Showing 105001 words to 108000 words out of 206525 words
ya musu ya fice Dan yanaso ya biya gidan malam kabiru ya masa tambayoyi daket ghaisha ta shawo hankalin zee tayi shiru da kanta ta kaita har bedroom ta kwantar da ita ta zauna tana shafa mata kanta da maga
nganu masu dadi na lallashi har tayi bacci ta fito ummi ta Saki jikinta ganin sun nuna sun fita jin ciwon abinda mahbeer yama zee Daddy suna fita da direbansa gidan malam kabiru yaje yana kofar gida tare da Almajiransa ya fito
da sallama ya iso malam
kabiru ya tashi tsaye" Alhji yau kaine da kanka to bismillah ciki suka shiga bayan sun gaisha Daddy yace" dama malam akan yaro nane auran gida ne na hadashi da yar kanena to auran sama da wata guda bai taba kusantartaba babu wani Abu da yashiga tsakaninsu
na aurataiyya da ita kuma yakeson Kara aure nikuma nasaka ya saketa yanzu kuma dama akwai mugayan mafarkai da nakeyi akansu kullum ina Addu'ar Allah ya kade fitina tsakanin su to najiyane ya rikita ganin mahbeer cikin wani mugun yanayi Wanda hakan yana nuf
in tabbas mutikar suna tare mahbeer zai zama gawa to abin ya tsoratani tun asubah nayi sadaka ina Addu'ar Allah ya baiyana mun me hakan yake nufi to shine da sukazo da haka na raba auran shine nake so naji banyi kuskureba ko sab'ama Allah kuma" to Alhaji a
dukan halamu sun Nuna yaron bayason zama da ita tunda har yanason Kara aure inda rashin lfy yakeyi bazaiyi sha'awar Kara aureba amma duk dak da haka da sai kumasa uzuri kuji dalilinsa nayin haka amma. kuma hakan babu laifi tunda shine baya son zama da ita
za'a iya rabaso domun anshiga hakkin yarinyar Dan idan tanada karfin sha'awa zata iya bin maza awaje kaga anyi barna tabbas mafarkinki akwai wani Al'amari Wanda Allah kadaine yasansa shine yayi sanadiyar mutuwar auran nasu shi babu Rabon zaisha walaha ko k
uma ma yabar duniyar baki dayanta Dan haka, ni yanzu bazance kunyi laifiba Dan kun raba auran wannan shine daide kowa sai ya auri abokin rabonsa ajiyar zuciya Daddy ya sabke" nagode malam zan iya aura mata daya daga cikin yan uwansa" zaka iya tunda babu ab
inda ya shiga tsakaninsu amma saide kanesa bazata auri sama dashiba da sun kwanta aure to fa hakan bazai yuba mutikar yana duniya Allah ya haramta hakan amma tunda basu kwanta aureba zaka aura masa saide ni anawa ganin kabarta ta kawo miji da kanta saboda
gudun komawa yar gidan jiya" tabbas hakane to nagode insha Allah baza a tisaba Allah yabata miji nagari" amin shiko yaron kirawosa zan masa yan tambayoyi Daddy bai musaba ya kira number mahbeer bugo daya ya daga dady yaba malam ya masa tambayoyi bai boye
masaba irin yada yake tsintar kansa da yada yakeji game da khalisat bayan sun gama wayarne malam yace"to kaga irinta ko wlh dinka asirine ke dawainiya dashi amma babu komai nace yazo zuwa yamma zan masa rubutu na kwana uku insha Allah sai na karya ko menen
e ajikinsa idan yaso sai kubasa matarsa Dan yace yana Sonta ajiyar zuciya Daddy ya sabke" to nagode, zan tafi gun aiki kudi ya ajiyewa malam ya tashi suka fito kabiru sai godiya yakeyi Daddy ya shiga mota suka tafi dama yasan zaa rina yarinyar tayi halin m
ugun halin uwarta,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sardauna tunda ya fita bai dawoba ko gidansu yau baijeba aiki ya rikeshi marasa lfy gareshi sosai kwananan hospital d'insa aciki take abun babu sauki sai agun Allah misalin karfe shida ya fito daga Office dinsa ya rufe
waya manne kunnesa, takunsa yake cikin isa da takama da kuzari ya fito ahabar hospital yaci Karo da Ahmed da bandar"OK Nura zamuyi magana wasu yarane zan gani yanzu kitt ya tsinke kiran yana murmushi Ahmed ya kai masa dukan wasa "kai suwaye yaran? kallon
Tara saura kwata yamusu" suwa ko idan ba kuba waima daga ina kuke? Bandar yace" daga gun aiki jiya da yau bamu haduba shine muka biyo mu gaisa murmushi yayi" to ai kasan baza a hada mai mata da gwarayeba idanu suka zaro gira ya daga musu"yes. yara ko karya
nayi kartin banza kuna yawo kuna cinye diyan mutane agari taya zakuyi aure kaiko meye yake kaika gidanmu kwana biyu Ahmed ne yayi kan? Sardauna da. gudu Sardauna ya nufi motarsa yana dariya Ruma da idanu ta bishi tana lasar baki cike da mamaki dama doctor
yana dariya yana zuwa ya bude motarsa ya shige yamata key ya janye glass din motar ya leko" wlh Ahmed tausayinka nakeji Dan karna jinyataka karfi yau nakeji bye ya masa gwalo ya nufi get da idanu suka bishi har aka bude masa get ya fice aguje bandar yace"
sai mutafi wlh Faisal tunda yasan dadin abun ya zama Mara's kunya dariya Ahmed yayi kowa ya shiga motarsa suka fice Ruma tace" wlh Dr Sardauna sai na lashi zumarka inason garjejen kato irinka naji yana sukuwa kaina zakayi dadi da fawa ta fada tana shigewa
ciki
Sardauna tunda ya fito ya dauki hanyar Barhim estate yake sharara gudu sosai sai gashi kofar get din gidansa honr yayi aka bude masa get ya shige Nisha tana zaune a tamkamemen parlonsu ta nuts a cikin kujera lemon tsamine ahannunta tana tsotsa ta
yi wanka taci kwaliya Riga da siket na material blue color yamata kyau knocking kofar parlo akayi ta Mike ta nufi kofar ta murza key ta bude Sardauna na tsaye murmushi ta sakar masa
gira ya daga mata ta matsa ya shigo ta rufe k'ugunta ya riko" my sweet
heart sannu da zuwa sunsunata ya fara yana yamutsata rumgumeshi tayi tana sabke ajiya zuciya sweetheart sakinta yayi yana murmushi "matsoraciya ni babu abinda zan miki dariya tayi ta kama hannusa suka nufi gun kujeru lemun tsamin ya amshe ya jata suka zaun
a" Neesher ya gida ina kaza ko kincinye? rau rau tayi da idanu" my Dr wlh yanzuma inaso nacinye soyayun kuma kiwuya nakeji na soya wata ta fada tana Dora kanta kirjinsa kanta ya shafa ya kamo tafin hannuta yana murzawa ya dago kanta idanunta ya bude ya Sak
i murmushi ya rumgumeta gam ya tura hannusa cikin rigarta yana murza kirjinta da ya ciko ba laifi dadin murzar takeji ta lafe jikinsa sosai ta Kara rumgumeshi tana nishi hannusa ya tura ya shafo marata ya danna da karfi tasaki ihu" wayyo sweetheart murmush
i yayi ya ciro hannusa ya kamo fuskarta ya sumbaceta" my Neesher wlh kin gamamun komai aduniya tunda kika amshi ajiyata kika riki gam ya fada yana hada bakinsu ya shiga sumbatarta wani irin kissing yake mata mai tsayawa azuciya kiran sallah ne ya dakatar d
ashi ya zare bakinsa anata yana dariya cak ya dauketa ya Goya yana juyi da ita tsakiyar parlo yana ihu" my Neesher nazama Dady Sardauna zai haihu zanyi baby wlh inason yara Allah yasa ki haifomun uku gaskiya my Neesher kinyi sosai irin wannan saurin cafkew
a haka sannu Nisha abun ya girmame mata kwanciyarta tayi agadon bayansa ta numshe idanunta tana dariya"my Dr ka ajiyeni muje kayi alwalla ni wlh duk ban gane inda kadosaba menene na cafke bedroom d'insa ya nufa da ita ya zaunar da ita saman gado ya shiga b
athroom agurguje yayi wanka ya dauro alwalla,
ya fito daure da towel ya goge jikinsa ya saka jallabiya ruwan toka mai shegen kyau ya kama hannu Nisha ta sabko" Oya shiga kiyi alwalla kiyi sallah da nadawo zamu leka gida sai kiciyo kazarki acan cikin m
urna ta rumgumeshi tana dariya murmushi ya sakar mata ya janyeta "bye mamar baby sai na dawo ya fice Nisha ta shiga bathroom dinsa ta dauro alwalla ta fito ta janyo masa kofar ta nufi dakinta, bangaran mahbeer yau yashiga tashin hankali rabasa da zee baby
amma bayan yaje gidan malam kabiru ya kwantar masa da hankali ya bashi rubutu da magugun yace bakin kwana ukune insha Allah zai warke kuma ya fadawa dadynsa zai maida, musu auransu ya shiga farin ciki matuka ya dawo gidansu ya tisa ghaisha gaba harda kuka
ta roki dady su yafe masa ba laifinsa bane tsakanin d'a da mahaifi sai Allah tunda Dady yacemata asirine khalisat ta masa takejin tausayin d'anta tace ta yafe masa amma bashi ba khalisat har abada da to ya amsa amma yana fita gidansu khalisat ya nufa suka
sha hirasu, ta soyayya yana Kara jadada mata zai aureta
***
zaune suke aparlo ghaisha da ummi Raiyan zee baby na jikin ghaisha akwance daga ita sai skert baki iya gwiwa da Riga mai Dan kauri pink colour tanada dogon hannu amma ta kamata kirjinta ya cik
a rigar dam kam zai fasa rigar ta Saki gashin kanta ya rufe mata fuska hafeeza tace"sister wai mekike jirane da baki tafi gidanki ba Najib dake yake latsa waya yace" ganemun hanya tashi masa ki tafiyarki d'ago kanta tayi ta kalli ghaisha ashagwab'e tace" u
mmina kina jinsu fa ki musu magana murmushi ghaisha tayi" kai bata zuwa ina ruwanku da ita kunjini da yara ummi Raiyan dariya ta musu tana girgiza kai Daddy ne ya shigo da sallama suka amsa nawwara da nanah suka taresa ya kamo hannusu suka zauna zeey baby
ta tashi zaune "Daddy kagani su hafeeza da Najib suna... bata idasaba su Sardauna suka shigo da sallama shida Nisha yana rike da hannuta da sauri zee baby ta dago da kanta ta kallesu karaf idanunsu ya sark'e da juna ita da Sardauna gabansu na wani irin bug
o da sauri ya dauke kansa yana istigifari hafeeza ta Mike ta taro Nisha Sardauna gun daddy ya nufa yana murmushi"my Daddyna albishirinku wlh bazan boye farin cikina ba tsaye dadyn ya Mike ya ware masa hannayensa "welcome my son jikinsa ya fada ya rumgumesh
i ya masa rada akunne idanu daddy ya zaro yana murmushi "wai da gaske my boy "wlh my daddy ghaisha tace"Autana zo mana dariya yai ya nufi gunta zee baby wani irin bakin ciki ne ya tokare mata zuciya taan binsu da mugun kallo jitake kamar ta kashesu Nisha t
a saki hannu hafeeza ta nufi gun zeey baby da gudu tana dariya "
my dear nayi missing d'inki wani mugun kallo zeey ta watsama Neesha......................
✍
🏻
*
💖💖👩🏻
🦱
ZEE BABY
👩🏻
🦱
💖💖
*
MALLAKAR UMMU FAREESA NE
*DAN ALLAH KARKU FITARMUN
DA BOOK WAJE*
*
👉🏻
39*
....Nisha itakam batasan ma zee nayi ba jikinta ta fada tana dariya ta rumgumeta nutsuwata na tatataro na kakalo murmushi dan wani mugun haushi Nisha nakeji da na Sardauna na rasa dalili Dole na rumgumeta tunda banida hu
jja" my dear ya gida nima nayi missing d'inki ummi tace" Aisha Baby kadai kika gani ko? kunya ta kama Nisha tasaki zee ta miki taje ta rumgume ummi Raiyan" ummi ina yini kanta ta shafa"lfy ya gida da fatan kina lfy? " Alhmdllh Sardauna gun ghaisha ya ISO
ya zauna yana murmushi ya dora kansa kafadarta "momyna kinsan me? " ah ah sai kafada daddy yayi dariya" wlh Faisal anyi marar kunya ai sai ka fada mata zee ko jin zazakar muryar Sardauna mai fitar da amon dadi kusa da ita da dadadan kamshinsa gaba ki daya
ta rasa nutsuwarta wani irin shaukine ya kamata gashin jikinta sai mik'ewa yake tanajin wani iri jikin ghaisha ta koma ta rumgumeta tana sabke ajiyar zuciya ta kalli Sardauna saboda sunyi kusanci dayawa amma koda wasa bai kalleta ba idanunta ta lumshe ta
boye kanta jikin ghaisha Sardauna yace" momyna wlh kin kusa yin jiki fah dukansa
ghaisha tayi tana dariya Daddy yace" kya dara wlh nima haka yacemin za ta kara dukansa ya Mike dan dama kusancinsa da zee yayi yawa so yake yabar gurin mik'ewa yayi ya nuf
i gun ummi Raiyan ya zauna yana gaisheta ya bata labari Nisha nada ciki kunya tasa Nisha mik'ewa tazo ta gaishe da Daddy ta zauna kusan ghaisha ta gaisheta rumgumota ghaisha tayi" masha Allah Aisha Allah ya inganta kanta ta sada zee baby ta rasa abinda yak
e mata dadi Dole ta zauna ta saki ranta ta rumgumo Nisha" my dear kice zamu bararaje zanyi d'a ko diya Nisha shiru sai lokacin Sardauna ya kalli zee yada take cikin farin ciki yaga tayi masa mugun kyau da sauri ya kauda kansa dan Allah kade yasan me yakeji
Nisha tama zee rada" my dear please akwai soyeyar kaza? dariya zee tayi "babu amma gidan Daddah nagani dazu da yamma muje kici ta mike ta kama hannu Nisha ghaisha tace ina zaku? " ummi nama zataci soyaye nagani gidan Daddah tajata suka fice ghaisha nakira
n zee tazo ta yafa gyale itada Takeda ciyayi akai tana fita haka kin zowa tayi tana dariya suka fice
ummi murmushi tayi dan ba karamun dadi takeji ba idan taga ana kaunar zee ghaisha tace Sardauna kaci wani Abu kuwa? murmushi yai" ghaisha banajin cin ko
mai coffee kawai zansha idan nakoma gida" OK zuwa gobe zansa nanuwa mai aiki ta samo ma Aisha yar aiki insha Allah" yauwa momyna godiya Muke" kici gidanku mahabeer ne ya shigo da sallama adakile Daddy ya amsa Sardauna ya Mike ya taresa yana murmushi ya rum
gumesa" bro Albishirinka cikin sanyin jiki yace" goro rada yama mahbeer Daddy ya tab'e baki "Faisal Allah yama albarka ina alfahari dakai ako ina murmushi mahbeer yayi ya kamo hannu Sardauna suka zauna mahabeer ya kalli Sardauna ya rike hannusa" Dr namu da
n Allah kasa baki su Daddy su yafemun subani matata wlh ina sonta sun rabamu sunsa namata saki daya idanu Sardauna ya zaro ya kalli Daddy" haba my daddy dan Allah ya kukayi haka suna son junansu ku rabasu ghaisha tace "dallah can rufemun baki kasan abunda
yayi ne ya fada maka wlh babu kai babu ita sakin mahabeer Sardauna yayi ya Mike yaje gun Daddy ya rumgumeshi "Daddy kuyi hakuri ku yafe masa dan Allah abi komai asannu ku maida musu auransu ajiyar zuciya ya sabke" naji jeka mayi tunani amma idan kun hadu y
a fada maka laifinsa kallon mahbeer Sardauna yayi yanaso yaji Karin bayani mahbeer yame nuni sayi magana gobe kafada ya daga Alamar Allah kaimu
Mahbeer gun ummi Raiyan ya nufa ya zauna" ummina dan Allah kiyi hakuri wlh ina son matata ba laifina bane mu
rmushi tayi"haba mahbeer wlh karka damu baby kanwarka ce kainefa kaje kakawo abunka kayi hakuri Daddy da ya huce za'a maida muku auranku godiya yayi mata sosai Najib da hafeeza tun dazu basu gano bakin sai yanzu suka gane inda zancan ya dosa ya kalli hafee
za suna danne dariyarsu amma saida ta fito nawwara tace" kai kai kai da yaya mahbeer kuke ko? Najib yace"Daddy tunda yaya bayaso ni abani mana wani mugun kallo Sardauna ya watsama Najib Wanda yasa hafeeza takusa sakin fitsari aguje tayi hanyar bedroom yace
"wallahi zakuci ubanku waye kukewa dariya ai tuni ta banko kofar cikin wani taku ya nufi Najib "dan ubanka matar yayan nakace kake cewa abaka auranta ya fada idanunsa sun kade sunyi Ja Najib ganin idan fa Sardauna ya damkesa ilatashi zaiyi yasa ya Mike da
Sauri yayi gun ghaisha tsawa ta daka masa" Dan gidanku karkazo mun nan Mara's kunya Daddy ne ya katse Sardauna "Faisal zo nan yi hakuri ai gaskiya ya fada wlh sai na aurawa Najib ita yo meye aciki mik'ewa mahbeer yayi ransa amugun b'ace yabar gidan Sardaun
a wani irin duhu yake gani ransa ya baci sosai da furucin Daddy duk da yasan ya haramta zee har abadan bazai ta son matar yayansa ba bayan hakama sauran wani Dan kar gano irin Bacin ran da yake ciki ya nufi kicin ya hado coffee yanajin tsanar zee da mahbee
r na mamaye zuciyarsa idan ya tuna sun malaki juna parlon ya dawo ya
zauna yasha coffee d'insa kusa da ghaisha tana shafa kansa" auta meye kuma naga duk ka canza shagwabe mata yayi"ni babu komai fah momy murmushi ta Saki tana shafa kansa Daddy yace" ku
jini da yaro wai shinan fushine yayi ya tafi ghaisha da Daddy suke hirasu banza Sardauna yayi dasu kiss yama ghaisha ya Mike ya nufi daddy yamasa kiss" my daddy good night zamu tafi gida ummi good night dariya tayi" night Dr Daddy yace" Dr anzama dady ko s
hiru yayi yana Sosa kai ya fice ya nufi part d'in Daddah, bangaran zee baby da Nisha kuwa suna rike da hannu junansu har part d'in Daddah suka iskota da mairan karfe suna hira zee ta fada jikin Daddah tana dariya" tsohuwa munzo cin kaza Nisha kusan tsoho
ta zauna tana tsokanarsa"ke Aisha ja'ira amarya ko Dan kwanon tuwa baki kawomun ba ko? dariya tayi zee ta taso" baxata kawoba nakama zamuci ta fada tana shiga kitchen ta daukowa Nisha cinyar kaza guda biyu asoye jajur ta zuba a plate ta kawo mata daddah t
abi zee da kallo" iye sannu zainaba masu kwadai anyaku Aisha bakiyi cikiba zee tasa dariya"wallahi daddata shine ma? tsoho yace" oh zamani Nisha taja hannu zee suka koma gefe can nesa da su daddah suka zauna Nisha tace" nagode my dear wlh yawuna har tsinke
wa yakeyi sweetheart har ya dasamun suna mai kaza ta fada tanacin naman zee namata dariya Nisha tace" my dear wlh My Dr ya iya soyayya yana kasheni da salonsa nagama haukacewa Akan sa ina mugu mugun sonsa ina ji dashi shidin jarumine wlh dazu bakika kaunar
da yanuna munba nida babynsa wlh Yaya Faisal yayi arayuwa zee baby yawun bakintane ya k'ame baki daya hankalinta yayi mugun tashi gudun karta ganota ta Mike tana murmushi "my dear bari na dauko wayata nima na nuna miki pic dinmu da yaya mahbeer dariya Nis
ha tayi" aikuwa yi Sauri kuma ai iyayan soyayya ne kilama kema
kinyi cikin tun kafinma nayi ficewa zee tayi tana murmushi ta nufi kofar fita