Showing 63001 words to 66000 words out of 206525 words
wani dan d'aki suka shiga wata babbar kwaryace da faifai aruf
e ya bude wani ruwane bakikirin aciki sai wani irin wari ke tashi hannu yasa ya tsamo ledoji gida uku abin Al'ajabi babu dugon k'azamin ruwan jikin ledar ya bata ta amsa "to ki kiyaye yau kwanansu goma sha daya cif ina tsafi akansu sharadin sune Jan leda t
a farko ki tabatar kin zubawa mijinki maganin a abunci sau uku rak karki kuskura wani ya ganki kuma karki bari wani yayi anfani da kwanon da zaici abuncin mutikar kikayi haka ba ki bari yayi fashin cin abuncinba kuma wani bai gankiba wlh kin gama dashi ko
cewa kikayi ya sama garin Katsina wuta sai yasa ko ya kwanta kimasa yankan rago wlh da kansa zai kawo wukar na biyu kuwa yaron da kikeso ya auri yarki wannan na farar ledar zatayi kokari ta barbada masa inda zai tsallaka amma shi bazan gayamiki illar saba
sai kinzomun godiya sharadin shine ta tabbatar shine zai tsallaka da farko dan idan ba hakaba to fah Wanda ya tsallaka Hamm to idan shine ko da. Wani yabi bayansa to babu abinda zai samesa na uku shine tsanwar ledarnan ta jik'a maganin sai yayi kwana uku
tarika wanke fuskarta sau uku arana tayi k'ok'ari suna magana koda so dayane har tsawon kwana talatin da tara to fah ranar aikinku zai kammala ki kiyaye karku kuskure barinma ke wlh idan kika kuskure to wannan ruwan kwarya sai yafiki daraja aduniya ki kiya
ye aikinku akwai tsauri mutanan sunada taurin kai da karfin Addu'a nasha wuya hada maganinan anyi asara jarirai biyu saboda aikin ki da yarki don haka karki bari aiki ya b'aci ranar da kika cika kwana arba'in ba daya to wlh duk abinda Alhaji ya mallaka yaz
ama naki kuma ranar za'a daurawa yarki aure da d'ansa sabanin haka saide a d'aura da wata kuma keko kare sai yafiki daraja zaki lalace ki tozarta aduniya dan dama na gayamiki sharadin kafin nayi tsafinan kikace kin amince karki dawo sai kwanaki sun cika "k
arka damu zan kiyaye yau ina farin ciki wannan k'aramin aikine babu mai wuya aciki duka zamuyishi fitowa sukayi Asiya tayi masa godiya ya kara jadada mata karta dawo sai bayan kwana talatin da tara tazo masa da labari mai dadi kudi ta Tule masa na uban mam
aki suka fito suka tafi mota suka shiga suka tafi zuciyarsu fari kalla suka nufi gida,
******
Zaune yake cikin hadaddan Office d'insa saman lumtsumemiyar kujera sai juyi yake yana zugar sigari farin gilashi manne afuskarsa ya had'e cikin
kananu kaya
Wanda suka yimasa masifar kyau kwarjininsa ya fito sosai gashin kansa bakikirin sai sheki yakeyi ya dan sabko kadan bisa wuyansa wayarsa karama ta dauki ringin kin kallon wayar yayi lumsassun idanunsa ya lumshe ya daga kai sama ya feso da hakin taba knock
ing kofarsa akayi saida akayi sau uku ya bude idanunsa cikin zazzakar muryasa yace"yes turo abude bai karasa ba Ahmed ya shigo"wlh Dr Sardauna bakada mutumci dan kun hanani kanwarku shine yau kwana hudu baka jiniba baka nemeni ba, murmushi gefen baki Sarda
una yayi"sorry Abokina wlh aiyuka sunmun yawa yanzu ko 20 minute banba da na fito daga tiyata wlh marasa lfy garemu dayawa kwana biyu sai dare nake zuwa gida ykk ya soyayya ka hakurane?? " ban saniba dan rainin hankali ai Dole zan barta tunda yayamu yamun
fin karfi amma wlh ina son zee baby yar fara kyakyawa baki Sardauna ya table"wai kuwa Dr kasan wani Abu? " sai ka fada "hmm bandar fah alondon wlh yar mutane ya lalata ko ince suka lalata juna gashi abun ya damesa" Ahmed nifa kasan banason gulma kabar maga
nar yace sai yazo dukan wasa Ahmed ya kai masa"dallah can malin malin karkamun wa'azi hayakin sigari ya cika baki dashi ya fesa ma Ahmed "dan rainin hankali kai ko da yaushe idan mutum yazo gunka sai kamasa rainin hankali "Allah baka hakuri aboki daga fadi
n gaskiya, Kiran sallah azuhur aka fara Sardauna ya Mike ya dauro alwalla suka nufi masallaci Dr sai tsiya yakema Ahmed banza ya masa da Ruma suka hadu a harabar asibitin ta gaishesu adakile Dr Sardauna ya amsa suka wuce Ahmed"yace ya dai ko uwar guzuma n
a cikine mugun kallo Sardauna ya masa suka shiga cikin masallaci,
✨✨✨
Kwance take saman bed tana nade cikin blanket tana sharara bacci cike da mafarkin Dr Sardauna ya rumgumeta saman faffadan kirjinshi yana mata waka mai dadi hannusa saman breast d'
inta yana mulmula mata ahankali cikin Salo mai tsayawa azuciya ta lumshe idanu tana nishi hannuta cikin sumar kansa tana shafawa Nisha ce ta shigo d'akin da gudunta ta fado saman zee baby"my dear tashi dallah kwana biyu nayi missing dinki wlh zabura nayi c
ike da haushin Nisha na Mike na shagwab'e "haba my dear kin kwafsamun wlh ina cikin wani mafarki ne fa mai bala'in dadi na fada ina lumshe idanuna tsikar jikina na mik'ewa breast DINA sai motsi sukeyi gashin jikina sai yamm yakemun nisha ta dafani "my dear
lafiyarki kuwa nutsuwata na tataro na rumgumeta "wlh lfy kawai dan na tashi daga baccine sakinta nayi na sabko na shiga bathroom nan najima ina ina cikin shauki Sardauna kawai nake gani daket na tataro jarumta nayi wanka nafito daure da towel "my dear bak
ida jiki gaki figigiya dake masha Allah sai diri mai kyau da hips ga uwa uba boobs wlh kiraki na burgeni murmushi nasaki na shirya agagauce cikin Riga da siket yan kanti pink colour sumun mugun kyau cif na daure gashina da ribbon na fesa turare"wow my dear
yaufa kin fito balarabiyarki sak wlh kinzama kamar baby "tashi muje parlo yunwa nakeji tun safe da my heart ya kawomun tea fah nasha mik'ewa tayi suka fito sai hirasu suke wasa da dariya ghaisha ce da khalisat a parlo sai nawwara jikinta akwance zee ta z
auna ta rumgumota"ummina imiss u dariya ghaisha tayi "me too momy atashi aci abunci Nisha gwara da kikazo kika tasota ai mik'ewa tayi taja Nisha suka nufi kan dining,
Ban garan Aunty amarya ko bayan sun dawo zamanta tayi tace bazata komaba sai dare Asi
ya tamata sallama ta tafi itako tanan sai bayan sallah isha tayi shirin tafiya uwarta ta kara jadada mata yada zata kula da sharunda da malam ya fada mata, zaune suke aparlo zee da Nisha da khalisat sai
hira shirme zee take musu hafeeza sai dariya take mus
u yada nisha ta biye mata Mahabeer ne ya shigo da sallama zee ta Mike ta tarosa harda riko hannusa "my heart wlh nayi missing d'inka "my zeena nima nayi missing d'inki sosai da fatan kina lfy? " lfy lau zama sukayi nisha ta gaishesa da su hafeeza ya amsa f
uskarsa asake "Ya Mahabeer bari kaga pic d'in da mukayi nisha bani wayata idanu ta zaro"au kina nufin baki dauko ba wlh tana part d'in Daddah harata nayi na Mike "Ya mahabeer tsaya na amso da gudu ghaisha ce ta fito ta zauna mahabeer ya koma kusanta ya zau
na yanama zee magana ta tsaya amma ta fice da guda"Allah my heart sai na amso akofar parlo tajita tayi karo da mutum male male ta fada saman faffadan kirjinshi wani irin mugun shock ne ya debesu atare zuciyoyunsu suka buga atare da sauri tana k'ok'arin jan
yewa shima yana k'o'karin janyeta kansa ya kauda ya tureta ta fadi k'asa ya shige parlo mik'ewa nayi raina ab'ace amma sanin bamu harakar juna yasa nayi hakuri dan shma da dane sai ya mareni ya shigar dani jikinsa na shaki kamshinsa haka na nufi hanyar gid
an Daddah kamshinsa ya dagamun hankali jina akirjinsa yasa tsikar jikina mik'ewa ga kasala amma Dole na basar ina shiga na dauko wayar na dawo part d'inmu kusan mahabeer na zauna shiko yana jikinta ghaisha sai kansa take shafawa tamkar wani dan jariri yamu
n mugun kyau Ya Mahabeer nashiga nunawa pic d'inmu ina dariya ta karfin hali asace nake kallonsa ko kallon inda nake bayayi haka yasa nima na daina masa kallon sata na shiga sha'anina khalisat kuwa ta zuba masa idanu tamkar zata cinyesa sab'anin nisha da
Allah ya samata mugun tsoron Sardauna sam bata iya zama inda yake yanzuma jitake ta takura su Daddy suka shigo da sallama shida Aunty amarya zee baby ta dago tana dariya "Oyoyo Daddy ai tanakai kallonta ga Aunty amarya ta Mike zumbur jikinta na karkarwa id
anunta suka rikide sukayi jajur da gudu tayi kan Aunty Amarya "Wallahi baki isa ki shigo mana da wannan masifar ba Aunty Amarya tanajin haka tayi kofa da gudu jikinta na r
awa zee beby kafin ta cinma Aunty Amarya ta fara ganin duhu luuu tayi zata fadi kafin
ta isa gunsu Mahabeer da gudu yayi kanta itako Aunty Amarya tuni tana kofa tana zaro idanu duk abinda ake Sardauna ko kansa bai dagoba ko ghaisha da tace ya dagata kansa ya dauke saman cinyarta ya Mike ya ficiwarsa daga parlon Mahabeer ya tarota jikinsa t
a zube tana buge buge "wlh sai nayi maganinta muguwa ghaisha ta karaso gunsu tana mata Addu'a kamar yada Mahabeer yake mata Daddy ya iso"Wai me ke faruwane da momy Mahabeer yace Daddy Aunty Amarya ce............
✍
🏻
💃🏻
Yar ilu ce
🌹
*
💖💖
👩
🏻
🦱
ZEE BABY
👩🏻
🦱
💖💖
*
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN DA BOOK WAJE*
*
👉🏻
22*
...."naga tana nunawa wai karta shigo sunkuyowa Daddy yayi yana mata Addu'a "Mahabeer inaga kamar Aljanunta fah basason Mariya ne bakinta ya fara fitar da kumfa a
binda ya tsorota Nisha ta fado kanta tana kuka gaisha ta janyeta hafeeza ma kuka takeyi Daddy ya buga musu tsawa" Mahabeer ko muje asibitine?? "Daddy ba ciwon hospital bane Addu'ar sukaci GABA da mata cikin ikon Allah tayi wata irin atishawa mai firgitarw
a da ihu mai uban karfi saida khalisat da hafeeza suka gudu amma nisha na gunta tana hawaye tana tofa mata Addu'a Mahabeer yasa nisha ta kawo ruwa ya karanta suratul yasin ya tofa aruwan ya dura mata da karfi tasha ya shafa mata ajiki ta kuma atishawa da h
amma tai lamo jikin Mahabeer sai bacci Daddy yace"Alhmdllh tayi bacci kai momy Allah ya rabaki da Aljanun nan sun dameki Mahabeer kaita ka kwantar da ita mik'ewa yai ya dauketa ya nufi bedroom d'insu yaje ya kwantar da ita ya lulubeta ya fito ghaisha hard
a kwalla tausayi Mahabeer zama yai kusan ghaisha yayi tagumi kansa ta shafa "kayi hakuri ba komai bane zataji sauki tana tashi lfy zata tashi amma abun yabani mamaki irin wannan lamarin watarana sai sunga abinda bai musu bane ba suke haka Mahabeer yace" wl
h nima nayi mamaki Daddy yace babu abin mamaki sharrin jinnu yawane dashi "Khadija ina mariya wai? "naga fah ta nufi kofa da gudu inajin tsorata tayi kofar Daddy ya nufa abin dariya yabashi da taji tsoron zee yana fitowa ya ganta rab'e ya nufi gunta "haba
mariya saikace wata yarinya tsoron Aljannu kara matse Jakarta tayi ta tataro nutsuwarta dan kar yagano itace sila"Daddyn nanah wlh tsoron Aljannu nakeyi gashi aljannunta basu sona dariya yayi ya kamo hannuta "mujeto ga yarki can yar k'arama da ita ta tsaya
a parlo tana zaune gun ghaisha shiru tayi yana rike da hannuta har parlo ya saketa wuff ta shige d'aki ta boye maganin ta fito parlo
"Aunty ghaisha sannu da gida? " mariya kece da sannu ya mama da jikinta? " Alhmdllh tana gaisheku ya jikinta momy? "tay
i bacci" Allah bata lfy hira suka ci gaba dayi Daddy yace"khadija abamu abunci mana Dariya tayi ta Mike ta kalli mahabeer ta kamo hannusa"muje kaci abunci kayi hakuri zata tashi lfy mariya tashi muje kuci abunci khalisat kirawo Aisha da hafeeza maza kuci a
bunci mik'ewa tayi ta nufi bedroom suko suka nufi kan dining khalisat na shiga taga Nisha rumgume da zee gam idanunta arufe tace"hafeeza Nisha bacci takene?" idona biyu meye ai duk uwarkice taja mata tunda ita takebi hafeeza ta rufe mata baki"yi hakuri Nis
ha tashi muje kici abunci? " banaci na koshi mik'ewa tayi suka fito itako tana kwance rumgume da zee, Dr Sardauna yana fita ya shiga motarsa yabar gidan danma karsu nemesa ya dubata kai tsaye gidansu mashakurah ya tafi, yau har cikin ya shiga da motarsa
ya kirata ta fito suka shiga ya gaishe da iyayanta ta kaishi parlon baqi inda suke zama sai surutu take zuba masa kallonta yayi"wai meyene yanzu kika koyi rufe rufen jiki kina wani sunne kai sweet baby ko shirin amarcin ne? " kai my Dr wlh ba haka bane naf
iso karka sake ganin kome nawa sai na shiga gidanka baki ya tab'e daga baya Kenan ya fada cikin rainin hankali ya dan jima sosai sun dan tab'a hira ya Mike ta rakoshi harda shagwab'arta dariya ma ta bashi ya lallabata ya shiga mota yamata key direct gidans
u Ahmed ya nufa har parlon su umma ya shiga ya gaishesu tukun ya fito ya nufi bangaran Ahmed yaga arufe yayi mamaki dan umma tace yananan baki Sardauna ya ciza"shege munafuki ko ina ya tafi adaranan ya fada yana wucewa mota ya shige ya bata wuta ya nufi gi
da kida ya kunna ya kure sauti wakar ethiopia ce dan yana mugun son wakokinsu sigari ya kunna yana zugarta yana kada kansa
saida ya biya shopping mall yayi tsince tsince abubuwa ya kashe kudi ba kadanba kan kayan ciye ciye da turaruka masu uban tsada, yan
a zuwa gida part d'insu ya shige ya nufi bangaransa ya bude hadaddan d'akinsa sai uban kamshi ke tashi carpet malale ko ina ga manyan kujeru tamkar d'akin Amarya bed d'insa kadai abun kallone ledojin hannusa ya ajiye harda su ghaisha yama sayaya amma bashi
da niyar komawa part d'insu ayau yayi niya sai gobe kayan jikinsa ya cire ya daura towel ya nufi bathroom shower ya kunna yasakarwa kansa
ruwa yajima sosai kafin yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito dan bacci yakeji sosai yau ga gajiya jikinsa ya goge y
a murza maiyukansa masu kamshi da dadi yasaka jallabiya ya shimfida darduma ya tayar da sallah wayoyinsa har biyu sai ringing suke atare, raka'a hudu yayi ya dauki Alqura'ani ya fara karatu yajima sosai dan yafi awa guda yana karatu akinrasa yafi so goma
sujada yayi nanma yajima yana tasbihi ga ubangijinsa yana nema gafara Allah yana kara neman kusanci ga Allah subahanahu wata'alah yanama Annabinmu Muhammad s,w,a kirari Yajima sosai ya dago ya daga hannuwansa sama yashiga kwararo Addu'a ya shafa ya Mike ya
nufi gun wayarsa yana dubawa Wanda suka kirasa yaga bandar yamasa kira uku mashakurah kira hudu Daddy kira biyu Ahmed kira uku sai number da babu suna kansa ya dafe"oh sweet baby ko miyene kiranta yayi wayar akashe kin Kiran Ahmed yayi yana murmushi ya ki
ra bandar shima akashe wayar kiran Daddy yayi bugo daya ya daga"Faisal ina ka shiga bakaci komai ba"Daddy gidansu Ahmed naje da nazo bacci ya daukeni" to maza fito ko tea kasha ko coffee maza mu har mun kwanta dare yayi" to Daddy ganinan"yauwa Dr dariya Sa
rdauna yai ya kashe wayar ya nufo parlo Mahabeer na zaune da casbi ahannusa Dr ya kallesa "bro bakayi bacci ba har shabiyu? " wlh tunanin halin da zeena take ciki ya hanani bacci baki ya tab'e "ni na tafi cikin gida nasha coffee nazo na kwanta wlh bacci
nakeji mik'ewa Mahabeer yayi"muje naga ko ta tashi ko tea na hada mata baiwar Allah bataci komaiba Dr Sardauna baice komaiba suka fito can ko lokacin da Sardauna yakira Daddy d'akin Aunty Amarya yake tanajin yana maganar Sardauna yazo yaci wani abu kar ya
kwanta haka zuwat ta Mike ta saci kallon Daddy taga baya kallon gefenta cikin rawar jiki ta nufi idan ta boye maganin ta dauko ta shiga toilet ta ciro Wanda Sardauna zai tsallaka ta fice daga dakin direct dakin su khalisat ta nufa cikin sa'a taci Karo da k
halisat ta fito shan ruwa ta kirata suka lab'e ta sinto ledar ta maganin "amshi babu lokaci da safe namiki bayani kiyi maza kije kofar parlo ki Barbada maganin wannan Sardauna zai shigo yanzu kinga darene babu Wanda zai shigo yanzu ki badeshi baki daya "m
omy na menene?? " kece zaki San ko nameye nan gaba badai sonsa kikeba? " eh momy"to maza jeki ba lokaci ta fada tana komawa
bangaranta da gudu khalisat ta nufi kofar parlo cikin rawar jiki ta barbade kofar parlon zuciyarta fari tas tana murna kuma daid
ai lokacin tajiyo murya Sardauna na tafe yana waya da gudu ta nufi hanyar bedroom tana cikin farin ciki Karo sukayi da Nisha"ke lfy me ya fito dake kuma kike irin wannan dariyar yawa zarara batace komai ba ta rab'e ta shige ciki Nisha kuwa ta nufi kitchen
don hadama zee tea ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ko da khalisat ta shigo zee tana bathroom Dan haka ta haye bed ta shige cikin blanket hafeeza ma bacci takeyi Dr Sardauna ko suna fitowa suna dab da shiga bandar ya kira Sardauna ya daga rike hannu M
ahabeer yai "bro ka jirani mana murmushi yai ya jirasa suna ta hirasu da bandar Akan yana tafe insha Allah nan da kwana biyar mahabeer ganin
hirasu ba mai karewa baceba ya janyo hannu Sardauna "muje mana ciki wai kuyi wayar kiyawa Sardauna yai mahabeer ko
ya fizge hannusa"to Nima kabarni naje naga Rabin raina ya fada yana murmushi ya nufi parlon yana sanyo kafarsa kansa ya Sara gabansa ya fadi da Sauri ya furta" Auzubillahi minal shaidaninr Rajim bismillahir Rahamanir la'ilaha innah anta subahanaka inni kut
um minal zalumin ya fada yana shiga tsakiyar parlon kamar cira qaya yaji bayajin faduwar gaban sai kasala kadan kadan parlon shiru alamun kowa yayi bacci