Showing 18001 words to 21000 words out of 144199 words
sonshi sosai aranta wlh, ahaka tana lumlumshe idanu bacci yayi awon gaba da ita.
**
Around 5 Mama ta tadata daga bacci, da kyar ta tadunma Mama, Mama tace “ke yarinya sai nauyin
bacci kaman wani kato, tashi kin manta yau zaku koma makaranta eh? Hope kin dauki permission wajen aiki an baki shift na yamma”? Gyadama Mama kai tayi cikin gajiyan bacci, hannu Mama tasa tadagota ta taro kafadanta hakan yasa Rashida tasauke kanta akan ka
fadar Mama tana kara lumshe idanu still cikin bacci, dan jijjigata Mama tayi tace “Rashida” ahankali tabude idahunta tass takalli Mama dasu Mama tace “I think drop most of ayyukanki tunda kin koma school kinga yanzu year 5 kike you need to study well, nako
sa naga diyata tazama likita, saura 1yr yanzu, Allah ya aramin rai, ranan super wax zan saka amin combination da super lace” dan murmushi kadan Rashida tayi tanason taji Mama na maganganu haka it makes her happy, Mama tace “yanzu dai kinga kina bukatan lok
acin hutawa da lokacin karatu bakiga yanda kike gajiya ba da kyar kike tashi, ki saki sauran ayyukan ki rike na hotel din nan kadai tunda anfi biya, su Maman Miwa da sauran wajajen nan ki sakesu” dan murmushi tayi sai kawai tahau yunkurin tashi ahankali da
n muryanta baya fita sosai sabida daga bacci ta tashi tace “Mama so kike na bar aiki sabida mudinga karban abincin sadakan da yan anguwan nan suke kawo mana out of pity?” Tadanyi shiru daidai takarasa mikewa tsayen batare data kalli Mama ba tace “this year
is clinicals, zamuyi aiki a pediatric da obstetrics&gynecology, I can manage everything Mama trust me, Alhamdulillah kome aka koyamin sau daya ya zauna akaina, sannan daga yanzu koda ranan Sunday ne zan dinga zuwa library duk sati sau daya nayi muraji’an
duka abinda aka koya mana na that week, I can study Mama, I can do my duties na kula dake da siyamana kayan abinci da kudin magunguna, I can manage my work also” tana maganan tayaye labule tafita daga dakin tawuce waje saida tafara sa abinci awuta sannan t
awuce bayi tayi wanka tafito lokacin har sanwan yayi tazuba taliya sannan takoma daki tashiga saka kaya Mama na zaune kan dadduma tana kallonta, tana kallon yanda taketa ciro kayan ghana masgon dasuke agoge daga gani kasan dan kaya mai kyau take nema na zu
wa school abu Mama taji ya tsaya mata a wuya sai kuma ta daure kawai ta dauke kanta daga kallonta.
Wani doguwan rigan atampa maroon ta zaba ta maida gefe, taciro lab coat nata dayake a goge shima ta ijiye gefe sannan ta maida sauran kayan ta shirya tsaf t
awuce tafita tasake juya taliyan sannan tadawo tasa hijabi ta kabbatar salla.
Tana idarwa bata tsaya yin azkar ba ta fita ta juyo taliyan a kula tasama Mama ruwan zafi na wanka sannan tadawo tasake zama kan dadduma tafara azkar tana gamawa ta kalli Mama
dake kallonta tace “Good Morning Mama na nikadai, Mama naji dadi nikadai kika haifa nake moreki banda kanni dazaki dinga raba attention naki akanmu” most time tana maganan ne idan taga abu na damun Mama dan tasata tai murmushi, ganin Mama batai
murmushi b
a yasa takama hannunta tarike dasauri ahankali tace “Mamaaaaaaa” tai maganan ashagwabe tana lankwasa kai, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “babban burina arayuwa shine ki zama likita Rashida, banson wani abu dazai hanaki zama, kina bukatan lokacin dazaki k
aratu, banson ki fadi, banson ki sami carry over, nasan kinada kokari but dudda haka karatu yanada amfani, kina all this ayyuka bazaki sami lokacin yi ba, ki manta da kula dani Allah daya tsaga mana baki bazai hanamu abinda zamusa abakin ba, after this yea
r next year zaki gama, please Rashida kibar ayyukan nan and focus a karatu” tunda Mama ke maganan take kallonta batason sata cikin damuwa hakan yasa tace “to naji Mama amman tunda kinga satın nan muka koma karatu da practicals bazasuyi serious ba kibari na
yi aikin zuwa karshen wata abiyani kudina saina dena kinji, zancen night shift ai HOD mu tasan dani bata taba sani a night shift ba sabida ke Mama, so ko yanzu ma bazan bazanyi night shift ba, kinga na karbi albashina saimu ijiye, kuma Mama kidena damuwa y
arki ta dauko brain dinki bazan fadiba In sha Allah bayan kinamin addu’a, to yanzu kin hakura na karasa zuwa karshen watan nan duk sai na saki aikin nabar na hotel din?” Shiru Mama tayi tana kallonta Rashida da taurin kai da kafiya hmm, ijiyan zuciya tasau
ke tace “okay! Yau sha uku ga wata, karshen wata zaki sallame kowa, next month banson ganinki kina zuwa ayyuka nan” gyadama Mama kai tayi tace “naji” tashi Mama tayi tace “ai shikenan” tawuce sip wani akwati zata dauko dasauri Rashida ta tashi tace “Mama s
top ki kirani na dauko miki” dasauri tasa hannunta tadauki akwatin tasaukar dashi kasa Mama tazo wajen ta zauna itama Rashida ta zauna gaban box din tana jiran tadauki abinda zata dauka tasake daukan akwatin ta maida sama, wata yar jaka Mama tadauko acıkın
box din tamika mata tace “gashi ungo” dasauri Rashida ta kalli jakan data bata tace “na menene Mama”? Tasa hannu tana karba, zage zip din box din Mama tashigayi tace “naki ne kibude” da sauri taciro bakin ledan data gani cikin jakan dayake a kulle tashiga
budewa saiga crocs a ledansu pink color mai kyau ba asalin designers one dinba but irin normal wanda ake saidawa a market yan 5k-7k dakuma stethoscope pink shima mai kyau, da mamaki take kallon kayan dakuma murmushi akan fuskanta tama kasa cewa komi Mama
ta kalleta tace “bakiso ne oya bani kayana, last month danaje clinic wata Hajiya tarabamana kudi a envelop naduba naga 20k ne shine na shiga kasuwa na siya miki crocs naga shi likitoshi kesawa a clinic dimu duka likitocin wajen shine akafansu shine na shig
a kasuwa na sayomiki ashe haka takalmin keda tsada dubu takwas aka saidamin na hada miki da wannan abun gwajin nace nima y’ata tai kaman yan gayun likitocin danake gani a clinic dinmu” hawaye ne yacika idanun Rashida tana kallon Mama na bata labarin Mama t
akare da “nazo naboyesu nace bazan baki ba sai ranan dazakuyi resuming school” daidai lokacin hawaye ya sauko daga idanunta Mama tace “ke mehaka kuka kikemin”? Kawai rungume Mama tayi da gudu ta kankameta ahankali tace “thank you Mama thank you” shafa baya
nta Mama tayi tace “gabaki dayan rayuwanki Rashida nine na cinye miki ita, bakida lokacin kanki, komi kika samu ni, kome kikeyi sabida nine, konace ki sayawa kanki abu bakiyi saisa na saya miki kema ki shiga sahun yan gayu aga y’ata fess fess akara kallont
a sabida yanda tai kyau, Allah yakawo miji na gari” cikin shagwaba ta ture Mama tace “ni bazanyi aure ba Mama, bazan taba iya barinki ba” baki Mama ta kama tace “ke kodai zan kaiki gidan zumane amiki rukiya kaman me aljanu bazaki aure ba” gyadama Mama kai
tayi tadauki takalminta tana budewa daga leda tace “inhar ban samu mijin dazai yarda na daukeki muje gidanshi tareba ina ganinki ina baki kulawa wlh gara na kare rayuwana ahaka” da sauri Mama tamata dakuwa tace “kinci mai garinku Rashida” dariya Rashida ta
yi sosai tace “wlh Mama da gaske nake bazan taba rabuwa dake ba Allah Mama” ganin Mama zatai magana yasa ta tashi da sauri tace “bari nasa takalmina” fararen kafanta ta zura cikin crocs din sun mata bala’in kyau Mama tace “Masha Allah Tubarkallah komi kema
yarinyana kyau wlh, kinga kafanki aciki kuwa dudda kafan fara ba lalli amman yayi kyau” wani juyi tayi cikin takalmin tace “Mama inason takalmin thank you
so much Mamaa, bari na tafi” tawuce tasa doguwan rigan data fito dashi yakamata ya nuna her flat tum
my sosai da very full chest nata cus she has boobs kaman Mama, itama Mama harda rama yasa ba’a ganin nata yanzu, dan kwali ta daura tayafa gyalenta tai arranging lab coat nata a bag pack da books da stethoscope da Mama ta siyamata da komi ciki ta goya abay
a tasa yar wayanta a aljihun riganta da earpiece tace “natafi Mama” Mama tace “dan Allah kici abinci kinji kada ki manta” dasauri tace “to Mama zanci, bye Mama” Mama tace “ubangiji Allah bada za’a Allah ya taimaka Allah ya tsareki Allah yakuma baki miji na
gari”.
Shagon Maman Miwa taje ta gayamata ta koma school da safe zata dinga zuwa aiki, nan da nan tayi wanke wanke ta share ko’ina tai mopping after 8 tagama komi Maman Miwa tabata 2k saikuma ta bata 200 tace “kihau adaidaita kitafi makaranta baki takab
a” murmushi kadan tayi tace “nagode Maman Miwa” sannan tawuce tafito MamanMiwa tabita da kallo tace yarinya ga kyau har kyau ba miji.
Adaidaita sahu ta tare ta shiga sai BUK direct department dinsu ta wuce staircase tahau tana tafiya daidai lokacin wani
guy da wata young lady kaman mate na Rasheeda suna sanye da kayan gida lab coat a hannunsu na saukowa hada ido Rashida tayi da guy din da sauri ta dauke kai tacigaba da tafiya abinta tana hayowa su suna saukowa hade fuska yarinyar tayi tace “Bilal yaushe
zaka fadamin inda kahadamin suprise birthday party”? Gabaki dayan hankalinshi nakan Rashida dake hayowa abinta batare data kara kallon inda suke ba, mintsilin shi yarinyar tayi abaya hakan yasa yakalleta da sauri yace “sorry Layla come again me kikace”? Ab
u taji ya tsaya mata awuya sai kawai tawuce da sauri tana sauka da sauri yabita da sauri yace “Layla wait common” tuni tafice dan tsayawa yayi daidai Rashida tahau staircase din dayake kai yabita da kallo sabida kyau datamai doguwan atampan riganta yamata
kyau over, dudda ko man baki babu a lips nata balle hoda ko kwalli ahankali yace “we’re going to clinic you don’t need to go up kasa zamu” kaman bada ita yake magana ba kala bata cemai ba kawai ta juya tashiga sauka da sauri yabita yace “wai mesa bakimin m
agana Rashy?” Chak ta tsaya saikuma tajuyo ta kalleshi tace “kada ka sake kuskuren kirana da sunan nan only those that are dear to me ke kirana dashi not you” ta juya, dasauri yabita yace “I don’t understand why exactly you’re angry with me, I told you nac
e miki ina sonki ne banda knowledge na your mother’s illness, agidanmu baza’a taba barina na auri yar wacce takeda H…….” “Bilal!!!!” Rashida takirashi da karfi ta daga hannu zata kaimai mari ranta abala’in bace tace “the next time bakin nan naka zai ambato
mahaifiyata wlh saina zubar da hakoranka! Nataba cemaka wani abu? Nace ka aureni dama? I don’t even know kana existing so go to hell!” Tana maganan tajuya fuuuu yabita da kallo kowa na department nasu yasan Rashida da masifa but shi he just said it badan
rashin mutunci ba he was trying to tell her baza’a bari ya aureta agidansu ba knowing Mamanta nada HIV, baza’a taba bari ya auro diyar unholy mace ba, still he was trying to tell her su zama friends dan he was feeling guilty yanda yagama cewa yana sonta la
st year dan last year yayi joining nasu dan transfer ya karba daga former school dayake medicine a Sudan, sun fara soyayya sosai yan aji sukamai gulma Mamanta nada HiV bai yarda ba dan bata taba fadamai ba saida aka kirashi akace yazo ga Mamanta tazo clini
c itama tana wajen Maman shine yaje ko yagani daga ranan yayi ghosting nata yaki kiranta yadaina daukan wayanda kotamai magana a class yayi banza da ita saima yazo yana kula yan matan class nasu sosai danya bakanta mata rai, saikuma during this 2weeks holi
day saiyaji wani irin soyayya ta na tasomai yau daya ganta saiyaji tafi ko yaushe kyau sonyayyan yadawomai fresh azuciye kaman yahadiyeta dan wlh duk department nasu baiga me kyanta ba kawai dai no one can approach her ne sabida masifan ta da fitina.
Koda yafito yaga harta shige bus nasu ta zauna taciro yar wayanta ta makala earpiece tasa a kunne sabida yanda zuciya ta ke tafarfasa, ahankali yasauke ijiyan zuciya yawuce wajen motar shi inda Layla take a tsaye tana hararanshi yabude yana mata murmushi y
ace “wai ke lafiyanki common shiga mota muje” yashiga mota yatada yaja motan Rashida ta kalla sannan tasake sauke ijiyan zuciya taso Bilal last session nasu sabida she thought shine mutum na farko daya sota for who she is dan ta dauka yasan waye ita kowa n
a department nasu ai yasani so tadauka yasani, tun bata kulashi tafara kulashi sabida yanda yake shige mata, she really liked him suna waya but rana daya kawai yadaina kulata yadaina amsa wayanta yana kula yan matan ajinsu agabanta yana cemusu yana sonsu j
ust to hurt her, abin yamata ciwo sabida tanada kishi but bata taba nunawa ba, bata taba nuna tadamu ba saima daina kallonshi datayi da kallon inda suke cus she’s even blaming herself data budemai zuciyanta bayan tasan duk wanda zatai soyayya dashi baya go
ing anywhere, idan ba lectures gareta ba earpiece zatasa a kunne tana karatu tanabin everything da aka musu, she’s a fast learner na ban mamaki, takoyama kanta rayuwan she’s enough for herself, she doesn’t need people cus gani take kowa yimata kallon yar
mai HIV ake diyar fasuka, babu abinda ba’a kiran Mama dashi har anan ajinsu su ana cewa Mama karuwa ce cus gata kyakkyawa daman, batason wata ko wani yashigo space nata and hurt her saisa she’s always always protecting her space bawai batason tayi kawa ban
e ko kawance baya burgeta bane, no kawai she don’t wanna get hurt, kawayenta na layinsu duk iyayensu sun raba yaransu da ita saisa ta maida kanta and centered her life to be just she and her mom.
Yan ajin always sees her as mafadaciya ko magana kama Ras
hida zai iya koma muku fada saisa suna avoiding nata suma but during group work ko wani abu zatai participating that is idan bamata daukin nauyin yin aikin gabaki dayaba dan tanada bala’in kokari haka dai rayuwan ta yake.
Sunkai asibiti dudda sun saba
da hospital din still saida akai orientation sannan aka nuna musu roaster gobe zasu fara taduba taba bata night, daga 8 ne shift nata zuwa 1 kullum banda asabar da lahadi all thanks to HOD nata! She’s so happy da roaster sukai few abu by 11 suka tafi dire
ct hotel din ta wuce takai wajajen 1 tawuce wajen changing room nasu tabude locker dinta taciro uniform nata tashiga chanzawa daidai tagama chanza kayan tana kokarin saka karamin farin hijabinta aka turo door aka shigo changing room din wata cleaner na ce
Joy tai murmushi tana kallon gashinta dasauri Rashida takarasa saka hijabin Joy tace “Hi kinzo muje Madam zata mana magana kafin mufara aiki a seminar room” maida locker Rashida tayi tarufe tadauki wayanta da earpiece tasaka a aljihun wando tawuce tafito J
oy tabiyota abaya wani babban hall sukaje da kujeru ke cike su kusan 34 cleaners din na afternoon zama sukayi Madam dinsu dake tsaye gaban hall tace “I called for this meeting sabida na sanar daku Oga na gari he can come anytime, alot of you dakukai join
ing this hotel like 2yrs ago baku sanshi ba, he can come at any moment or day idan yaga dama, baya tolerating the slitest of dirt dan haka kuyi aiki dakyau, Rashida!” Dago kanta Rashida tayi takalleta Madam tace “since kina afternoon duty yanzu anytime kik
a shigo before ki goge anywhere ki tabbata kinzo wajena kin amshi key kin goge office din Oga, for afternoon kene mai gyara office din da safe kuma Kola, abubuwan mop na gyaran office dinshi is different dana general gyara after the meeting you will follow
me ki karba” Gyadamata kai Rashida tayi tace “Yes Ma” tunda take aiki yau ne rana na farko dataji anyi maganan mai hotel dinma kusan shekara biyu kenan bai taba zuwa ba ko kuma yataba zuwa bata sani bane oho dai, addressing nasu tayi na kusan 20mins sanna
n tace
“dismiss follow me Rashida” binta Rashida tayi abaya suka wuce office nata tamata handing over key card da sabon bucket mop su air freshener da sauransu a cleaning trolly tace “gashi maza maza 5th floor ai kinsan office din” Gyadamata kai Rashida ta
yi tafice daga office din tawuce elevator ta shiga zuwa 5th floor din, wani special corridor akebi aje office din da shi kadaine a hanyan corridor din, key wanda take kati ta manna a kofan kofan yabudu hakanan kawai gabanta yafadi batasan mesa ba hannunta
tasa ta tura kofan ahankali ciki duhu dan an kashe wuta, hannu tasa tafara kunna wutan Babban office ne sosai daya hadu bana wasa ba, akwai dogon sofa banda table da chair ga babban tv ga desktop gawani mini library da akayishi design na tree kowani branch
anyi naming nashi countey ga books na garin awajen saikuma wasu kofofi guda biyu daban daban ahankali tasa kafanta ta shiga ciki sannan ta maida kofan tarufe tana kallo dudda bawani datti, sauka idanunta yayı kan zanenta dake bangon office din dayayi wani
irin mahaukacin kyau she can’t believe she drew this, daina kallo tayi tashigo ciro brush na cire cobweb.
JOIN MY WATSAPP GROUP DANAKE UPDATE NOWW!!
https://chat.whatsapp.com/LQB0yaXytjU2hoN1Pg2HAw
[5/20, 7:53 AM] +234 806 065 9266:
💫
SANYI DA ZAF
I
💫
✍
🏻
M SHAKUR
EPISODE
🔟
BARI NA LISSAFO MUKU ABUBUWAN DA HABISHMA UNDERWEARS KE SAIDAWA
💃
Pants(cotton, seamless, lace, spandex, plus size,thongs, gstrings etc),
Bras(nursing, padded, non padded, uk, wired, wireless, seamless,
t-shirt bras, plus sizes etc)
Tights(long, short, leggings, bumshorts, laser cut tights, jeans etc)
Underskirts(silk, cotton, long, short, box, plain etc)
Sleepwears(pyjamas, adult and children pyjamas,