Showing 102001 words to 105000 words out of 172989 words

Chapter 35 - MAR’ADAM’S COMPLETE

30 Aug 2026

39

hakurinki dan muddin kikayi kuskure sake zuwa inda yake zai iya kasheki tunda har ya rantse

“ya allah ka taimakeni kasa na samu ciki a karon mu na biyu dashi yanzu ta shiryawa kowani rigima zaiyi idan ciki ya bayyana ajikinta a boye take goge hawayen dake bin kuncinta ,har mami tagama tayi laziminta da sauran addu'o,inta

.bacci bai yi nasarar d

aukar maryam ba kuka take qasa qasa . Tana jin motsin mikewar mami ta shanye kukanta Tare da goge hawayen idanunta amman hakan bai hana mami gane wani abu ba ,daidai inda fuskarta take tazo ta zauna tare da kamo hannuta ,"me kike tunanin maryam ko kum

a nace me ya dawo dake dakin nan har ya hanaki bacci ?

Kafin maryam tace wani abu mami ta km jiho mata wata tmbyr “sai ma naga kmr kuka kika yi ko?

Maryam ta Mike zaune suna fuskartan juna da mami ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka

yi nasarar zubowa...."mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi fa? sai

km ki kama min kuka.” wani abu adamcy yayi miki ?ahankali ta girgirwa mami kanta “ki fad’a min idan wani abu yayi miki da kyar maryam ta iya bude bakinta ..." ammi me yasa yaya

Adam ya tsaneni haka ?kullum so nake naga na rayu dashi har qarshen rayuwa amman shi kullum burinsa ya ruguza rayuwar gidan aurenmu da ni kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar kowasu maurata ".

“basan abinda na aikata masa

ba da kullum yake son ganina cikin qaqa na kanyi .Ida abubuwa da yake min suka cigaba da faruwa bana tunanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da bugawa , mami tambayar min shi laifin me nayi masa ?”wallahi ni ina qaunar zama dashi muddin raina .”mami ta

rungumeta ajikinta tana mai tausaya mata "kukan ya isa haka babu abinda kika masa halinsa ne haka

halin bakar zuciya irin tasa yana damuna ni kaina na gaji da halinsa ,amman matsawar Ina raye ba zaki taba kasancewa cikin bakinciki ba , bugu da qari

har yanzu kina da sauran damar rabuwa dashi dan bazan cigaba da baki hakuri ki cigaba da zama dashi ba dan duk wani abinda zaa masa anyi masa idan dai ba rayuwarmu yake nema ba .”

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗

MAR'ADAMS



💖💖💖💖

💗💗💗

💗💗💗

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

AREWABOOKS USERNAME

AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdulla

hi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 19

Sosai mami ta dinga rarrashin maryam tana masu addua “allah

ya daidaita tsakaninku ,Allah ya saka tausayinki acikin zuciyar adamcy ,allah ya kawo zaman lafiya a tsakaninku har

qarshen rayuwarku “ahankali maryam Ke amsawa da “Ameen mami ,sai abu na gaba maryam na fahimci kina sakaci da addua ,Ina son kinsan wani a

bu ba’a nasara sai an rike Allah,idan ka rike Allah,Allah ta’ala zai taimakeka ki jajurce da adduoi maryam “ki rage wasu abubuwa ki maida lamarinki zuwa ga Allah maryam ta gyad’a mata kai alamun taji ,tana nan kwance ajikin mami har ta fara gyangyad’i ala

mun bacci .ahankali mami ta d’an buga bayanta tana cewa “maryam kwanta kiyi bacci da sannu allah zai kawo mana saukin wannan tashin hankali sannan ya kawo fahimtar juna a tsakaninki da mijinki .“maryam ta tashi daga jikin mami tana shafa idanunta sannan

ta zame ta kwanta zuciyarta cike da soyayyar mijinta mami ta mike itama ta samu gurin nan kusa da maryam ta kwanta sai dai ita sam bacci yaki d’aukarta, kwakwaluwarta ne ya shiga cajin tunani

dan dole tasan abun yi tun kafin adamcy ya kashe maryam da b

akincikinsa dan zuwa yanzu hakurinta ya fara qarewa akanshi .”

Juyi kawai mami take akan katifa kafin ahankali ta taashi ta sauko daga saman katifa ta tsaya gaban maryam tana kallon fuskarta bacci take, sai dai kana kallonta zaka san a matuqar

wahale take baccin dan kana kallon yadda take sauke numfashi da ajiyar zuciya da karfi .”d’auke kwayar idanunta mami tayi ta fara zagaye d’akin kafin ta fara zance zuci ita kad’ai “dan dole zulai kiyi wani abu akan zaman ya’yanki “ to mai zanyi ?mai zanyi

? ta tambayi kanta har sau biyu tana cure hannuwanta waje d’aya “Kiyi qoqari adamcy ya kusanci maryam ko Allah zai basu rabo wata killa sanadiyyar hakan ya sauko ya sausauta mata ya rungume aurensu. “tabbas haka zakiyi zuciyarta ta bata wannan shawarar “

to ta yaya zan masa magana ya fahimci abinda nake nufi ?”ta sake jefawa kwakwaluwarta tambaya shiru tayi yayinda ta koma ta kwanta akan katifa tana sauke numfashi tana mai sake had’e hannuwanta guri d’aya kafin ahankali ta soma sakin wani irin murmushi

sakamakon abinda zuciyarta ta shirya mata wanda zai kawo mata saukin al’amuran ta, alokaci d’aya ta sauke wani naunayen ajiyar zuciya “dole dai kina bukatar shawarar shahida kafin ki aikata komai .”

Washegari da misalin karfe tara na safe maryam

tana zaune akan kujerar sofa tana danna waya yayinda mami ke zaune akan salayya tana lazimi ATA ya shigo bakinsa d’auke da sallama sallamarsa kawai maryam ta amsa batare da ta kallesa ba ta cigaba da daddanna wayarta shima ko kallonta bai yi ba ya cigab

a da tsayuwa mami ta d’an kallesa yana sanye da jallabiya yayi mata kyau sosai sai dai bata jin dadin ganin yadda ko yaushe fuskar nan tashi take a had’e’ ,sannan bata jin dadin ganin shi da maryam haka zaman su sam babu sha’awa kana ganin yanayinsu kasan

gabad’aya zukatansu basa cikin

walwala da jin dadi most especially adamcy wanda zaka fahimci baya son ko bisa kuskure ya kasance a duk inda maryam take .yayinda ita kuma tafi qaunar su kasance tare akoda yaushe ya rungumeta babu kyama ,mami na kallonsa

ya juya cikin takun isa ya fita daga d’akin ganin tana lazimi ,bayansa mrym tabi da kallo har ya fice gabad’aya tasa hannu d’aya ta dafe goshinta tana jin wani tuttukin bakinciki tana jin zafi da ciwon abinda yake mata na kyarma da rashin son kallont

a inda take ,amman ita ta rasa dalilin da yasa zuciyarta kullum take sake macewa akanshi ,a kullum zata d’aura kwayar idanunta akanshi to wallahi son shi da qaunarsa ne Ke sake huda zuciyarta da gangar jikinta” zata so ta mallakesa kamar yadda mahaifiyarta

take buri amman hakan taki samuwa kullum babu abinda take hangowa attare dashi sai zallar qiyayyarta sam komai nata baya burgesa ita kuwa kwarjininsa kesa bata iya d’aukarwa kanta mataki ,bata iya tunkurarsa da komai tana matuqar jin tsoronsa aranta “da s

anyi jiki mami ta qaraso inda take zaune ta kai hannunta ta dafata, ta d’ago tana duban mami da idanunta dake cike da ruwan hawaye mami tasa gefen hijab dinta ta goge mata hawayen da suka zubo mata batare da saninta ba wani wahallen ajiyar zuciya ta sauk

e tana kawar da fuskarta gefe“

“maryam !”

Mami ta kira sunanta ahankali maryam ta waigo inda mami take ta sake zuba mata idanunta tana kallonta fuskarta da tsananin damuwa ahankali ta sauke idanunta “ki daina damun kanki akan adamcy idan ba haka ba

zaki rasa lafiyarki idan hakan kuma ta kasance babu ruwansa hasalima bazai ta’ba zama damuwarsa ba sai dai ta zama damuwarmu “kiyi hakuri ki dinga kawar da damuwar nan aranki sannan ki dinga kaiwa allah kukanki ,nasani maryam kina hakurin zama da adamcy n

e saboda Kina matuqar ganin girmana da mutuntani da kuma qaunar da Kike masa nima kuma haka ne acikin zuciyata maryam ina qaunarki ina qaunar ku kasance a inuwa d’aya dashi .”numfashi ta sauke da karfi tana kallon mami “eh shine ma dalilin da yasa bakya so

n na rabaku maryam .

Maryam ta tsurawa mami idanunta “ko karya ne bakya sonsa ?zazzafan numfashi maryam ta sauke ta kasa cewa komai dan tasan gsky mami ta fad’a “kina dai danne sonshi ne saboda rashin qaunar da yake nuna miki amman ni naji ajikina ki

na qaunar adamcy ,maryam taji dadin yadda mami ta fahimci hakan sai dai kuma zuciyarta tayi rauni wasu sabbin hawaye suka zubo mata mami ta sake share mata “kuka bayayi miki kyau maryam hakan ya sake karya wa maryam gwaiwa ta fashe da wani kuka sosai .“wal

lahi mami ban san lokacin da son shi ya shigeni ba “nice silarsa maryam kuma nayi danasani had’aku aure ,mami ta fad’a da matsanancin tausayinta ,duk yadda mami take jin qaunar adamcy ji take tafita qaunarsa maryam ta tsananta kuka tana tuna tun lokacin

data fara jin qaunar yaya Adam din acikin ranta rungumeta mami tayi tsam tana rarrashi

alokacin wayar maryam ta soma ringing mami ta zare jikinta tana kallon maryam itama d’agowa tayi ta kalli mami sannan ta kalli screen din wayarta bata dauka ba ta cig

aba da goge hawayenta yayinda kiran ya cigaba da shigowa still maryam bata d’aga ba .”

mami ta d’an yi gyaran murya “wake kiranki ne tun d’azu ?ummah ce !ta bata amsa atakaice idanunta na cigaba da zubar da hawaye “me yasa bazaki d’auka ba kika sani k

o kiran mai mahimanci ne ?shiru maryam tayi ta kasa cewa komai dan tasan kiran me take mata, ita kuma ta gaji da abubuwan mahaifi yarta ,kullum abu d’aya kuma babu wani biyan buqata “ki d’auki kiranta kar rashin d’aukar kiran yasa hankalinta ya tashi tayi

tunanin ko wani abu ne“.ahankali maryam ta gyad’a mata kai tana “cewa mami bari naje na dafa miki ruwan zafi “to shikenan maryam amman ki hada min da abinci “bamu da komai fa mami ,karki damu ki dafa min abinda kuke dashi . Mrym ta mike tsaye ta fito tana

qoqarin d’aukar kiran mahaifiyarta daya sake shigowa ta sauko kunnenta manne da waya “umma dan allah ki daina kirana na tura miki sako mami tana gidan nan bana son taji komai “ amman me yasa zaki fad’i haka ummah?” kema Kinsan mami tana matuqar qaunata

“a’a umma nifa gsky na gaji kawai abarshi na hakura bazan iya ba dan duk abinda zaa zuba cikin abinci bazai ci ba tunda baya cin girkina ,shiru maryam tayi tana jin yadda mahaifiyarta ta balbaleta da bala’i ta inda take shiga bata nan take fita ba.”

“kiyi hakuri ummah ba wai bana ganin qoqarinki bane saboda mami idan ta fahimci akwai abinda muke shiryawa d’anta zata ji babu dadi to shikenan gara ma wannan zamu iya sake gwadawa ko za’a samu ya kwanta akai ,to shikenan amman dan allah ummah karki kir

ani kiyi chart dina muyi komai ta chart ta qarasa mgnr tare da shiga kitchen ta soma qoqarin d’aurawa mami abinda zatayi breakfast dashi cikin kankani lokaci ta gama dafa ruwan zafi ta zuba cikin flaks sannan ta dafa shinkafa da miya ta fito tana qoqarin

qarasawa dining mami ta sauko tana cewa “sannu da aiki maryam ?murmushi ta saki tana cewa “kai mami wani aiki kuma byn shinkafa da miya ce kawai na dafa miki. murmushi mami tayi tana cewa “kawo min nan diyata ta qarasa inda kujeru suke ta zauna maryam t

a biyo bayanta ta ajiye kular abinci akan center table maryam tace “nasan idan kowa yaci abincina yace babu dadi mamina bazatace babu dadi ba ?”ina sam bazan fad’a haka ba zuba min na matsu banji dandanon abincin my daughter ba “abincin dai mami sai dai

kiyi hakuri babu komai aciki ta qarasa mgnr muryata a sanyaye “karki damu maryam fara had’a min shayi cike da kulawa maryam take hidima da mami yayinda mami ke nuna mata farincikinki a zahiri amman a bad’ani bakinciki ne cunkushe acikin zuciyarta suna zau

ne ata ya fito yana taku a natse akan step sanye da kananan kaya jikinsa sai fitar da sihirtaccen kamshin turarensa yake ,ya qaraso

parlour’n qasa hannuwansa duka zube cikin aljihun wondonsa tun daga nesa ya hango mami zaune tana breakfast da ruwan te

a zalla babu wani abun hadi danginsu soyayyen Kwai da bread ko arish da sauransu abinda yasan ba d’abiarta bace, abun yayi matuqar bashi mamaki dan haka kai tsaye store ya shiga adaidai lokacin maryam ta mike ta nufi hanyar sama d’auko chazar wayarta

.”

yana shiga dube dube ya fara bai ga komai ba ya fito ya shig kitchen duk sai daya duba cabinet din kitchen din nan ma bai ga wani abun kirki da zaa had’awa mutun breakfast mai kyau dashi ba dan haka jiki a sanyaye ya fito yana kwallawa maryam

kira yayinda mami tana nan zaune tana kallon tv tana cigaba da kora ruwan tea da sauri maryam ta sauko tana dubansa gabanta na wani irin bugawa da karfi muryarta a raunane tace “ yaya gani ?“meye haka ?me ya faru kuma ?itama tayi karfin halin tambayarsa

har ya d’aga hannunsa ko me ya tuna ya sauke ya dafe goshinsa a fusace ya cire hannunsa ya d’an saci kallon mami ita kuma ta zuba masa idanu tana ji da ganin abinda zai faru maryam taja baya tana jin yadda zuciyarta ke rawa “meye wancan agaban mami ?ya sak

e wulla mata tmbya tayi shiru tana dubansa a tsorace ya zira hannunsa daya cikin aljihunsa yana sake yin magana a tsawace “meye haka ina magana kina jina ?abinci ne !”what ?!ya furta a tsawace .”

ta sake ja baya kar ya wanka mata mari dan a yanayin

da yake kallonta babu sausauci “amman zaki iya bawa mahaifiyarki irin wannan breakfast din ? gabanta yayi wani irin mugun fad’uwa ya tsura mata ido hakan ya bala’i bata tsoro gbdy ya sake canza mata ya fara taku zuwa inda take tsaye tana yar kyarma tana ba

ya baya yana biyota har sai data kurewa bango “wallahi ba da gangan nayi ba babu komai a store ne komai ya qare iya abinda muke dashi na bawa mami .” afusace ya d’aga hannu zai wanka mata mari cikin wani irin masifaffen tsawa yaji sautin muryar mami “wall

ahi idan ka ta’bata ban yafe maka ba .” cak ya tsaida hannunsa tamkar an dasashi zuciyarsa na tafasa cike da zafin zuciya ya sauke hannusa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya juyo ya soma taku cike da ‘bacin rai ya qaraso ya zauna kusa dai

ta kamar mai neman gafara ya fara kame kame “umm umm ummm nace ba “kace me ?”shiru yayi yana kallon mami yayinda maryam tayi sauri ta haye sama tana wai wayensu “ina jinka adamcy ?”Kiyi hakuri sweetheart banji dadin yadda naga kina breakfast haka ba “ ban

a zama a gida bansan babu komai a gidan nan ba sannan wannan yarinyar bata fad’a min babu komai ba ya qarashe maganar kamar zai yi kuka.”

mami ta kallesa sosai ta gano halin damuwar daya shiga adalilin breakfast dinta, daman kuma tayi hakan ne dan ya

gani numfashi ya sauke yana sosa keyarsa yana cigaba da

kallon mami ahankali mami ta tabe baki “to ka bata damar da zata fuskanceka bare ta fad’a maka babu komai acikin gidan nan “?amman !”sai kuma yayi shiru yana runtse idanunshi .”amman me adamcy ?kai

kanka kasan baka da wata kalmar da zaka fad’a min na yarda a matsayinka na magidanci baka bawa matarka wannan damar ba sam matarka bata da cikakken iko acikin gidan nan yadda kake nuna baka qaunar jamaa da yanuwanka haka kake nunawa matar aurenka ,kai kank

a kawai kasani baka damu da damuwar kowa ba dan haka karka rainawa kanka hankali ka nemi daurawa yar mutane laifi “ta qarashe maganar cikin fad’a saboda halin adamcy baqaramin damunta yake ba ,shi mutun ne wanda babu ruwansa da damuwar jama’a sai dai kansh

i da aikinsa ya kamo hannun mami ya soma rarrashinta “sweetheart Kiyi hakuri kema Kinsan yanayin aiki ne sai ahankali ,ni kaina bana samun time din kaina kamar yadda kika sani amman at least data fad’a min zan sa a kawo komai “ta bishi da wani mummunar ka

llo “wai yaushe ka bawa maryam wannan damar yarinyar nan haka take rayuwa cikin qunci acikin gidan nan ga rashin so ga yunwa dame zataji ?”allah sarki maryam baiwar allah allah dai ya qara miki hakuri amman na cuceki na hadaki da damuwa ,na hadaki da mutun

mara kirki ,na hadaki da mutun mara zumunci wanda ko yan’uwansa baya so bare wata aba maryam wallahi adamcy baka da tausayi da amana nayi danasanin hada auren nan allah dai ya gyara maka wannan bakar zuciyar taka .”

Kuka yaci karfin mami .”

jikin A

TA yayi mugun sanyi babu abinda ya tsana kamar hawayen mahaifiyarsa da bai da kamarta jin kukanta yake har cikin zuciyarsa ya sake matsowa kusa daita yasa kanshi akan cinyarta yana jin yadda zuciyarsa yake tafasa yana jin kukanta yana ganin laifinsa amman

yafi ganin laifinta domin kuwa itace sanadin da yasa ya kasa sauke nauyin da allah ya daura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login