa da wani gigitaccen mari yana sake nuna ta how dare you ?".

" duk nan babu wanda ya isa bare ke din banza da ko kwatan matsayi kowa anan baki kai ba ." abinda n

ake miki ina yi ne dan bana sonki ,suma kuma da kika ga zan rabasu dan nasan basa son juna sukai aure, bana goyon bayan auren da ba'a so, dan bana son a aura min matar da bana só kamar yadda adabaibayeni dake "yayi maganar da karfi jikin maryam yana rawa t

a fad'a jikin aunty shahida tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya ."gabad'aya parlour'n yayi shiru tamkar babu wasu halittu acikinsa, babu wanda bai tausayawa maryam ba illa aunty abida wacce taji dadi aranta kuma hankalinta ya kwanta ta qara tabbatarwa kan

ta sultana ce macen da zatai wining din heart dinsa dan haka ta washe baki cikin jin dadi tace tana ".

"kema maryam da karanbani kike keda kika san matar cushe bata daraja ,me ya kaiki saka masa baki a maganarsa ?."you're very stupid kema nace ki sa

ka min baki a maganata ne ?"ko ina ruwanki ? kai tsayuwar me ma kikewa mutane anan ?da mijinki nake da issue ba dake ba oya leave "ya nuna mata kofar fita cikin kuka tace "ah ah ni ai yar'uwarka ce dole ina da ikon da zanyi magana kuma ma ai anan ka sameni

ba daga sama na shigo ba ,magana kuma dole nayi wallahi wannan kam ba irin matarka bace sam baku dace ba ka jira matarka na nan zuwa amman kam sam ba mata bace " abida i saiid out of this hall kuma ko da wasa karki sake shiga hurumina idan ba haka ba zan

baki mamaki .yaya ibrahim ya kama hannun matarsa yayi hanyar

waje daita amman aunty abida ta turje tana cewa "ka sakar min hannu babu inda zani da kyar ya samu ya fitar daita ya dawo ."

"Me ye laifinta adamcy ai gsky maryam ta fad'a maka "wato laifi

tudu ka take naka ka hango na wani ya kalli Aunty shahida da kyau yace "ina mata abinda nake mata ne saboda bana sonta kuma da ina da dama zan iya rabuwa daita har abada ,haka zalika shine dalilin da yasa zan kashe auren auta domin zukatan kowa ya huta, y

aje ya auri wacce yake so itama ta samu wanda take so yake sonta ya qarasa mgnr gumi na karyo masa sannan ya kalli nana hauwa'u "Ke maza ki koma d'aki "da mugun sauri ta juya tayi hanyar d'akin tana jin wani irin fad'uwar gaba mai tsanani hisham ya kallesa

kawai batare da yayi magana ba duk da maganar yake son yi amman idan yace zai yi komai zai qara rikicewa ne shurunsa ne yafi zama alkhairi ."

A rikice mami ta fito alamun tashin hankali aunty khadija na biye daita ."ta tsaida nana hauwa'u aunty kha

dija ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login