Showing 57001 words to 60000 words out of 172989 words
ne
da mahaifinsa da mahaifina the same mother the same father wani irin kallo yayi mata mai cike da tunhuma,itama kallonsa tayi numfashi ya fesar yace “shi kuma mijin da nayi miki fa ya zanyi dashi ?tayi murmushi tana cewa “allah sir ka daina min haka wallah
i kana d’aga min hankali ,kai kanka kasan kafi karfina bare wanda kake fad’a wannan sai dai na qara dagewa da aikin ibada wata killa na samu irinsa a aljanna yayi murmushi yace muje “.
Ahankali suke takawa yayinda mutane suke gaishesa wasu ya amsa was
u kuma ya d’aga masu hannu “kefa ko anyi miki interview ko ba’ayi miki ba dole zaki yi aiki damu “sure tunda inda kai ba ,ai sunanki na can tuntuni kinga office dinki can ta kalli inda ya nuna mata “woow gsky naji dadi sosai “kinga ga office dinki ga na mi
jinki in sha allahu “tayi murmushi kawai tana cewa “subai’a fa ?nifa nafi son naji kana magana kana had’awa daita zai yi magana kenan, wayarsa ta d’auki qara sauti ,ya soma qoqarin d’auka bata tsaya jiransa ba ta cigaba da tafiya dan daman da kyar take iya
jirawa dashi da sauri ta qarasa tana shiga aka kira sunanta .”
Sai da tayi addu’a sannan ta shiga office din ta gaishe da mutumin data gani zaune mai suna wale yana duba wasu fararen takardu,ya d’ago ya kalleta a natse sannan ya sake kiran sunanta “m
aryama hussein !”tace yes sir ! sai daya bata izinin zama sannan ta zauna a natse tana wasa da yatsun hannunta wanda ya zame mata jiki ,ya d’an saci kallonta yana mamakin matsayin da aka bata ,domin kujera ne da suka dade suna neman wanda zai maye gurbinsa
, sai dai lokacin daya fara auno mata tambayoyi akan kasuwanci da kuma matsayin da zata taka ya ajiye mamakinsa a gefe domin kuwa ta cancanci ta hau matsayin kuma irinta mai kamfanin ya dade yana nema .”
bata wani jima ba ta fito har da award aka
bata sakamakon aikin da tayi dasu daman kuma sun ajiye ne domin rana irin ta yau “congratulations sauran abokan aikinta suka shiga yi mata tana amsa masu da “thank you tare da rungumar mata daga cikinsu duk wannan farinciki da take ciki bai kawo mata nats
uwa ba saboda rashin ganin subai’a da batayi ba ta ciro wayarta ta soma nemanta tana tafiya ahankali har ta fito haraban ma’aikatan subai’a ta d’auka tana kuka hankalin maryama ya sake tashi sosai ciki tsanani tashin hankali tace “subai’a kina ne na shigo
har an d’aukeni aiki banganki ba ? tana shirin sake yin magana ta hangota a bayan wata bishi tana qoqarin fitowa .”
Da sauri maryama ta qaraso ta tsaya tana qare mata kallo tsab hawayenta yasa zuciyar maryama tsananin bugawa “me Ke faru dake subai’a
?kukan me kike yi ?muryata cike da kuka tace “na rasa aikin nan ,da yawa wad’an da suka d’auka alfarma ne yanzu bansan ta yaya zamu cigaba da rayuwa ba daman da allah da aikin nan na dogara gashi ban samu ba muddin sai da wata alfarma zan samu aikin nasan
har abada bazan samu ba .”ta riko hannunta maryama tana cigaba da kuka ta soma rokonta “dan girman allah maryama karki barni haka ki taimakeni ki
bar min aikin nan nasan zaki samu wanda yafishi gabad’aya idanun subai’a sun rufe har sai da maryama ta kira
sunanta sannan ta tsaigaita kukanta “ki kwantar da hankalinki ki bar kuka nan haka” amman ta yaya babu sunanki bayan ..”sai kuma tayi shiru ta janyo hannuta zuwa ciki “zo muje .”
maryama na gaba subai’a na bayanta har suka qarasa bakin office din jame
s ta nemi izinin ganinsa aka bata damar shiga ,wanda ta samu wannan damar ne saboda ammar domin yadda yake mata yasa mutane dayawa d’aukar sonta yake maryama ta shiga tare da subai’a dake kuka har lokacin .”bayan ta gaishesa cike da ladabi tace “dan allah
ina neman wata alfarma agareka ya kalleta dan shima ta burgesa yadda ma’akatan suka dinga yaba kwazonta tun kafin tazo kuma zuwanta wale ya sake tabbatar masa iri irinsu basu dayawa a duniya dan tunda ya sheida masa ya kira mai gidansa seun ya sheida masa
muryarta a matukar sanyaye ta soma magana kamar zatayi kuka “dan allah sir wannan yaruwa tawa nake son ta maye gurbina ma’ana acire sunana a saka nata .”ya kalleta a tsanake domin yasan yadda ake shan wahalar neman aiki yanzu da kudinka ma baka samu “.
“Saboda allah zakayi karka tsaya tunanin komai ni inda aikin da zanyi domin tallafa rayuwata for now ,ita kuma bata dashi da wannan aiki Kawai ta dogara ga mahaifinta ya rasu ko da yake nima marainiya ce amman dai tafini bukatan aikin nan saboda tana d
a kanne dayawa da mahaifiya mara lafiya dake karkashin kulawarta itace komai nasu “da wannan maganar ta karyar da zuciyar James ya kalli subai’a cike da tausayawa yace “sorry oo !”zan iya miki wannan alfarma sai dai bazata maye gurbin kujerarki ba “tayi sh
iru tana tunani abinda zata ce kafin tayi magana ya cigaba” kujerarki ke kad’ai ake bukata sakamakon oga ammar sunanki ya bayar gashi yanzu kinzo da wata magana “karka ji komai a saka a duk inda zaa sakata nidai burina ta samu aikin ni zuwa gaba in sha all
ahu zanyi aiki daku amman a yanzu burina subai’a ta samu aiki .”
Mr James ya saka sunan Subai’a ya cire sunan maryama “ suka fito zuwa gindin wata bishiya maryama na cewa subai’a “congratulations na tayaki murna kawata yanzu kin zama cikakkiyar maa
ikaciya ta fad’a tana murmushi subai’a ta rungumeta cike da farinciki “na gode na gode maryama allah ya saka miki da mafifincinsa nayi imani zaki samu aikin da yafi wannan da kika bar min tana kuka tana gode mata” haba subai ki daina kuka kawai dan na sada
ukar miki da aikina kike wannan godiya da kuka haka ?” ta goge mata hawaye tana cewa ni na zan bar ki na wuce gida nasan akwai abubuwan da zaku yi kafin ku wuce ina miki fatan alkhairi allah yasa ki fara aiki a saa ta juya a hankali ta soma taku subai’a ta
bi bayanta da kallo hakika bazata ta’ba manta alkhairinta gareta ba .”
Da wuri maryama ta dawo gida koda ta shigo kai tsaye bangaren ummah ta shiga ta sheida mata amman ta isketa a dakinta tana bacci dan haka ta fito ta shiga bangarensu ta zauna a p
arlour’n tana sauke numfashi tare da dafe goshinta ko cikakken minti biyar batayi ba ,Aunty ta fito da mamaki take kallonta “lafiya naga har kin dawo ?lafiya aunty nan ta zayyane mata komai sosai ran aunty ya baci kamar ta rufeta da duka musaman data lura
ko ajikin maryama dan babu alamun damuwa atare daita “me yasa zaki bada aikinki bayan Kinsan muma muna fama da kanmu ? “aunty kiyi hakuri kin sani ni zan iya cigaba da aikin zanena kafin na samun wani aikin ita fa ?bata da wani sanar hannu da zatayi kuma r
okona tayita tana kuka saboda bata da hanyar da zata kula da kannenta da mahaifiyarta fatana allah yasa ya zame min alkhairi ta qarasa mgnr muryarta na rawa alamun kuka “.
Aunty ta samu waje ta zauna kusa da ita tana cewa “shikenan allah yasa ki sam
u wani wanda yafi shi muryarta a raunane tace “Ameen ko da ummah da habib suka ji suma abun bai masu dadi ba amman babu yadda suka iya tunda ta bayar sai hakuri da fatan alkhairi .”washegari tana zaune a parlour’n su tare da aunty kiran ammar ya shigo ta t
ashi ta koma dakinta sannan ta d’auka tana dauka ya rufeta da fad’a “kin kyauta saboda shakuwa da qaunar da nake miki yasa na tsaya lallai Ke zaa bawa wannan matsayin saboda ina son shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninki da Adam amman kika zuba min qasa a i
do ,ina ganin idan shakuwa ta shiga tsakaninki dashi zai taimaka kwarai wajen janyo hankalin gareki shine kika bar wata .”
sanyayyen murmushi tayi kamar tana gabansa “to amman ai na fad’a maka akwai wanda zan aura .”“wanda zaki aura din banza ,wallahi
ko ba dan Adam ba nan gaba kadan zaki fara gano illar abinda kika aikatawa kanki ,kuma duk abinda ya faru babu ruwana ke kar ma ki sake nemana ko da yake ma tafiya zan yi gobe kuma zan dauki lokaci ban dawo kasar ba “allah ya kaika lafiya “Ameen amman bab
u ruwana dake wallahi ko a hanya kika gani kika min magana sai bata miki rai “a ina ma zan ganka dole sai ma’aikata kuma babu abinda zai kaini tunda bana aiki a karkashinku tayi mgnr aranta alokacin ya katse kiran .”
ranar yau din jinsa maryama tayi d
abam wani irin damuwa ta tsinci kanta ciki ita kanta tana jin mai yasa tayi abinda tayi kowa ya kalli fuskarta zai ga canji laifin kanta ta gani me yasa ma ta bar wayarta a kunne bata kashe ba da wata killa bai qara mata damuwa akan wanda take ciki ba tayi
shiru yayinda a cikin zuciyarta takewa kanta fatan alkhairi
.”awanni sukai ta zuwa suna wucewa amman maryama bata daina jin damuwa dan haka fito ta nufi bangaren ummah tana shiga ta isketa tana tsinke ewedu “sannu da aiki ummah!Yauwa maryama ya zaman gida
?gamu dai yanzu zamu fara ummah tayi murmushi “zaki samu wani aiki nan kusa ta zauna kusa daita ta d’auki gayen ewedu ta fara tsinkewa “gobe nan ma zan fara nema ssi ku tayani da addua,in sha allahu alkhairi zamu ji .”
Ahankali sukai ta hirarsu dag
a nan umma ta sako mata maganar sadam “maryama kin dai san komai daga Ke har sadam baku kawowa zuciyarku zaku zama abu d’aya ba sai gashi allah yayi ikonsa dan haka ki saki jikinki dashi karki tsaya sai yajaki ajiki ai kin fahimceni ina ganin nan da wata b
iyu masu zuwa zaa daura maku aure” maryama tayi shiru ba dan bazata aikata abinda take butaka ba bata da option dole zata jashi ajiki tuni ma ta sadaukar da rayuwarta garesa ko ba dan shi umma ta wuce komai gareta nan ta garasa yininta tare sukai komai a k
itchen har karfe shida da rabi ta buga ta fito parlour’n inda ta iske yaya sadam zaune shiru a falon da alamun yayi zurfi cikin tunani maryama ta qaraso idanunta akanshi kallon minti goma tayi masa sannan tace “meke damunka yaya sadam kayi shiru haka ? “
Ya sauke numfashi tare da sauke kwayar idanunshi akanta a natse ta samu waje ta zauna kusa dashi tana cewa “ya wurin aikin naka ? babu komai aiki kuma alhamd wasu abubuwa né suka sha min kai amman in sha allahu zan shawo kan komai na gode sosai da kula
warki “no karka damu yaya sadam , sukai shiru na kusan minti goma sannan ya kira sunanta “.marayam! ta tsura masa ido kawai tana kallonsa “ya batun aikin da kika fita nema ?”naje na samu amman na bawar qawata subai’a aikin “why ?!ya tamvayeta yana dubanta.
“saboda tafini bukata aikin itace komai na gidansu gashi mamanta bata da lafiya ga rashin mahaifi da sukai yaya sadam wallahi ina tausaya mata “gsky abar tausayi ce kin kyauta sosai da kika bar mata .”
taso yayi mata fatan samun wani aikin amman taji
yayi mata shiru “yaya sadam a fahimtata naga baka son auren mace mai aiki ya kalleta kawai “nasan kana da dalilinka kin haka amman ka yarda dani zan kare maka mutuncin aurenka wallahi bazan maka wasa da aurenka ba ,nima fa nasan ciwon kaina bayan hakinka
dake kaina akwai hakin allah dan allah ka bari nayi ayyukana “zan duba !ya fad’a atakaice tare da mikewa tsaye “na gode sosai “.
******
Cikin sauri ata ya shigo office dinsa mataimakinsa na biye dashi ya zauna a mazauninsa yana kallonsa batare da y
ace
komai ba “good morning sir “morning! Ya amsa atakaice yana maida hankalinsa Kan system “uhm amma sir ko zan iya magana yanzu “uhm ! Ya fad’a a takaice daman
akan yarinyar nan dana baka labari tana da kwarewa sosai akan lissafi duk wani lissafi na ka
mfanina nan tasan kansa ta hada komai daake bukata takardunta sunyi kyau sosai kuma anyi mata interview komai nata daidai ,amman abun mamaki tace bata bukatar aiki damu wai a dauki wata amadadinta .”ATA ya dago kyawawan idanunshi a natse yana furta “ what
? She rejected our job duk yadda aiki yake wahala a kasar nan? .”
Ya kankantar da idanunshi tare da yin shiru yana tunanin abinda zai sa wani mutun biladam mai jini ajiki yayi rejecting din aiki a maakatarshi ya hade rai sosai cike da takaici a fuskar
sa sannan Ya koma ya zauna sosai akan kujera yana jujjuyawa a hankali yana cigaba da tunanin Ya furzar da iska mai zafi yana tsotsa keyarsa “ina ganin wannnan yarinyar tana da damuwa a brain dinta ,kai kwata kwata ma dakikiya ,for god sake ni me ye damuwat
a yanzu ? me yasa zaka kawo min wannan banzar maganr ?meye damuwata daita dan taki amsar aiki inda ga mutane can bila adadin suna nema ?ya qarasa mgnr cike da jin haushi yana ja tsaki “ noncess !Ya furta yana dungule hannunsa .
“Am very sorry sir da
man dan ka bukaci mai ilimin lissafi ne shiyasa har muka bukaceta amman dai tace zuwa nan gaba zata iya kasancewa damu “I don’t care kawai make sure bata samu aiki a koina ba a duk fadin garin nan, kai har karshen rayuwarta duk inda kuma aka dauketa aiki l
et me know .”
“an gama sir …ring din wayarsa yasa seun yayi shiru tare da daukar wayar ya mika masa cike da girmamawa Ya amsa ya manna a kunnensa tare da mikewa Ya qarasa jikin window office dinsa yana kallon haraban ma’aikatan yana amsa wayar ransa duk a
bace “daga can bangaren nana hauwa’u ta gaishesa “ ina kwana yaya ?”lafiya ya kike auta? “lafiya ! daman na kira na fad’a maka zan biya na d’auki maryam muje gaishe da mami “okay ! ya fad’a tare da katse kiran .”ya cigaba tsayuwa yana jin zafi aransa .”
Nana hauwa’u tayi shiru kafin daga baya ta mike tsaye ta kammala shirinta ta fito ta shiga mota kai tsaye hanyar gidansa ta dauka daman sunyi waya da maryam din itace ma tace ta kirasa ta fad’a masa a bakin kofar gidan ta tsaya ta kirata bayan ta fito
ta shiga gaban mota suka dauki hanya suna tafiya suna hira maryam tace “sister ya zamanku da yaya hisham kuwa naji kwana biyu bakya magana akanshi “na gaji sister na kawo ido na zuba masu duk wanda yayi da kyau zai gani ina sauke duk abinda ya rataya a wu
yansa na zamantakewa aure hakinsa ne ban tauye masa ba idan ya nema zan bashi
,idan bai nema ba huta roro zama haka maryam ta sauke numfashi tace “duk da haka dai ai naki da sauki tunda yana cin abincinki “eh to da sauki gsky Kinsan daman shi ba mai daukar
abu da zafi bane kamar yaya bane .
“Ni dai gsky babu wani sauki a zamanmu dashi muddin yana gida bani da kwanciyar hankali sausaucin da nake samu dukkaninmu kuna kokari dani ,kuma na gode sosai da kulawarku ‘yanuwa allah ya bar zumunci amman ina ji
n tsoron ranar da zai hadu da wacce yake so yace zai qara aure ina rokon allah kafin zuwan ranar allah ya kasheni dan nasan bakincikin da zan qunsa yafi wanda nake qunsa yanzu “ babu wannna ranar for now mami fa tace muddin yana son qara aure sai ya kwanta
r miki da hankali shi kuma Kinsan halinsa da wahala ya kwantar da kai “kina ganin har yarinyar mafarkinsa in da zasu had’u mami bazata yarda ya aureta ba ?”yadda idan mutun ya mutu baya dawowa haka labarin wannan mafarkin nasa yake.”
Maryam tayi shiru
tana tunani nana hauwa’u ta dafata tana cewa “don’t worry siater komai zai daidaita kinji “ naji amman rayuwarta abar tausayi ce baya son ganina baya son ko jin muryata idan ya ganni ko yaji muryata Kmr ya matu mgn kadan nayi yace na cika surutu ni yanzu
dan allah ina da magana ?tai mata tmby tana dubanta girgiza mata kai nana hauwa’u tayi “wallahi bancin na bar gidansa mami zata shiga damuwa wallahi dana gudu,” ki gudu kije ina? kar ma ki soma muna tare babu inda zaki maryam ta girgiza kai tana jin zafi a
ranta sister wallahi baki san abinda nake hadiya bane .”idan kika tafi babu ni babu ke har abada zumunci mayi a lahira maryam tayi saurin goge hawyenn daya soma bin gefen idonta tare da cewa “ nima wasa nake babu inda zani muna tare mutu ka raba tafiyar mi
ntuna ta kawosu bakin get din estate dinsu sukai hon masu tsaron get suka bud’e masu suka shigo sukai parking .”
atare suka nufi gidan mami suka kunna kai ciki tare da sallama a parlour’n suka iske Aunty shahida ,da Aunty khadija ,har ma da Aunty zabi
ba zaune sai mami da mamaki maryam ta bude baki cikin tsananin farinciki da gudunta ta kwaso bata zube gaban kowa ba sai a gaban aunty shahida ta ruqunqumeta tsam ajikinta tana cewa “wayyo allah babbar yaya naji dadinku daman sister kinsan suna nan ne ?ko
daya yadda kika gansu yanzu nima haka nagansu ta zame jikinta ta durkusa gabanta “ina yini babbar yaya aunty shahida ta shafa fuskarta “ya kike maryam “lafiya lau .” ta isa gaban mami ta durkusa ta gaisheta cike da farinciki da girmamawa cike da kulawa mam
i ta amsa tana kallonta a tsanake “ dan tun washegarin tarewarta sai yau ta sake