Showing 9001 words to 12000 words out of 144199 words

Chapter 4 - SANYI DA ZAFI COMPLETE

M Shakur   

26 Aug 2026

54

awajenka is addu’a, jekai wanka za’a kawo maka kayayyakin dazakasa” gyadamata kai yayi agajiye yace “Mom please ke kikawomin banson hayaniyan kowa” tsayawa tayi ta kalleshi ahankali tace “tom zan kawo maka da kaina” dagoshi tayi yatashi tsaye

ahankali yawuce bayin dake nan bedroom din, girman bayin yayi girman wani gida, wanka yayi yayi brush yadaura towel yafito yana kallon saman gadon inda tundaga kan takalmi har zuwa kan agogo an jeramai akan gadon tsaf dazai saka wasu kayan sarauta ne masu

kyau sunsha aiki, anatse yake komi ya shirya cikin kayan da aka musu aikin royalty ya feffesa turare yadan juya yakallo kanshi amadubi yayi wani irin kyau na ban mamaki hulan dayasa

yasake maidashi wani cikakken mutum bude kofa yayi yafito daga bedroom din

wasu bayi ne ma’aikata a falon suna ganinshi suka duka dukansu. “Takawanka lafiya Yarima Riyad, taho a sannu dan kwalisa abin begen Sarauniya Maryama, barka da fitowa, Allah yakara maka lafiya, makiyinka fadawanka, duk wanda yaja dakai ya shirya yasha kas

a….” Wucewa yayi fuuuu yafita danshi bayason wayan nan surutun nasu, da Munir yaci karo yana kokarin shigowa flat dinsu hakan yasa ya tsaya yahade rai kaman suna fada Munir yace “katashi, are you feeling better can you walk”? Gyadama Munir kai yayi yay gab

a kawai, Munir yabishi abaya direct inda aka binne sarki yayi yana zuwa ya shiga wajen batare da an hanashi ba yayi shiruuuuu idanunshi sukai ja, almost everyday indai Mai Martaba baida wani uzuri saiya kirashi da daddare yaji yayake ina kuma yake, kullum

cikin fada yakemai daya daina yawon kasashe yakan yawan cemai yanda yake gudunma gidan nan da alamu shine wanda gidan nan zai rike kuma gam, ana cewa sarakuna basu da lokacin yaransu shidai mahaifinshi nada lokacinshi, Baba ya fara koyamai business how to

make 1naira yakoma billions, Baba guides him through everything, duk business dazai fara saiya kira Baba, sai Baba ya amince zai farayi, kuma bai taba takura mishi ba, hawaye yaji sun taru a idanunshi da sauri ya runtse idanun yana fuzar da iska dan baiso

suma zubo but he’s deeply hurting, da ace yasan Baba zai rasu dabaiyi tafiyan nan ba, sosai yama mahaifinshi addu’a sannan yafito Munir yagani awajen da Kabeer dasu Shaibu yan uwanshi dukansu yajiki sukamai ya amsa sai kallonshi suke Kabeer yace “kasha mag

ani kuwa you still look sick? Ko zaka koma ka kwanta ne”? Gyadamai kai yayi ahankali yace “nasha, I’m fine thank you” dannewa Kabeer yayi ganin yanda yakemai magana kaman alfarma yakemai dayake amsashi yadai daure yace “to mutafi fada” atare dukansu suka w

uce fada, sauran yayyinsa da yan uwansa natamai hira da uhm a’a kawai yake amsasu cus gashinan ne kawai, gaida mutane sukayi sai yima Riyad gaisuwa ake ana kiran sunanshi shi baimasan ya akayi akasanshi hakaba dan baicika zama ba, su Waziri dai duk suna ka

llon komi, kowa yazo saiyamai gaisuwa amai yajiki, yanda ma ake kallonshi sai abin yasa yaji sabon zazzabi na nema ya lullubeshi.

Mom nazaune afalonta tana jan charbi ita dawasu kawayenta wanda suke mata Sarkin daga wasu garin dasuka kawo mata gaisuwa a

ka shigo flat din Matan Waziri ne da babban diyarta Haleema da ake kira da Lims, tana sanye da doguwan riga abaya black ta yana gyalen akanta, tanada tsayi da dan jiki kadan duka duka bazata wuce 24, 25 ba, tana shiga dasauri tawuce wajen Mom kafinma Maman

ta tai gaisuwa tace “Mom ina kwana” takalli sauran matan wajen cikeda girmamawa tace “ina Kwanan ku” amsawa sukayi Mom tamata murmushi tace “Halima ba kina school ba yaushe kika dawo”? Mahaifiyarta tace “nima ganinta nayi agida da safen nan ta iso daga Lon

don wlh na aika driver yaje yakawota tunda taji rasuwan Mai Martaba hankalinta yakasa kwanciya” sosai Mom ke kallonta akunyace Haleema ta sunnar dakai Mom tace “school fa idan kikai missing exam ko test fa” Maman ta tace “project ma fa takeyi this month za

su gama komi da komi” babu wasa kan muryan Mom tace “kibi first available flight ki koma school gobe kinajina” gyadama Mom kai tayi ahankali tace “to Mom” Mom bata sake cewa komiba tacigaba da magana da manya, ahankali Haleema kebin dakin da kallo gabanta

na faduwa addu’a take Allah yasa suhadu ta ganshi, Allah yakawoshi side din nan dudda tasan ba lallai yadawo ba barinma yaji da baki adakin amman tasan inhar yana gari yafi zama wajen Mom da bangarensu na samari.

Kallonta Mamanta tayi tace “tashi kije waj

en su Batul mana” juyowa Mom tayi takalleta tace “tashi kije wajen yan uwanki” batai musu ba tashi tayi tawuce tafita Matan Madaki tabita da kallo tace “yarinyar akwai natsuwa ga kunya ga kawaici ta dace da Riyad sosai yanda shima baida maganan nan” wani k

alan dadi Matan Waziri taji Mom tai dan murmushi batace komiba.

Ahankali take tafiya ita kadai tana danna wayanta kamshin turaren dataji yasa ta dago kanta dasauri Riyad tahango yafito daga fada yana shigowa nan compound din Mom wlh kusan duka yaran sar

ki tasansu da yaran yan uwa dan afadan nan aka haifeta anan ta girma bata taba ganin yaro mai kyau da farin jini da aji irin Riyad ba kap gidan nan babu wanda yakaishi kyau, ga tsayi ga gayu ga jidakai ga miskilanci ga kudi kudinshi na kanshi bawai kudin B

aban su ba dan babu wanda yakaishi kudi a yaran sarki, gashi Mai Martaba na sonshi, ga kakanshi na bangaren Mom Attorney General yafi kowa tsatso mai kyau da gata ayaran sarki.

Faduwa gabanta yayi sosai amman tadaure ta tsaya awajen jikinta har bari ba

ri yake, tahowa yayi wajen batare daya kalle inda takeba zai wuce dasauri tace “Yarima Riyad!” Tsayawa Riyad yayi chak batare daya juyoba dasaurinta Halima taje ta gabanshi ta tsaya adan kunyace tace “ina yini ya hakuri?” Dan kallonta yayi trying to rememb

er waye ita, shifa wasu kannin nashima ba saninsu yagamayi ba dan baya shiga lamarin gidan nan baison komi game da sarautan, dauke kanshi yayi ganin yanda take murmushi tana kallonshi, kaman ance dole yayi magana yace “who are you”? Wow the way he talks is

super adorable, da kyar ta iya controlling zuciyanta dake neman fitowa ta danne kome takeji tace “Haleema” dan kallonta yayi irin kallon okay but still baigane ta ba and he doesn’t care din nan yajuya zai wuce dasauri tace “Ya Riyad sabida kai nazo gobe z

an koma school” dan tsayawa yayi wannan karan yajuyo kalleta da kyau shifa har yanzu bai santaba and sabida shi tazo? Akan wani dalili? Are they related in anyway? Infact baida karfin bude baki ma yayi all this questions hakan yasa yadan tabe baki yace “th

anks” kawai yawuce ya shiga flat din Mom……

Jin akwai baki abangaren Mom yasa yajuya yagazaya ta baya yashigo gidan yaje ya kwanta.

**

Yana zaune adakinshi dashi da Munir har yanzu bai gamajin sauki ba yana sanye dawani 3quater da singlet wayanshi

yahau ringing kallon wayan yayi ganin Mom yasa yadauki wayan kai tsaye tace “kazo dakina ina son ganinka” ahankali yace “okay Mom” tashi yayi ahankali Munir dake taba wayanshi yace “ina zaka?” Slippers yashiga sawa yace “Moomm” yadauki wani farin t-shirt y

asaka kawai yawuce Munir daya gane abinda yake nufi wato Mom nakiranshi hakan yasa yacigaba da abinda yakeyi ahankali yabude dakin Mom tana zaune kan couch din dake dakinta ganinshi yasa tanunamai gefenta tace “taho nan” shigowa yayi ya maida kofan dakin y

arufe yataho wajen kujeran zama yayi saikuma ya kwanto yayi filo da cinyanta he’s really feeling mutuwan mahaifinshi so duk walwalanshi bayanan, hannunta Mom tadaura saman kanshi ta shafa tai shiru kafin tasauke ijiyan zuciya tace “kasha magani kuwa? Dr za

i zo anjima” ahankali yace “nasha” dan ijiyan zuciya tasauke tace “da banson namaka maganan nan yanzu cus nasan kanajin mutuwan Babanka, I know how much you love mahaifinku Riyad but I have to dan kowace matan sarki maganan da datake ma danta maza kenan, n

ima dole nama nawa” dan dago idanunshi yayi ya kalli Maman nashi baice komiba, ahankali tace “inaso kai aure Riyad!” dawani irin sauri Riyad yatashi zaune daga jikin ya kalleta yama kasa magana cus maganan yazo mishi ne bagatatan, Mom dake kallonshi itama

looking damn serious tace “and bakowace kalan yarinya nakeso ka auromin ba Riyad, inaso ka auri yarinyar da zuciyana ta aminta da ita yarinyar da nice na zabeta, all yammatan zamanin nan yanzu burinsu is suyi aure su raba yaro da mahaifiyarshi I will never

allow you marry such girls, I have a girl a

mind dina gaskiya” haderai yayi kana ganin fuskanshi kasan bama yason maganan dasauri yace “Mom aure!”? Wani mugun kallo tamai tace “kaga Riyad banson shirme don’t even start all abinda kakeso kace, I supported

you duk yawace yawacen dakake kana touring round the world bantaba hanaka ba dan nasan it’s your hubby, bantaba takuraka ba dudda normally normally ba tun yau yakamata kai auren ba, but yanzu lokaci yayi it’s an order you have to settle down, aure zakayi a

nd i have a girl danakeso ka aura diyar Waziri Haleematu, ita nakeso ka aura!” Wani kalan tashi yayi dasauri yamike tsaye yana kallon Mamanshi da babu wasa akan fuskanta itama tabishi da kallo tazubamai idanu rass aka tace “kaine the most successful child

acikin yaran sarki, you’ve archived alot Riyad at a very young age, ga ilimi kwali daban daban gareka, ga businesses da companies daka bude, ga natsuwa ga kamala ga kwarjini, naji kishen kishen dama mai Babban daki kaine zabinta sabida yanda mahaifinku ke

sonka, Waziri shima nasan kodan yanda diyarshi ke sonka kuma yana mata kwadayinka kaizai dangwalamawa, to yaji maganan kuma kanason auren diyarshi komi yazo cikin sauki idan yana bangaren mu zai mana aikin yima sauran manyan fada maganan a zabeka, instead

of su Kabir yan uwanka ko kannen babbanku dake neman kujeran sarautan, gwara kai dana kaikafi kowa chanchanta and bazan hutaba saina maidakai sarki, ai tsoron kada ka zama sarki yasa daga shigowanka garin suna neman halakamin kai amman Allah bai basu iko b

a, kuma naji dadin abinda yafaru hakan yanunama jama’a cewa an tsaneka ana tsoron kada ka zama sarki saisa har anfara yunkurin kasheka, saisa saida na tabbatar kowa yasan abinda yasameka”.

WANNA TALK TO NI M SHAKUR DIRECTLY?? KIMIN MAGANA A WATSAPP +2

347012181461

[5/20, 7:53 AM] +234 806 065 9266:

💫

SANYI DA ZAFI

💫





🏻

M SHAKUR

KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? S

HEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???

JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA

🔥

GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA

🙈

CHAT ME UP DO

N SHIGA

+2347012181461

EPISODE 6





Wallahi kanshi ma sarawa yafarayi jin maganganun da Mom kemai, first of all duk wani abun na sarautan su bayaso saisama baya iya zama agarin, baison hayaniya baison how they do things cus is always fighting, makirc

i and politics, and baijin tunda ya girma yatabayin cikakken 2months like good 60days agidan ba bini bini yabar country, lokutan salla ne yasan dole yake dawowa sabida yanda Baba ya maida abin mandatory yanason duka yaranshi to be home sabida hawan salla a

nd other activities na al’adu, shi mutum ne

da baisan mulki he prefer business nashi, he derive joy a business, it gives him purpose, for aure kuma dudda yasan culture nasu ne amaka aure abaka mata but shi kwata kawata baitaba sanin Mom zatamai hakaba cus

Mom is highly educated and expose, itama bata cika biyema culture ba saisa ma take barinshi to live his dream life, ko kadan bai shirya aure ba cus bayason commitment for now, his plan is nan da 2yrs zaiyi aure yanzu kawai aure baya lissafinsa, dukawa yayi

ahankali gaban Mom yadafa kafanta kaman zaiyi kuka yace “Mommmmm” ahankali itama Mom tana kallonshi tace “Riyaddddd! You don’t have to say abinda zaka fadi kasan nasanka sama da kowa aduniya ko?” Gyadamata Kai yayi Mom tace “I know how you despise sarauta

, mulki infact bakamasan komi akaiba, I know for auren zakace baka shirya ba bakasan damuwan mace da sauransu” sai kawai takai hannuwanta tai cupping face nashi cikin tattausan lafazi tace “dama akwai abinda zan taba so aduniyan nan dabaza ka iyamin ba Riy

ad”? Ahankali Mom tace “I thought nine number 1 dinka like you always say”? Dasauri cikin raunin murya Riyad yace “Mom u are my number 1 kema kin sani” kai tsaye Mom tace “inhar nine number one din naka then karka karamin gardama kan maganan nan it’s an or

der allow me to do everything am I clear?” Yadade yana kallonta yanda take kallonshi babu wasa kan idanunta yasa ya sauke kanshi kasa alamun dai baiso but baice komiba, baya iyama Mahaifiyarshi gardama, cikin fushi Mom tace “kamin shiru? Ban isa dakai bane

ko ban isa nace maka haka nakeso kayi kayiba”? Tai maganan tana shaking leg in anger, abu yahadiye awuyanshi har saida taga motsin adam apple nashi asanyaye yace “okay” tsayarda shaking leg din tayi tai murmushi sai kawai ta matso ta mannamai peck agoshi

tace “I wish kowacce uwa zata sami d’a mai mata biyayya kaman Riyad dina data zama very very lucky, Allah maka albarka kaji, Haleema is a good girl tana matukar sonka tun tana yar yarinya, she will keep my son happy I’m sure of that, so karka damu, zancen

sarauta kuma I will teach you everything and you will do well kaji”? Gyadamata kai yayi zuciyanshi duk ba dadi duka duka kwanan Babanshi nawa da rasuwa but kowa is after kujeranshi, look at matayensu kaman ba mazajensu ne suka rasu ba dukansu kokarin daura

yaransu kan Sarautar suke sunma manta da rasuwan shima yanzu yazama sarkin one day haka matarshi zatayi kenan itama yana mutuwa all focus dinta will be yanda danta zai gajeshi bamatada lokacin yimai addu’a tashi kawai yayi yajuya yayi kofa.

Mom tabis

hi da kallo ranta fess, dolema Riyad dinta yadinga intimidating kowa, yafi duka yaran sarki kyau ga kwarjini ga haiba ga natsuwa, ga jan aji, ga kudi, ga rashin magana, ga rashin shiga mutane, gashi baida kallon mata shi kadai keda qualities na sarki and b

azata hutaba saita maidashi sarki wannan alkawari ne!.

Dakinshi yashiga Munir dake danna laptop yabishi da kallo ganin yanda mood dinshi ya chanza tashi daya, Wucewa yayi yafada gado yakife cikinshi tareda lumshe idanu Munir baicemai komiba yacigaba

da abinda yakeyi abinshi.

Yana fita Mom ta daga wayanta takira matan Waziri da ake kira da Mariya ringing daya ta daga wayan tace “ranki shi dade Uwardakina, Allah yaja zamaninki Umman Riyad” dan murmushi Mom tayi kafin cikeda isa da jiji dakai tace “d

ole gobe Haleematu zata koma makaranta ne”? Dasauri Mariya tace “ai Uwardakina ko makarantan kikace karta kara zuwa saita zauna” jinjina kai Mom tayi tace “tom inaga bazata tafi goben ba dan zan turo Riyad yazo ya ganta inaso nahada su aure inyaso bayan ya

ganta zata iya tafiya” wani ihu Mariya tayi cikin waya saikuma ta zube kaman tana gabanta tace “nagode nagode Uwardakina da wannan karamci naki, kidubi kowa na gidan nan amman kuka zabinma

Yarima Riyad Haleematu nagode, namiki alkawari bazaki taba samin ma

tsala damu ba, I will forever be loyal to you, Haleema zata bautamiki Uwardakina, kuma da yardan Allah kujeran sarautan nan ta Yarima Riyad ce ai naji jita jita, da yardan Allah shine magajin sarki” dan murmushi Mom tayi tace “Waziri ya shigo yakirani” tan

a maganan ta katse waya wani ihu Mariya tayi tamike da gudunta tafice zuwa dakin Haleematu kai tsaye tabude kofan yarinyar na zaune sanye da rigan bacci tana kokarin hada kaya Maman kawai ta dagata tana juyawa tana rawa abinma saiyasa Haleematun dariya ta

ce “Mommy menene kike murna haka”? Cikeda jin dadi tace “yanzun nan Sarauniya Maryama takirani tace tanason hada aurenki da Yarima Riyad gobe ma zata aikoshi gidan nan” wani kalan zaro idanu Haleema tayi she can’t believe abinda taji tun tana yar yarinya t

akeson Yarima Riyad yahadu ne over wlh, lips nata rawa suka fara farinciki yahanata magana tace “Mommy mekikace? Yarima Riyad mene? Dan Allah maimaita”?Kyalkyacewa da dariya Mama tayi tace “dalla cewa nayi za’a aura miki Riyad zaki zama matan sarki dan ina

mai tabbatar miki shi za’a bawa Sarautan” ihuuuu tayi tareda wani kalan tsalle ta rungume Mamanta sai kawai tahau tsalle sosai lekowa dakin Waziri da shigowan shi kenan yayi ganinsu yayi murmushi waya na kunnenshi Mama zatamai magana yadaga hannu yace “in

ajinki ranki shi dade” wucewa falo yayi yazauna Mama da Haleema suka biyoshi a speaker yasaka wayan dashi da Mom ke magana suna shirya komi kaman ba mutuwa aka musu ba, planning auren da yanda zasu sami kujeran suke hankali kwance.

**

Wuraren 10 yafi

to daga dakinshi yana sanye cikin wani farin yadi da akamai dinkin jumper yamai kyau sosai sai kamshi yake zubawa kaman zaije gasan turare, binshi da kallo Mom tayi tana murmushi tace “Son katashi? Munir yashigo yakai sau uku nacemai bai isa yatasheka ba,

bayan kunyi sallan asuba tare a mosque” karasowa yayi yazo kusadab da ita yazauna ahankali yace “morning Mom” as usual pecking nashi tayi a goshi tareda shafa kumatunshi tace “morning Riyad, yaya jikin? Zakai breakfast yanzu ne”? Girgiza mata kai yayi alam

un no, dasauri tace “to maza je Gwaggon ku ta aiko dazu akiraka kadawo saikai breakfast kafin kafita fada ko”? Dan gyadamata kai yayi yatashi ahankali yayi kofa haryasa hannu zai bude kofan tace “idan tamaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login