Showing 3001 words to 6000 words out of 144199 words
tadauki jakanta tarufe tagoya abaya tasa hannu tabude kofan bayin hada ido tayi da maza biyu daketa sintiri awajen ta ballamusu harara tacire board na close dake gaban kofan bayin takoma ciki ta ijiye sannan ta gunguro ga
rbage can din da kyar sabida nauyi amman ta daure tafita tafito dashi ko kallonsu batayiba saima wakanta data cigaba dayi abinta tawuce tasauka har kasa tazaga baya inda suke ijiye dattin saida ta jujjuya ganin babu kowa yasa tabude marfin bolan batare dat
a kalli cikiba tace “you are safe yanzu you can come out” kafinma ya yunkuro tajuya abinta tahau tafiya dan sauri take is already 3:30 by 4 zata shagon abinci gashi this whole drama yabata mata lokaci, da kyar ya iya ya lallaba yafito daga bolan sai amai d
uk wani abu dayaci saida ya amayar dashi sai kakkabe jikinshi yake yadago zai mika mata gyalenta daidai tanashan kwana harta tafi, he wanted to say thank u dudda she’s a crazy wicked girl tana zubamai dirt tana murmushi but she helped him, hannunshi yakai
aljihunshi yataba but baiji wayanshi ba kuma baisan a ina ta fadi ba wlh kuma shi bazai duba bolan nan ba, daidai wani cleaner na gunguro nashi bolan dasauri yace “please bani aron wayanka nakira” binshi yayi da kallo ganin kaman ba lafiya yasa yabashi way
anshi Munir yakira kafin yayi magana yace “Munir kazo ka daukeni a airport pls karka fadama kowa kana zuwa katambayi wajen zuba bola ina wajen” kafin yayi magana ya katse wayan yabama yaron yazauna awajen kawai feeling terribly sick kusan 1hr yana wajen j
ikinshi yadau mugun zafi ga tsigan jikinshi na tashi kaman zai mutu yana zaune ahaka yaji ance. “Riyad” dasauri yadago kanshi da gudu gudu sauri sauri Munir yataho wajen yace “what happened to you like this? Wat are you doing here? Why are you so dirty”? T
ashi yayi yana kokarin yima Riyad magana yace “someone
tried to kill m…..” kawai ya sume da kyar Munir yasamu wani cleaner yazo kawo datti shima aka tayashi daukanshi suka tafi mota aka sashi sai gida bayan yakira Mom akira Dr.
Tawani special secret gat
e Munir yabiyo aka budemai already ga mutane tsaitsaye Gwaggo (Mai Babban daki) gawata black beauty mata dake sanye da hijab mai dan kiba (Mom), Wambai, Waziri, Kabeer da su Halilu, Ibrahim da Shuaibu, Baffa Mujitapa dukansu suna wajen da family Dr nasu, y
ayi parking agurguje Munir duk sukai wajen fashewa da kuka Mom tayi tace “what happen to yarona Munir? Wakeson kashemin shi daga shigowanshi garin nan? How did they even know ya shigo? Gwaggo jini a hannunshi look, Doctor do something” Mom tai maganan tana
kama hannunshi ashe wukan ta yankeshi dazu, atare dukansu mazan suka ciccibeshi zuwa wani dabkareren flat na Mom Gwaggo tace “meya sameshi haka Munir? Jibi jikinshi? Meya faru Munir”? Dasauri Munir yace “Gwaggo nima bansani ba but kaman he was attacked ne
, yana kokarin fadamin wai ana kokarin kasheshi ya sume ba wayanshi taredashi, shi babu akwati, akusa dashi, awajen bola naganshi da bag pack yana mota dawani dan kwali black, kafin yafadamin komi kuma yasuma” gam Mom tarike hannunshi har daki kan wani tas
keken gado aka kwantar dashi Dr yashiga dubashi yanda skin nashi da fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace “a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he’s allergic to dirt da kazan
ta right from small, kuyi sauri pls” fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace “wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan?” Anatse Wambai yace “call the police I think sai anbincika airport din maybe t
a CCTV za’a gani” faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace “Dr an gama” dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi
yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace “anjima kadan zai farfado don’t worry” dan murmushi tayi tareda gyadamai
kai Waziri yace “ki zauna dashi” Gwaggo tace “nima ina nan kome za’a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d’ana ba yanzu halakamin jika za’ayi wlh jinina yasha karfin kowa” kallon Munir
Mom tayi ahankali tace “thank you Munir” gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace “ki tsare yaron nan ki dage da addu’a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma
babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi
tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuw
arsa dakuma lullubinsa” gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace “Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi” Gwaggo tace “kwarai” Mom tace “shi kadai
Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi” kankame hannunshi tayi tace “Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan
zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari” sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu’a aka.
JOIN GROUP DANAKE POSTING NOVEL DIN NAN
https://chat.whatsapp.com/CrKHphXCxK09RvYbrO1cCU
[5/20, 7:53 AM] +234 806 065 9266:
💫
SANYI DA ZAFI
💫
EPISODE 3
️
⃣
✍
🏻
M SHAKUR
WHEN WAS THE LAST TIME KIKA SAYI SABON PANT?
🤭
TALK T
RUE
BRA DINKI SUN KOMA RUWAN KASA TSABAGEN SAWA KULLUM
😒
TO IDAN NACE YAU NAKAWO MIKI HABISHMA UNDERWEARS FA
👙💃
SUNA SAIDA PANTS, BRAS, NURSING BRA, MATERNITY GOWNS, NO LEAKAGE PANTS NA PERIOD, KAYAN BACCI DA SAURANSU
🔥
SUNADA MOST AFFORDABLE KAYA
GA VERY CHEAP DELIVERY NATIONWIDE GO AND BUY NOWWWW!!!
https://www.tiktok.com/@habismaunderwears?_t=8lzVAMnAhgk&_r=1
4 daidai tashiga wani babban kanti na abinci irin local restaurant din nan, wata katuwar mata dake zaune a tsakiyan shagon kan kujer
a ga lalitan uban kudi a hannunta tana kirgawa ne ta kalleta tace “Allah yasoki baki latti ba” batace komiba kai tsaye tace “ina wuni Maman Miwa” batare data amsaba tace “nidai je ga wanke wanken ki chan na jiranki” bata damu da yanda tamata maganan ba dud
da akwai mutane a shagon sunacin abinci tace “bari nai salla naje nayi” bata jira amsanta ba tawuce ciki chan bayan gidan shagon bayi taje tacire kayan jikinta tafito da dogon riga na abayan dake jakanta tana neman gyalen ta tuna tabawa mutumin nan tsayawa
tayi chak sai kawai taja gajeren tsakiya saurin datake tazo nan yasa ta manta bata amsaba, karamin farin hijabin tasaka ta dauro alwala tafito tasami waje tai salla sannan ta cire hijabin tasa kan igiya fari ne batason ruwan wanke wanke ko mai ya bata mat
a taje gaban makwarara, ga wanke wanke zaka dauka na gidan biki ne ga manya manyan tukunyan abinci, omo ta dauka ta tara ruwa abaho dukta kawo sannan ta dauki wayanta kirar vivo duk taci screen tasaka earpiece ta danna waka ta soke wayan aljihun dogon riga
n tashigayin wanke wanken da sauri sauri dan tanada kuzari sosai batada kasala ko son jiki.
Wata yar budurwa ce tazo wajen ganinta tana wanke wanke tana waka kasa kasa like zero worries dinnan yasa ta harareta tajuya tafito tadawo cikin shagon tazo gaban
mahaifiyarta dahar lokacin take kirga kudi tace “wai Mama Yar gidan HIV dinchan kikesa take mana wanke wanke har yanzu banace ki sallameta ba gashi gashi abinda ake cewa ita da Mamanta sunada shi” batare da maman ta kalletaba tace “koyar gidan kanjamau ce
ba HIV ba ina ruwana ko kinada wanda zaki samo dazatamin wanke wanken nan ta share ko’ina har zuwa katon shagon nan akan dubu biyu kullum aduk fadin garin kanon nan?” Baki yarinyar tabude zatai magana Maman Miwa tace “kinga ki kyaleni fa, nagadai nace
kiyi
aikin nan bayi zakiyi ba” dasauri yarinyar tace “Mama ni kyamanta nakeji wlh, sunada HIV tana mana wanke wanke” dasauri Maman Miwa tace “wai sau nawa zan gayamiki Maman ta kedashi ba itaba yarinyar datake karatun likita, to koma tanadashi me ruwana nagada
i ciwon nan ajini yake kuma baya kwarara acikin ruwan wanke wanke ko? Miwa dan Allah ki barni na kirga kudin nan kinatasa ina mance abinda na kirga” tsaki yarinyar tayi tawuce tafita daga shagon cikeda bacin rai.
Kafin 1hr tagama wanke wanken nan tass, tu
kunyoyin har bayansu ta wanke kal sai kyalli suke ta share ko’ina tashigo shagoma ta share tsaf tai mopping lokacin biyarda rabi sannan takoma baya tasa hijabinta tadauko jakanta ta goya abaya tafito tazo gaban Maman Miwa tace “nagama” kallonta Maman Miwa
tayi tace “ohh kudinki ko”? Gyadamata kai tayi, kudin hannunta Maman Miwa tashiga kirgawa taciro 10k tabata tace “gashi na litinin zuwa yau juma’a” murmushi tayi for the first time dan gaskiya she hardly smile kaganta tana murmushi ko dariya to sai in tana
tareda Mamanta, takirga kudin tass dubu goma chip chip tace “nagode Allah yabiyaki” tajuya tawuce kallo Maman Miwa tabita dashi ance duk muguntan ka kaji an maka wani addu’an saikaji ranka ya sosu harta fita waje Maman Miwa tace “Rasheeda!” Dasauri yariny
ar tajuyo jin an kirata, komawa cikin shagon tayi tace “na’am gani” kallon sales girl dinta Maman Miwa tayi tace “samata shinkafa da tuwo a takeaway takaima Mamanta” wani kalan murmushi tayi dayasa wani hot dimples suka lotsa a kumatunta Ya Allah! She look
s damn beautiful dasauri tace “nagode sosai, nagode nagode” Maman Miwa sai kallonta take dan wlh today is the first time in almost 3months data fara musu aiki take ganinta tana murmushi, yarinyar kam badai kyauba, ta tabbata badan cutan su ba da tuni wani
babban Alhaji ya aure ta, kawomata abincin akai a leda ta amsa wannan karan saida ta duka tace “nagode sosai Maman Miwa” murmushi Maman Miwa tamata tace “sai Allah yakaimu gobe” gyadamata kai tayi tafice Maman Miwa tabita da kallo wani zubin she wants to
be wicked amman kuma indai kai ba shaidan bane u can’t be wicked to this girl cus zata maka aiki tsakani ga Allah dabazaka taba ganin abinda zakai complain akai ba, wanke wanke take maka tsaf, tai shara tai moping kaga ko ina na kyalli, banda haka daidai
da tsinke bata taba sata a shagon ba wlh ko kwayar magi bai taba bataba dudda ko basudashi, kowa ya tsaneta kowa kyaranta yake sabida Mamanta but if u look at it ciwo nakan kowa, zata gudu tabar mahaifiyarta ne sabida tabada HIV? No, ba HIV ba ko HIVVV uwa
rta kedashi uwarta ce, dudda ma taji labari ance mai kudi mahaifiyarta ta aura but taje tai fasikanci tasamo HIV yakorota yace cikin ma ba nasa bane, hmmm tasauke ijiyan zuciya tace “Allah ya kyauta dai”.
Tafiyan datayi zaiyi nisan tafiyan inda zakaje k
abiya 200 ko 300 kan adaidaita sahu amman akafa tai tafiyan nan tana shiga layinsu ta tsaya gaban wani chemist ta kirga 6500 tabashi tace “ga kudin maganin nagode” karba yayi yace “an dawo daga aikin Rashy” gyadamai kai tayi batace komiba ya karbi kudin ya
na kokarin kirgawa daidai ta juyo zata fito wasu maza guda biyu na zuwa wajen daya daga cikinsu yakalli mai shagon yace “kai Bala nagaya maka idan kana bari yarinyar nan na shigowa shagon ka bazaka taba yin ciniki ba ni nama fasa sayan abinda nazo saya mts
www yawa kake wlh gaye” yajuya harya fara tafiya Rasheeda tace “ko dabba yafi jahilin namiji mara ilimi daraja tirr, adaije makaranta akaro ilimi katon banza” chak saurayin ya tsaya saikuma ya juyo yanuna kanshi yana kallonta kur itama Rashida ke kallonshi
yace “dani kike”? Dasauri Mai chemist din Bala yazagayo yana daga marfin kanta yafito yace “badakai takeba Rashida tafi gida kudin sun cika nagode” wani kalan kallo tama mai chemist din tace “akanme zakace badashi nakeba Bala? Inba dashi nakeba waye yamak
a kama da jahili awajen nan”? Wani tahowa gayen yayi azuciye zai daketa yace “zan sumar dake wlh ke” dasauri Bala yatareshi yace “me haka kai Sani dukan mace zakayi”? Wani kalan dariyan daru Rasheeda tayi tasauke jakanta dake goye
abayanta ta ijiye ledan a
bincin hannunta duka akasa tanuna kanta tace “nizaka daka?” Tasake dariyan keta tace “billahillazi yauka tabani saidai uwarka ta haifo wani zan gwada maka ni dakake gani kaman maza dari ce anan, try me I will make sure namaka abinda baxaka so ka karabin ha
nyan danake bi ba” tai maganan azuciye cike da fushi da masifa da rashin tsoro, dasauri Bala mai chemist yakalli abokin Sani yace “please rikeshi ku tafi dan Allah Kamal” kamashi abokin yayi yace “muje Bros shareta pls ba riba a fada da mace” Rasheeda tace
“kasan Jahili baida ilimin sanin hakan wannan dahar yanzu ake raba shayin safe dashi agida” haba wani kalan fizge kanshi yayi yakawo mata duka da duka karfinshi kaucewa Rashida tayi da sauri yasami bango batai wata wataba ta daga kujeran dake wajen na zam
an mutum plastic chair ne ta rapkamai a fuska kafan kujeran ya yakushi bakinshi haba bakinshi sai jini ganin jini abakinshi yayo kururuwa zaiyo kanta da sauri abokinshi da Bala mai chemist suka rikeshi, itama Rasheeda cikeda fitina ba tsoro azuciye tace “k
u sakeshi yazo bakaga komiba duk bakin dazai kokarin bullying dina wlh saina fasa bakin, kai kayi kadan kahanani sakewa agarin nan sabida ka ganka namiji, akan wani dalili zaku hanani sakat bazan iya zuwa nasai abubu? Shaguna nawa nadena zuwa na layin nan?
Wannan danake zuwa yanzu shima kuce ban isaba sabida wani dalilin ku na banza da wofi, cuta nakan kowa, babu wanda yasan karshen shi, yes Mamana nada HIV and so what? Kubi duniya a sannu kai kanka bakafi karfin kasami cutan ba dakiki kawai mahaukaci, kato
n banza wanda ake gutsurama buredi agidansu har yau akasa dashi da kannenshi sabida baida zuciyan nema, kar Allah yasa ka kara zuwa shagon siyan abu, jahili kawai” cika shagon akayi da mutane sabida yanda Rashida ke zubamai zagi shikuma yana kokawa dasu Ba
la asakeshi ya daketa ganin yanda ta fasamai baki, cikin taron mutanen wani dan tsoho ya leko ganinta sai kawai ya shigo cikin shagon yakai hannu ya karbe kujeran ya ijiye gaisheshi mutanen wajen sukahau yi. “Barka da yamma Baba Liman” cikeda hikima na man
ya ya dubi Sani yace “ayakuri Sani, kekuma wuce mutafi” hannunta yakama yace “wuce mutafi” batai musu ba akumbure cikeda taurin kai tace “ni jakata” sakinta yayi yana kallonta taduka tadauki jakanta ta goya abaya da ledan abincin tarike a hannu tana nishi
kaman kirjinta zai fashe sabida fushi saikuma ta dago azuciye dan tanada naci wani zubin kaman mayya, takalli uban mazan dake wajen duk ana kallonta tace “Baba Liman kagayama yan anguwan nan su kiyayeni nida mahaifiyata, bamu shiga gidan kowaba munyi sata,
Mama harni baya shiga gidajensu sabida yanda kowa ya kyamace mu, bamu rokesu kudi ba, banzo nacema kowa yabani kaza zankai mahaifiyata asibiti ba dan haka su fita daga rayuwata dana mahaifiyata Baba, sufita na gayamusu, I am enough for Mamana! ni kadai za
n iya kula da ita, nayi girma kuma Alhamdulillah inada karfin yimata komi kowa yafita harkana, ban nemi fadan kowaba ban shiga hurumin kowaba dan haka duk wanda yashigo tawa koshi waye wlh sai inda karfina yakare kagaya musu Baba Liman” tayi maganan with a
sound warning, ahankali tsohon yace “ya isa!” wucewa tayi fuuuuu tafice daga shagon kowa na wajen jikinshi yayi sanyi wani dakeda shago kusada na chemist yakalli yaron yace “kudaina abinda kukeyi mutanen nan ba akanku suke zaune ba, wlh Allah zai iya saka
musu, shidai cuta nakan kowa, yau dauka fasikanci matan tayi tasamu Allah masani amman ina mai tabbatar muku, gulma, keta, rashin mutunci da sa’ido da menene menene kukema matan da yarta kadai ya kore zunubansu” anatse Baba Liman yace “muji tsoron Allah,
mun kyamaci mutanen nan shi kadai ya isa wlh kudena takura musu kar Allah yakamaku, kar Allah yakamaku” yawuce shima yatafi, dasauri Bala yace “nima kada ka kara zuwan mini shagona kaje wani chemist din” tsaki Sani yayi yace “ka dinga shiganmata ko zaka mu
tu iyayyenka dai damuka sani bazasu taba barinka auren tijararriyan yarinyar me kanjamau dinchan ba” yayi maganan yana ficewa dağa shagon abokinsa na binsa.
Gidansu na wajajen karshen layin, wani dan karamin gidane sosai ciki da falo daya ne sai bayi ba
kitchen a tsakar gidan suke girki, ko’ina kal kal agidan, maida kofan tayi tarufe tasa sakata tasauke ijiyan zuciya sannan tai murmushi dan bataso Mama tagane ranta yabaci daganan zaure tai shouting “Mamaaaaa, Mama nadawo” tai ciki da gudu labule ta daga
Maman na zaune kan dadduma kaganta kamansu daya sak da Rasheeda itama tanada haske but ba kaman Rasheeda ba, batada kiba ko kadan ta rame ta bushe sosai, duka duka bazata wuce 40