Showing 9001 words to 12000 words out of 206525 words

Chapter 4 - ZEE BABY COMPLETE

Lading   

01 Sep 2026

30

lallabata ta danci ya bata magani tasha dan batada matsala da magani saboda

ta saba cin kwayoyi Allura ce ko zata mutu babu uban da ya isa ya mata ita tanasha ya rungumeta yana lallabata ba jimawa tayi bacci ajiyar zuciya ya sabke ya duko ya mata kiss saman goshinta ya kara shigar da ita jikinsa ya rufeta ruf, koda akazo rabon a

bunci bai amsaba dan shi bai fiye cin abunci ba idan yana tafiya kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanusa dan bacci yakeji bai jimaba ko baccin ya daukeshi jirginsu na sharara gudu cikin hazo

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Karfe takwas na safe jirginsu ya sabka E

gypt sabka da jirgiya yayine ya tashi Mahabeer da ya kananade zee suna shakar barci manne da junansu idanu ya bude cike da mamakin irin baccin da yayi tashinta yayi taki tashi dan sam bacci bai ishetaba bakinsa ya kai kunneta " my zee,na kitashi mun iso ca

iro juyan jirgi za'a mana zuwa Nigeria kinji my zeena? Shagwab'e masa tayi tanarke masa tana turo baki ashagwab'e tace" Ahukuhya? " na'am my zeena ya akayi" shiru tayi tana kallonsa murmushi yai mata " bacci ko kai ta daga masa, tana lumshe idanunta ganin

mutane sun fara fita ya mikar da ita Dole ta tsaya mikewa yayo ya ciro karamar akwatunsu ya gyara mata mayafin abayar ya kama hannuta suma suka sabko dogayan motocinan sai kwasar yan k'asa k'asa takeyi suka shiga aka kaisu inda zasu zauna kafin jirgin da

zashi Nigeria ya shirya suna zaune tana manne

Kusansa yayi ta lallabata taci wani Abu taki Dole ya hakura basu wani jimaba sosai ko awa daya basuba suka shiga jirgi yanzuma jirgin na shirin tashi yaga tanason yin amai rumgumota yayi yana bubbuga bayant

a ya shiga mata rada akunne" my zeena please karkiyi amai ki daure wlh damuwa nake shiga yanda yake matan cikin ikon Allah taji batajin aman ta dago kanta ta zuba masa shanyayun idanunta tana murmushi tana shafar fuskarsa haka suka kure junansu da ido har

jirgin ya nutsa sararin samaniya idanuta ta janye tana dariya ta dora kanta kafadarsa, ana raba abunci akazo kansu lemo kadai ya amsa adan cup yasha itako tace tea Mahabeer ya matsa ata amshi pizza ya bata abaki taci ta koshi ya bata magani saboda jikinta

akwai zafi ya kwantar da ita jikinsa ya rufeta da mayafi ba jimawa tayi bacci dan dama ita wuni baccine tunda bata na dare bare yanzu safiyace shima baccin ya daikeshi ya jingina bayansa da kujera

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

karfe shabiyu da rabi na r

ana jirginsu ya diro garin Kano Mahabeer idanusa biyu jirgi ya sabka ya tashi zee idanu ta bude " munzu gida fah yanzu sai Katsina murmushi tayi ta shafi fuskarsa mikar da ita yai dan

masu sabka har sun sabka yan Kano yan Abuja ne basu fitaba tashi yai ya

d'aura mata Niqab dinta ya kama hannuta dayan hannusa, rike da jaka itama tana rike da jaka saida zasu fito wata latijuwa takira Mahabeer dan ita Abuja zata ya dawo " d'ana gaskiya ka iya rikon mace rayuwar auranku ta burgeni kai da yar balarabiyarka gata

dai yarinya karama amma akwai nutsuwa Allah ya sabketa lafiya Allah ya karamuku dankon soyayya Allah yasa mutu ka raba kai da ita yaji dadin Addu'arta cikin farin cikin ya amsa yana godiya, suka sabko kallon gurin take ya burgeta sosai suna

Fitowa ta

cire niqab ta tatare abayar ta dauré Mahabeer ya fara mata fada ta rufe jikinta surata duk awaje kar wasu yan iska su kalle masa ita shagwabe masa tayi yayi hakuri zafi takeji yanda ta shagwabe yasa yaji tausayinta maybe ko zafin takeji amma ransa bayason

wani yaga kyawunta ya yaba ta lokacin su Daddy sun jima da isowa tarbarsu bayan sunje sun gama sa hannu anga posport dinsu sukaje gun kayansu Mahabeer ya jido ya zubaso cikin abun tura kayan bayan angama aunasu suka fito inda jama'arka ke tsayuwa domin ta

rbar baki Daddy ne ya fara hangosu ya kirasu Mahabeer yaga yan gidansu su shida ne sukazo sai Nawwara ita karamace Dr Sardauna na hango cikin wani danyan boyal baki mai masifar tsada da kyau ya manna bakin gilashi kan fuskarsa wlh fadin kyawun da Sardauna

ya zuba bata lokacine saide fuskarsa ba walwala harda mashakurah nagani taci uban kwalliya ta kece raini agaskiya tayi mutokar yin kyawu tana kusa da masoyinta sai wasu mace da namiji sukam ban sansuba sai ghiasha fuskarta dauke da farin ciki Mahabeer ya

nunawa zee baby yan gidansu idanun da zata dago idanusu ya sark'e da juna amma ita bata ganin kwayar idanusa saboda gilashi ranta amutikar bace amma zahiri wani makirin murmushi dauke kan fuskarta ta kauda kanta tace" Auzubillahi minal Shaidanir Rajim Mah

abeer ya kalleta yana nuna mata Daddy tana hangosa saboda ta sansa sosai ta pic ta yada Jakarta ta saki hannu Mahabeer ta ruga da gudu tana dariya shima dariya yakeyi Sardauna tsaki yaja ya kauda kansa aransa yace " Allah rabamu da jaraba gudu take amma ga

ni take kamar an kara mata nisan gurin dariya suke ta mata yada ta zage tana gudu ko ina na jikinta motsi yakeyi masha Allah sai kallonta jama'a suke dan zee ba kyau Bade da sura tana dabda isa gurin Daddy sai kawai ta yanke jiki ta fadi da gudu sukayo kan

ta Mahabeer ya kira sunanta da karfin gaske "Zainab.... arikice yayi kanta da gudu kafin yazo Daddy har ya dagota amma abin mamaki bata mutsi babu alamar rai jikinta Mahabeer ya karasu ya amsheta yana kirkiza agigice amma bata motsa hankalin Daddy yayi mut

ikar tashi ya kalli Sardauna da yakema mashakurah masifa akanme zata to indai tana tare dashi karta kuskura taje kwalla tausayin zee ta goge ta sada kanta kasa Daddy haushine ya cikashi yace "dan ubanka zo maza dauki yarinyar muje asibiti mafi kusa ka dub

amun lafiyarta idanu Dr Sardauna ya zaro bakinsa na rawa yace" Daddy ni kuma zan dauketa saboda Allah ga Wanda ya kawota nan Daddy bai sake maganaba yaje gun Mahabeer yace ya ajiye Zainab ya tashi baiyi musuba ya ajiyeta yace duk su tafi har mashakurah yac

e ta biyosu ya kalli Dr Sardauna yace" idan ka cika dan halak karka tabata kabarta ta mutum ka kaimun gawarta Katsina komin dare mu muntafi sai ka kawo mana gawarta yaja tawagarsa ghasha tazo ta dafa Sardauna cikin lallaba kome tacemasa oho kai ya kada yan

a kallon masoyiyarsa da aka hana tabishi saboda wannan banzar lips dinsa ya ciza da karfi yana kallonsu Mahabeer sai kukan zuci yakeyi kayansu yaje ya turo suka fice mashakurah harda kukanta an rabata da masoyinta bazata amotarsa ba sororo yayi yana gani

har suka fice ransa yayi mugun baci ya nufi gunta yana yamutsa fuska ya kalli hannuwansa yaja tsaki sunkuyowa yai ya yaja mata rigarta ya ciccibeta ransa amutikar bace

amma sai yaji sakwat kamar ya dauki yar karamar yarinya batada nauyi ko kadan miyau ya z

ubar ya kara hade face yayi waje da ita shikadai yasan yada yatsara cin uwarta da zai mata da zaran ta farfado....



🏻

‍♀Sai kunji next page insha Allah Wanda zamu shiga tarinhinsune kuma karashen Free Page ne Dan chakwayiyar da rikita rikitar gaba b

ata cikin Faree Page

*Karku manta kudin* *wannan book nera dari* *ukku ne kacal zakusha* *karatu maicike da* *abubuwa daban daban*

*na rayuwar duniya da wata irin rikitacciyar soyayya mai zafin gaske ga me bukata ya tuntubeni awannan number mu kashe

magana Yanda* *zaki sambadi karatunki* *akan dari ukku kacal*

🤸🏻

‍♀



👇🏻

*+22796515805*

Rahma ce ummu Fareesa

🤸🏻

‍♀

🤸🏻

‍♀

🤸🏻

‍♀

*

💖💖👩🏻



🦱

ZEE BABY

👩🏻



🦱

💖💖

* *HATSABIBIYA* *RAMLAT RETURN*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

__________

_________________________

*

🌈

KAINUWA WRITERS



🏼

ASSOCIATION*

🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________

*Story & Written*

*By*

*Real Ladingo

😉

*

*Bismillahir Rahamanir* *Rahim*

*idan kina bukatar book dinan Akan nera dari ukku yake ki tuntubeni saman number nen zamu kashe magana

😉

+22796515805*

*Free Page*

Page 5

*.....asalinsu* Alhaji Hasheem Almahadee magawata haifafan garin tahoua ne cikin Niger sun gaji sarauta GABA da baya mahaifinsa ne kan kujera mulki shidayane gun iyayansa rana tsaka aka riske gawar iyayansa lokacin yana kasar waje karatu labari na zuwar ma

sa, ya dawo gida domin ahalin yanzu shine Wanda zai hau kan mulki anshirya komai aka hada yan mata biyu rana daya aka aura masa, amma sai me ana gobe nadin sarauta aka nemesa sama da kasa aka rasa, Abu kamar wasa, saida aka shafe shekaru biyu babu labarin

Hasheem Almahadee Wanda suka kulla manakisar kuwa tuni sun hau kan sarautar suna zuba mulkinsu matan da aka aura mishi kuwa tuni an kashe auran shikuma baisan ya akayiba ya tsinci kansa a daura Nigeria yana yawo garari wani bawan Allah mai suna Alhaji Nuh

u haifafan katsina ne amma mahaifiyarsa ce ta daura shi ya temakesa yana ganinsa yasan aikin jifane cikin ikon Allah ya dawo haiyacinsa yasha mamaki da ya gansa a Nigeria Katsina Nuhu ya tambayesa ko shi na wani garine dan ya ganshi jajur ga kyau tamkar ba

larabe bai boye komaiba ya labarta masa koshi waye Dan kasar niger ne buzune na Tahoua yagaji sarauta gaba da baya saboda itane aka fito dashi an kashe masa iyaye amma yace baya shawar komawa gida indai akan sarauta aka fito dashi yawon duniya ya hakura za

i zauna ana Allah yasa haka yafi Alkhairi shikenan mafarin zaman sa tare suke hada hadar kasuwanci shida Nuhu tamkar uwa daya uba daya haka suke bayan shekaru kusan goma hasheem da nuhu sunyi aure sun zama wasu sunyi arziki shakaru na tafiya arzikinsu na b

unkasa kuma har lokacin bai taba jin son komawa gidaba hasheem yanada yara hudu Abdulmutallab sai mai binsa Hauwa'u sai Faisal sai Salmanu daga kansu haihuwa ta

Tsaya sun taso cikin gata da kulawa Hasheem da zainab sunba 'ya'yansu tarbiya sun sami karat

un boko da na Addina Allah ya kara bunkasa dukiyar Hasheem dan haka yace yaran sa kowa ya zabi kasar da yakeso ya tafi ya biyawa kowa yaje karatu lokacin Faisal yanada shekaru sha bakwai yace saudia nuhu ya tsaya masa kan komai saboda Hasheem yafi sonsa a

yaran Nuhu akwai yayarsa acan madina Faisal ya tafi yake karatunsa cikin kwanciyar hankali da nasarori gidansu na Katsina abin kallone dan babu abinda babu aciki Hasheem na kula da yaransa shida zainab Abdulmutallab ne ya matsa masa saida ya gayamusu garun

su ya nemi izininsa ya tafi Tahoua gun dangin mahaifinsa cikin ikon Allah yasami tarba maikyau amma banda mai martaba ana Allah ya hadasu da Khadija suka kulla soyayya kafin ya dawo yana dawowa magana tayi karfi Dole hasheem ya tafi shi da Nuhu aka sanya r

anar aure khadija yarinyace kyakyawa itama buzuwace GABA da baya farace tas kama Abdulmutallab sunyi aure cikin so da kaunar juna da mutum ta juna bayan bikinsu da shekara biyu ta haifi danta namiji yaci sunan Nuhu bayan shakaru hudu ta haifi Mahabeer shim

a sai bayan sharu hudun ta haifi mace mai sunan maijidda ko yayeta batayiba cikin ikon Allah tasake samun cikin ta haifo zankadeden danta namiji kyakyawa ajin karshe jajir dashi yaron

Akwai farin jini tamkar ba'a taba haihuwa ba shine yaci sunan Almah

adee wato Faisal tun yana karaminsa akwai son gaskia da son girma bayason raina ko kadan ga miskilanci da jiji da kai bai fiye fara'a ba idan ba yana tare da khadija ba wacce suke kira Ghaisha Kakansa hasheem ya saka masa Sardauna saboda yaron kana kallins

a kasan jinin sarautane ba karya sunan ya bishi tun yana karami yace karatun likita zaiyi ya temaki mutane to fah tun yana karami sukece masa Dr Sardauna kyawunsa ya fits daban agidan Dan sak kamar Hasheem ya fito yanada kanne hudu shima Najib ke

bimasa sa

i Zainab sai hafeeza da auta Nawwara bangaran Mariya Amarya da Abdulmutallab ya aura saida ta kwashe shekaru biyar ta haifi yarta daya nana khadija sunan uwar gidansa sai mareniyar yarta da tazo da ita Khalisat idan ka ganta bazaka taba cewa ba yar gidan b

ace babu banbanci yarinyace kyakyawa amma ba canba batada laifi dai farace saidai batada hayaniya shiru shiruce suna zaune lafiya bazaka taba cewa ghaisha da Mariya kishiyoyineba sai Hauwa kanwar Abdulmutallab tana aure itama cikin Katsina da yaranta hudu

sai salmanu shima yayi aure da yaransa biyu wannan zuri'ar Allah ya hada kansu suna kaunar junansu yaransu sun taso cikin hadinkai da kaunar junansu Faisal ne kawai da baya kasar rashin auransu ya damesu sunata Addu'ar Allah ya janyo hankalinsa gid

****

*****

Faisal bayan ya kwashe shekaru tawas saudia yana, karatu bai taba zauwaba gidaba kuma bashida kiyuwa duk da ana aiko masa, kudi daga gida hakan baisaba yazauna ranar da ba karatu fita ya keyi neman na kansa dan yanaso shekarun biyu da suka rage ya

koma kasarsa yabasu mamaki dan yanzu haka ya tara uban dukiya taban mamaki amma babu wanda ya sani ranar ya fito zai tafi daidai wani super market wani shahararan mai kudi sun fito da iyalinsa daga, siyaya zai shiga mota yada takarda ta fado aljihunsa da

sauri ya nufi wajan daide ya dauka motar ta tafi dan taxi ya gani ya shiga yace yabi waccen motar bayansu sukebi har kofar gidan ya biya dan taxi ya nufi gun mutumin amma har sun shige gida yayi sallama yajima kafin ya fito yake tambayarsa, lafiya ya bas

hi takardar da ya yada bai saniba ya amsa ya duba saida ya tsorata dan takardun kadarorinsane da ya mallakawa yarsa kwaya daya Raiyan godiya yayi ta masa ya jasa suka shiga ciki yayi masa alheri sosai amma yaki amsa yace yayine don Allah sosai tarbiyar Fai

sal ta burge Fahad Abbu Rahaman to daganane suka saba ya sama masa aiki a kamfaninsa kullum yana gidan kamar dan gida sai abunda Fahad Abu Rahaman bai saniba Raiyan tun ranar da taga Faisal ta mutu akan sonsa tun tana daurewa har ta baiyana masa kiyawa yay

i saboda tsoron balaraban saudia bayaba hausa dansa duk shima ba hausarba ne idan ma ba ance maba ba barabe baneba to bazaka ganeba saidai su suna banbance jansin su Abu kamar wasa Raiyan ta kwanta jinya ciwo hankalin iyayanta yayi kololuwar tashi har aman

jini takeyi likita yace sumata abunda takeso zuciyarta takai matakin karshe dab take da bugawa nanne suka tambayeta ta fadamusu damuwar sunyi rantsuwa da Allah zazu mata dan basu taba zaton harakar soyayya ce jin sun mata alkawali yasa, tace Faisal ne tak

eso ranar anyi tashin hankali sunce saidai ta mutu taya zazu aurar da ita da Wanda basusan asalinsa ba kuma ba hausarsu dayaba, da sukaga fadan bayayi suka dawo lallashi suna rokonta tace ta janyen tunda sun mata alkawali har kuka suka mata amma fur takiya

karshema da, numfashinta ya dauke saida, tayi sati bata farfadoba ganin zazu rasata yasa sukace sun yada ta zureshi saboda alkawali amma ba ruwansu da ita kuma yada yasasu bakin ciki taki musu biyayya itama sai ta zubar da hawaye haka akayi bikin Hasheem

da Abdulmutallab su ne sukazo akayi komai amma Faisal yace shi yananan bazai komaba saidai ya rika zuwa ziyara. bayan aurene Ashe mahaifin Raiyan kodiri dayawa aransa sosai Raiyan da Faisal soke zuba soyayya kamar ba gobe Ashe shima yana sonta ganin kamar

abin bazai yubane yasa da farko yace bayason ta bayan auransu da shekara biyu ya kammala karatunsa

cike da nasarori ya sami aiki a Jeddah Dole sukabar madina koda sukaje sallama gidansu Raiyan ba Wanda ya kulasu haka suka tarkata suka tafi lokacin tana

fama da laulayin ciki yana bata wuya saida ya warware sosai ta samu sauki, ranar haihuwa ta zagayo taci uwar azaba amma kasa haihuwa tayi da kanta sai tiyata akamata aka ciro yara ukku maza biyu mace daya kyawawa, masha Allah ranar Faisal ya nuna tsantsa

r farin cikinsa amma babu Wanda yazo daga gidansu Raiyan sai wata Faisal ya samo take kula dasu, ranar suna ya sakawa mazan Hassan da hussaini macan sunan mahaifiyarsa, Zainab ranar anyi bidira a Nigeria yan uwa sai jin dadi sukeyi suna jinjina al'amarin

Ashe rabone tunda Fahad yaji labarin Raiyan maza ta haifa yaji dadi sosai yasan yanzu zai cika burinsa haka akayi ta tafiya rayuwa na gudu yaransu sun girma sosai saide sunfi shagwaba zee baby yarinyar akwai fitina sosai ga mugunta har uwayan bata bariba g

ashi muguntar ta tafi karfi suma mazan imusu takeyi makaranta mai tsada ubansu ya sakasu ko acan bata barin yaran mutane har malaman sun dukanta to ranar basu ba koyarwa idanu take likewa ta koma gefe tana dariya ahaka saida aka canza masu maranta ukku dai

de lokacine Faisal karami yazo karatunsa na likitanci Wanda zai dauki tsawon shekaru biyar amma yana madina sai karshan wata yake zauwa jeddah

sam jinunsu bai hadu da zainab idan tayi ba daidai ba dukanta yake ba da wasaba kuma hakan yanawa iyayanta da

di dan duk rashin tsoronta to tsoronsa takeyi ba da wasaba dan babu irin azabar da baya mata yan uwanta har kuka sukeyi tasha masa kunama amma duk yaji zafi zai dake sai bayan ya gusa yaje yayiwa kansa Allura ta rufe masa idanu yafi akirga amma dan taurin

rai bai taba nunawa yaji zafin abun ba to wannan abubuwan yasa zee baby take tsananin tsoronsa tana tunanin to shi wani irin mutumne

dan taga yada mutane suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login